صفة الوضوء والصلاة (مرئي)
PROJ-187
Yaya zan yi alwala?
M
Sauti
1
Sautin kiran Salla
2
Ya ku waɗanda suka yi imani, idan kun tashi za ku yi salla, to, ku wanke fuskokinku da hannayenku zuwa gwiwoyi, kuma ku shafi kawunanku, kuma (ku wanke) ƙafafunku zuwa idon sawu. Kuma idan kun kasance masu janaba, to, sai ku tsarkaka. Idan kuma kun kasance marasa lafiya, ko a halin tafiya, ko ɗaya daga cikinku ya dawo daga bayan gari, ko ku ka sadu da mata, kuma sai ba ku sami ruwa ba, to ku yi taimama a doron ƙasa mai tsarki, ku shafi fuskokinku da hannayenku da shi. Allah ba Yana nufin Ya sanya ƙunci a tare da ku ba ne, a’a, Yana nufi ne Ya tsarkake ku, kuma Ya cika ni’imarSa a gare ku, don ku zamo masu godiya.
Suratul Ma'ida: 16
3
Babu salla ba tare da Alwala ba, babu Alwala ba tare da Niyya ba, kuma babu Niyya ba tare da Ikhlasi ba, kuma wurin niyya shi ne zuciya, ba Harshe ba.
4
Da sunan Allah
An shari'anta faɗin Bisimillah a farkon alwala.. da ita ne muke fara alwalar mu..
5
Muna wanke Tafukan Hannu sau uku, farawa daga saman yatsu zuwa GavarTafin Hannu
6
Muna wanke Hannaye har zuwa wuyan hannu sau uku a jere.
7
Farawa tana kasancewa daga hannun dama, zamu wanke shi sau uku, sai kuma na hagu sau uku
8
Haka nan ya halatta a wanke hannun dama, sannan na hagu, sannan dama, sannan Hagu.haka dai
9
Tare da tabbatar da shigar da ruwa tsakanin yatsunmu.
10
Sannan sai mu tafi zwa ga kuskurar baki da shaƙa ruwa..
11
Kuskurar bakin ana yin ta ne ta hanyar sanya ruwa a cikin bakin, sannan a motsa shi a ciki, sannan kuskura shi sai a furzar da shi
12
Shaƙa ruwa yana kasancewa ne da jan ruwa zuwa hanci ta hanyar numfashi, sannan sai a fyace shi, kuma da hannun hagu ake yin shaƙar
13
Yana daga sunna kai wa Matuƙa wajen yin shaƙar, matuƙar dai ba azumi muke ba, ko kuma muna tsoron cutuwa.
14
Kuma kuskurar baki da Shaƙa ruwa suna da hanyoyi biyu:
15
Wasalu (Tazarce): Shi ne: Yana kasancewa ne da ɗibar cikin tafin hannu ɗaya na ruwa, sai a yi kurkura da rabinsa, sannan a shaƙa hanci da sauran rabin ...
Za mu motsa ruwan a cikin baki, sa'annan mu furzar da shi, sannan mu fyace da ruwan da muka shaka a hanci da hannun hagu.
Za mu yi haka har sau uku, cikin kanfata uku na ruwa.
16
Amma shi Faslu (Rabawa): shi ne Raba kurkure baki, da kuma shakar ruwa, sai mu dauki kamfata daya ta ruwa mu cika baki da ita, sannan mu motsa shi, sannan mu zubar da shi, sannan mu sake kamfata ta biyu mu shaka, sannan kuma shakawar za a yi ta ne da hannun hagu.
17
Mai bin kuskurar Baki da Shaqa Ruwa shi ne Wanke fuska
18
Iyakar fuska ta wajen tsawo ita ce: daga Matsirar Gashi na al'ada har zuwa ƙarshen Haɓa, ta wajen faɗi kuma shi ne tsakanin kunnuwa biyu.
19
Tare da wajabcin wanke kowane gashi dake fuska; Kamar gashin gemu, gashin baki, gashin gira, gashin ido, da kuma hana-ƙarya, wanda shi ne gashin da ke tsirowa a karkashin leɓen kasa.
20
Kuma wanke fuska yana da hanyoyi biyu:
21
Na farko: Sai mu ɗebi ruwan da hannayenmu biyu, sa'annan mu wanke fuska da shi, tun daga matsirar gashi na al'ada zuwa karshen haɓa, kuma daga kunnen dama zuwa kunnen hagu, Kuma idan ya kasance gemu mai yawa ne, to, sunna ne mu shigar da ruwa a ƙarƙashinsa, kuma mu tsefe gemun
Muna yin wannan sau uku, wanda shi ne Cikawa, ko sau biyu, ko sau ɗaya, kuma yana daga cikin Wajibi
22
Na Biyu: Mu ɗebi ruwa da hannun dama kawai, sa'annan mu sanya shi a fuska, sannan mu wanke fuskar da hannu biyu kamar yadda ya gabata a hanya ta farko, sai mu yi haka sau uku.
23
Jeranta gaɓɓan alwala farilla ne, kuma jiɓinta a tsakaninsu shi ma farilla ne, ta yadda ba za mu gabatar da wata gaɓa a kan wata ba, kuma ba za mu yi jinkirin tashi daga wata gaɓar zuwa wata mai bi mata ba.
24
Bayan gama wanke fuska, sai mu tafi zuwa wanke hannaye
25
Iyakar hannayen da yake wajibi ne a wanke su: tun daga gefen yatsun hannu har zuwa gwiwar hannu, tare da wanke gwiwar hannun.
26
Za mu fara da wanke hannun dama daga gefen yatsun tafin hannu, da kuma tsattsefe yatsun tare da cuccuɗa su, sa'annan mu kai ruwa ga gwiwar hannu.
27
Sannan sai mu koma kan hannun hagu, sannan mu wanke shi daga yatsun hannun tare da tsefe su zuwa gwiwar hannu.
28
Sai mu tafi zuwa shafar kai. Sai Mu jiƙa hannuwanmu da sabon ruwa, sa'annan mu sanya jiƙaƙƙun hannayen a gaban kai, sai mu ja su zuwa ƙeya, sannan mu mayar da su wurin da muka faro. Babu bambancin shafa a tsakanin mai Sanƙo, da kuma mai gashi.
29
Sannan za mu shafi kunnuwa da ragowar ruwan da muka yi shafa kai da shi, kuma za mu yi haka sau daya.
30
Siffar shafar kunnuwa ita ce: Za mu saka yatsan manuniya cikin hudar kunnuwa biyu, sai mu shafe su, kuma za mu goge bayan kunnuwa da babban yatsa, sai ya zama mun yi shafar kunnuwan biyu ciki da waje.
31
Sannan sai mu matsa zuwa ga wanke ƙafafu, iyakar ƙafafu da ya wajaba a wanke shi ne: tun daga gefen yatsu har zuwa idanun sawu, haka ma wanke duga-dugai wajibi ne.
32
Zamu fara da ƙafar dama, kuma mu tsattsefe tsakanin yatsun kafar. Mu kula da wanke duga-dugai, da bayan ƙafafu biyu.
33
Sannan mu wanke kafar hagu, kamar yadda muka yi a ta dama, kuma kada mu manta da tsefe yatsun ƙafa, da kuma tabbatar da wanke diddige gabaɗayansa, da kuma kai war ruwa ga idon sawu.
34
Na shaida babu abin bauta na gaskiya sai Allah, Shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, kuma na shaida cewa Annabi Muhammad bawanSa ne, kuma ManzonSa ne.
35
Sunna ne bayan gama alwala a yi Zikiri da Addu'a, kuma Sunna ne ya ƙara da faɗin:
36
Allah Ka sanya ni a cikin masu tuba, kuma Ka sanya ni cikin masu son tsarkaka.
37
Ko kuma:
"Tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareka, na shaida babu wani Ubangiji sai Kai, ina neman gafararKa, kuma ina tuba a gareKa"
M
Abin da aka rubuta a kan Allon kallo
1
YAYA ZAN YI ALWALA
2
Ya ku waɗanda suka yi imani, idan kun tashi za ku yi salla, to, ku wanke fuskokinku da hannayenku zuwa gwiwoyi, kuma ku shafi kawunanku, kuma (ku wanke) ƙafafunku zuwa idon sawu. Kuma idan kun kasance masu janaba, to, sai ku tsarkaka. Idan kuma kun kasance marasa lafiya, ko a halin tafiya, ko ɗaya daga cikinku ya dawo daga bayan gari, ko kuka sadu da mata, kuma sai ba ku samu ruwa ba, to, ku yi taimama a doron ƙasa mai tsarki, ku shafi fuskokinku da hannayenku da shi. Allah ba Yana nufin Ya sanya ƙunci a tare da ku ba ne, a’a, Yana nufi ne Ya tsarkake ku, kuma Ya cika ni’imarSa a gare ku, don ku zamo masu godiya.
Surat Al-Ma'idah: 16
3
Wanke tafukan hannaye
4
Kuskurar baki da shaƙa ruwa
5
Sadarwa (Tazarce)
6
Rabawa
7
Wanke fuska
8
Ta farko
9
Ta biyu
10
Niyya da yin Bisimillah
11
Wanke tafukan hannaye
12
Kuskurar baki
13
Shaƙa ruwa
14
Wanke fuska
15
Wanke hannaye tare da guiwar hannu
16
Shafar kai da shafar kunnuwa
17
Wanke ƙafafuwa, tare da Idanun Sawu
18
Wanke hannaye
19
Shafar kai
20
Farkon Kai: Shi ne goshi da kuma mafarar matsirar gashi na al'ada
21
Ƙarshen Kai= shi ne inda gashi ya ƙare a ƙeya
22
Shafar Kunnuwa
23
Wanka ƙafafuwa
24
Annabi tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi ya ce:
"Boni (Tsananin Azaba) a wuta ya tabbata ga dugadugan (da ba a wanke su a alwala), don haka ku kyautata alwala"
Abu Dawud ne ya rawaito shi
25
Na shaida babu abin bauta na gaskiya sai Allah, Shi kaɗai wanda ba shi da abokin tarayya, kuma na shaida Annabi Muhammad BawanSa ne, kuma ManzonSa ne.
Muslim ne ya rawaito shi
26
Ya Allah Ka sanya ni a cikin masu tuba, kuma Ka sanya ni cikin masu son tsarkaka.
Al-Tirmizi ne ya rawaito shi
27
"Tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareka, na Shaida babu wani Ubangiji sai Kai, ina neman gafararKa, kuma ina tuba a gareKa"
Al-Nasa’i ne ya rawaito shi a cikin “Aikin yini da dare.”
YAYA ZAN YI SALLAH?
Salla tun daga Kabbara har zuwa Sallama
M
Sauti
1
Sautin Iƙamar Sallah
2
Sautin Iƙamar Sallah yana cigaba da gudana
Halarto da Niyya shi ne farkon abin da Mai Sallah zai fara yi, kuma bigirenta shi ne Zuciya
3
Sai mu fuskanci Alƙibla, idan ka kasance Liman ne, ko kai kaɗai kake sallar to ka sanya Sutura a gabanka
4
Ka yi Kabbara (wacce take nufin Allah shi ne mafi girma)
Kabbarar Harama da ita ake shiga Salla, kuma babu makawa sai an furta ta da Harshe
5
Kuma zamu ɗaga Hannayenmunmu zuwa daidai kafaɗunmu, muna masu fuskantar da tafukan Hannayenmu zuwa Alƙibla
Ko
Kuma Zamu ɗaga su zuwa daidai Kunnuwa irin dai yadda Muka yi
6
Sai mu sanya hannayen a ƙirji bayan Kabbarar, ko a ƙasan ƙirji, a sama da cibiya, ko a karkashin cibiya, duk hakan daidai ne.
Zamu sanya hannun dama a kan Tafin Hannun Hagu
Ko kuma hannunmu na dama ya riƙe bayan Hannunsa na Hagu
Ko kuma mu riƙe Sangalalin Hannun Hagu, da hannun na dama
7
"Ya Ubangiji na ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafadarta, Ya Ubangijina ka tsaftace ni daga zunubaina kamar yadda kake tsaftace farin tufa daga datti. Ya Ubangijina ka wanke ni daga zunubaina da ƙankara, da ruwa, da raɓa"
Muna yin Addu'a da Addu'ar buxewa bayan kabbarar Harama kuma kafin fara Karatu, kuma Haqiqa Wasu Addu'o'in buxe Sallah wasu da yawa an rawaito su, kuma yana daga cikin Sunnah a Nau'anta su
8
Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin nesantawa daga Rahama
Bayan Addu'ar buɗe Salla sai A'uziyya ta biyo baya, sannan a Karanta Fatiha
9
Cikin tsoron Allah, da kuma nutsuwa, za a karatun Aya bayan Aya
10
Amin
Fadin ta sunna ne ga mai salla, ko da kuwa shi limami ne, ko mamu ne, ko shi kaɗai yake yin sallar, kuma ita ba aya ba ce daga cikin Fatiha, sai dai ita ɗin addu’a ce wacce take nufin: Ya Allah, ka amsa mana.
11
Bayan Fatiha, sai mu karanta gwarbwadon abin da ya sauwaƙa na Alƙur'ani, ko dai sura gabaɗayanta, ko kuma wani sashe nata, kuma bayan mun kammala karatun, sai mu ɗan yi shiru kafin mu tafi zuwa ruku'u.
12
sai Ka yi Kabbara
Kabbarar ciruwa daga tsayuwa zuwa Ruku'u.
Wannan shi ne wuri na biyu a cikin Sallar da Annabi mai tsira da amincin Allah, yake ɗaga hannayensa. Sunna ne mu ɗaga hannayenmu zuwa saitin kafaɗu ko kunnuwa.
13
Sai mu sanya Tafukan Hannaye a kan gwiwoyi, mu ware yatsunmu mu ɗora a kai, kamar muna masu damƙar guiwar.
Har sai mun nutsu a cikin ruku'u, muna masu nisanta hannayenmu daga barin kuiɓunanmu, kuma kada mu bayyana gefen kuncinmu ta hanyar karkatar da kai zuwa wani ɓangaren namu.
14
Zamu miƙar da bayanmu, kada mu yi doro da shi, kuma mu mikar da kanm, ya yi daidai da bayanmu, kada mu ɗaga shi, kuma kada m sunkuyar da shi.
15
(Subhana Rabbiyal Azim)
Zamu maimaita tasbihin sau uku, shi ne mafi karancin kamala, amma idan aka yi tasbihin sau ɗaya ya wadatar, kuma zamu iya ƙarawa idan muna so, kuma zamu iya yin wani tasbihin daga a cikin Tsbihan da suka zo a Sunna
16
Zikiran da ake yi a cikin ruku'u suna da yawa.
17
Sami'allahu li man hamidah
Muna fadan hakan ne yayin da muka ɗago daga ruku'u, idan muna Salla mu kaɗai, ko kuma a dayan limami.
18
Sai mu ɗaga Hannayenmu daidai kafaɗu ko daidai kunnuwa, wannan shi ne guri na uku da da aka rawaito cewa ana ɗaga hannaye
19
Sai mu daidaita a tsaye, mna mas faɗin:
Rabbana wa lakal hamd
20
Bayan mun tashi daga Ruku'u, muna da damar mu saki hannayenmu, ko mu mayar da su kan ƙirji.
21
Sunna ne a tsawaita tsayuwa bayan ruku'u, kuma a samu nutsuwa a cikinta.
22
Allah Akbar
Daga nan sai mu yi ƙasa muna masu yin kabbarar ciruwa daga tsayawa zuwa sujada.
Zamu iya ajiye Hannaye kafin gwiwoyi, ko gwiwoyi kafin hannaye, dk wanda ya fiyi mana sauƙi.
23
Kuma dole ne mu yi sujjada a kan Gaɓɓai Bakwai; Kamar yadda Manzon Allah, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya koyar da mu:
Goshi tare da Hanci, Da tafukan Hannaye, ƙafufuwa, da gwiwoyi.
24
Zamu sanya qarshen yatsun ƙafa su fuskanci Alkibla, kuma mu kafe ƙafafun.
Zamu buɗe cinyoyinmu, mu kuma raba cikinmu da cinyoyin.
Mu ɗage gwiwar hannunmu ta bar ƙasa, kuma ta yi nesa da kuyaɓanmu, sai dai idan muna yin Salla cikin jam'i ne kuma muna tsoron kada mu cutar da wadanda suke tare da mu.
Kuma mu sanya tafin hannunmu daidai kafaɗu, ko daidai kunnuwa.
25
"Subhana Rabbiyal A'ala"
Zamu maimaita tasbihin sau uku, shi ne mafi karancin kamala, amma idan aka yi tasbihin sau ɗaya ya wadatar, kuma zamu iya ƙarawa idan muna so, kuma zamu iya yin wani tasbihin daga a cikin Tsbihan da suka zo a Sunna, sannan kuma zamu iya roƙon abin da muke so na alherin Duniya da Lahira.
26
Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Lokacin da bawa ya fi kusa da Ubangijinsa shi ne a yayin da yake sujada, sai ku yawaita yin Addua"
27
Allahu Akbar
Zamu ɗago da kawunanmu daga Sujjada muna masu kabbara.
Zamu shimfiɗa ƙafar hagu, mu zauna a kanta, kuma mu kafe ta dama, yatsunta suna masu fuskantar Alƙibla.
Ko
Mu kafe duka ƙafafun biyu sai mu zauna a kan dugadugansu.
mu Shinfiɗa tsintsiyar Hannayenmu; Hannun dama a cinyar dama, Hagu kuma a cinyar Hagu.
28
Rabbig fir li
Zamuikirin ne a tsakanin sujjadu biyu, a sanda mka samu nutsuwa.
29
Allahu Akbar
Sa mu yi kabbara m tafi sujjuda ta biyu, wacce ta yi kama da ta farko ta fuskar siffa da kuma abin da ake faɗa a cikita.
30
Allahu Akbar
Mu zo raka'ah ta biyu, kamar yadda muka yi raka'ah ta farko:
Inda hannaye ske, da karatun Fatiha, da aya ko ayoyi daga Alqur’ani.
Sannan Mu yi Ruku'u
Allahu Akbar
Sai mu tashi
Sami'allahu li man hamidah
Sannan mu tafi zuwa Sujada
Allahu Akbar
Sai Mu yi Sujjada biyu, sannan Mu yi zaman Tahiya
Allahu Akbar
Allahu Akbar
Allahu Akbar
31
Bayan mun gama raka’a ta biyu, za mu yi zaman Tahiya, kuma za mu zauna muna masu shimfiɗa ƙafarmu
32
Zaman shimfiɗa ƙafa ana yin shi ne yayin sallah Mai Raka'a biyu Kamar sallar Asuba, juma'a da Idi biyu, kuma haka ake yi a Tahiyar Farko na sallah Mai Raka'a uku da hudu, da kuma zaman tsakanin sujjadu Biyu.
33
Babu laifi ga mutumin da ba zai iya zama a kan Kafafuwansa ba saboda girman jikinsa, ko saboda ciwon ƙafafunsa, ko akasin haka, ya yi irin zaman da zai iya.
34
A Tahiya, zamu ɗora hannun dama a Cinyarsa ta Dama, kuma ya dunƙule dukkan yatsun, amma ban da dan manuniya, ita miƙar da ita ake yi.
35
Ko kuma mun yi da'ira da babban yatsan Hannu tare da na tsakiya, sai mu yi nuni da manuniya.
36
Shi kuma hannun hagu, ko dai mu sanya shi a cinyar hagu, ko kuma mu riƙe Gwiwa da shi.
Ana so a dinga kallon manuniyar Hannun Dama yayin da ake yin Tahiya
37
“Daɗaɗan gaisuwa sun tabbata ga Allah, Da Salatai da kuma Daɗaɗan Amincin Allah su tabbata a gareka ya kai wannan Annabi da Rahamarsa da Albarkarsa, Amincin Allah a garemu da Bayin Allah Managarta, Na shaida babu abun bautawa na Gaskiya sai Allah kuma na Shaida cewa Annabi Muhammad Bawansa ne kuma Manzonsa ne”,
Tahiyar farko kawai zamu karanta idan anyi sallah Mai Raka'a uku ce ko Hudu.
Amma idan Sallar ta kasance Mai Raka'a biyu ce, kamar Sallar Asuba, Sallar Juma'a, ko Idi biyu, to sai mu cika tashahhud din ta hanyar karanta Salatin Ibrahimi.
"Allah kayi Salati ga Annabi Muhammad da Alayan Muhammad kamar yadda kayi Salati ga Annabi Ibrahim da kuma Alayan Annabi Ibrahim lallai kai ne Abun godewa kuma mai girma, Allah ka yi Albarka ga Annabi Muhammad da Alayan Annabi Mugammad kamar yadda kayi Albarka ga Annabi Ibrahim da Alayan Annabi Ibrahim lallai kai ne abin yabo kuma Maxaukaki",
38
“Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah”,
“Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah”,
Sallamar tana zuwa ne bayan kammala Tahiyar karshe, da kuma yin addu'o'in da aka ambata a Sunnar Annabi Amma ana yin wannan ne a cikin sallah mai raka'a biyu.
39
Muna jiyo Kabbara a hankali
Amma idan salla ta kasance Mai Raka'a uku ce, kamar Magariba, ko mai hudu, kamar Azahar, la'asar da Isha.
40
To bayan Tahiyar ta farko, zamu mike mu ƙaro raka’a ɗaya idan Sallar Magriba ce, ko kuma raka’a biyu idan Sallar La'asar ce, ko Isha, sai mu karanta Fatiha, tare da dukkan bayanan da suka gabata. cikin ruku'u, da Sujada, da tsayuwa da Zama.
41
Allahu Akbar
42
Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana zaman Tawarruk a tahiyar ƙarshe a kowace Sallah mai tahiya biyu.
43
Zaman Tawaruƙ a Tahiyar ta ƙarshe kawai ake yin shi a Salloli masu Raka'o'i uku da hudu, kuma yana da siffofi sama da ɗaya:
44
A shimfiɗa kafar Hagu, a kafe ta dama, sai a fito da su ta ɓangaren dama, ka ɗora mazaunai a ƙasa
Ko
A Shimfiɗe duk ƙafafuwan biyu a ƙasa, sai a futo da su ta bangaren Dama
Ko
Ya shimfiɗa ƙafar Dama, kuma ya shigar da ta Hagu a tsakanin Cinyarsa da ƙaurinsa na Dama
45
A Zaman Tahiyar ƙarshe, Zamu yi Tahiya, sannan mu biyo da Salati ga Annabi (S.A.W)
46
Kafin Sallama, bayan an gama Tahiya ta karshe; to ana so ya nemi tsarin Allah daga abubuwa guda huɗu: Azabar Jahannama, da kuma Azabar Kabari, da kuma Fitinar Rayayyu da ta Matuwa, da kuma Sharrin Dujal
Kuma zamu iya roƙon duk Alkhairan Duniya da na Lahira
47
“Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah”,
“Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah”,
Ba a idar da Sallah har sai sai bayan an yi Sallama
48
Da zarar mun yi sallama ne zai zamanto mun gama Sallarmu
Inan neman Gafarar Allah, Inan neman Gafarar Allah, Inan neman Gafarar Allah
49
Yana daga cikin Sunna Mai Sallah idan ya yi Sallama sai ya yi Istigfari sau Uku, sannan ya Ambaci Allah Maɗaukakin Sarki da abin da ya zo na Zikiriri daga Manzon Allah (S.A.W)
M
Abin da aka Rubuta a kan Allon kallo
1
kai Liman ne ko kai kaɗai ne
2
Kabbarar Harama
3
Zamu ɗaga Hannayenmu zuwa daidai Kafaɗu
4
Ko daidai da Kunnuwa, irin Hanyar dai da aka sani
5
Zamu ɗora Hannayen a kan ƙirji
6
ko saman Cibiya
7
ko Qasan Cibiya
8
Hannun Dama zamu dora shi a kan Tafin Hannun Hagu
9
Ko kuma mu riqe Sangalalin Hannun Hagu da hannnu damar
10
Addu'ar buɗe Salla
11
"Ya Ubangijina ka nesanta tsakanina da kurakuraina kamar yadda ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafadarta Ya Ubangijina ka tsaftace ni daga zunubaina kamar yadda kake tsaftace farar tufa daga datti. Ya Ubangiji na ka wanke ni daga zunubaina da ƙanƙara, da ruwa da kuma raɓa" Muslim ne ya rawaito shi
12
Nau'anta su yana daga cikin Sunna
13
A'uziyya
14
Ina neman tsarin Allah daga Shaidan abin nisantawa daga Rahama
15
Fatiha
16
1. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai. 3. Mai rahama Mai jin ƙai. 4. Mamallakin ranar sakamako. 5. Kai kaɗai muke bautata wa, kuma Kai kaɗai muke neman taimakonka. 6. Ka shiryar da mu tafarkin nan madaidaici. 7. Tafarkin waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi fushi da su ba, ba kuma ɓatattu ba.
17
Amin
18
Addu'a ce ma'anarta shi ne: Ya Ubangiji ka Amsa
19
Zamu karanta abin da ya sauwaƙa na Alƙr'ani
20
Ruku'i
21
Allah akbar
22
Baya yana daidai ce ba tare da an yi doro da shi ba
23
Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Maigirma
24
Daga cikin Zikiran cikin Ruku'a da aka rawaito akwai:
25
"Subbuhun Ƙuddusun Rabbul Mala'ikati war Ruh"
26
"Subhanakal lahumma wa bi hamdika, Allahmmag fir li"
M
Sami'allahu li man hamidah
28
Rabbana wa lakal hamd, hamdan kasiran ɗayyiban mubarakan fihi
29
Muna sakin Hannayenmu
30
Ko mu ɗora su a ƙirji
31
Sujjada
32
Goshi da Hanci
33
Tafukan hannaye
34
Guiwoyi biyu
35
Da kuma ƙafafu biyu
36
Subhana Rabbiyal A'ala...
37
"Lokacin da bawa ya fi kusa da Ubangijinsa shi ne a yayin da yake sujjada, sai ku yawaita yin Addua" Muslim ne ya rawaito shi
38
Zaman Shimfiɗa ƙafa a ƙasa
39
Zaman a kan dunduniyar ƙafafu
40
Rabbig fir li (Sau uku)
41
"Allahummag fir li, war ham ni, wajbir ni, wahdi ni, warzuƙ ni"
42
Asuba
43
Juma'a
44
Idi guda Biyu
45
Azahar
46
La'asar
47
Magariba
48
Isha'i
49
“Daɗaɗan gaisuwa sun tabbata ga Allah, Da Salatai da kuma Daɗaɗan Amincin Allah su tabbata a gareka ya kai wannan Annabi da Rahamarsa da Albarkarsa, Amincin Allah a garemu da Bayin Allah Managarta, Na shaida babu abun bautawa na Gaskiya sai Allah kuma na Shaida cewa Annabi Muhammad Bawansa ne kuma Manzonsa ne”,
50
"Allah ka yi Salati ga Annabi Muhammad da Alayan Muhammad kamar yadda ka yi Salati ga Annabi Ibrahim, da kuma Alayan Annabi Ibrahim, lallai kai ne Abin godiya, kuma mai girma, Allah ka yi Albarka ga Annabi Muhammad da Alayan Annabi Mugammad kamar yadda ka yi Albarka ga Annabi Ibrahim, da Alayan Annabi Ibrahim, lallai kai ne abin yabo, kuma Maɗaukaki",
51
Azahar - La'asar - Magriba - Isha'i
52
Asuba -Jumu'a-Idi guda biyu
53
"Allah ka yi Salati ga Annabi Muhammad da Alayan Muhammad kamar yadda ka yi Salati ga Annabi Ibrahim, da kuma Alayan Annabi Ibrahim, lallai kai ne Abin godiya, kuma mai girma, Allah ka yi Albarka ga Annabi Muhammad da Alayan Annabi Mugammad kamar yadda ka yi Albarka ga Annabi Ibrahim, da Alayan Annabi Ibrahim, lallai kai ne abin yabo, kuma Maɗaukaki",
54
“Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah”,
55
"Kuma idan ya zauna a Raka'ar ƙarshe, sai ya yo gaba da ƙafarsa ta hagu, kuma ya kafe ɗayar, kuma ya zauna kan Mazaunansa" Bukhari ne ya rawaito sho
56
Zaman Tawarruk
57
“Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga Azabar Wutar Jahannama, da kuma Azabar kabari, da Kuma Fitinar Rayuwa da ta Mutuwa, da kuma Sharrin Fitinar Dujal" Muslim ne ya rawito shi
58
"Ya Allah, na zalunci kaina da yawa, kuma babu mai gafarta zunubai sai Kai, ka gafarta mini da wata irin gafara daga gare Ka, kuma ka yi mini rahama, lallai ne Kai Mai gafara ne, Mai jin ƙai." Bukhari ne ya rawaito.
59
Astagfirullah (Sau uku)
60
An karɓo daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi- daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi ya ce: “Farkon abin da za a fara yi wa Bawa hisabi a kansa a ranar tashin ƙiyama daga cikin ayyukansa shi ne Sallarsa.Idan ta yi kyau, to ya rabauta kuma ya yi nasara, idan kma ta ɓaci, to ya taɓe kuma ya yi Asara. Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi