Addini ne na ɗabi'a ta asali da hankali da kuma tsira.
Addini ne na ɗabi'a ta asali da hankali da kuma tsira.
MUSULUNCI Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai. Shin ka tambayi kanka: Wa ya halicci sammai da ƙasa da abinda yake cikinsu, na halittu masu girma? Wa ya ƙera wannan ƙwararran tsari nagartacce a cikin su? Ta yaya wannan kasantacce mai girma yake tsaruwa kuma yake tabbatuwa tare da ƙa’idojin sa, waɗanda suke kiyaye shi, kiyaye wa ta ƙwarewa tsawon waɗannan shekaru? Shin wannan kasantacce (halittu) shi ne ya halicci kansa? Ko ya zo ne ba daga wurin kowa ba? Ko kuma an same shi kawai kwatsam?
Addini ne na ɗabi'a ta asali da hankali da kuma tsira.
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai.
Shin ka tambayi kanka:
Wa ya halicci sammai da ƙasa da abinda yake cikinsu, na halittu masu girma? Wa ya ƙera wannan ƙwararran tsari nagartacce a cikin su?
Ta yaya wannan kasantacce mai girma yake tsaruwa kuma yake tabbatuwa tare da ƙa’idojin sa, waɗanda suke kiyaye shi, kiyaye wa ta ƙwarewa tsawon waɗannan shekaru?
Shin wannan kasantacce (halittu) shi ne ya halicci kansa? Ko ya zo ne ba daga wurin kowa ba? Ko kuma an same shi kawai kwatsam?
Wa ya halicce ka?
Wa ya sanya wannan nagartaccan tsari a gaɓoɓi masu aiki na jikinka da jikunan sauran samammu masu rai?
Babu mutumin da zai yarda a ce da shi: Ai wannan gidan kawai ya samu ne ba tare da wani ne ya gina shi ba! Ko a ce da shi: Ai babu ita ce ta samar da wannan gidan! To ta yaya wasu daga cikin mutane za su yarda da wanda yake cewa wannan duniyar mai girma ta zo ne ba tare da Mahalicci ba?. Ta yaya mai hankali zai yarda ace da shi wannan ginin (na sama da ƙasa) wanda ke cike da ƙwarewa ya samu ne haka kawai?
Tabbas akwai wani abin bauta Mahalicci Mai tsara wannan halittar da abinda yake cikinta, shi ne kuwa: Allah - tsarki ya tabbata a gare shi Ya ɗaukaka -.
Ubangiji - tsarki ya tabbata a gare Shi - Ya aiko mana da manzanni, Ya kuma saukar musu da littattafai na Allah (wahayi), na ƙarshansu shi ne al-Kur’ani, wanda Ya saukar da shi ga (Annabi) Muhammad cikamakin Manzannin Allah, ta hanyar littattafanSa da ManzanninSa:
Ya sanar da mu kanSa da siffofinSa, da hakkinSa a kammu, Ya kuma bayyana mana hakkin mu da ya ɗorawa kansa.
Ya kuma nuna mana cewa Shine Ubangiji, wanda Ya halicci halittu, kuma Shi rayayye ne baYa mutuwa, halittu kuma suna damƙarSa ne, kuma ƙarƙashin rinjayarSane da tasarrufinSa.
Ya bamu labarin cewa daga cikin siffofinSa akwai sani, haƙiƙa Ya game ko’ina da saninSa, kuma Shi Mai ji ne Mai gani ne, babu wani abu da yake ɓoyuwa a gareShi a cikin ƙasa ko a sama.
Ubangiji! Shi ne Rayayye, Tsayayye, wanda rayuwar duk wani hallita daga gare Shi ne, Shi kaɗai, tsarki ya tabbata a gare Shi, Shi ne kuma Tsayayye wanda rayuwar kowanne halitta take tabbatuwa da shi, tsarki ya tabbata a gare Shi, Allah - Maɗaukakin sarki Ya ce:{Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wanene wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma}[Suratul Baƙarah: 255].
Kuma Ya ba mu labarin cewa Shi ne: Ubangiji ! Wanda Ya siffantu da siffofi na cika, kuma Ya azirta mu da hankula da abubuwan ji, da suke riskar abubuwan mamaki na halittarSa da ikonSa, wanda hakan yake nuna mana girmanSa da karfinSa da cikar siffofinSa, kuma Ya dasa mana kyakkyawan tunani da suke nuni akan cikarSa, ta yadda ba zaiyiwu a saffanta Shi da wata siffa ta tawaya ba.
* Ya sanar da mu, cewa Ubangiji Yana saman sammanSa, ba yana cikin halittarSa ba ne, kuma halittarSa bata shiga cikinSa ba.
* Ya bamu labarin cewa, Ya wajaba akanmu mu miƙa wuya gare Shi - tsarki ya tabbatar maSa - Shine Mahaliccin mu, Mahaliccin kowanne abu kuma Mai jujjuya shi.
Mahalicci Yana da siffofin girma, ba zai yiwu ba Ya siffantu da buƙata ko tawaya. Ubangiji baYa mantuwa baYa bacci, baYa cin abin ci, ba zai yi wu ace Yana da mata ko ɗa ba, duk wasu bayanan da suke saɓawa girman Mahalicci to ba ingantaccen wahayi bane wanda manzannin Allah - aminci ya tabbata agare su - suka zo da shi ba.
Idan ka kasance kana imani da Ubangiji Mahalicci… to shin ka taɓa tambayar kanka wata rana game da manufar da tasa aka halicceka? Kuma me Allah Yake nufi da mu, kuma mecece manufar samuwarmu?
Shin zai yi wu Allah Ya halicce mu sannan Ya bar mu a zube sasakai? Shin zai yi wu a ce Allah Ya halicci waɗannan halittun ba tare da manufa ko dalil ba?
A haƙiƙanin gaskiya Ubangiji Mahalicci Mai girma "ALLAH" Ya bamu labari akan manufar halittarmu, itace bautar Allah Shi kaɗai, me kuma Yake so daga garemu? kuma Ya bamu labarin cewa Shine wanda Ya cancanci a bauta maSa, Ya kuma bayyana mana ta hanyar ManzanninSa - aminci ya tabbata a gare su - ta yaya zamu bauta maSa? Ya zamu nemi kusanci gareShi ta hanyar aikata umarninSa da barin abubuwan da Ya hana ? Yaza mu sami yardarSa ? Mu kuma kiyayi uƙubarSa, kuma Ya ba mu labarin makomarmu bayan mutuwa.
Ya bamu labarin cewa ita wannan rayuwar duniyar kawai jarrabawa ce, kuma cewa tabbatacciyar rayuwa cikakkiya da sannu za ta kasance a lahira bayan mutuwa.
Ya kuma bamu labarin cewa wanda ya bautawa Allah kamar yadda Ya umarce Shi, kuma ya hanu daga abinda Ya hana shi; to yana da daddaɗar rayuwa a duniya, da dawwamar ni’ima a lahira, wanda kuma ya saɓa maSa ya kafirce maSa to taɓewa ta tabbata gareshi a duniya, da kuma dawwamar azaba a lahira.
Wanda ya dubi abinda mafi yawan mutane suke bautawa a yau; zai sami wannan yana bautawa mutum, wani kuma yana bautawa gunki, wani tauraro yake bautawa, haka dai, baya kamata ga mutum mai hankali ya bautawa wani sai Ubangijin talikai, Cikakke a siffofinSa, to, tayaya (abin halitta) zai bautawa abin halitta irinsa ko ƙasa da shi, wanda ake bautawa ba ya kasancewa mutum ko gunki ko bishiya ko kuma dabba!
Dukkanin addinan da mutane suke bi a yau - in banda Musulunci - Allah baZai karɓa ba, domin addinai ne da mutum ya ƙirƙira, ko addinan na Allah ne sai hannun mutum ya canja su.
Amma Musulunci, shi addinin Ubangijin talikai ne, baya canjawa, littafin wannan addinin shine al-Kur’ani mai girma, shi littafi ne tsararre kamar yadda Allah Ya saukar da shi, kuma bazai gushe ba a hannun musulmai zuwa yau da harshen da aka saukar da shi ga manzo cika makakin manzanni.
Yana daga cikin tushen Musulunci kayi imani da dukkanin Manzannin da Allah Ya aiko su, kuma dukkan su sun kasance ne daga cikin mutane, Allah Ya ƙarfafe su da ayoyi da mu’ujuzozi, Ya aiko su domin kiran mutane zuwa bauta maSa Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya.
Karshan manzanni shine (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, Allah Ya aiko shi da shari'ar Allah mai cikewa mai shafe shari’o’in manzannin dake gabansa, Ya kuma ƙarfafe shi da mu’ujuzoji masu girma, mafi girman su shine al-Kur’ani zancan Allah ne Ubangijin talikai, mafi girman littafin da aka taɓa samu a tarihin mutum, mai gajiyarwa ne a abinda ya ƙunsa da lafazinsa da zubinsa, da hukunce-hukuncen sa, a cikinsa akwai shiriya ga gaskiya, wacce za ta kai ga rabauta a duniya da lahira, haƙiƙa ya sauka ne da harshan larabci.
Akwai dalilai masu tarin yawa na hankali da kuma na ilimi waɗanda suke tabbatar da abinda babu kokwanto a cikinsa, cewa shi wannan al-Kur’anin zancan Mahalicci ne - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -, kuma ba zai taɓa yiwuwa ba ace mutum ne ya tsara shi.
Yana daga tushen Musulunci, imani da mala’iku, da imani da ranar alƙiyama, lokacin da Allah Zai tayar da mutane daga ƙaburburansu a ranar alƙiyama, domin yi musu hisabin ayyukan su, wanda ya aikata kyawawan ayyuka alhalin shi yana mumini, to shi yana da tabbatacciyar ni’ima a aljanna, wanda kuma ya kafirta ya aikata ayyuka munana to yana da azaba mai girma a cikin wuta.Yana daga tushen musulunci cewa kayi imani da abinda Allah Ya ƙaddara shi na alheri ko na sharri.
Kuma saboda cewa mu mun san ba zaiyiwu mu tafi a wannan rayuwar ba ba tare da kowanne mutum ya sami sakamakon abinda ya aikata ba na alheri ko na sharri; (a ce) babu wata uƙuba ga azzalumai, kuma babu wata sakayya ga masu kyautatawa?
Addinin Musulunci tsari ne da ya game dukkanin rayuwa, yayi daidai da ɗabi’a na halitta da hankali, kuma madaidaitun rayuka suna karɓarsa, Mahalicci Mai girma ne Ya shar’anta shi ga halittarSa, kuma shine addini na alheri da rabauta ga mutane baki ɗaya a duniya da lahira, ba ya banbance ƙabila da ƙabila, ko nuna wariyar launin fata, mutane a cikinsa daidai suke, wani mutum a Musulunci baya wuce wani sai da gwargwadon aikinsa na gari.
Yana daga abinda Allah Yake ƙarfafashi a cikin AlKur’ani cewa: Imani da Allah Shi ne Ubangiji kuma abin bauta, kuma Musulunci shi ne addini, (Annabi) Muhammad kuma shi Manzo ne, lamari ne da ya wajaba akan kowa, mutum ba shi da zaɓi, a ranar alƙiyama a kwai hisabi da sakamako; wanda ya kasance mumini mai gaskiya, to yana da rabo, da sakamako mai girma, wanda kuma ya kasance kafiri, to, taɓewa bayyananniya ta tabbata a gare shi. .
Littafin: “MUSULINCI ADDININ MANZANNIN ALLAH” ne, a dunkule yana kunshe da tsantsar addini a Tauhidi, domin kadaita Allah, mutum yana yin imani da Allah shi kadai, Kwal, da kuma (annabi) Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, cikamakin annabawa, kuma ya kafa tsarin adalci da daidaito, ya yi imani da Mala’iku da ranar Alkiyama, shi kuma addini ne na tunani da hankali, wanda yake kira ga mika wuya ga Allah gaba daya, wanda yake tabbatar da kwanciyar hankali a duniya da lahira.
Ko wanne abu yana nuni akan akwai mahalicci Wa ya halicci sammai da kasa da abinda ke tsakanin su na halittu masu girma wadanda ba’a iya gane yawansu? Wa ya kera wannan nagartaccan tsarin kayatacce a sama da kasa ? Wa ya halicci mutum ya kuma ba shi ji da gani da hankali? Ya sanya shi mai iko akan tsururutar ilimai da gane hakikanin abubuwa ? Yaya zaka fassara wannan kira gwananna dake na'urorin (gabban) jikinka da suke kuma a jukkunan kasantattu suna aiki? kuma wanene ya kage su? Ta yaya wannan kasantacce mai girma yake tsaruwa kuma yake tabbatuwa tare da ƙa’idojin sa, waɗanda suke kiyaye…