Littafi
Littafi
HANYOYI MASU AMFANI DON SAMUN RAYUWA MAI DAƊI
Littafin Hanyoyi masu amfani don samun rayuwa mai daɗi na Shaikh Abdurrahman bn Nasir al-Sa’di - Allah Ya yi masa rahama - yana magance sabubban tabbataccen jin daɗi na haƙiƙa daga mahangar imani mai zurfi, yana shiryar da mai karatu zuwa nutsuwar zuciya ta hanyar imani da aiki na gari, da zikirin Allah, da gamsuwa da abin da Allah Ya bayar, da tafakkuri a kan ni’imomi, da kyautatawa, da dogaro ga Allah, da haƙuri, da kyakkyawan ƙimanta al’amura, da salo mai kyau. Yana sanya taswira ga rayuwa mai natsuwa a gabanka, madaidaiciya, kuma mai daɗi duk da juyin-juya-halin rayuwa.
TUSHE GUDA UKU DA DALILANSU
Littafin yana tattauna muhimman ƙa’idojin da ya wajaba ga musulmi ya koya: Sanin Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da sanin Addinin Musulunci, da kuma sanin Annabi Muhammadu - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; kuma yana jaddada muhimmancin waɗannan ƙa’idoji wajen gina imani da aikata nagartattun ayyuka, dan dogara ga hujjoji na Al‑Kur’ani mai girma da Sunnar Annabi.
MUHIMMAN DARUSA GA ƊAUKACIN AL'UMMA
Littafin Muhimman darussa ga ɗaukacin al'umma na Sheikh Abdul’Aziz Ibnu Bāz - Allah Ya yi masa rahama - taƙaitaccen saƙo ne mai girman fa’ida, wanda babban malamin ya tsara domin ya zamo tushen ilimi ga daukacinmusulmai; ya tattauna tushen Addini a cikinsa da ginshiƙansa: Na abinda ya shafi Tauhidi da Imani da Musulunci, zuwa hukuncin tsarki (ɗahāra) da Sallah, da Ladubban Musulunci, da bayani kan abubuwan gargaɗi na shirka da saɓo, a kan salo mai sauƙi kuma mabayyani, yana dogara a kan ingantattun nassoshi daga Alƙur’ani da Sunnah, domin kusantar da aƙida da ibada ingantattu ga kowane…
TAƘAITACCEN BAYANI A KAN AƘIDAR MUSULUNCI
Littafin yana bayyana tushen imani waɗanda suka haɗa da imani da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da ManzanninSa, da ranar lahira, da ƙaddara; kuma yana gabatar da ƙa'idojin asali waɗanda wajibi ne a kan musulmi ya yi imani da su kuma ya yi aiki da abin da suka wajabta, yana mai ƙarfafa muhimmancin dangantaka da Allah ta hanyar zurfafa fahimtar aƙidar Musulunci.
TSARI GA WANDA YAKE SON YIN UMARAH DA HAJJI
Littafin "Tsari ga wanda yake son yin Umarah da Hajji" na Sheikh Muhammad bn Saleh al-Uthaimeen, shi jagora ne da ya tartar kuma karbabbe ne ga dukkanin musulmin da yake tsinkaye don yin ayyukan Hajji da Umarah. Littafin yana gabatar da wani sharhi cikakke ne don ladubban tafiya, da hukunce-hukuncen harama, da abubuwan da suka wajaba ga mai yin Hajji da Umarah, yana mai dogara ga Alƙur'ani mai girma da Sunnar Annabi, kamar yadda littafin yake bayanin miƙatan Hajji a rarrabe, da Nau’ukan ibadu, da hukunce-hukuncen sallar matafiyi, yana mai bayyana yadda ake yin kowane rukuni daga cikin rukunan…
SAƘO A KAN JINANEN ƊABI'A GA MATA
Littafin SAƘO A KAN JINANEN ƊABI'A GA MATA na Sheikh al-Allamah Muhammad bin Salih al-Uthaymeen, Allah Ya yi masa rahama -, wani saƙo ne na ilimi ingantacce wanda ya yi nazari da bincike kan jinanen ɗabi'a na mata, waɗanda su ne haila da jinin cuta da jinin biƙi, yana mai dogaro da Alƙur'ani mai girma da Sunnah tsarkakakkiya, haɗe da tabbatacciyar fahimta ga zantukan malamai a kan waɗannan mas'aloli. An fayyace hukunce-hukuncen jinane a cikinsa, tare da bayyana banbance-banbance masu laushi a tsakanin halaye, da kuma gabatar da dalili na shari'a domin tabbatar da shiriya da natsuwa ga mace…
TAKAITACCEN BAYANI GAME DA MUSULUNCI KAMAR YADDA YA ZO A CIKIN AL-KR'ANI DA SUNNAR MANZON ALLAH
MUSULUNCI Littafi ne mai muhimmanci wanda ya ƙunshi taƙaitacen bayani game da musulunci da yake bayyana mafi muhimmancin tushensa da koyarwarsa da kyawawunsa wanda aka samo su daga tushe na asali shi ne al-Kur'ani mai girma da sunnar annabi, littafin abin fuskantarwa ne ga baki ɗayan baligai daga musulmai da waɗanda ba musulmai ba da yarukansu a kowane zamani da wuri duk da saɓanin yanayi da halaye. (Kwafi ne da yake ƙunshe da dalilai daga al-Kur'ani mai girma da sunnar Annabi) 1-Musulunci shi saƙon Allah ne zuwa ga mutane baki ɗayan su, shi ne saƙon Allah wanzajje cikamakin saƙonnin…
صفة الوضوء والصلاة (مرئي)
Yaya zan yi alwala? M Sauti 1 Sautin kiran Salla 2
الإسلام والإلحاد وجها لوجه
Gujewa daga Ilhadi (Musanta samuwar Allah) zuwa Musulunci Tambaya da amsa Da sunan Allah, godiya ta tabbata ga Allah, kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah, da Alayan sa da Sahabban sa da kuma waɗanda suka jiɓince shi؛ bayan haka: Wannan wani ɗan ƙaramin littafi ne: "Gujewa daga ilhadi (Musanta samuwar Allah) zuwa musulunci". Dan ƙaramin littafin zai gabatar da wani bayani ga "Dabi'ar ilhadi' da matsalolin sa, kuma yaya Ilhadi yake warwara idan ya haɗu da abubuwa bayyanannu na hankali da ɗabi'ar da aka halicci mutum da ita. Kuma ɗan littafin zai bujiro da sashin dalilain…
RANATA TA FARKO A MUSULUNCI
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. GABATARWA Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, wanda ya aiko Annabin Sa Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - rahama ga talikai, ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sa Allah, Shi kaɗai yake, ba Shi da abokin tarayya, Ubangijin jama'ar farko da na ƙarshe, kuma ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad bawan Sa ne, kuma Manzan Sa ne, cikamakin AnnabAwa da Manzanni - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - aminci mai yawa har zuwa ranar sakamako, bayan haka: Mutane gaba ɗaya suna bincike akan farin ciki mai bada nutsuwa, daga…
ABIN ZABOWA DAGA ABIN KASUWANCI MAI RIBA A CIKIN LADAN AIKI NA GARI
كتاب جامع لجملة من أحاديث النبي -صلى الله عليه وسلم- الصحيحية في ثواب الأعمال الصالحة كطلب العلم والطهارة والصلاة، وصلاة التطوع، والجمعة والجنائز، والصدقات والصوم والحج والجهاد، وقراءة القرآن، وذكر الرحمن وغيرها.
Imanin da Allah wanda Ya wajabta shi akan bayinSa daga abinda ya zo a cikin Alkur'ani mai girma da Sunnar Annabta.
Wata BAKANDAMIYA ce wadda ta tattaro dukkanin tushe da muhimman kudirce - kudircen (zuciya) da mas'alolinsa, tana keɓantuwa da ƙulla mas'aloli na Aƙidah da Littafi mai girma (Alƙur’ani) da kuma Sunnah mai tsarki, tare da kwaɗayi akan dasa Aƙida ta taƙaitacciyar hanya kuma gamammiya, daidai da ibarori masu sauki a tsakiyar bayani, da kuma bayyanawa ga mas'alolin kudircewa, tare da tsaftace Bakandamiyar daga bincike-bincike zance (ilmul kalam) da falsafa, kuma yana nufin gabatar da abubuwan kudircewa da usulubin da zai yi saukin fahimtarsa da gamewarsa ga dukkanin matakan ilimi.
Taƙaitaccen saƙo game da Musulunci kamar yadda yazo cikin Al-Kur'ani da Sunnanr Annabi
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin ƙai. MUSULUNCI (Kwafin da babu Nassoshi a cikin) [1] [1] Ana iya samun wani kwafin na wannan saƙon wanda yake haɗe da dalilai daga Al-Kur'ani da hadisan Annabi kan kowace Mas'ala a cikin sa, don karantawa jeka wannan shafin: https://islamhouse.com/ar/books/2830071. Saƙo ne mai muhimmanci wanda ya ƙunshi taƙaitaccen bayani game da Musulunci, yana bayyana mafi muhimmancin tushensa da koyarwarsa da kyawawunsa wanda aka samosu daga tushe na asali shine Al-Kur'ani Mai girma da Sunnar Annabi, kuma saƙon an fuskantar dashi ne zuwa baki ɗayan baligai na musulmai da…
TAƘAITACCEN BAYANI MAI AMFANI GA LADAN DA LIMAN DA MAI HUDUBA DA KUMA HUKUNCE HUKUNCEN MASALLACI
Littafin yana gabatar da cikakken bayani game da hukunce-hukuncen kiran sallah da ikama, da limancin sallah, da huɗubar Juma'a, da kuma ladubban masallaci; haka kuma yana tattauna ayyukan ladanai da limamai da masu huɗuba, yana kuma mai ƙarfafa muhimmancin koyon hukunce-hukuncen shari'a da suka shafi waɗannan ayyuka domin tabbatar da gudanar da su yadda ya kamata. Haka kuma ya ƙunshi nassoshin da aka ruwaito daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - tare da sharhinsu, don tabbatar da an yi aiki da su daidai.
WANENE YA HALICCE NI? KUMA SABODA ME?
Ko wanne abu yana nuni akan akwai mahalicci Wa ya halicci sammai da kasa da abinda ke tsakanin su na halittu masu girma wadanda ba’a iya gane yawansu? Wa ya kera wannan nagartaccan tsarin kayatacce a sama da kasa ? Wa ya halicci mutum ya kuma ba shi ji da gani da hankali? Ya sanya shi mai iko akan tsururutar ilimai da gane hakikanin abubuwa ? Yaya zaka fassara wannan kira gwananna dake na'urorin (gabban) jikinka da suke kuma a jukkunan kasantattu suna aiki? kuma wanene ya kage su? Ta yaya wannan kasantacce mai girma yake tsaruwa kuma yake tabbatuwa tare da ƙa’idojin sa, waɗanda suke kiyaye…
MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH
Musulunci shine miƙa wuya ga Allah Mahaliccin kasantacce kuma Mai jujjuya al'amiransa, da jawuwa gareShi dan so da kuma girmamawa, tushen Musulunci shine imani da Allah, kuma cewa Shine Mahalicci, dukkan wanda baShi ba abin halitta ne, kuma cewa Shi Shine wanda Ya can-canci bauta Shi kaɗai baShi da abokin tarayya, babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, yana da sunaye kyawawa, da siffofi maɗaukaka, cika tsantsa ta Sa ce, batare da tawaya ba, Bai haifaba kuma ba'a haifeShi ba, kuma baShi da wani kini ko tamka, baYa sauka baya jikintuwa a cikin wani abu daga halittarsa. Musulunci shine addinin…
Musulunci addinin Ubangijin talikai ne.
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin ƙai. Wanene Ubangijin ka? Wannan itace mafi girman tambaya a cikin samammu; kuma shine mafi muhimmancin tambayar da sanin amsarta yake wajaba akan mutum. Ubangijinmu Shi ne wanda ya halicci sammai da kasa, ya kuma saukar da ruwa daga sama, sai ya fitar daga wannan ruwan nau’ukan‘ya’yan itatuwa da bishiyoyi abin ci a garemu da dabbobin da muke ci. Shi ne wanda ya haliccemu ya kuma halicci iyayammu, ya halicci kowanne abu, shi ne wanda ya sanya dare da rana, shi kuma ya sanya dare lokacin bacci da hutu, yini kuma lokacin neman abin ci. Shi ne wanda ya sawwake…
الشهادتين
Idan kana son shiga Musulunci, to ya wajaba a kanka ka faɗi Kalmar Shahadar nan mai zuwa da sautin da za’a ji, ka fahimci ma'anarta kuma ka yi imani da ita: Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah (Wannan kalmar tana nufin cewa babu wani ɗaya da ya cancanci bauta sai Allah), kuma ina shaida cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, kuma cewa (Annabi) Isa ɗan Maryam shi bawan Allah ne kuma ManzonSa ne. Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaida cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne.
YADDA SALLAR ANNABI - TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA AGARE SHI - TAKE
Littafin Yadda siffar sallar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi take -, babban malami Sheikh Abdul’Aziz Ibnu Bāz - Allah Yayi masa rahama - ya dunƙule bayani ne akan siffar sallar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, akan wani tsari mai sauƙi, da kuma manhaja gogaggiya, ya dogara akan nassoshi ingantattu, domin ya zama mai shiryarwa ga Musulmi a sallarsa. Haƙiƙa a cikinsa ya bayyana rukunan sallah da sunnoninta da siffofinta tun daga alwala har zuwa sallama, ya tara dalilai da kuma bayanai, yana mai yin kira zuwa ga cikakken koyi da Annabi - tsira da…
TABBATACCAN BAYYANI A KAN YAWANCIN MAS'ALOLIN HAJJI DA UMRA DA KUMA ZIYARA A KAN DORON LITTAFI DA SUNNAH
Littafin yana yin sharhin hukunce-hukuncen Hajji da Umra da Ziyara akan doron Littafi da Sunnah, yana bayyana wajiban Hajji da Umra, da abubuwan da aka haramta a lokacin harama, da kuma ladubban ziyarar Masallacin Annabi, yana mai gargaɗi a kan bidi'o'i a cikin waɗannan ibadu.
LADUBBAN TAFIYA DA HUKUNCE-HUKUNCENTA
Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Annabimmu Muhammad da alayansa da sahabbansa baki ɗaya. Bayan haka: Wannan taƙaitaccan saƙo ne ne akan LADUBBAN TAFIYA DA HUKUNCE HUKUNCENTA, mun yi ƙoƙarin kawo bayanin mafi yawan abinda matafiyi yake da buƙata zuwa gareshi. Allah kaɗai nake roƙo da Ya sanya wannan aikin domin Shi ne kaɗai, kuma Ya anfani da al’ummar musulmi baki ɗaya. Na farko: Ladubban tafiya
TAƘAITACCEN BAYANI A KAN SIFFAR UMARAH DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCENTA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Annabimmu Muhammad, da alayensa da sahabbansa bakiɗaya. Bayan haka: Wannan taƙaitaccan bayani ne a kan siffar aikin Umarah da hukunce-hukuncenta da kuma ladubbanta, mun yi kwaɗayi a kawo bayanin galibin abinda mai yin Umarah yake da buƙatuwa zuwa gare shi. Allah muke roƙo Ya sanya shi tsarkakakke don zatinSa mai girma, kuma Ya amfanar da dukkanin musulmai da shi.
WASIYYATA
Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah, bayan haka: Ni (............................................................) Lambar katin ɗan ƙasata: Na yi wasiyya, ni ina cikin hayyacina abin lura a shari'a na cikakken hankalina da kuma kyakkyawan riskata, cewa ni ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai yake, ba Shi da abokin tarayya, kuma cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, kuma cewa (Annabi) Isa bawan Allah ne kuma ManzonSa ne kuma kalmarSa ce wacce Ya jefata zuwa ga Nana Maryam kuma rai ne daga gareShi, kuma cewa aljanna…
SIFFAR UMRAH
Taƙaitaccen littafin «Siffar Umarah» Na Shehin malami Abdul’Aziz bn Baz - Allah Ya yi masa rahama - yana bayanin ayyukan Umrah akan wani tsari (salo) fayyatacce, kuma mai sauƙi, domin ya zama jagora a aikace da zai taimakawa musulmi akan gudanar da ayyukan sa (na Umrah), cikin ƙanƙan da kai da kuma sauƙi, yana kuma tare da addu’o’i, da zikirai da a aka ruwaito a kowanne mataki.
TAƘAITACCEN BAYANIN SIFFAR AIKIN HAJJI
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Annabimmu Muhammad da alayensa da sahabbansa baki ɗaya. Bayan haka: Wannan taƙaitaccen saƙo ne a kan siffar Hajji, mun yi kwaɗayin kawo bayanin mafi yawancin abinda maniyyaci yake buƙatuwa zuwa gare shi. Allah muke roƙo Ya sanya shi tsarkakakke ne don zatinSa mai girma, kuma Ya amfanar da dukkanin musulmai da shi. Shimfiɗa
TAƘAITATTUN SAƘONNI BIYU A KAN ZAKKA DA AZUMI
Littafin yana tattauna farillan zakka da azumi, yana bayyana hukuncinsu da fa'idodinsu, tare da tunatarwa da haƙƙoƙin Allah a kan bayinSa. Ya ƙunshi bayanin hukuncin zakka da nau'o'in dukiyoyin zakka, da falalolin Ramadan da hukuncin azumi da ladubbansa, a cikin salo na ilimi da ke haɗawa tsakanin tushe na shari'a da kuma fuskantarwa ta tarbiyya.
NI MUSULMI NE
Wanan maƙalar ta yi bayanin abubuwan da ake son a fahimta game da Musulunci, da wanene Musulmi, da kuma yadda zaka kasance Musulmi na haƙiƙa, kamar yadda ta ƙunshi ambaton kyawawan abubuwa na Musulunci da sashen ladubba da ɗabi'u masu daraja, da matsayin 'ya mace, da haƙƙoƙin ɗan uwa da maƙwabci da al'umma baki ɗaya. Haka nan ta yi bayanin cewa Musulunci yana umarta da kira zuwa ga dukkanin abubuwa kyawawa, kuma ba ya hani face daga dukkanin abubuwa munana.
MANZON MUSULUNCI Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su ara tabbata a gare shi -
Littafin "MANZON MUSULUNCI. (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -" yana bijiro da rayuwar Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga nasabarsa da tasowarsa zuwa auransa mai albarka, da farkon wahayi, da farkon Manzancinsa da yake na karshe, kuma yana bayyana mu'ujizojin Annabci da alamomin gaskiyarsa, kuma yana bayanin shari'ar da ya zo da ita da gudunmawarta a kiyaye haƙƙoƙin mutum da karamcinsa, kamar yadda yake bayyanar da matsayar abokanan rigimarsa da kuma shaidar da suka yi masa, tare da bayani akan manyan ɗabi'unsa waɗanda suka…
AƘIDA INGANTACCIYA
Saƙon yana nufin bayyana ingantacciyar aƙidah wadda aka aiko dukkanin Annabawa da ita, kuma aka saukar da Littattafai da ita, kuma aka kira halitta zuwa gareta, itace kaɗaita Allah a cikin RububiyyarSa da UluhiyyarSa da kuma sunayenSa da siffofinSa, da kuma wajabcin yin imani da rukunan imani guda shida, domin ya zama hanyar rayuwa ga muminai, da shi ne zai tsira daga ɓata, kuma ya rabauta a duniya da lahira.
FALALA DA LADUBBAN MASALLACIN ANNABI DA HUKUNCE-HUKUNCEN ZIYARAR ƘABARIN ANNABI -TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARE SHI- DA ƘABURBURAN SAHABBANSA BIYU -ALLAH YA YARDA DA SU-
Littafin yana bayanin falalar Masallacin Annabi da ladubban ziyartarsa, haka kuma yana gabatar da ladubban ziyartar ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da na sahabbansa guda biyu - Allah Ya yarda da su -, yana mai jaddada muhimmancin natsuwa da tsarki da kuma nisantar ayyukan bidi'a a lokacin ziyarar.