فضائل وآداب المسجد النبوي
FALALA DA LADUBBAN MASALLACIN ANNABI DA HUKUNCE-HUKUNCEN ZIYARAR ƘABARIN ANNABI - TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI - DA KABURBURAN SAHABBANSA BIYU - ALLAH YA YARDA DA SU -
FALALA DA LADUBBAN MASALLACIN ANNABI DA HUKUNCE-HUKUNCEN ZIYARAR ƘABARIN ANNABI - TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI - DA KABURBURAN SAHABBANSA BIYU - ALLAH YA YARDA DA SU -
Wallafar
Kwamitin ilimi a ƙarƙashin shugabancin harkokin Addini na Masallacin Harami da Masallacin Annabi.
1447 Bayan Hijira
Gabatarwa
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga wanda aka aiko shi rahama ga talikai, da alayensa da sahabbansa da wanda ya bi sunnarsa, ya kuma nemi shiryuwa da shiriyarsa har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:
Wannan wani taƙaitaccen saƙo ne, wanda ya ƙunshi mafi muhimmancin falalolin Masallacin Annabi, da ladubban ziyartarsa, da ladubban ziyartar ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da na sahabbansa guda biyu. Mun tattaro shi ne domin masu ziyartar Masallacin Annabi, domin su kasance cikin sani da fahimta game da falalar masallacin Annabin al'umma - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da ladubban ziyartarsa da yin sallah a cikinsa, muna roƙon Allah Mai karamci Mai baiwa Ya amfanar da shi, kuma Ya sanya shi mai kyau, kuma saboda Allah ne kaɗai; lallai Shi ne Mafi alherin wanda ake roƙa, kuma Mafi karamcin wanda ake fata.
Kwamitin ilimi
Na Farko: Falalar Masallacin Annabi
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma Ubangijinka Yanã halittar abin da Yake so kuma Yake zãɓi. Zãɓi bai kasance a gare su ba. Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma (Allah) Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka68} [al-Kasas: 68], Kuma Allah Ya zaɓi wannan gurin domin ya zama masallaci ga Annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma ya keɓance shi da falaloli masu yawa, daga ciki:
Yana ɗaya daga cikin masallatai uku waɗanda ake shirya tafiya zuwa gare su:
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: «Ba'a ɗaura sirdi, sai zuwa masallatai uku: Wannan masallacin nawa, da Masallaci mai alfarma, da masallacin al-Aƙsa» [1]. [1] Bukhari ne ya fitar da shi, a lamba ta (1189), da Muslim a lamba ta (1397), kuma lafazin nasa ne.
Lallai sallah a cikinsa ita ce mafi alheri daga sallah dubu a cikin waninsa sai dai Masallaci mai alfarma:
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Sallah a cikin masallacina wannan (ita ce) mafi alheri daga sallah dubu a cikin waninsa, sai dai masallaci mai alfarma ([2])» [2] Bukhari ne ya fitar da shi, a lamba ta (1190), da Muslim a lamba ta (1395), kuma lafazin na Bukhari ne.
Shi ne Masallacin da aka gina harsãshinsa a kan taƙawa tun farkon yini:
Daga Abu Sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na shiga wurin Manzon Allah ﷺ a gidan ɗaya daga cikin matansa, sai na ce: 'Ya Manzon Allah, wanne ne daga cikin masallatai biyu wanda aka gina shi a kan tsoron Allah?' Sai ya ɗauki cikon tafin hannu na tsakuwa, ya buga ƙasa da shi, sannan ya ce: «Shi ne masallacinku wannan» na Masallacin Madina[3]. [3] Muslim ne ya fitar da shi a lamba ta (1398).
Cewa ladan mai neman ilimi a cikinsa, kamar ladan mujahidi ne a tafarkin Allah:
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Duk wanda ya zo Masallacina wannan, bai zo ba sai don alherin da zai koye shi ko zai koyar da shi, to shi yana da matsayin mai yaƙi ne a tafarkin Allah, kuma duk wanda ya je don wanin hakan, to shi yana matsayin mutumin da yake kallon kayan waninsa»[4]. [4] Ibnu Majah ne ya fitar da shi a lamba ta (227), da ingantaccen isnadi.
Cewa a cikinsa akwai Raudah maɗaukakiya:
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -, daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Tsakanin gidana da mumbari na, dausayi ne daga cikin dausayan aljanna, kuma mumbari na yana kan tafkina ([5])» [5] Anhaɗu a kansa: Bukhari, a lamba ta: (1195), Muslim, a lamba ta: (1390).
Na biyu: Son ziyartar Masallacin Annabi maɗaukaki
Saboda waɗannan falalolin mai yawa da wasunsu, an so ziyartar Masallacin Annabi don yin sallah a cikinsa da kuma ibada.
- An sunnantawa mai Hajji da waninsa ziyartar Masallacin Annabi kafin Hajji ko bayansa, kuma wannan ziyarar ba ta daga cikin sharuɗɗan Hajji ko rukunansa ko kuma wajibansa ba, kuma ba ta da wata alaƙa da shi.
Kuma ba'a shar'anta wa ziyarar masallacin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wani kebantaccen adadi na salloli, ko zama na wani kebantaccen lokaci a Madina ba; a'a, ziyarar tana tabbata da sallah guda ɗaya, koda kuwa ta kasance ta farilla ce ko nafila. Sai dai, duk sanda adadin sallolin ya ƙaru a cikinsa, to ladan ma zai ƙaru.
Kuma an so wa mai ziyarar Masallacin Annabi, ya yi dukkan sallolin farilla a cikinsa, da kuma nafilfili; saboda lallai sallah a cikinsa ta fi falala akan sallah sau dubu a waninsa sai fa Masallacin Harami.
NA UKU: LADUBBAN ZIYARAR MASALLACIN ANNABI
Idan musulmi ya zo Masallacin Annabi, to mustahabbi ne a gare shi ya siffantu da ladubban shari'a waɗanda suka shafi masallatai gaba ɗaya, da kuma Masallacin Annabi musamman, kuma su ne:
Ya zo masallaci da nutsuwa, da kamala, da tsarki, da shiga mai kyau, da ƙamshi mai daɗi. An karbo daga Abu Huraira - Allah Ya yarda dashi -, cewa Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata agareshi- ya ce: «Idan an tada sallah, to kada ku zo mata kuna gaggawa, ku zo mata cikin natsuwa, ku sallaci abin da kuka riska, kuma ku cika wanda ya wuce ku, domin lalle ɗayanku idan ya nufi sallah to yana cikin sallah ne»[6]، Daga Abu Sa'id al-Khudiri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanka ranar juma'a wajibi ne akan kowanne baligi, kuma ya yi asuwaki, ya shafa tirare in ya samu"[7]," Amma mace ita kam idan ta zo masallaci, to yana wajaba a kanta ta kasance mai suturtuwa da hijabinta, kuma ba ya halatta gareta ta shafa tirare, saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: «Idan ɗayarku ta halarci masallaci, to kada ta shafa turare»[8]. [6] Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (636), da Muslim a lamba ta (602). Anhaɗu a kansa: Bukhari, a lamba ta: (846), Muslim kuma a lamba ta: (858), kuma mai mafarki shi ne wanda ya balaga. [8] Muslim ne ya fitar da shi a lamba ta (443).
An so ga mai ziyara ya gabatar da ƙafarsa ta dama a lokacin shiga masallacin Annabi, da kuma zuwa da addu'ar shiga masallaci, to an so ga mai zaiyara ya gabatar da ƙafarsa ta dama a lokacin shiga masallacin Annabi kamar sauran masallatai, kuma yayi addu'a da wannan addu'ar: «Da sunan Allah, tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah, ya Allah Ka gafarta min zunubaina kuma Ka buɗe min ƙofofin rahmarKa»[9]، Hakanan kuma ya:ce «Ina neman tsarin Allah Mai girma da kuma fuskarSa Mai karamci da ikonSa dadaɗɗe daga Shaiɗan abin korewa (daga rahamar Allah)»[10]. [9] Ibnu Majah ne ya fitar da shi a lamba ta (771), da ingantaccen sanadi. [10] Abu Dawud ne ya fitar da shi, a lamba ta (466), da isnadi mai inganci.
Yin gaisuwar masallaci (Tahiyyatul Masjid): An sunnanta ga wanda ya shiga Masallacin Annabi don yin sallah a cikinsa, ya yi sallah raka'a biyu gaisuwar masallaci kafin ya zauna, daga Abu Katadata al-Harith ibn Rib'i al-Ansari - Allah Ya yarda da shi -, ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Idan ɗayanku ya shiga masallaci, to kada ya zauna har sai ya yi sallah raka'o'i biyu»[11]. [11]An haɗu a kansa, Bukhari a lamba ta: (1171), da Muslim a lamba ta: (714).
Kwaɗayin yin sallah a sahunan farko; dan abinda ke cikinsu na falala mai girma, kuma hakan ba ya samuwa sai da gaggawa zuwa gare ta, saboda hadisin Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi -: cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Da mutane sun san abin da ke cikin kiran sallah da sahun farko, sannan ba za su samu ba sai sun yi ƙuri'a a kan sa; to, da sunyi ƙuri'ar»[12]، kuma saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ga sahabbansa - Allah Ya yarda da su -: «Ku yo gaba, ku yi koyi da ni kuma waɗanda ke bayanku su yi koyi da ku, mutane ba za su gushe ba suna jinkiri, har sai Allah Ya jinkirta su»[13]. [12] Anhaɗu a kansa: Bukhari, a lamba ta: (615), da Muslim kuma a lamba ta: (437). [13] Muslim ne ya fitar da shi a lamba ta (438).
Amman mata, to mafi alheri garesu shi ne yin sallah a sahun baya, da nisantar maza, saboda hadisin Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Mafi alherin sahun maza shi ne na farkon su, kuma mafi sharrin su shi ne na ƙarshen su, mafi alherin sahun mata shi ne na ƙarshen su, kuma mafi sharrin su shi ne na farkon su"[14]," Amma idan suka yi sallah su kaɗai, ko kuma akwai shamaki a tsakaninsu da maza, kamar yadda lamarin yake a Masallacin Annabi, to mafi alherin sahunsu shi ne na farkonsu; saboda gushewar illar hakan. [14] Muslim ne ya fitar da shi a lamba ta (440).
Sallah a bayan liman, da gargaɗi akan wucewa gabansa; saboda hadisin Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Kaɗai an sanya limami ne dan a yi koyi da shi»[15]. [15] Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta (722), da Muslim a lamba ta (417).
Bai halatta ga mai sallah ya shige gaban liman ba sai dai a hali na lalura da cikar masallaci da masallata, ta yadda ba zai samu wurin sallah ba sai a gaban liman.
Kula da cike wurare a tsakanin sahu da daidaita su, amma tare da kiyaye matsa wa mutane da takura musu, da tsallake wuyoyinsu, da wucewa ta gaban masallata; domin hakan yana jefa mutum cikin zunubi.
Sallah a cikin Raudah mai daraja ga wanda hakan ya sawwaƙa a gare shi; saboda hadisin Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi -, daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Tsakanin gidana da mumbari na, dausayi ne daga cikin dausayan aljanna, kuma mumbari na yana kan tafki na ([16])» [16] Anhaɗu a kansa: Bukhari, a lamba ta: (1195), Muslim, a lamba ta: (1390).
Kuma babu wata keɓantacciyar falala da ta zo game da sallah a cikin Raudah; sai dai ya tabbata cewa ita dausayi ce daga cikin dausayan Aljanna -kamar yadda hadisin Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi - wanda ya gabata ya nuna- kuma ibadu suna samun fifiko saboda falalar lokacinsu da wurinsu.
* Mai ziyara zai zaɓi lokutan da suka dace don yin sallah a Raudha, kuma ya kintaci lokutan da cinkoso yake raguwa, saboda bai halatta ya cunkushe 'yan'uwansa musulmai ba, ko ya tsallake mutane, ko ya tsallaka sallar masu sallah domin yin sallah a cikinta, domin kuwa sallah a Raudha nafila ce, don haka ba a riskarta ta hanyar aikata abin da aka haramta. Kamar yadda kuma mai ziyara zai kiyaye bin dokoki da ƙa'idojin da aka tsara na shiga Raudha, da zaɓar lokutan da suka dace, da kuma bada haɗin kai ga masu gudanarwa da ke kan aikin tsara shigar masu ziyara cikinta.
Ribatar lokuta da yawaita ayyuka na gari waɗanda ke kusantar da shi ga Mahaliccinsa, kamar Sallah, da karatun Alƙur'ani, da zikiri, da addu'a, da halartar majalisan zikiri, da darussan ilimi, da wuraren koyar da Alƙur'ani mai girma, da sauransu.
Girmama Littafin Allah mai girma da ɗaukaka da kiyaye shi daga wasa da takardunsa, da yin rubutu a kansa, ko kuma wulaƙanta shi da ajiye takalmi a gefensa, ko sanya shi a ƙasa da makamancin haka, saboda faɗinsa - Maɗaukakin sarki -: {Wancan ne. Kuma wanda ya girmama ibãdõdin Allah, to, lalle ne ita (girmamãwar) tanã daga ayyukan zukãta na ibãda32} [al-Hajj: 32].
Runtse idanu daga abinda Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya haramta: To yana wajaba akan mai ziyartar Masallacin Annabi ya runtse idonsa daga abinda bai halatta a gare shi ya kalla ba, kuma ya sani girman aikata zunubi a cikin waɗannan wurare, da abinda yake biyo baya akansa na uƙubobi, domin lallai saɓo yana yin girma a yawa da yanayi da girman zamani da wuri, kuma haka nan ayyuka na biyayya, kuma mace musulma ta dage akan lizimtar hijabi na shari'a, da rashin bayyanar da ado domin kada ta fitini maza, domin lallai wannan laifinsa mai girma ne.
Kiyayewa daga shagaltuwa da ɗƙɓaukar hotuna ko kallon hotuna da bidiyoyi a cikin waya, kuma lamarin ya fi tsanani da haɗari idan waɗannan hotuna da bidiyoyin sun kasance ababen haramtawa ne.
Tsaftace Masallacin Annabi daga dukkan abinda bai kamata da shi ba, na rigima, da ɗaga murya, da cigiyar abinda ya ɓata, da sayarwa, da makamantan haka na al'amuran da basu kamata ba a cikinsa ko a cikin sauran masallatai; saboda hadisin Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Idan kuka ga wani yana sayarwa ko yana saye a cikin masallaci, to sai ku ce: Kada Allah Ya baka ribar kasuwancinka, kuma idan kun ga wani yana cigiyar ɓatan abunsa, to ku ce: kada Allah a dawo maka da shi»[17]. [17] Tirmizi ya fitar da shi a lamba ta (1321) da Ibn Khuzaimah a lamba ta (1305), da ingantaccen sanadi.
Kwaɗaitarwa akan tsaftar jiki, da kiyayewa daga wari mara kyau kamar tafarnuwa da albasa da hayaƙi da gumi, da makamantansu daga abin da ke cutar da 'yan'uwansa masallata; saboda hadisin Jabir ibn Abdullahi - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Lallai Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Wanda ya ci tafarnuwa ko albasa, to ya yi nesa damu - ko cewa ya yi: Ya yi nesa da masallacinmu - ya zauna a gidansa"[18]. [18] Bukhari ne ya fitar da shi a lamba ta: (7359), da Muslim a lamba ta: (564).
Himmantuwa da tsaftar Masallacin Annabi da rashin zubar da shara a cikin Masallaci da kuma filinsa, kamar ragowar abinci da shimfiɗun buɗa-baki musamman a watan Ramadan, ko kuma tofar da miyau a hanyoyi da filaye, da makamancin haka.
Ka nisanci sallah a hanyoyin wucewa da bakunan ƙofofi da wuraren cunkoso, saboda abinda hakan ke haifarwa na ɓarna, da toshe hanyoyi, da kuma cutar da musulmi.
Sallar maza da mata a wuraren da aka keɓewa kowannensu, a cikin Masallacin Annabi ko a filayensa, kada namiji ya yi sallah a gefen mace, haka nan mace a gefen namiji, kuma a kiyayi yin sallah a gaban liman gwargwadon iyawa.
Gabatar da ƙafar hagu yayin fita daga masallaci, kuma in zai fita ya ce: «Ya Allah ni ina roƙonKa daga falalarKa»[19]، Ko kuma ya yi salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: «Ya Ubangiji Ka gafarta min zunubaina, kuma Ka buɗe min ƙofofin falalarKa»[20]. [19] Muslim ne ya fitar da shi da lamba (713). [20] Tirmizi ya fitar da shi a lamba ta: (314), da sanadi sahīhi.
Na huɗu: Hukunce-hukunce da Ladubban ziyarar ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da ƙaburburan sahabbansa biyu - Allah ya yarda da su -
* An so ziyartar ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da ƙaburburan sahabbansa biyu: Abubakar da Umar - Allah Ya yarda da su -, ga mutanen Madina da wanda ya zo mata baƙo mai ziyara; saboda gamewar dalilai da suke nuna shar'antuwar ziyarar ƙaburbura, daga cikinsu akwai faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Na haneku daga ziyartar ƙaburbura, to ku ziyarcesu»[21]. [21] Muslim ne ya fitar da shi da lamba (977).
Haƙiƙa faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayi a kan falalar yin sallama ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bayan wafatinsa: «Babu wani mutum da zai yi mini sallama, face Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya dawo mini da raina har sai na mayar masa da sallamar»[22]. [22] Ahmad ne ya fitar da shi, a Musnadinsa, lamba ta: (10815), da isnadi kyakkyawa.
* Kuma ba'a shar'antawa mata ziyartar ƙabarinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba, ko ƙabarin waninsa cikin musulmai, domin ziyarar ƙaburbura an shar'anta ta ne a haƙƙin maza, amma mata an hana su ziyartar ƙaburbura, an rawaito daga Ibn Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: «Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya la'anci mata maziyarta ƙaburbura, da masu riƙon su masallatai da fitilu»[23], Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: «Lalle Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya la'anci mata masu yawan ziyarar ƙaburbura»[24]. [23] Abu Dawud ya fitar da shi, a lamba ta (3236), da Tirmizi a lamba ta (320), da Nasa'i a lamba ta (2043). [24] Tirmizi ya fitar da shi a lamba ta (1056), da Ibn Majah a lamba ta (1576), da isnadi hasan.
* Ba ya halatta ɗaura sirdi dan ziyarar ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ta yadda zai yi niyya da tafiyarsa ziyarar ƙabarin kaɗai, sai dai ya yi niyya da tafiyarsa ziyarar masallaci da sallah a cikinsa, idan ya sauka a Madina sai aka shara'anta masa ziyarar ƙabarin, kamar yadda aka shara'antawa mazaunan Madina daga cikin mutanenta; saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Ba'a ɗaura sirdi, sai zuwa masallatai uku: wannan masallacin nawa, da Masallaci mai alfarma, da msallacin al-Aƙsa»[25]. [25] Bukhari ne ya fitar da shi, a lamba ta (1189), da Muslim a lamba ta (1397), kuma lafazin nasa ne.
LADUBBAN DA AKA SHAR'ANTA A WAJEN ZIYARAR ƘABARIN ANNABI - TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI - DA ƘABURBURAN SAHABBANSA BIYU - ALLAH YA YARDA DA SU -.
Mai ziyarar ya tsaya ta gaban ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sannan ya yi masa sallama - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da ladabi da ƙasa-ƙasa da murya, yana mai cewa: (Aminci ya tabbata a gareka ya Manzon Allah da rahamar Allah da albarkarSa), idan kuma ya ƙara a kan hakan ya ce: (Ina shaida cewa haƙiƙa ka isar da saƙo, ka bada amana, ka yiwa al'umma nasiha, ka yi yaƙi saboda Allah haƙiƙanin yaƙi) to babu laifi da hakan; domin cewa wannan gaba ɗayansa gaskiya ne.
Sannan ya yi taku kaɗan a hannunsa na dama domin ya fuskanci ƙabarin Abubakar al-Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi -, sai ya ce: «Amincin Allah ya tabbata a gareka ya Abubakar Siddiƙ, Amincin Allah ya tabbata a gareka ya halifan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, Allah Ya yarda da kai Ya kuma gamsar da kai, Ya kuma saka maka da alkhairi a madadin al'ummar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -».
Sannan ya yi taku kaɗan a hannunsa na dama dan ya zama yana mai fuskanci ƙabarin Umar bin Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -, sai ya ce: (Aminci ya tabbata a gareka ya Umar al-Faruƙ, Allah Ya yarda da kai kuma Ya gamsar da kai, kuma Ya saka maka da alkhairi a madadin al'ummar Annabi Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -).
Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su - ya kasance idan ya dawo daga tafiya, sai ya zo ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya ce: «Aminci ya tabbata a gareka ya Manzon Allah, aminci ya tabbata a gareka ya Abubakar, aminci ya tabbata agareka ya babana, sannan ya juya»[26]. [26] Baihaƙi ne ya fitar da shi a al-Sunanu al-Kubrah a lamba: (10271), da ingantaccen sanadi.
Ba a shafan ganuwar ƙabari ko shingensa, kuma ba a sumbantarsu:
Imam Malik - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: "Idan ya yi sallama ga Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai ya tsaya ya fuskanci ƙabarin; ba alƙibla ba, ya kusanto ya yi sallama, kuma ba zai taɓa ƙabarin da hannunsa ba" [27]." [27] al-Shafa ta Alƙali Iyadh (2/199).
Shugabannin Musulinci sun yi ittifaƙi a kan cewa kada ya shafi ƙabarin Annabi ﷺ da hannunsa, kuma kada ya sumbaceshi.
Kada ya tsawaita tsayuwa a kan ƙabari, saidai ya yi sallama sannan ya juya.
Imam Malik - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: "Bana gain cewa ya tsaya a warin ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana addu'a ba, sai dai ya yi sallama ya wuce" [28]. [28] al-Shafa (2/199).
Nafi’u - Allah Ya yarda da shi - ya ce: "Ibnu Umar ya kasance yana sallama ga ƙabarin.. Na gan shi sau ɗari da fiye da haka yana zuwa wurin ƙabarin sai ya ce: “Aminci ya tabbata ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. Aminci ya tabbata ga Abubakar, Aminci ya tabbata ga babana,” sannan ya juya.” [29]. [29] al-Ajurri ne ya fitar da shi a cikin littafin Shari'ah (5/2374) lamba ta (1853).
Amma abinda wasu daga cikin masu ziyara suke aikatawa, na ɗaga murya a ƙabarinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da tsawaita tsayuwa a nan, to hakan ya saɓawa shari'a.
Ba ya halatta a roƙi Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ko waninsa cikin halittu don janyo amfani ko kawar da wata cuta, ko neman biyan buƙata, ko yaye baƙin ciki, ko warkar da mara lafiya, ko neman ceto, ko tsira daga azaba, ko makamancin hakan na addu'o'i, domin lalle roƙon wanin Allah a kan abin da babu mai iko a kansa sai Allah, haramun ne kuma shirka ce babba, Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce: {Kuma Ubangijinku ya ce: "Ku kira Ni in karɓa muku. Lalle waɗannan da ke kangara daga barin bauta Mini, za su shiga Jahannama sunã ƙasƙantattu 60} [Gafir: 60], Kuma - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce: {Lalle ne waɗannan da kuke kira, baicin Allah, bãyĩ ne misãlanku: to, ku kirãye su, sa'an nan su karɓa muku, idan kun kasance mãsu gaskiya!194} [al-A'araf: 194], Allah - Maɗaukaki - Ya ce: {Kuma lalle ne wurãren sujada na Allah ne, saboda haka kada ku kira kõwa tãre da Allah (da su, a cikinsu18}. [al-Jinn: 18].
Kada ya roƙi Allah a gurin ƙabari, idan kuwa yayi nufin yin addu'a sai ya matsa daga ƙabarin, ya fuskanci alƙibla sannan yayi addu'a, kuma kada ya fuskanci ƙabari da addu'a.
Imam Malik - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: "Bana ganin cewa ya dace ya tsaya a ƙabarin Annabi ﷺ yana yin addu'a."
Ba'a shar’antawa mutanen Madina da kuma maziyarta daga wajenta yawan kai-kawo ga ƙabarin ba a lokacin shiga masallaci ko fita daga gare shi , domin ana jin tsoron hakan ya zama daga cikin mayar da ƙabarin wurin idi.
Kuma haƙiƙa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi hani game da haka sai ya ce: «Kada ku riƙi ƙabarina idi, kuma kada ku maida gidajanku ƙaburbura, a duk inda kuke ku yi mini salati, domin cewa salatinku zai isar mini»[30]. [30] Ahmad ya fitar da shi a Musnadinsa, a lamba ta (8804), da isnadi kyakkyawa.
Kuma ma'anar: “Kada ku riƙi ƙabarina idi” shi ne yawaita kai masa ziyara a wani lokaci ko hali keɓantacce, kamar keɓance ziyartarsa a kowacce rana ko mako ko wata. Ko kuma wani yanayi ayyananne da ake ziyartarsa saboda samuwar sa, an kuma ce: Wato kada ku mayar da shi wani mausimin da zaku dinga taruwa a cikinsa[31]. [31] Ka duba: Almufuradat na al-Raghib al-asfahani (594), da Sharhus Sudur bitahrim raf'il ƙubur na ash-Shaukani (16).
Imam Malik - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: "Kuma baya lazimtarwa wanda ya shiga masallaci kuma ya fita daga gareshi daga cikin mutanen Madina tsayawa a wajen ƙabarin ba, saidai wannan na baƙi ne"[32]. [32] al-Shifa na al-Qadi 'Iyad (2/204), al-Madkhal na Ibnu al-Hajj (1/262).
Kuma faɗinsa - Allah Yayi masa rahama -: "Wannan na baƙi ne kawai": yana nufin ziyara gaba ɗaya, ba maimaita ta ba a lokacin shiga da fita.
Kada ya tsaya a gaban ƙabari kamar siffar mai yin sallah, na ɗora ɗayan hannu akan ɗayan akan ƙirji ko ƙarƙashinsa; wannan siffar ta keɓanci sallah ne, kuma ita siffa ce ta Tawalu’u da ƙanƙanar da kai wacce ba ta halatta sai ga Allah - Maɗaukakin sarki -.
Ba'a fuskantar ƙabari daga nesa domin yin sallama ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kamar yanda wasu daga cikin mutane suke aikatawa; domin wannan sahabbai - Allah Ya yarda da su - ba su kasance suna aikata shi ba, haka kuma magabata na ƙwarai daga cikin Limamai huɗu da wasunsu.
Rashin halaccin fuskantar ƙabari maɗaukaki da addu'a ko da karatun Alƙur'ani da makamancin su daga kowace fuska, to wannan yana daga jinsin abinda ke kafin shi, na fararrun abubuwa, kuma ba ya halatta ga musulmi ya farar da abinda Allah bai yi izini da shi ba a cikin Addininsa, Haƙiƙa Imam Malik - Allah Ya yi masa rahama - ya yi musun ayyuka masu kama da wannan, kuma ya ce: "Babu abinda zai gyara ƙarshen wannan al'ummar sai abinda ya gyara farkonta". [33]Majmu'u fatawa Bin Baaz (110/ 16).
Rashin shagaltuwa da ɗaukar hoto da yaɗawa kai tsaye yayin yin sallama ga Annabi ﷺ.
Allah Ya Yi tsira da aminci ga Annabinmu Muhammadu da alayansa da sahabbansa Ya yi aminci amincewa.