Littafin: SHARHIN MA’ANONIN KIRAN SALLAH , yana ƙunsar kalmomin kiran sallah, sai ya yi musu sharhi sharhi na imani. Yana kuma bayyana muhimmancinsa a bangaren aƙidah da kuma tarbiya, kuma yana bayana cewa kiran sallah ba wai ya taƙaitu ga kiran sallah ne kaɗai ba, a’a shi kira zuwa ga Tauhidi ne na yau da kullum da kuma rabauta. Zai bujuro da kalmomin kiran sallah ya yi bayanin abinda suke nufi filla-filla, tun daga girmama Allah da shaidar Tauhidi da Manzanci, zuwa ga kiran sallah da kuma rabauta, har zuwa rufewa da Kabbara da kuma Tauhidi, da salo mai tasiri. Yana haɗa kalmonin kiran…
Harshe: lang_ha
Shiryawa: Kwamitin ilimi na Cibiyar hidimar bayanan Addinin Musulunci a cikin harsuna daban daban.
Kwamitin ilimi na Cibiyar hidimar bayanan Addinin Musulunci a cikin harsuna daban daban.
Kiran sallah, kira ne na Ubangiji, Musulmi yana jinsa sau biyar a rana, yana tuna masa girman Allah yana kuma kiran sazuwa ga alheri da rabo. Shi ne lokacin haɗuwar mutum da Mahaliccin sa, yana barin hayaniyar duniya a cikinsa, domin ya tsaya yana mai ganawa da Ubangijin sa.Ba a ɗaukar kiran sallah a matsayin sanar da lokacin sallah kawai, a’a, kira ne na samun natsuwa da imani da jaddada haɗuwa da Allah.Kiran sallah yana ɗauke da ma’anoni masu girma, suna farawa da girmama Allah, kuma suna ƙarewa da kira zuwa ga sallah yadda musulmi zai sami natsuwarsaA kowane lokaci aka kira sallah ana ji a cikin zuciya cewa rayuwa ta haƙiƙa tana farawa ne da kusanci ga Allah.
KALMOMIN KIRAN SALLAH
Allahu Akbar Allahu Akbar, Allahu Akbar Allahu Akbar. (Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma).
"Allah ne Mafi girma".
Babban Lafazin “Allah”, yana nufin abin bauta, suna ne na Ubangiji Mahalicci Mai girma da ɗaukaka, dukkanin sunayan Allah kamar suna bin wannan sunan ne kuma suna siffanta shi ne, Allah Shi ne tilo Makaɗaici, wanda Bai haifa ba kuma ba’a haife Shi ba, Shi ne Mahaliccin sammai da ƙasa.
Faɗin “Allahu Akbar”, Ma’ana: Allah Shi ne Mafi girman kowanne abu, kuma mafi birinƙasar a jingina maSa abin da bai dace da buwayarSa da cikarSa ba.
Allahu Akbar (Allah ne Mafi girma).. wannan kalmar tana tunawa musulmi cewar babu wani abu a wannan rayuwar da ya wajaba ya shagaltu da shi kamar Mahaliccinsa, kuma ya wajaba akan mutum ya tafiyar da rayuwarsa daidai da nufin Allah da kuma shari’arSa, ba wai daidai da yadda yake so ba da kuma sha’awarsa ba, Allah Shi ne Mafi girman dukkanin abinda ke cikin duniyar.
Allah Akbar (Allah ne Mafi girma), mai aikin hannu yana ji zai tsayar da sanaarsa, haka manomi sai ya tsayar da nomansa, ɗan kasuwa zai kulle wurin kasuwancinsa, malami sai ya tsayar da koyarwarsa; domin cewa Allah Shi ne Mafi girma akan kowanne abu da kowane aiki. Wannan tsayawar da nufatar wurin sallah dalili ne akan cewa Allah Shi ne Mafi girma a zuciyar mumini sama da komai na daɗin duniya.Allahu Akbar (Allah ne Mafi girma) akan kowanne bala'i da masifa, da kuma kowanne yanayi na rayuwa, wanda ya yi da hakan to masifu zasu zama ba komai ba a wurinsa, kuma zuciyarsa ta natsu domin yana tare da Allah, yana yarda da hukuncinSa, yana da tabbas da hikimarSa da juya lamuranSa.
Ashhadu an lā ilāha illal lāh, ashhadu an lā ilāha illal lāh. (Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.
Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah).
Ashhadu an la ilāha illal lāh. (Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah).
Wannan ita ce shaidawa ta farko, ma’anarta kuma shi ne: Tabbar da Allah Shi ne Mahaliccin komai, kuma Ubangijinsa, Mamallakin sa kuma Mai jujjuya sa. Kuma Shi Allah Shi ne wanda Ya wajaba a bautawa Shi kaɗai banda waninSa, kuma babu abin bautawa da cancanta sai Allah Shi kaɗai, kuma Shi kaɗai yake ba Shi da abokin tarayya, kuma ba Shi da ɗa, babu irin Shi, ba kuma za’a karkatar da ibada ba ga wanin wanda ba Allah ba, kuma ba za’a kira wanin Shi ba.
Wannan shaidawar ita ce mafi girman shaida a duniya, ita ce kuma tushen imani a dukkanin saƙo da Allah Ya aiko, dukkan Annabawa aminci ya tabbata a gare su, kamar (Annabi) Nuhu da (Annabi) Ibrahim da (Annabi) Musa da (Annabi) Isa har zuwa ga (Annabi) Muhammad sun kira mutanensu ne akan tabbatarwa da kuma karɓa, da kuma imani da cewa ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Ita ce kalmar da Allah Ya halicci halitta saboda ita, kuma Ya aiko da Manzanni domin tabbatar da ita, Ya kuma saukar da littattafai domin bayaninta, Ya kuma sanya aljanna ta zama sakamako ga wanda ya zo da ita domin Allah kaɗai tun daga zuciyarsa, Ya kuma haramta wuta ga wanda ya mutu yana mai sakankancewa da ita.
Ita ce mabuɗin aljanna, kuma ƙofar tsira, kuma asalin Addini kuma tushen Tauhidi.
Saboda wannan kalmar ne za’a tashi mutane daga ƙaburburansu, a kuma yi musu hisabi a ranar Alƙiyama, duk wanda ya rayu a kanta ya kuma cika rayuwarsa da ita to haƙiƙa ya rabauta rabo mai girma, wanda kuma ya yi watsi da ita, bai faɗeta ba, to ya cancanci dawwama a cikin wuta.
Ashhadu anna Muhammadan rasulullāh, Ashhadu anna Muhammadan rasulullāh. (Ina shaidawa lalle (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne,
Ina shaidawa lalle (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne).
Ina shaidawa lalle (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne.
Ma’anar wannan shaidawar, shi ne musulmi ya shaida cewa lalle Allah ya aiko (Annabi) Muhammad cikamakin saƙonnin Ubangiji, mai kuma isarwa mutane saƙon Ubangijinsu zuwa garesu, kuma musulmi ya tabbatar babu wata hanya ta bautawa Allah da rabauta da yardarSa face sai ta shaidawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da manzanci, da kuma bin sa da koyi da shi, da kuma bautawa Allah da shari’ar da Manzon Allah (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya isar da ita. Kuma duk wata ibada da mutum yake neman kusanci da ita da Manzon nan bai zo da ita ba to ɓatacciya ce, ba zata anfani mai ita ba anan duniya da kuma lahira, a’a za ma a hukunta shi a kanta a yi masa uƙuba, domin ya bautawa Allah da abin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai isar masa da shi ba.
Wannan shaidawar ta ƙunshi cewa wannan Manzon - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bawan Allah ne kuma kuma Manzo ne na Ubangijin talikai. Kuma tana ƙunsar cewa lalle wannan Manzon - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - shi ne cikamakin Manzanni - amincin Allah ya tabbata a gare su -, kuma babu wani Annabi a bayansa. Kamar yadda take ƙunsar imani da sauran mu’ujuzojin da ya zo da su, kuma mafi girmansu shi ne Alƙur'ani, shi ne cikamakin saƙon Allah, saƙon da yake ba zai taɓa gushewa ba da harshen da ya sauka da shi, an kuma tsare shi daga barin ƙari da ragi da kuma jirkitawa.Kuma lalle wannan Alƙur'anin mai daraja ba’a taɓa gasa da shi a Balagarsa da Hukunce-Hukuncensa da shiryarwarsa ba, haƙiƙa Allah Ya ƙalubalanci ‘yan Adam a kan su zo da ko da Sura ɗaya ce irinsa, suka kasa a kan duk waɗannan shekarun har kuma zuwa yau, mutune ba za su taɓa iyawa ba.
Kuma wannan shaidawar tana tattare da cewa Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, abin sani ya zo ne domin ya mayar da mutane zuwa ga Tauhidi, kamar yadda kafin shi (Annabi) Ibrahim da Musa da Isa - aminci ya tabbata a gare su -suka yi, to shi Manzo ne na Ubangijin talikai, ya tafi ne akan hanyar da dukkan Annabawa suka tafi a kanta a wurin isar da saƙon Ubangijinsu, sai dai cewa babu wani Annabi a bayansa.
Hayya alas salah, hayya alas salah. (Ku yi gaggawa zuwa ga sallah, ku yi gaggawa zuwa ga sallah).
Ku yi gaggawa zuwa ga sallah.
Ma’anar jumlar: Ya ku muminai, ku taho zuwa ga bautar Ubangijinku, domin Shi Mai yawan gafara ne kuma Mai yawan jinƙai ne, Yana karɓar tuba, kuma Yana yafe kusakurai.
Kai!! Wannan babban matsayi ne, Allah Ya umarci mutum a kowanne wuri da al’ummar musulmi suke don ya bayyanar da kiran, kuma ya kira su a kowacce rana sau biyar, domin ya ce da su:
Ku taho, ku zo ga bautar Ubangijinku.
Wannan kira ne, kuma faɗakarwa ne ga muminai da cewa haƙiƙa lokacin su na bautawa Allah ya yi, kuma ya wajaba a kansu su bar duk wani abu na duniya da zai shagaltar da su, su fuskanci wannan ibadar, su kuma bar abin da yake a hannunsu na kasuwanci ko noma su fuskanci Allah.
Wannan kuwa babban dalili ne a kan gaskiyar imani, kuma ana gabatar da shi ne a kan duk wani abu na jin daɗin duniya.
Wannan fa kira ne da yake kiran mutane zuwa sallah wacce take nan ne bawa yake ganawa da Ubangijin sa kai tsaye, ibada ce da take rusa bambanci, take sanya mutane daidai wa daida a gaban Ubangijinsu.
Hayya alal falāh, hayya alal falāh. (Ku taho zuwa ga tsira, Ku taho zuwa ga tsira).
Ku taho zuwa ga tsira.
Tsira yana nufin yarda da samun rabo da aminci da tsira a duniya da lahira, da kuma jin daɗi na har abada, da samun shiriya zuwa ga ingantacciyar hanya.
Yana daga cikin ma’anoninta (Alfalah), rabauta da yardar Allah, da kuma rabauta da aljanna da tsira daga wuta; domin wanda ya yi imani ya kuma yi sallah to haƙiƙa ya rabuta, wanda kuma ya rabauta to haƙiƙa ya tsira, ya rabauta da dawwama ta har abada a cikin aljanna.
Lalle ladani (mai kiran sallah), yana faɗakar da muminai a lokacin kowacce sallah a kan su taho zuwa ga aminci da amintuwa da hutun zuci, da tsarkin ruhi, da kuma jin daɗi a duniya da lahira.
Allahu akbar Allahu akbar, lā ilāha illallāhu. (Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah).
Rufewa da kabbara da kuma Tauhidi.
Ana kammala kiran sallah da maimaita kalmar: "Allahu Akbar" (Allah ne Mafi girma), da kuma ƙarfafa "lā ilāha illallāhu", (babu abin bautawa da gaskiya sai Allah). Waɗannan jumlolin biyu suna ƙarfafar ma’anonin da suka gabata ne, kuma a kansu ne tushen samuwar ɗan Adam take. Wannan tabbaci shi ne mafi gaskiyar tabbaci a duniyar nan, daidai ne shin mutum ya gane ko bai gane ba, ya san shi ko bai san shi ba, lalle tabbatattun abubuwa da suke manya to jahiltar wasu cikin mutane ba ya cutar dasu.Wannan tabbacin ba ya taɓa jirkitawa kuma baya canjawa duk yadda zamani ya yi nisa, haka kuma duk yadda abubuwa suka dinga faruwa, shi ne: Allah Shi ne Mafi girman kowanne abu, kuma Allah Shi ne Abin bauta na gaskiya, kuma Shi ne kaɗai wanda Ya cancanci ibada Shi kaɗai, Kuma bautar wani da ba Shi ba ɓatacciya ce.
Wanna kira ne mai girma domin girmama abin da Allah Ya girmama, kuma shaidawa Allah ne da abin da Ya shaidawa kanSa, kuma Manzanni suka shaida maSa aminci ya tabbata a garesu, kuma muminai suka shaida da hakan.
Daga ƙarshe:
Kiran sallah ba wai kaɗai kira ne kawai zuwa ga sallah ba, a’a kira ne domin samun rabo da rabauta da tsira, shi saƙo ne da yake maimaituwa a Masallatai sau biyar a kowacce rana, domin ya faɗakar da zuciya, kuma yana tunatar da mu cewa lalle Allah Yana kusa, kuma samun natsuwa abu ne mai yi wuwa, kuma hanya zuwa ga rabauta tana farawa ne daga sallah da ganawa tsakanin bawa da Mahaliccinsa
To ka maimaita tare da ladani; Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma, babu abin bautawa da cancanta sai Allah, sai ka maimaita shaidawar Tauhidi, kuma ka shaida da abin da Allah Ya shaidawa kanSa da shi, kuma ka shaida abin da ManzanninSa suka zo da shi na gaskiya, zaka kasance cikin waɗanda suka rabauta da musulmai masu Tauhidi.
Ka buɗe zuciyarka domin imani, ka ce:
“Ashhadu an lā ilāha illal lāh, wa ashhadu anna Muhammadan rasulullāh." ("Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma ina shaidawa lalle Muhammadu Manzon Allah ne”).
Za ka shiga cikin rahamar Allah, kuma zaka rabauta da jin daɗi a nan duniya, da kuma tsira a lahira, za’a tasheka a ranar Alƙiyama a tawagar muminai.
Littafin yana bayyana tushen imani waɗanda suka haɗa da imani da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da ManzanninSa, da ranar lahira, da ƙaddara; kuma yana gabatar da ƙa'idojin asali waɗanda wajibi ne a kan musulmi ya yi imani da su kuma ya yi aiki da abin da suka wajabta, yana mai ƙarfafa muhimmancin dangantaka da Allah ta hanyar zurfafa fahimtar aƙidar Musulunci.
Sifar Alwala (Sauƙaƙaƙƙen bidiyo) Ɗabbaƙawa a aikace da ke bayanin yadda siffar alwala taka daki-daki, yana da matuƙar muhimmanci saboda alwala sharaɗi ce na ingancin sallah. Kalli bidiyon ka ko yi ingantacciyar Siffar alwala. Siffar Alwala
Ɗabbaƙawa a aikace a taƙaice na kaifiyyar aiwatar da sallah, domin mu bauta wa Allah bisa basira kuma sallarmu ta kasance mai cikar rukunai da sharuɗɗa. Sifar Sallah Idan muna son yin sallah to ya wajaba mu yi tsarki daga ƙaramin hadasi da kuma babban hadasi. Kuma mu yi sallah da tufafi masu tsarki masu suturce al'aurarmu. Kuma jikinmu da wurin sallarmu su kasance masu tsarki daga najasa. Mu fuskanci alƙibla Kuma mustahabbi ne mu yi sallah zuwa ga sutura.
TAƘAITACCEN BAYANI MAI AMFANI GA LADAN DA LIMAN DA MAI HUDUBA DA KUMA HUKUNCE HUKUNCEN MASALLACI
47 harsuna
TAƘAITACCEN BAYANI MAI AMFANI GA LADAN DA LIMAN DA MAI HUDUBA DA KUMA HUKUNCE HUKUNCEN MASALLACI
Littafin yana gabatar da cikakken bayani game da hukunce-hukuncen kiran sallah da ikama, da limancin sallah, da huɗubar Juma'a, da kuma ladubban masallaci; haka kuma yana tattauna ayyukan ladanai da limamai da masu huɗuba, yana kuma mai ƙarfafa muhimmancin koyon hukunce-hukuncen shari'a da suka shafi waɗannan ayyuka domin tabbatar da gudanar da su yadda ya kamata. Haka kuma ya ƙunshi nassoshin da aka ruwaito daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - tare da sharhinsu, don tabbatar da an yi aiki da su daidai.