Mafi Yawan Bincike
Shin ka tambayi kanka? Waye ya halicceka? kuma saboda me? kuma me zai faru bayan mutuwa?
Littafin ya ƙunshi tambayar samuwa da kuma halitta, kuma yana tabbatar da samuwar Mahalicci Mai cikakkiyar hikima da cika a hankalce, kuma yana bayyanar da cewa manufar rayuwa ita ce bautawa Allah Shi kaɗai, kuma Musulunci shi ne Addinin gaskiya abin kiyayewa, kuma yana yin kira zuwa ga imani da Manzon Allah (annabi) Muhammad da kuma bin koyarwarsa, kuma yana gargaɗarwa daga shirka, yana ƙarfafa hisabi da sakayya a Lahira.
These files are generated automatically from the book's text; their layout may differ from the printed edition.
Shin ka tambayi kanka? Waye ya halicceka? kuma saboda me? kuma me zai faru bayan mutuwa?
Waye Ya halicceka ya kai wannan mutumin? Da zaka yi duba zuwa jikinka ƙarƙashin na'urar hangen kananun halittu, da ka ga wata irin duniya ta kyautatawa da kuma gajiyarwa, dukkanin wani tantanin halitta a cikin jikinka yana ƙunshe da waɗansu bayanai na ƙwayoyin halitta a cikinta waɗanda jerin lambobinsu a ƙulle suke. Shin ka tambayi kanka waye ya rubuta maka waɗannan jerin lambobin ƙwayoyin halittar? kuma waye ya sanya su a wurin da ya dace?
Dukkanin wani gini babba, haka kuma dukkanin wani gida maƙasƙanci, yana hakaito labarin wanda ya gina shi; shin zai yiwu a hankalce a samar da wannan duniyar mai faɗi da kyawunta da ingancinta da kiyaye rabe-rabenta ba tare da wanda ya yi ta ba?!
Ya kai mutum kamar yadda hakalinka ba zai karɓi ace maka: Lallai akwai wata wayar hannu mai inganci wacce aka kyautata ƙerawa ta bayyana haka kawai ba tare da wanda ya zanata ba haka kuma ba tare da wanda ya ƙerata ba, ko kuma wata haɗaɗɗiyar hanyar sadarwa ta na'urori tana aiki da daidaituwar sautuka da kuma inganci ba tare da wanda yake tsarawa ko mai lura da ita ba. Haka nan hankali ba zai yarda cewa: Lallai wannan duniyar da dukkan abinda ke cikinta na tsari da ƙirƙira da dokoki masu inganci da kyakkyawan tsari, haƙiƙa an samar da su ne ba tare da Mahalicci ba?!
Lallai cewa kowane yanki a cikin wannan duniyar, tun daga mafi ƙanƙantar ƙwayar komayya har zuwa mafi girman curin taurarin sama, suna nuni akan girman Mahaliccinsu; to yana koruwa a hankalce ace wannan tsarin mai inganci ya faru ne daga hargitsi. Lallai hankali ba zai yarda a ce wannan duniyar ta faru daga rashi ba, ko kuma wannan ƙayataccen tsarin ƙullalle a ce ya faru haka kawai a makance!
Kamar yadda ingantaccen hankali da kuma madaidaiciyar ɗabi'ar mutum wacce Allah Ya halicce shi a kanta suna jagorantar mutum ne zuwa ga imani da samuwar Mahallicin wannan halittar, domin cewa su suna sanyamu mu lura a cikin siffofin wannan Mahallicin da kuma haƙƙinSa a kanmu.
Lallai cewa lura a cikin siffofin wannan Mahallicin yana buɗe mana ƙofofin riska mai zirfi dangane da lalurar siffanta Shi da cika kai tsaye da kuma tsarkakeShi daga dukkanin tawaya.
Wannan yana nufin cewa Mahallici yana siffantuwa ne da dukkanin siffofin kyau da girma, Shi - tsarki ya tabbatar maSa - Mai iko ne akan dukkan komai, Masanin kowanne abu, Gwani a cikin dukkanin abinda Ya halitta kuma Ya ƙaddara, wannan cikar ba kawai mujarradin yi wuwar tabbatuwa ba ne, kai larura ce ta hankali, domin cewa kowace tawaya a cikin siffofinSa zata kai zuwa ga ɓaci a cikin halitta da kuma jujjuya al'amurran mulki, wannan kuwa shi ne abinda yake koruwa tare da abinda muke ganinsa na kyautatuwa a cikin duniya.
Kamar yadda tsarkake Shi daga tawaya yana hukunta cewa Mahallici ya kasance Mawadaci daga ababen halittarSa, dan haka ba ya buƙatuwa zuwa ga wani, kai kowa da kowa mai buƙatuwa ne zuwa gare Shi a cikin samuwarsu da kuma wanzuwarsu, kuma Shi - tsarki ya tabbatar maSa - abin tsarkakewa ne daga abokin tarayya da kuma ɗa, domin cewa hakan yana daga bayyanar tawaya da kuma gajiyawa, Allah - Mai girma da ɗaukaka - abin tsarkakewa ne daga dukkanin hakan.
Tunda Allah Ya kasance Shi ne Mahallici Mai girma Mai siffantuwa da siffofin cika da girma, kuma Shi ne wanda Ya samar da mu kuma Ya samar da duniya daga babu, kuma Shi ne Mamallakin dukkanin abinda ke cikinta, kuma Shi ne wanda Yake azirta mu kuma Yake kewayemu da rahamarSa, Shi ne Mai jujjuyawa Mai tasarrufi da kowane abu; shin yanzu ba ya wajaba akanmu mu gode maSa kuma mu yi bincike ta yaya zamu samu yardarSa, kuma ta yaya zamu bada haƙƙinSa wanda ya wajaba akanmu, kuma mu yi aiki dan tabbatar da manufar da Ya haliccemu saboda ita?!
Shin za'a iya cewa Allah Ya haliccemu sannan ba Ya bayyana mana abinda Yake nufi daga garemu? dan me yasa muke a nan? wace manufa ce da kuma hadafi na samuwarmu a cikin rayuwa? kuma me zai faru garemu bayan mutuwa?
Ka yi lura tare da ni, da a ce mutum ya gina babban bene, kuma ya ƙara masa abubuwan zamani na kere-kere, har sai da yakai ƙarshen gama shi, kawai sai ya rusa shi gabaɗaya ba tare da wani sababi ba, shin zai yi wu mu siffanta wannan mutumin da hikima? shin yanzu a hankalce ba zamu ɗauki cewa irin wannan tasarrufin wasa ne da ba ya dacewa da mai hankali ba ?.
Idan wannan aikin ya kasance ba abin karɓa ba a cikin haƙƙin mutum, to ta yaya zamu riya cewa Allah Gwani ne Masani, haƙiƙa Ya halicci wannan duniyar ƙayatacciya da ƙayatarwa da kuma ingantawa, sannan Ya rusata ba tare da wata manufa ko hikima ba?!
Haƙiƙa Allah Ya halicci mutane dan wata hikima mai girma, ita ce bauta maSa Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, kuma Ya haliccesu dan Ya jarraba su a cikin wannan duniyar, kuma Ya sanya musu ma'alƙawarta da za'a tashesu a cikinta a ranar alƙiyama dan a yi musu hisabi akan ayyukansu; wanda ya yi imani da Allah kuma Ya amsa kiranSa to ni'imar aljanna zata kasance gare shi yana madawwami a cikinta, wanda kuma ya bijirewa gaskiya to zai zama daga cikin 'yan wuta.
Ibada haƙƙi ce ta wajibi a kanmu domin ita ce manufa daga samuwarmu, kuma ita ce dalili na godiyarmu da kuma tabbatarwarmu ga Rububiyyar Allah da kuma UluhiyyarSa.
To ka lura cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Shi ne wanda Ya halicceka kuma Ya girmamaka da ji da kuma gani, kuma Ya kewayeka da ni'imomin da bazasu ƙirgu ba. Shi ne wanda Yake gudanar da jini a cikin jijiyoyinka, kuma Yake azirtaka da ruwa da kuma iska, kuma kai a kowane lokaci kana buƙatuwa zuwa gare Shi, da badan rahamarSa da kuma kulawarSa ba, da ka halaka ƙarfinka ya ƙare, kai lallai cewa Shi - tsarki ya tabbatar maSa - Ya lamunci arziƙinka alhali kai kana ɗan tayi a cikin mahaifiyarka, gajiyayye baka mallaki komai daga cikin al'amuranka ba.
Shin yanzu wannan Mahallicin Mai girma bai cancanci mu bauta maSa ba kamar yadda Shi Yake so, ba kamar yadda kai kake so ba?! Ka lura, da a ce ka so ka baiwa babarka wata kyauta, shin kai zaka zaɓi abinda ranka yake so ne, ko kuma za ka yi ƙoƙari a cikin sanin abinda ita take so dan ka faranta mata rai da abinda ya dace da ita? haka nan bautar Allah - Mai girma da ɗaukaka -, ba ta kamata ta zama ta dace da soye-soyen rayukanmu ko kuma al'adar da muka gada, bari dai kamar yadda Shi Ya so - tsarki ya tabbatar maSa -, da kuma yadda Ya umarce mu da ita.
Wajibi ne bauta ta zama abar tsarkakewa ga Allah - Maɗaukakin sarki - Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, dan haka ba ya halatta ga mutum ya juyar da bauta ga wanda ba Mahaliccinsa ba, kuma mafi girman zunuban da suke wajabta dawwama a cikin wuta shi ne yi wa Allah shirka, hakan shi ne mutum ya bautawa wanin Allah cikin halittunSa, kamar bautawa gumaka ko rana ko wata, ko bautawa mutum ko dabba ko wani mutum na gari, to dukkanin hakan suna daga cikin nau’ukan shirka da kafirci, kuma duk wanda ya mutu akan haka to sakamakonsa shi ne dawwama ta har abada a cikin wutar Jahannama.
Haƙiƙa Allah Ya iko Annabawa da Manzanni masu yawa dan su sanar da mu manufar samuwarmu a cikin wannan duniyar da kuma hadafin rayuwa, kuma dukkanin Manzanni saƙonsu ɗaya ne , shi ne saƙon Musulunci da kuma kira zuwa ga bautar Mahallicci Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, sai dai akwai wanda ya jirkitar kuma ya canja abin da Manzannin da suka gabata suka zo da shi, sai Allah Ya aiko cikamakin Manzanni (annabi) Muhammad, kuma Ya saukar masa da ƙarshen saƙonnni ga mutane shi ne Alƙur'ani mai girma. Akwai dalilai masu yawa na hankali da ilimi waɗanda suke tabbatar da cewa Alƙur'ani zancen Allah ne, kuma cewa shi ne Littafi ɗaya tilo wanda ba'a canja shi ko jirkitashi ba, kuma haƙiƙa Allah Ya bamu labari a cikin Alƙur'ani cewa ba zai karɓi kowane Addini daga mutum ba inba Musulunci ba, kuma cewa dukkanin Manzanni saƙonsu ɗaya ne: Shi ne kira zuwa ga kaɗaita Mahalicci da kuma bauta maSa Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, kuma Allah Ya bamu labari a cikin Alƙur'ani cewa aljanna da kuma ni'ima ta har abada zasu kasance ne ga muminai, kuma akwai wuta da kuma azaba mai raɗaɗi ga wanda ya bautawa wanin Allah, ko yaƙi shiga Musulunci.
Abin da Musulunci ya banbanta da shi daga waninsa shi ne cewa musulmai su kaɗai ne masu ikon gabatar da dalilai na hankali da haƙiƙanin ilimi, ta hanyar dogara akan tushe na sani da kuma aminci, dan tabbatar da cewa Alƙur'ani mai girma wanda ke tare da su a yau shi ne zancen Allah Mahalicci - tsarki ya tabbatar maSa -, wanda aka kiyaye daga canjawa da kuma jirkitawa.
Alƙur'ani mai girma shi ne littafin da Allah Ya saukar da shi ga AnnabinSa Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, haƙiƙa ya yi fito na fito da mutane da shi, tun sama da ƙarni goma sha huɗu akan su zo da kwatankwacinsa, kai har sura ɗaya kwatankwacinsa, sai suka kasa akan hakan, kuma fito na fito ɗin bai gushe ba yana nan har yau ba tare da wani ya samu damar kawo wani abu kwatankwacinsa a balaga, da bayani, da gajiyarwa, da kuma shara'antawa ba, amma tare da hakan a duk tsawon zamaninnika wani bai iya zuwa da wani abu kwatankwacinsa ba ko kuma wanda ya yi kusa da shi ba. Gajiyarwa a cikin Alƙur'ani ba kawai a lugarsa ba ne wacce takai ƙololuwa a fasaha da kuma bayani, kai ta zarce dan ta ƙunshi dalilai na hankali da kuma ilimi waɗanda suke ƙarfafa cewa shi zancen Allah ne; idan Alƙur'ani mai girma ya kasance yana ƙunsar dalilai bayyanannu waɗanda suke tabbatar da cewa shi zancen Allah ne, to lallai cewa tasarrufi na hankali da na manɗiƙi shi ne yin imani da shi da kuma bin abin da ya zo a cikinsa, canji akan dogara akan wasu litattafan daban waɗanda suka tasirantu da cushe-cushen mutane a cikin wallafa su.
Lafiyayyen hankali yana jagorantarmu zuwa cewa zancen Mahalicci, wanda Ya ƙayatar da halitta kuma ya inganta tsarinsa, shi ne mafi gaskiyar tushe ga sanin haƙiƙa, lokacin da muka samu wannan gajiyarwar a luga a cikin Alƙur'ani, da haƙiƙu na ilimi, da shari'ance-shariance cikakku, ƙari da kiyayeshi daga jirkitawa tsawon zamaninnika, dan haka babu wurin gudu daga miƙa wuya da cewa shi zancen Allah ne.
Bayan nan, lallai cewa imani da abin da ya zo a cikin Alƙur'ani ba kawai zaɓi ne na imani ba, kai shi tabbata ce ta hankali wadda take tafiya tare da manɗiƙi na bincike akan haƙiƙabin abubuwa.
Haƙiƙa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya bayyana a cikin Alƙur'ani mai girma cewa Shi bai haliccemu ba kawai dan wasa, kaɗai Ya halicce mu ne dan bauta maSa -.
Kuma Allah Ya bamu labari a cikin Alƙur'ani cewa wannan rayuwar duniyar wacce muke rayuwa a cikinta ita mujarradin marhala ce wacce aka sawa lokaci zata ƙare nan kusa, sai dai cewa rayuwa ta haƙiƙa ta har abada zata kasance ne a lahira, lokacin da muminai zasu shiga aljanna kuma kafirai zasu shiga wuta.
Mahalicci wanda Ya samar da mu daga nabu, Mai iko ne da dukkanin ƙarfafawa akan cewa zai dawo da mu zuwa rayuwa bayan mutuwa, kuma a cikin abin da ke gefanmu na ayoyin Allah a cikin kasantattu, muna shaida dalili abin tabbatarwa akan ikon Allah wanda ba zai ƙare ba a cikin raya abinda ya mutu; kamar yadda Allah Yake fitar da wuta daga korayen bishiyoyi, kuma Yake fitar da shuka da 'ya'yan itatuwa daga bushasshiyar ƙasa, kuma Yake halittar ɗan tayi a cikin mahaifiyarsa daga maniyyi, to lallai cewa Shi - tsarki ya tabbatar maSa - Mai iko ne akan Ya raya matattu kuma Ya tashe su daga ƙaburburansu dan sakamako a ranar alƙiyama, to Allah Mai iko ne akan dukkan komai. Yana daga zalinci da rashin adalci a ce rayuwar azzalimi da wanda aka zalinta ta ƙare ba tare da hisabi ko sakamako ba.
Mutum zai iya yin tambaya, saboda me Musulunci (shi kadai) ba tare waninsa cikin Addinai ba?!
Lallai cewa mafi girman abin da mutum ya banbanta da shi daga sauran halittu shi ne hankali, kuma aikinsa shi ne tunani da kuma bincike game da haƙimanin abubuwa.
Lallai cewa Musulunci wani Addini ne wanda yake dacewa da kuɓutaccen hankali da kuma madaidaiciyar ɗabi'a, shi yana gabatar da amsoshi na manɗiƙi (hankali) ga manyan tambayoyi na samuwa: Dan me yasa muke a nan? kuma mecece manufa akan rayuwarmu? kuma mecece makoma bayan mutuwa?
Musulunci yana tsayawa ne akan kaɗaita Mahalicci da bauta, da kuma shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Wannan ita ce shahada ta farko, kuma ita ce tushen imani a cikin Musulunci, kuma tana nufin cewa babu wani abin bautawa da cancanta sai Allah Shi kaɗai.
Wannan shahadar ta ƙunshi:
Kaɗaita Allah: Wato yin imani da Ubangijin da Ya cancanci bauta Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, ba Shi da ɗa, kuma ba Shi da tamka.
Barranta daga shirka: Wato musunta dukkanin gumaka, da iyayen gijin da mutane suka ƙera su.
Musulunci yana wajabta yin imani da dukkanin Manzanni, musulmai suna yin imani cewa (Annabi) Isa bawan Allah ne kuma ManzonSa ne, kamar yadda Allah Ya bada labari a cikin Alƙur'ani, kuma lallai cewa shi ba ɗan Allah ba ne; domin Allah Mai girma ne kuma tsarki ya tabbatar maSa a ce Yana da mata ko ɗa, Shi Mawadaci ne daga gare su da ma dukkan komai. Haƙiƙa Allah Ya bamu labari a cikin Alƙur'ani cewa (Annabi) Isa ya kasance Annabi ne wanda Allah Ya ba shi ma'ujizoji masu yawa, kuma cewa Allah Ya aiko shi dan kiran mutanensa zuwa bautar Allah Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, kuma Ya bamu labarin cewa (Annabi) Isa bai nemi mutane su bauta masa ba, kai shi da kansa shi ne ma yake bautawa Mahaliccinsa; idan kana son ka zama kana mai yin imani da (Annabi) Isa akan haƙiƙar da Allah Yake son ta to wajibi ne akanka ka shiga (addinin) Musulunci.
Kuma Allah Ya bamu labari a cikin Alƙur'ani cewa (Annabi) Isa ya umarci mutanensa da bautawa Allah Shi kaɗai kuma ya gargaɗesu daga shirka.
Shin yanzu a hankalce zai yi wu mai hankali ya bautawa wani abin halitta irinsa, wanda yake jin yunwa yake jin ƙishirwa, kuma ba ya mallakawa kansa kare mutuwa ko cuta?! Ta yaya ya kai mutum zaka bautawa (annabi) Isa ɗan Nana Maryam alhali shi mutum ne ya kasance yana buƙatar abinci da abin sha, kuma ya kasance yana fuskantar Ubangijinsa ta hanyar yin sallah?! Shin zai yi wu ga hankali ya suranta cewa Allah Yana yi wa kansa sallah?! shin yanzu Allah bai zama mai siffantuwa da girma ba, wanda Ya kaɗaita a cikin cikarSa, abin tsarkakewa daga kamaceceniya da kuma misaltuwa, kuma dukkanin abinda ke cikin duniya yana ƙarƙashin ikonSa da kuma sarautarSa? Ta yaya a hankalce a ce mahaliccin sammai da ƙasa Ya kaskantar da kansa dan a haife Shi a matsayin jariri, sannan ya miƙa kansa ga halittarsa dan su tsire shi? lallai cewa wanda ake tsirewa kuma ake kashewa sune mutane masu ƙarewa, amma Mahalicci to Shi ne rayayye wanda ba zai mutu ba, tabbatacce wanda gyangyaɗi ba ya kama Shi ko bacci, shin yanzu bai zama daga cikar girmanSa da kuma ɗaukakarSa Ya zama abin tsarkakewa daga irin hakan ba?
Haƙiƙa Allah Ya bamu labari a cikin Alƙur'ani mai girma cewa dukkanin Manzanni sun zo ne da saƙo ɗaya wanda a taƙaice shi ne bautar Allah Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, shi ne kiran da suka yi wa mutanensu. Sai dai tsawon zamani wasu sun jirkita wannan saƙon madawwami, sai suka shafe hasken tauhidin da Annabawa suka zo da shi, sai Allah Ya aiko da ƙarshen Manzanni (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma Ya saukar masa da Alƙur'ani mai girma dan ya jaddada saƙon tauhidin da dukkanin Manzanni da suka zo da shi kafinsa.
A ƙarshe muna faɗa maka ya kai wannan mutum:
Lallai cewa Musulunci Addinin hankali ne da kuma ɗabi'a, kuma shi ne Addini ɗaya wanda Mahalicci Mai girma Ya shara'anta shi ga mutum; to yana wajaba akan kowane mutum mai hankali ya yi gaggawar shiga Musulunci hakan ta hanyar yin imani da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin Addini, da kuma (Annabi) Muhammad a matsayin Manzo. Wannan wani al'amari ne wanda babu wani zaɓi ga mutum a cikinsa; domin cewa Allah zai tambaye shi a ranar Alƙiyama game da abin da ya amsawa Manzanni da shi; idan ya kasance mumini ne to yana da rabo mai girma, idan kuma ya kasance kafiri ne to taɓewa mabayyaniya ta tabbata gare shi.
Idan ka kasance kana bincike game da tsira ta haƙiƙa a duniya da kuma rabauta a lahira, to ka sani cewa mafi girman shawarar da zaka riƙe a cikin rayuwarka ita ce ka shiga Musulunci, kuma babu wani abin da ya wajaba a kanka sai dai kawai ka furta waɗannan kalmomin daga zuciya mai gaskiya kuma mai imani: "Ina shaida cewa babu wani abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma ina shaida cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne". Sannan ka fara koyan sanin Addininka da kuma aiki da abin da shahadun nan biyu suke wajabta shi na yin imani da Allah da ManzonSa da kuma lazimtar rukunan Musulunci.
Ka faɗeta a yanzu, kada ka yi wani kaikawo; mutuwa zata iya zakke maka kwatsam, dan haka kada ka jinkirta wannan muhimmiyar shawara, kada ka barwa Shaiɗan wata dama dan ya karkatar da kai daga alheri, ka zama gwarzo, kuma ka fara hanyarka zuwa ga haske da kuma shiriya.
Ka yanke shawarka a yanzu, kuma ka fara sabuwar rayuwa wacce ke cike da nutsuwa da kuma yarda.
"Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaida cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne".
Related books
All books
WANENE YA HALICCE NI? KUMA SABODA ME?75 harsunaWANENE YA HALICCE NI? KUMA SABODA ME?
Ko wanne abu yana nuni akan akwai mahalicci Wa ya halicci sammai da kasa da abinda ke tsakanin su na halittu masu girma wadanda ba’a iya gane yawansu? Wa ya kera wannan nagartaccan tsarin kayatacce a sama da kasa ? Wa ya halicci mutum ya kuma ba shi ji da gani da hankali? Ya sanya shi mai iko akan tsururutar ilimai da gane hakikanin abubuwa ? Yaya zaka fassara wannan kira gwananna dake na'urorin (gabban) jikinka da suke kuma a jukkunan kasantattu suna aiki? kuma wanene ya kage su? Ta yaya wannan kasantacce mai girma yake tsaruwa kuma yake tabbatuwa tare da ƙa’idojin sa, waɗanda suke kiyaye…
WA YA HALICCI HALITTU? WA YA HALICCE NI? KUMA SABODA ME?69 harsunaWA YA HALICCI HALITTU? WA YA HALICCE NI? KUMA SABODA ME?
Littafin "Wa ya halicci halittu? Kuma wa ya halicceni? Saboda me ?" (Littafin) yana tattaunawane akan asalin samuwar halitta da kuma mutum, yana mai ƙarfafa cewa wannan halittar bata samu ba katsahan, ko kuma daga rashi, a’a tana da wani Mahalicci Mai girma, Shine Allah, wanda Ya sanya dokoki masu zurfi da zasu tafiyar da rayuwa da halittu. Littafin yana bayanin siffofin Allah, da kuma muhimmancin imani da Manzanni da littattafan da aka saukar daga sama, yana kuma ƙarfafa cewa lalle Musulinci shi ne Addini na gaskiya, wanda ya tattaro saƙonnin Annabawa, yana mai kira da a yi imani da shi,…
TUSHE GUDA UKU DA DALILANSU73 harsunaTUSHE GUDA UKU DA DALILANSU
Littafin yana tattauna muhimman ƙa’idojin da ya wajaba ga musulmi ya koya: Sanin Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da sanin Addinin Musulunci, da kuma sanin Annabi Muhammadu - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -; kuma yana jaddada muhimmancin waɗannan ƙa’idoji wajen gina imani da aikata nagartattun ayyuka, dan dogara ga hujjoji na Al‑Kur’ani mai girma da Sunnar Annabi.
Taƙaitaccen Saƙo Zuwa ga Mulhidi61 harsunaTaƙaitaccen Saƙo Zuwa ga Mulhidi
Wani taƙaitaccen saƙo ne zuwa ga mulhidi, wanda yake yi wa hankali magana cewa lallai daidaici da tsarin wannan duniyar yana kore faruwarta katsahan, kuma yana nuni akan wani Mahalicci Gwani. To shin zai yiwu a hankalce a ce duk wannan ya faru ne daga rashi? Dan haka ka buɗe zuciyarka don yin tunani da lura, kuma ka yi bincike akan gaskiya, domin za ka iya samun wani haske a ciki wanda zai shiryar da kai.