Mafi Yawan Bincike
ADDU’A DAGA ALKUR’ANI DA HADISI
Wallafar Mabukaci zuwa ga Allah-madaukakin sarki (Kuma Allah yana da sunaye mafiya kyau, to ku roke shi da su, kuma ku bar wadanda suke yin Ilhadi a cikin sunayensa, da sannu za'a saka musu abinda suka kasance suna aikatawa){1}. Surar Al'aaraf, aya ta 180. Allah-Na farko-Na karshe-Mabayyani-Boyayye-madaukaki-MafI daukaka Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai.
These files are generated automatically from the book's text; their layout may differ from the printed edition.
ADDU’A DAGA ALKUR’ANI DA HADISI
Wallafar
Mabukaci zuwa ga Allah-madaukakin sarki
DR. Sa'id Bn Ali Bn Wahf Al-kahdani (Kuma Allah yana da sunaye mafiya kyau, to ku roke shi da su, kuma ku bar wadanda suke yin Ilhadi a cikin sunayensa, da sannu za'a saka musu abinda suka kasance suna aikatawa){1}. Surar Al'aaraf, aya ta 180.
Allah-Na farko-Na karshe-Mabayyani-Boyayye-madaukaki-MafI daukaka Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai.
Gabatarwa
Madaukaki a girmansa-Mai girman daraja-Abin girmamawa-Mai ji-Mai gani-Mai yawan sani
Masanin halittarsa-Wanda ya cancanci yabo-Mabuwayi-Mai iko-mai iko da komai-Mai karfi Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa muna neman taimakonSa, muna kuma neman gafararSa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu da munanan ayyukan mu, duk wanda Allah Ya shiryar da shi to babu mai batar da shi, wanda kuma Ya batar da shi to babu mai shiryar da shi, Ina kuma shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Shi da abokin tarayya. Ina kuma shaidawa lalle (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzanSa ne - tsiran Allah da amincin su tabbata a gare shi da iyalan sa da sahabban sa - da duk wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako , da aminci da amincewa mai yawa . To bayan haka:
Mai karfi-Mawadaci-Mai hikima-Mai hakuri-Mai rangwami-mai yawan gafara ga bayinsa-Mai gafara Wannan tsakure ne daga littafina ((Zikiri da Addu’a da yin magani da Tawaida daga Alkur'an da Sunnah)){2}. Na tsakuro bangaren Addu'a a cikinsa, dan amfani da shi ya saukaka, kuma na kara wasu addu'o'i da fa'idoji masu amfani a cikinsa in Allah madaukakin sarki Ya so. Ina rokon Allah - Mai girma da daukaka - da sunayanSa kyawawa da siffofinSa Madaukaka, Ya sanya shi domin Sa ne, lalle Shi Majibincin hakan ne kuma Mai iko ne akansa. 2. An buga asalin wannan littafin - godiya ta tabbata ga Allah - tare da fitar da hadisansa yalwatacciyar fitarwa a sifili na hudu, Zikirai (Garkuwar Musulmi) a sifili na daya da na biyu, Addu’a kuma a sifili na uku, magani da tofi kuma a sifili na hudu.
Mai karbar tuba-Mai tsinkayarwa-Mai shaida komai-Mai kiyayewa-Mai tausasawa-Makusanci-Mai amsawa Allah Ya yi tsira da aminci ga annabinmu Muhammad, da iyalansa da sahabbansa, da mabiyansa da kyautatawa zuwa ranar sakamako
Masoyi-Mai godiya-Mai yawan godiya-Shugaba-Abin nufi da bukata-Mai rinjaye--Mai karfin rinjaye Wanda ya rubuta shi: Sa'id Bn Ali Bn Wahf Al-Kahdani
Mai gyara halitta-Mai kiyaye ayyukan bayi-Mai shiryarwa-Mai hukunci-Tsarkakakken sarki-Mai amintarwa-Mai kyautatawa An tace shi a: Sha’aban, 1408.
FALALAR ADDU’A
Mai yawan kyauta-Mai jinkan muminai da kafirai a duniya-Ma jin kan muminai kadai a lahira-Mai karamci- Mafi karamci-Mai tausasawa-Mai budawa bayi-
Mai azurtawa-Mai yawan azurtawa-Rayayye-Wanda ya tsayu da kansa-mai reno-sarki- Mamallaki Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: ((Kuma Ubangijinku Ya ce ku rokeni zan amsa muku, hakika wadanda suke girman kai ga babarin bautata za su shiga Jahannama suna makaskanta))[4}{ Surar Gafir, aya ta: 60. Kuma Allah - Mai girma da daukaka - Ya ce: ((Kuma idan bãyiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to, lalle Ni Ina kusa ne. Ina karɓa kiran mai kira idan ya kirã Ni. Sabõda haka su nẽmi karɓawaTa, kuma su yi ĩmãni da Ni: tsammãninsu, su shiryu)) Surar Bakara aya ta: 186. Kuma Annabi - tsira da amincin Allah tabbata a gare shi - ya ce: ((Addu'a ita ce ibada, Ubangijinku Ya ce ku rokeni zan amsa muku)){3}. Kuma Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: ((Lalle Ubangijinku mai girma da daukaka Mai kunya ne, kuma mai karamci ne, Yana jin kunyar bawanSa idan ya daga hannuwansa zuwa gare Shi , da shi (bawan) Ya dawo da su babu komai)){4}. Kuma Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: ((Babu wani Musulmi da zai roki wata bukata wacce babu zunubi a cikinta, babu kuma yanke zumunci, face sai Allah Ya ba shi dayan abu uku: Kodai Ya gaggauta masa (karbar) Addu’ar sa, ko kuma Ya ajiye masa ita sai ranar al-kiyama, ko kuma Ya kawar masa da wani mummunan abu irinta". Sai (Sahabbai) suka ce; Kenan mu yawaita? Sai ya ce: "Allah shi ne mafi yawaitawa)){5}. Abu Dawud, 2/78, mai lamba1481, da Tirmizi, 5/211, mai lamba 2959. da ibn Majah, 2/1258, mai lamba 3828, kuma Abani-Allah Ya ji kansa - ya inganta shi a cikin Sahihul jami'i'ussagir 3/150, kuma Ibnu Majah ya inganta shi, 2/324. 4. Abu Dawud ya fitar da shi a 2/78, a lamba 1488 da kuma Tirmizi 5/557 a lamba 3556, da ibnu Majah, 2/ 1271, a lamba 2/1271, mai lamba 3865, kuma Ibnu Hajar ya ce: ((sanadinsa mai kyau ne)). kuma Albani ya ingantashi a cikin Sahihut Tirmizi , 3/179. Tirmizi ne ya fitar da shi, 5/566, a lamba 3573, da Ahmad 3/18 a lamba 11150, kuma Albani ya inganta shi a cikin Sahihu Jami’us Sagheer 5/116, da Sahihul Sunanit Tirmizi 3/ 140.
Shi daya-makadaici-Mai girman girma-Mahalicci-Mai yawan halitta- Mai halitta-Mai surantawa Yana daga ladubban Addu'a da kuma dalilan karbarta {6}: Ka duba wadannan Ladubban da dalilan amsawa tare da dadalilansu a cikin asalin wanannan littafin 3/927-975
Amintacce mai amintarwa-Mai shaida akan bayi-Mai kewayewa da komai-Mai kiyayewa- mai iko-Mai isarwa- Mai ishewa-Mai yalwatawa 1. Tsarkake niyya domin Allah.
Matabbacin gaskiya-Mai kyau-Mai tausasawa-Mai kunya-Mai suturta bayinsa-Abin bauta-Mai damka Ya fara da godewa Allah da yabo agareShi, sannan salati ga annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kuma cika da haka.
Mai shinfida arzuki-Mai bayarwa-Mai gabatarwa-Mai jinkirtarwa- Mai bayyanawa-Mai yawan baiwa-Mai jibintarwa 3. Samun tabbas akan Addu’a da sakankancewa da amsawa.
Ma jibi ci - Mai taimako-Mai warkarwa-Mamallakin mulki-Mai tattara mutane Naci a Addu’a da barin gaggawa.
Hasken sammai da kasa-Ma'abocin girma da karamci- Makagin sammai dakasa{2} 5-Halarto da zuciya a Addu’a. Duba wadannan sunayen tare da dalilansu daga Alkur’ani da Hadisi a littafin:(sharhin sunayen Allah kyawawa a hasken kur'ani da sunnah)... na mawallafin.
6- Addu’a a lokacin yalwa da kuma tsanani.
7. Kada a roki kowa sai Allah Shi kadai.
8- Kada a yi mummunar Addu’a ga iyali da dukiya da ‘yaya da kuma rai.
9- Kankar da murya a Addu’a tsakanin boyewa da bayyanawa.
10- Tabbatar da laifi, da kuma neman gafara akansa, da tabbatar da ni’ima, da godewa Allah akanta.
11-Kada a matsawa kai sai an yi SAJA’I a Addu’a.
12- Kankar da kai da halarto da zuciya, da kwadayi da tsoro.
13. Mayar da hakkin muatane tare kuma da tuba.
14- Yin Addu’a sau uku.
15- Fuskantar alkibila (Ka’abah).
16- Daga hannuwa a Addu’a.
17- Alwala kafin Addu’a in zata samu (alwalar).
18- Kada (mai Addu’ar) ya yi shisshigi a addu'a
19- Mai addu' ya fara da kansa, idan zai yi addua'ar alkhairi ga waninsa{7}. Hakika ya tabbata daga annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- cewa shi ya fara yin addu'a ga kansa, kuma ya tabbata cewa shi bai fara ga kansa ba, kamar addu'arsa da ya yi ga Anas da Ibnu Abbas, da mahaifiyar Isma'il, da waninsu, ka duba karin bayani a kan wannan mas'ala a cikin sharhin Nawawi na Sahihu Muslim, 15/144, da kuma Tuhfatul Ahwazi Sharhin Sunanul Tirmizi, 9/328. da Fathul Bari Sharhin Sahihul Bukhari, 1/281.
20- Ya yi Tawassali zuwa ga Allah da sunayenSa kyawawa, da suffofinSa madaukaka, ko da wani aiki na gari da mai addu'a ya aikata shi da kansa, ko da addu'ar wani mutum nagari rayayye kuma yake anan
21- Ya kasance abin ci da abin sha da tufafi na halal ne.
22. Kada ya yi Addu’ar sabo, ko yanke zumunci.
23. Ya zama yana umarni da kyakkyawa, yana hani ga mummuna.
24- Nisantar dukkanin laifuffuka.
Lokuta da halaye da wuraren da ake amsa addu'a a cikinsu{8}: Ka duba wadannan lokutan da halaye da wuraren, tare da dalilansu a fayyace a asalin littafin, 3/975-1117.
1- Daren Lailatul kadari.
2- Tsakiyar dare (daya bisa uku na karshensa).
3- Bayan salloli biyar na farilla.
4- Tsakanin kiran Sallah da Ikama.
5- Wani lokaci a kowanne dare.
6- Yayin kiran sallar sallolin farilla
7- Lokacin saukar ruwan sama.
8- Lokacin garken sahun (yaki) a kan tafarkin Allah.
9- Wani lokaci (na musamman) a ranar Juma’a.
Mafi rinjayan maganganu akan haka, shi ne karshen lokaci daga lokutan la'asar din ranar Juma’a, za kuma ta iya kasancewa lokacin Huduba da Sallah.
10- Lokacin shan ruwan zamzam, tare da niyya ta gaskiya.
11- A cikin sujjada.
12. Lokacin farkawa daga bacci a cikin dare, da yin Addu’ar da aka ruwaito akan haka.
13- Idan ya yi bacci da alwala, sannan ya farka da daddare ya yi Addu’a.
14-Lokacin da ya yi addu'a da ((Babu abin bautawa da gaskya sai kai, tsarki ya tabbata a gareka hakika ni na kasance daga cikin azzalumai)).
15- Addu’ar mutane bayan rasuar mamaci.
16- Yin addu'a bayan yabo ga Allah, da salati ga annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- a tahiyar karshe.
17-Lokacin kiran Allah da sunansa mai girma, wanda idan aka kira shi da shi yake amsawa, idan kuma aka roke shi da shi yake badawa {9} Ka duba sunan Allah mafi girma a cikin Hadisi mai lamba 203, da mai lamba104 da mai lamba 105 a wannan littafin..
18-Addu'ar Musulmi ga dan uwansa musulmi a bayan idansa
19- Addu'ar ranar Arafah a Arafah.
20- Addu'a a watan Ramadan.
21- A lokacin taruwar musulmi a majalisan Zikri.
22-Lokacin yin addu'a akan musiba da fadin ((mu daga Allah muke kuma gare shi zamu koma, ya Allah ka bani lada a wannan masifar tawa, ka kuma maye mini mafi alheri daga gareta)).
23- Addu'a a lokacin da zuciya ta fuskanci Allah da lokacin tsantsar ikhlasi.
24. Mummunar addu'ar wanda aka zalunta a kan wanda ya zalunce shi.
25-Addu’ar uba (ta alkhairi) ga dansa, da (mummunar addu'a) da ya yi wa dansa.
26-Addu’ar matafiyi.
27-Addu’ar mai azumi har sai ya yi buda baki.
28 Addu’ar mai azumi a lokacin buda baki.
29-Addu'ar mai tsananin bukata
30- Addu’ar shugaba mai adalci.
31- Addu’ar Da na kwarai ga iyayansa.
32-Addu’a bayan (gama) alwala, idan ya yi Addu’a irin wacce aka ruwaito akan haka.
33-Addu’a bayan jifan karamar Jamra (Karamin Shaidan).
34-Addu’a bayan jifan Jamra ta tsakiya (Shaidan na tsakiya).
35-Addu’a a cikin Ka’abah, wanda ya yi sallah a cikin Hijir to shi ma yana cikin Ka’abah.
36-Addu’a akan (dutsan) Safa.
37- Addu’a akan (dutsan) Marwa.
38- Addu’a a Mash'aril Haram, (Muzdalifa).
Mumini yana rokon UbangijinSa koda yaushe, a duk inda ya kasance, Allah Mai girma da daukaka Ya ce: ((Kuma idan bayina suka tambayeka dangane da Ni, to, lalle Ni ina kusa ne, ina amsa Addu’ar mai addu’a idan ya rokeNi, saboda haka su nemi amsawata, kuma su yi imani da Ni ko sa samu su shiryu)). Suratul Bakarah, aya ta: 186. Sai dai wadannan lokutan (da aka ambata) da yanayi da wurare, suna kebantuwa ne da wata falala ta musamman.
ADDU’A DAGA AL’KUR’ANI DA HADISI
Godiya ta tabbata ga Allah Shi kadai, tsira da aminci su tabbata ga wanda babu wani Annabi a bayansa.
1- ((Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai * Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai* Mai yawan rahama Mai yawan jinkai*. Mamallakin ranar sakamako*. Kai kadai muke bautawa, kuma gareKa kadai muke neman taimako*. Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya*. Hanyar wadanda ka yi ni'ima a garesu, ba wadanda Ka yi fushi a gare su ba, ba kuma batattu ba)). Suratul Fatiha, daga ayah ta 1-7
2- ((Ya Ubangijiinmu Ka karba mana, Kai mai ji ne kuma masani ne )). Suratul Bakarah, aya ta: 127
((Ka karbi tubanmu hakika kai Mai yawan karbar tuba ne Mai jin kai)). Suratul Bakarah, aya ta: 128
4- ((Ya Ubangijinmu Ka bamu kyakkyawa a duniya, kuma Ka bamu kyakkyawa a lahira, Ka kuma kiyayemu azabar wuta)). Suratul Bakara aya ta 201.
5- ((Mun ji kuma mun bi, muna neman gafararKa, Ubangijinmu kuma makoma na gareka)). Suratul Bakara, aya ta 285.
6- ((Ya Ubangijinmu ! Kada Ka kama mu in muka manta, ko muka yi kuskure, Ya Ubangijin mu ! Kada Ka dora mana nauyi, kamar yadda Ka dora shi akan wadanda suka zo kafin mu, Ya Ubangijinmu ! Kada Ka dora mana abinda ba zamu iya dauka ba, Ka yi mana afuwa, Ka gafarta mana, Ka yi mana rahama, Kai ne Mai jibintar mu, Ka taimake mu akan mutanan da suke kafirai)). Suratul Bakara, aya ta 286.
7- ((Yã Ubangijinmu! Kada Ka karkatar da zukãtanmu bãyan har Kã shiryar da mu, kuma Ka bã mu rahama daga gunKa. Lalle ne, Kai, Kai ne Mai yawan kyauta)). Suratu Ali Imran, aya ta 8.
8- ((Ya Ubangijinmu ! Lalle ne mu mun yi imani, to Ka gafarta mana zunubammu , Ka tsaremu daga azabar wuta)). Suratu Ali Imaran, aya ta: 16.
9- ((Ya Ubangijina Ka yi min baiwa daga gareKa ta zuriya mai albarka, lalle Kai Mai jin Addu’a ne)). Suratu Ali IImran, aya ta: 38.
10- ((Yã Ubangijinmu! Mun yi imãni da abin da Ka saukar, kuma mun bi ManzonKa, sai Ka rubũta mu tãre da mãsu shaida)). Suratu Ali Imran, aya ta: 53
11- ((Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana zunubammu da barnarmu a lamuran mu, Ka tabbatar da duga-dugammu, Ka taimaka mana akan mutanan da suke kafirai)). Suratu Ali Imran, aya ta: 147.
12- ((Ya Ubangijinmu ! Ba Ka halicci wannan (halittar) dan wasa ba, tsarki ya tabbata a gareKa, to Ka tsaremu daga azabar wuta*. Ya Ubangijinmu lalle kai duk wanda ka shigar wuta lalle Ka kunyatar da shi, azzalumai basu da wasu mataimaka* Yã Ubangijinmu! Lalle ne mũ mun ji Mai kira yanã kira zuwa ga ĩmãni cẽwa, 'Ku yi ĩmãni da Ubangijinku.' Sai muka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Sabõda haka Ka gãfarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare miyãgun ayyukanmu daga gare mu. Kuma Ka karɓi rãyukanmu tãre da mutãnen kirki* Yã Ubangijinmu! Ka bã mu abin da Ka yi mana wa'adi (alkawari) a kan manzanninKa, kuma kada Ka tozarta da mu a Rãnar ¡iyãma. Lalle ne Kai, bã Ka sãɓãwar alkawari)). Suratu Ali Imran, aya ta: 191-194.
13- ((Ya Ubangijinmu ! Mun yi imani, to Ka rubuta mu a cikin masu shaidawa)). Suratul Al’ma'idah, aya ta 83.
14- ((Ya Ubangijinmu ! Mun zalinci kawunanmu, kuma idan ba Ka gafarta mana ba, ba Ka yi mana rahama ba, tabbas za mu kasance cikin masu asara)}. Suratul A’araf, aya ta : 23
15- ((Ya Ubangijinmu ! Ka da ka sanya mu tare da azzalumai)). Suratul A’araf, aya ta: 47.
16- Ya Allah Ya Ubangiji ((Kai ne Waliyyinmu, to Ka gafarta mana Ka yi mana rahama, kuma Kai ne fiyayyan masu gafara*. ((Ka rubuta mana kyakkyawa a wannan duniyar haka nanma a lahira)). Suratul A’araf, aya ta 155-156.
17- ((Allah ya isar mini, babu abin bautawa da cancanta sai shi, a gare shi na dogara, kuma shi ne Ubamgijin Al’Arshi mai girma)). Suratut Taubah, aya ta: 129.
18- ((Ya Ubangijinmu ! Ka da ka sanya mu fitina ga mutanan da suke azzalumai * Kuma ka tserar da mu domin jin kanka daga mutane kafirai)). Suratu Yunus, aya ta: 85-86.
19- (( Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, inã nẽman tsari gare Ka da in tambaye Ka abin da bã ni da wani ilmi a kansa. Idan ba Ka gãfarta mini ba, kuma Ka yi mini rahama, zan kasance daga mãsu hasãra)). Suratu Hud, aya ta: 47.
20- ((Ya Allah ya ((Ya Mahaliccin sammai da kassai, kaine majibinci na a duniya da lahira, Ka karbi raina ina musulmi, kuma ka riskar da ni da managartan bayi)). Surar Yusuf, aya ta: 101 {10} {10} Ka duba don fa'ida: littafin na ibn Kaayyim, shafi na: 436 da 437,
21- ((Ya Ubangijina! Ka sanya wannan gari (Ya zama) amintacce, Ka nisantar da ni da ‘ya’yana daga bautar gumaka)). Suratu Ibrahim, Aya ta: 35.
22- ((Yã Ubangijina! Ka sanyã ni mai tsayar da salla. Kuma daga zũriyyata. Yã Ubangijinmu! Kuma Ka karɓi addu'ata)). Suratu Ibrahim, Aya ta: 40.
23- ((Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara gare ni, kuma ga mahaifãna, kuma da mũminai, a rãnar da hisãbi yake tsayãwa)). Suratu Ibrahim, Aya ta: 41
24- ((Ya Ubangijinmu ! Ka ba mu rahama daga gareka, kuma Ka shirya mana a lamari nan namu abinda yake daidai)). Suratul Kahf, Aya ta: 10.
25- ((Ya Ubangijina ! Ka yalwata min kirjina* Ka sawwaka min lamari na*. Ka warware kulli daga harshe na, za su fahimci magana ta)). Suratu Ɗāha, ayoyi na: 25-28.
26- ((Ya Ubangijina Ka kara min ilimi)). Suratu Taha, Aya: 114.
27- ((Babu abin bautawa da gaskiya Sai Kai, tsarki ya tabbata a gareKa, lallai ni na kasance cikin azzalumai)). Suratul Anbiya, aya ta: 87.
28- ((Ya Ubangijina kada Ka barni ni kadai, Kai ne kuma fiyayyan masu gajewa)). Suratul Anbiya, aya ta: 89.
29- ((Ya Ubangijina ina neman tsarinKa daga zungurin shaidanu * Kuma inã nẽman tsari da Kai, ya Ubangijĩna! Dõmin kada su halarto ni)). Suratul Mu’uminun, Aya ta: 97-98.
30- ((Ya Allah Ubangijinmu ! Mun yi imani, to Ka gafarta mana, Ka ji kanmu, Kai ne fiyayyan masu jin kai)). Suratul Mu’uminun, aya ta: 109
31- ((Ya Ubangijina Ka gafarta, kuma Ka jikai, Kai ne fiyayyan masu jin kai)). Suratul Muminina, aya ta: 118.
32- ((Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azãbar Jahannama daga gare mu. Lalle ne, azãbarta tã zama tãra))* Lalle ita (jahannama) ta munana a mazauna da matabbata)). Suratul Furkan, aya ta: 65-66
33- ((Ya Ubangijinmu ! Ka bamu sanyin idanu daga matanmu da zuriyar mu, kuma Ka sanya mu shugabanni ga masu tsoron Allah))[}. Suratul Furkan, aya ta: 74.
34- ((Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai* Kuma Ka sanya min harshe na gaskiya ga ‘yan karshe* Kuma ka sanya ni daga magadan Aljannar ni'ima)). Suratus Al-Shu’ara, Aya ta: 83-85.
35- ((Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su * Ranar da dukiya ba ta amfani haka’ya’ya (su ma ba sa anfani) * Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki)). Suratus Al-Shu’ara, Aya ta: 87-89.
36- ((Ya Ubangijina Ka kimsa min in godewa ni’imarKa da Ka ni’imtata a gareni, da kuma mahaifana da kuma in yi (aiki) na kwarai da zaKa yarda da shi, kuma Ka sanyani cikin bayinKa na kwarai)). Suratun Namli, Aya ta: 19.
37- ((Ya Ubangijina lalle ni na zalinci kaina, Ka gafarta mini)). Suratul Kasas, Aya ta:16.
38- ((Ya Ubangijina Ka tseratar da ni daga mutanan da suke azzalumai)). Suratul Kasas, Aya ta : 21.
39- ((Ina fata Allah Zai shiryar dani hanya madaidaiciya)). Suratul Kasas, Aya ta: 22.
40- ((Ya Ubangijina lallai ni mabukacine dangane da abinda Ka saukar zuwa gareni na alheri)). Suratul kasas, aya ta: 24.
41- ((Ya Ubangijina Ka taimakeni akan mutanan da suke mabarnata)). Suratul Ankabut, Aya ta: 30
42- ((Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne)). Suratus Saffat, Aya ta: 100.
43- ((Ya Ubangijina Ka kimsa min in gode da ni’imarKa wacce Ka ni’imtata ta a gareni da kuma mahaifana da kuma in aikata (aiki) na gari da zaKa yarda da shi, kuma Ka gyara mini a cikin zuriyata, lallai ni na tuba zuwa gareKa kuma lallai ni ina cikin musulmai)). Suratul Ahkaf, Aya ta: 15.
44- ((Yã Ubangijinmu! Ka yi gãfara a gare mu, kuma ga 'yan'uwanmu, waɗanda da suka riga mu yin ĩmãni, kada Ka sanya wani ƙulli a cikin zukãtanmu ga waɗanda suka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Lalle Kai ne Mai tausayi, Mai jin ƙai)). Suratul Hashr, aya ta: 10.
45- ((Ya Ubangijin mu ! GareKa muka dogara, kuma gareKa muka mayar da lamuran mu, kuma makona zuwa gareKa take)). Suratul Mumtahana, aya ta: 4.
46- ((Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu fitina ga waɗanda suka kãfirta, kuma Ka yi gãfara gare Mu. Ya Ubangijinmu! Kai ne Mabuwãyi, Mai hikima)). Suratul Mumtahana, aya ta: 4.
47-((Ya Ubangijina Ka gafarta min da iyayena da kuma wanda ya shiga gidana yana mumini, da muminai (maza) da muminai (mata)). Suratu Nuh, aya ta 28.
48- ((Ya Ubangijin mu ! Ka cika mana hasken mu, Ka gafarta mana, lallai Kai mai iko ne akan komai)). Suratut Tahrim, aya ta: 8.
49- ((Ya Allah Ubangiji! Ka shiryar da ni ga duk abinda suka yi sabani a cikinsa na gaskiya da izininKa, lallai Kai Kana shiryar da wanda Kake so zuwa hanya mikakkiya)). 11. An dosano daga Suratul Bakara aya ta: 213
50- ((Ya Allah Ka bani hikima, wacce duk wanda aka ba shi ita, to lalle an ba shi alkhairi mai yawa)). 12. An ciro daga Suratul Bakara: aya ta: 269.
51- ((Ya Allah Uabangiji! Ka tabbatar da ni da magana tabbatacciya a rayuwar duniya da lahira)). 13. An ciro daga Suratu Ibrahim, aya ta: 27.
52- ((Ya Allah Ubangiji ! Ka soyar mana imani, Ka kawata shi a zukatammu, Ka kyamatar mana da kafirci da fasikanci da laifuka, Ka sanya mu cikin masu shiryarwa)). 14. An ciro daga Suratul Hujurat, aya ta 7
53- ((Ya Ubangiji ! Ka tsare ni yi wa kaina kwauro, Ka sanyani cikin masu rabauta)). 15. An ciro daga Suratut Tagabun, aya ta: 16.
54- ((Ya Allah Ubangiji ! Ka ba mu anan duniya abu mai kyau, a lahira ma abu mai kyau, ka tsaremu azabar wuta)). 16. Bukhari ne ya ruwaito a Hadisi mai lamba 4522, da lamba 6389, da kuma Muslim mai lamba 2690.
55- Ya Allah Ubangiji! ni ina neman tsarinka daga fitinar wuta da azabar wuta, da fitinar kabari, da sharrin fitinar wadata, da sharrin fitinar talauci, Ya Allah ni ina neman tsarinka daga fiitinar Dujal, ya Allah Ubangiji ! Ka wanke zuciyata da ruwan kankara, Ka kuma tsarkake zuciyata daga kurakure, kamar yadda Ka tsarkake farin tufafi daga datti, Ka nisanta tsakanina da tsakanin kurakure na ,kamar yadda Ka nisanta tsakanin gabas da yamma,Ya Allah ni ina neman tsarinka daga lalaci da laifuffuka da bashi)){17}. 17. Bukhari, a lamba 832, da Muslim, mai lamba 589.
56- ((Ya Ubangiji ni ina neman tsarinka daga gajiyawa, da kasala, da tsoro, da tsufa, da rowa, kuma ina neman tsarinka daga azabar Kabari, kuma ina neman tsarinka daga fitinar rayuwa da ta mutuwa)){18}. 18. Bukhari, a lamba 2823, da Muslim, mai lamba 2706.
57- ((Ya Allah ni ina neman tsarinka daga wahalar bala'i da riskar tsiyata, da mummunan hukunci, da dariyar makiya)){19}. 19. Bukhari, a lamba 6347, da Muslm, a lamba 2707, lafazinsa:(( Manzan Allah-tsira da amincin allah su tabbata a gare shi- ya kasance yana neman tsari daga wahalar bala'i da riskar tsiyata, da mummunan hukunci da dariyar makiya)).
58- ((Ya Allah Ka gyara mini Addinina, wanda shi ne ƙashin bayan al’amarina, kuma Ka gyara mini duniya ta wacce nake rayuwa a cikinta, Ka kuma gyara mini lahira ta wacce a cikinta ne makomata take, ka sanya rayuwa (ta zamo) ƙarin duk wani alheri gareni, kuma Ka sanya mutuwa ta zamo hutu ce a gare ni, daga dukkan wani sharri)){20}. Muslim ne ya fitar da shi a lamba 2720.
59- ((Ya Allah ina rokonKa shiriya da tsoron Allah, da kamewa, da wadata)){21}. Muslim ne ya fitar da shi a lamba 2721.
61- ((Ya Allah Ubangiji Ka shiryarda ni Ka kuma datar dani, Ya Allah ni ina rokanka shiriya da dacewa)){23}. Muslim ne ya fitar da shi a lamba 2725.
62- ((Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa)){24}. Muslim ne ya fitar da shi, a lamba 2739.
63- ((Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga sharrin abinda na aikata, da kuma sharrin abinda ban aikatata ba)){25}. Muslim ne ya fitar da shi, a lamba 2716.
64- ((Ya Allah Ubangiji! Ka yawaita dukiyata, da yayana, Ka yi albarka a gareni cikin abinda Ka bani)), (( {kuma Ka tsawaita rayuwata a bisa biyayya gareka, Ka kuma kyautata aikina} Ka gafarta min)){27}. Addu'ar annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- da ya yi ga Anas tana nuni a gareta: ((Ya Allah Ka yawaita dukiyarsa, da yayansa, Ka kuma yi albarka a gare shi cikin abinda ka ba shi)). Bukhari, a lamba ta:1982, hakanan Muslim, a lamba 660. Bukhari a cikin Al'adabul al’Mufrad, a lamba ta: 653, kuma Albani ya inganta shi a cikin Silsilatul al'ahadsis Sahiha, a lamba 2241. kuma a cikin Sahihul Al'adabul Mufrad, shafi na 244, fadinsa-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana nuni a gare shi, lokacin da aka tambaye shi: wanene mafificin mutane? sai ya ce:((wanda rayuwarsa ta tsawaita, kuma aikinsa ya kyautata)), Tirmizi, a lamba 2329, haka kuma Ahmad, da lamba 17716, kuma Albani ya ingantashi a cikin Sahihut Tirmizi, 2/271, kuma hakika na tambayi babban malaminmu ibn Baaz -Allah ya yi masa rahama- a bisa yin addu'a da shi, kuma shin hakan sunna ne? sai ya ce: (Eh).
65- ((Babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah Mai girma Mai hakuri, babu wani abin bautawa da gaskiya face Allah Ubangijin Al’arshi mai girma, babu wani abin bautawa da gaskiya face Allah Ubangijin sammai kuma Ubangijin kasa kuma Ubangijin Al’arshi mai yawan baiwa)){28}. Bukhari, a lamba ta: 6345, da kuma Muslim, a lamba ta: 2730.
66- ((Ya Allah rahamarKa nake kauna, kar Ka barni da kaina daidai da ƙiftawar ido, Ka gyara min al’amura na dukkansu, babu wani abin bautawa da gaskiya sai Kai)){29}. Abu Dawud, a lamba, 5090, da Ahmad 5/42, kuma albany ya kyautata shi, a cikin Sahih Abi Dawud, 3/250, da Sahihul Al'adabi al’Mufrad, kuma babban malami ibnu Baaz ya kyautata Isnaadinsa, a cikin Tuhfatul al'akhbaar, shafi na: 24.
67- ((Babu abin bautawa da gaskiya Sai Kai, tsarki ya tabbata a gareKa, lallai ni na kasance cikin azzalumai))[30]. Tirmizi, a lamba ta: 3505, da Hakim, kuma al-zahbi ya inganta shi, 1/505, kuma ALbany ya inganta shi a cikin Sahihut Tirmizi, 3/168, lafazinsa:((Addu'ar zinnun (annabi Yunus) lokacin da ya kira shi, alhali yana cikin kifi: ((cewa babu abin bautawa da gaskiya sai kai, tsarki ya tabbatarmaka, lalle ni na kasance daga cikinazzalumai)). {Al'anbiyaa: 87}, cewa wani mutum musulmi ba zai roki wani abu da ita ba, face sai Allah Ya amsa masa)).
68- ((Ya Allah Ubangiji! ni bawanka ne dan bawanka dan baiwarka, makwarkwadata na hannunka, kaddararka mai zartuwa ce a gareni, hukuncinka adalci ne a gareni, ina rokonka da dukkanin wani suna naka, da Ka ambaci kanKa da shi, ko Ka saukar da shi a cikin littafinka, ko Ka sanar da shi ga wani daga halittarKa ko Ka kadaita da shi a cikin iliminka na gaibu a gurinka, Ka sanya Alkur'ani farin cikin zuciyata, da hasken kirjina, da yayewar bakin cikina, da tafiyar damuwata)){31}. Ahmad, 1/391, 452 da Hakim, 1/509, kuma Hafiz ya kyautata shi a cikin Takhrijil, Al’azkaar, kuma Albany ya inganta shi a cikin Takhrijil kalami Dayyib, shafi na 73.
69- ((Ya Allah Ubangiji Mai juya zukata, Ka tabbatar da zukatan mu akan biyayyarka)){32}. Muslim, a lamba ta 2654.
70- ((Ya Mai juya zukata, Ka tabbatar da zuciyata akan addininKa)){33}. Tirmizi, a lamba ta 3522, da Ahmad, 4/182, da Hakim, 1/525, da 528, al-Zahabi kuma ya inganta shi, Albany ma ya inganta shi a Sahihul Al-jami;i, 6/309, kuma Tirmizi ya inganta shi, 3/171. Hakika Ummu Salama-Allah ya yarda da ita ta ce: ((Mafi yawan addu'arsa-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ta kasance)).
71- ((Ya Allah ni ina rokanKa lafiya a duniya da lahira)){34}. Tirmizi, a lamba 3514, da Bukhari a cikin Al-adabul Al’mufrad, a lamba 726, lafazinsa a gurin Tirmizi: ((Ku roki Allah lafiya a duniya da lahira)), a wani lafazin kuma: ((Ku roki Allah rangwami da lafiya, hakika ba'a bawa wani (wani abu ba) bayan rai mafi alkhairi fiye da lafiya)), lalle Albany ya inganta shi a cikin Sahihul Ibnu Majah, 3/180, da 3/ 185, da 3 170, kuma yana da SHAWAHID, ka duba su a cikin: Musnadul Imam Ahmad da tsarawar Ahmad Shakir, 1/ 156-157.
72- ((Ya Allah Ka kyautata karshenmu adukkannin al'amura, Ka tserar da mu daga kunyatar duniya da azabar lahira)){35}. Ahmad, 4/181, da Dabarani a cikin Alkabir, 2/33/1169, haka nan a cikin addu'a a lamba 1436, da ibnu Hibban, a lamba 2424, 2425 (Mawarid), Alhafiz alhaithamy ya ce a cikin Majma'i Al-Zawa'id, 10/ 178: (( Mazajen Ahmad da daya daga Asanid Al-dabarani amintattu ne)).
73-((Ya Ubamgiji! Ka taimakeni, kada ka taimakawa wani a kaina (ka datar dani ambatonka), kada Ka bawa wanda zai hanani biyayyarKa rinjaye a kaina, Ka taimakeni (akan kafirai makiya addininKa), kada Ka dora wani daga halittarka a kaina, Ka riskar da makircinka ga makiyana (Ka azurtani dabarar kubuta daga sharrinsu), Kada Ka nunawa makiyana kare kansu, Ka shiyar dani kofofin alkhairai, Ka saukaka min bin shiriyarka, Ka taimakeni akan wanda ya zalince ni, ya Ubangjina! Ka sanyani mai yawan godiya a gareKa, mai yawan ambato a gareka, mai yawan tsoranKa, mai yawan mika wuya a gareka, mai kankar da kai a gareKa, mai yawan kukan tsoranKa, mai komawa gareKa. Ya Ubangijina Ka karbi tubana, Ka shafe zunubina, Ka amsa addu'ata, Ka tabbatar da hujjata (akan makiyanka), Ka shiryar da zuciyata, Ka dai-daita harshena, Ka fitar da kullin kirjina)){36}. Bukhari a cIkin Al'adabul Al'mufrad, a lamba ta: 664, da kuma 665, da Abu Dawud, a lamba ta: 1510, 1511, da Tirmizi a lamba ta: 3551, da ibnu Majah, a lamba ta: 3830, da Ahmad 1/127 a Hakim; kuma Al-zahabi ya inganta shi 1/519, kuma Albany ya inganta shi a cikin Sahihu Abi Dawud, 1/414, hakanan kuma a cikin Sahihul Al-Tirmizi, 3/178.
74- ((Ya Allah Ubangiji! Mu muna rokonKa daga alkhairin abinda annabinka Muhammad-tsiar da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya rokeka, kuma muna neman tsarinka daga sharrin abinda annabinka Muhammad-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya nemi tsari daga gare shi, kuma Kaine abin neman taimako, isuwa tana gareka, babu wata dabara, babu wani karfi sai ga Allah)){37}. Tirmizi, a lamba ta: 3521, da ibnu Majah, a lamba ta: 3846, da Ma'anarsa, kuma Tirmizi ya ce: (( Wannan Hadisi ne kyakkyawa Garibi)), Albani ya raunana shi, a cikin Dha’ifin Tirmizi, shafi 387.
75- ((Ya Allah ni ina neman tsarinka daga sharrin jina, da kuma sharrin ganina da sharrin harshena da sharrin zuciyata, da sharrin maniyyina)){38}. Abu Dawud, a lamba ta: 1551, da Tirmizi, a lamba 3492, haka nan Nasa'i a lamba, 5470, da waninsu, kuma Albany ya inganta shi, a cikin Sahihul, Tirmizi, 3/166, kuma Nasa'i ya inganta shi, 3/1108.
76- ((Ya Allah, ina neman tsarinKa daga kuturta mai sanya fararen taba, da hauka da kuturta mai sanya daddatsewar yatsu da kuma munanan cututtuka ([39]). Abu Dawud, a lamba ta: 1554, da Nasa'i, a lamba ta: 5493, da Ahmad, 3/192 kuma Albani ya inganta shi, a cikin Sahihun Nasa’i 3/1116, da Sahihut Tirmizi 3/184.
77- ((Ya Allah Ubangiji! hakika ni ina neman tsarinKa, daga dabi'u da ayyuka da soye-soyen zuciya ababan ki)){40}. Tirmizi, a lamba 3591, da ibnu Hibban, a lamba 2422 (Mawarid), da Hakim, 1/532, da Dabarani a cikin Al-kabir, 19/19/36. kuma Albany ya Inganta shi a Sahihut Tirmizi, 3/184.
78- ((Ya Allah Ubangiji! lalle Kai mai yawan afuwa ne, mai yawan karamci, Kana san afuwa Ka yi min afuwa)){41}. Tirmizi, a lamba ta: 3531, da Nasa’i a cikin Al-kubra, a lamba ta: 7712, kuma Albani ya inganta shi, a cikin Sahihut Tirmizi, 3/170.
79- ((Ya Allah ni ina rokanKa aikata alkhairai, da barin ababan ki, da san miskinai, kuma Ka gafarta min, Ka ji kaina, kuma idan ka yi nufin fitinar wasu mutane, Ka karbi raina ba tare da anfineni ba, kuma ina rokanka, sanka, da san wanda yake sonka, da son aikin da zai kusantar dani zuwa sanKa)){42}. Ahmad ya fitar da shi da lafazinsa, 5/243 da Tirmizi, a lamba ta: 3235, da makamancinsa, kuma ya ce: na tambayi Muhammad bin Isma'il- yana nufin Bukhari- sai ya ce: (wannan Hadisi ne kyakkyawa Ingantacce)), a karshen Hadisin -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce:((hakika ita gaskiya ce, ku karanceta kuma ku koyeta), da Hakim 1/521, kuma Albany ya inganta shi a cikin Sahihut Tirmizi, 3/318.
80- ((Ya Allah ina roƙonKa dukkan alheri, a yanzu haka da anjima, abin da na sani daga gare shi, da abin da ban sani ba, kuma ina neman tsarinKa daga dukkan sharri a yanzu haka da anjima, abin da na sani daga gare shi da abin da ban sani ba*. Ya Allah ina roƙonKa mafi alherin abin da bawanKa kuma AnnabinKa ya roƙeKa, kuma ina neman tsarinKa daga sharrin abin da bawanKa kuma AnnabinKa ya nemi tsarinKa da shi, ya Allah ina roƙonKa aljanna da abin da yake kusantota na magana ko aiki, kuma ina neman tsarinKa daga wuta, da abin da yake kusantota na magana ko aiki, ina rokonKa Ka sanya dukkan hukuncin da Ka hukunta gare ni ya zama alheri)){43}. Ibnu Majah, a lamba ta: 3846, da lafazinsa, da Ahmad, 6/134, lafazin kari na biyu nashi ne, da Hakim kuma ya ingantashi, Al-Zahabi ya wafaka mishi, 1/521, lafazin karin farko nashi ne, kuma Albany ya inganta shi a cikin Sahihul ibnu Majah, 2/327.
81- ((Ya Allah Ka kiyayeni da musuluci ina tsaye, Ka kuma kiyayeni da musulunci ina zaune, Ka kiyaye ni da musulinci ina kwance, kada Kasa makiyi ya yi min dariya, ko mai hassada. Ya Allah ni ina rokanka dukkan alherin da taskokinsa yake a hannunKa, ina kuma neman tsarinKa da dukkan sharrin da taskokinsa suke a hannunka)){44}. Alhakim, 1/525 kuma Zahabi ya inganta shi, Albani kuma ya kyautata shi, a cikina al-jami'i, 2/398, da Silsilatul Ahadis Sahiha, 4/54, a lamba 1540.
82- (Ya (Allah Ka kaddara mana tsoranka abinda zaka tsare da shi tsakaninmu da tsakanin sabonka, Ka kuma (kaddara mana) daga biyayyarKa abinda zaka isar damu da shi AljannarKa, kuma daga yakini abinda zaka saukaka mana dashi masifun duniya, ya Allah, kuma Ka sanya mu masu jin dadi da jinmu, da ganinmu, da karfinmu matukar Ka rayamu, Ka sanyasu masu wanzuwa a garemu (zuwa mutuwa), Ka sanya ramuwarmu akan wanda ya zalincemu, Ka kuma taimakemu akan wanda ya ki mu, Kada Ka sanya masifarmu a addininmu, Kada ka sanya duniya (ta zama) ita ce mafi girman manifarmu, ko matukar tunaninmu (damuwarmu), kuma Kada Ka dora mana wanda ba zai jikanmu ba)){45}. Tirmizi a lamba ta: 3502, da Hakim, 1/528 Zahabi ya inganta shi, kuma Albany ya kyautata shi, a cikin Sahihul Tirmizi, 3/ 168, da Sahihul Jami’i, 1/400.
83- ((Ya Allah ina neman tsarinka daga ragwantaka, kuma ina neman tsarinka daga rowa, kuma ina neman tsarinka da amaidani zuwa makaskanciyar rayuwa, ina kuma neman tsarinka daga fitinar duniya da azabar kabari)){46}. Bukhari, a lamba ta: 3822.
84- ((Ya Allah Ka gafarta min kura-kuraina, da jahilcina, da wuce gona da iri na a cikin lamarina, da abinda kai ne mafi sani dashi fiye dani, ya Allah Ka gafartamin kakacina (sakin bakina) da kokarina (gaskena) da kuskurena, da gangancina, dukkan hakan na gareni)){47}. Bukhari da Muslim: Bukhari, a lamba ta: 5398, Muslim kuma a lamba ta: 2719.
85- ((Ya Allah, na zalunci kaina zaunci mai yawa, kuma babu mai gafarta zunubai sai Kai, ka gafarta mini da gafara daga gareKa, kuma ka yi mini rahama, lallai ne Kai Mai gafara ne, Mai jin ƙai)){48}. Bukhari da Muslim: Bukhari, a lamba ta: 834, Muslim, a lamba ta: 2705.
86- ((Ya Allah gareKa na miƙa wuya, kuma da Kai ne na yi imani, gareka ne na dogara, gareKa ne na dawo, saboda Kai ne na yi husuma. Ya Allah lallai ni ina neman tsari da buwayarKa, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai (kada) Ka ɓatar da ni, Kai ne Rayayye wanda ba zai mutu ba, aljanu da mutane kuwa zasu mutu)){49}. Bukhari da Muslim: Bukhari, a lamba 6398, Muslim kuma a lamba ta: 2719.
87- ((Ya Allah ina rokonka abubuwan da suke kawo rahamarka, da dalilan gafararka, da aminci daga kowane zunubi, da ganima daga dukkan aiki na kwarai, da nasarar Aljanna, da kubuta daga wuta)){50}. Alhakim,1/525, ya kuma inganta shi, Zahabi da Baihaki kuma suka yi masa muwafaka a cikin Da’awat, a lamba ta: 206, kuma ka duba Azkar na Nawawi, shafi na 340, hakika Mai tahkikin Abdulkadir Al-Arna'uud ya kyautata shi.
88- ((Ya Allah Ka gafartawa muminai (maza) da muminai (mata)){51}. Saboda Hadisin Ubadah-Allah Ya yarda da shi-ya ce: Na ji annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: ((Wanda ya nemawa muminai (maza) da muminai (mata) gafara, Allah zai rubuta masa kyakkyawa a dukkanin wani mumini da mumina)). Dabarani a cikin Alkabir, 5/202, a lamba ta: 5092, da 3/334, da kuma lamba ta: 2155, kuma Alhaisami ya kyautata Isnadinsa a cikin Majma'uz Zawa'id, 10/210, kuma Albany ya kyautata shi a cikin Sahihul Jami'i, da lamba ta: 5902, 5/242.
89- ((Ya Allah Ka gafarta min zunubina, Ka yalwata mini a gidana, Ka yi mini albarka cikin abinda Ka azurtani)){52}. Ahmad, a lamba ta: 16599, da lamba 23114, da kum Lamba ta : 23188, da Tirmizi, da lamba ta: 3500, kuma Masu tahakikin Al-musnad suka ce, 27/144, kuma a cikin 38/145: ((kykkyawa ne dan waninsa)).
90- ((Ya Allah ni ina rokanKa daga falalarKa da jin kanKa domin cewa shi, ba bu mai mallakarsu sai Kai)){53}. Dabari ya fitar da shi, Haithami ya ce a cikin Majma'i Alzawa'id 10/159: ((Mazajensa Mazajen Sahihu ne, banda Muhammad bin Zayyad shi kuma amintacce ne)), kuma Albany ya inganta shi a cikin Sahihul Al-jami'i, 1/1278.
91- ((Ya Allah ni ina neman tsarinka daga tsufa, da fadowa (daga sama) da rusowar gini, da bakin ciki, da dilmiyewa, da konewa, kuma ina neman tsarinka da Shaidan ya fizgeni lokacin mutuwa, kuma ina neman tsarinka da in mutu ina mai juyawa tafarkinka baya, kuma ina neman tsarinka da in mutu abin sara)){54}. Abu Dawud ya fitar da shi da lamba ta: 1552, da kuma Nasa'i, a lamba 5531 da lamba 5532, Albany kuma ya inganta shi a cikin Sahihul Nasa'i, 3/1123, da Sahihu Sunani Abi Dawud 1/425.
92- ((Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga yinwa, saboda cewa ita tir da abokiyar kwanciya, kuma ina neman tsarinka daga Ha'inci domin cewa shi tir da Abokan sirri)){55} Abu Dawud ya fitar da shi a lamba1547, da Nasa'i a lamba ta: 5483, kuma Albany ya kyautata shi, a cikin Sahihu Nisa'i, 3/1112.
93-(( Ya Allah ina neman tsarinka daga gajiyawa da kasala (lalaci) da ragwantaka, da rowa, da tsufa, da rafkana, da talauci da kaskanci, da talauci, kuma ina neman tsarinka daga talauci, da kafirci, da fasikanci, da sabawa gaskiya, da munafinci, da yin aiki da jiyarwa, da riya, kuma ina neman tsarinka daga kurumta, da bebantaka, da hauka, da kuturta mai yanke gaba, da kuturta mai kandarewa, da munanan cututtuka)){56}. Nasa'i ya fitar da shi, a lamba ta: 5493, da Hakim, 1/530, kuma Albany ya inganta shi, a cikin Sahihul Al-jami'i, 1406, da Irwa'u Al-galil, a lamba ta: 852.
94-((Ya Allah ina neman tsarinka daga talauci, da karanci, da kaskanci, ina kuma neman tsarinKa da in zalinta ko azalunce ni)){57}. Abu Dawud ya fitar da shi, a lamba 1544, da Nasa'i, a lamba 5475, Albany ya inganta shi a cikin Sahihul Nasa’i, 3/111, da Sahihul Al-jami'i 1/407 kuma Albani ya inganta shi a cikin Mawridul Zam'an, 2/455,
95- (( Ya Allah ina neman tsarinka daga mumunan makwabci a cikin gidan zama, domin makwabcin tafiya (sahara) yana wucewa)){58}. Bukhari a cikin Adabul Mufrad, a lamba ta: 117, da Hakim, 1/532, Al-Zahabi ya inganta shi, kuma Nasa’i ya fitar da shi a lamba 5517, albani ya inganta shi a cikin Sahihul Al-jami'i, 1/408, da Sahihul Al-nasa'i 3/118.
96- ((Ya Allah ni ina neman tsarinka daga zuciyar da bata tsoron Allah da addu'ar da ba'a amsawa, da zuciyar da bata koshi, da ilimin da baya amfanarwa, ina neman tsarinka daga wadannan hudun)){59}. Tirmizi a lamba, ta: 3482, da Abu Dawud, a lamba 1549, kuma Babban malami Albany ya ingantashi, a cikin Sahihul Al-jami'i, da lamba 1295, da Sahihun Nasa’i, 3/1113.
97- ((Ya Allah ni ina neman tsarinka daga mumunan wuni, da mumunan dare, da mumunan lokaci, daga kuma mumunan aboki, da mumunan makwabci a gidan zama)) {60}. Dabarani ya fitar da shi, kuma Haithami ya ce a cikin Al-zawa'id 10/144: (( Mazajansa Mazajan Bukhari ne)). kuma Albani ya kyautata shi a cikin Sahihul Al-jami'i, 1'411 a lamba ta: 1290.
98- (( Ya Allah ina rokanka Aljanna, kuma ina neman tsarinka daga Wuta)). (sau uku){61}. Tirmizi ya fitar da shi a lamba ta: 2572, da Ibnu Majah, a lamba 3340, da Nasa’i a lamba ta: 5536, kuma Albani ya inganta shi, a cikin Sahihul Tirmizi, 2/319, da Sahihun Nasa’i, 3/1121, Lafazinsa;((Wanda ya roki Allah aljanna sau uku, Aljanna zata ce: ya Allah Ka shigar dashi Aljanna, wanda ya nemi tsarin wuta sau uku, wuta zata ce: ya Allah Ka tserar da shi daga wuta)).
99- (( Ya Allah Ka fahimtar dani addini)){62|. Ruwayar Bukhari da Muslim tana nuni a akan shi a addu'ar Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ga Ibnu Abbas- Allah ya yarda da su. Bukhari a lamba 143, Muslim kuma a lamba ta: 2477.
100- ((Ya Allah ina neman tsarinka da in taraKa da wani alhali ina sani, kuma ina neman gafararka ga abinda ban sani ba)){63}. Ahmad ya rawaito shi, 4/403, da ibnu Abi Shaibah, 10/337, da Dabarani a cikin Almu'ujamil Alau’sadh 4/284, kuma Albany ya inganta shi, a cikin Sahihul Altarghib wattarhib.1/19.
101-(( Ya Allah Ka amfanar dani da abinda Ka sanar dani, Ka kuma sanar dani abinda zai amfanar dani, Ka karamin sani)){64}. Tirmizi ya fitar da shi, a lamba ta: 3599, da ibnu Majah, da lamba 259, kuma Albani ya inganta shi, a cikin Sahihu Ibnu Majah, 1/47.
102- ((Ya Allah ina rokanka ilimi mai amfani, da arziki tsarkakke, da aiki abin karba)){65). Ibnu Majah ya fitar da shi, da lanba ta: 925, da Nasa'i a cikin Ayyukan wuni da dare, da lamba102, da Ahmad, 6/294, da 305, kuma Albani ya inganta shi, a cikin Sahihu ibnu Majah, 1/152.
103(( Ya Allah ina rokanka da cewa Kai ne Ubangiji daya tal, abin nufi da bukata, wanda bai haifa ba, ba'a haife shi ba, kuma wani kini bai zamo a gare shi ba, da Ka gafarta mini zunubaina, lalle Kai mai yawan gafara da jin kai ne)){66}. Nasa'i ya fitar da shi, da lamba 1300, Lafazin nasa ne, da Nasa’i a cikin Alkubra da lamba 7665, da Abu Dawud, da lamba ta: 985, kuma Albany ya inganta shi, a cikin Sahihut Sunanin Nasa’i , 1/147.
104- ((Ya Allah ina rokanKa lalle cewa godiya ta tabbata a gareKa babu wani abin bautawa da gaskiya sai Kai, {Kai kadai kake, baka da abokin tarayya} {Ya} makagin sammai da kasa, ya ma'abocin girma da karamci, ya rayayye ya tsayayye, ina rokonKa {Aljanna} kuma ina neman tsarimKa daga Wuta)){67}. Abu Dawud, da lamba 1495, da ibnu Majah, da lamba ta: 3858, da Nasa’i, da lamba 1299, da Tirmizi, da lamba 3544, kuma Albani ya inganta shi, a cikin Sahihu Nasa’i, 1/279, kuma a cikin Sahihu Ibnu Majah, 2/329.
105- ((Ya Allah ina rokanka, saboda ni na shaida cewa kai ne Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai kai, kai kadai tal,wanda ake nufa da dukkan bukatu, wanda bai Haifa ba, kuma ba’a haife shi ba, kuma babu wani tamka a gare shi)){68}. Abu Dawud, da lamba ta: 985, da Tirmizi, da lamba 3475, da ibnu Majah da lamba, da Ahmad 5/360, kuma Albani ya inganta shi a cikin Sahihu Sunanit Tirmizi, 3/163.
106- ((Ya Ubangijina! Ka gafarta mini, Ka kuma karbi tubana, lalle Kai Mai yawan karbar tubane Mai yawan gafara)){69). Abu Dawud, da lamba ta: 1518, da Tirmizi, da lamba 3434, Lafazin nasa ne, da Nasa'i a cikin Alkubra, da lamba 10292, da ibnu Majah, da lamba 3814, kuma Albani ya inganta shi a ckin Sahihu Ibnu Majah, 2/321, da kuma cikin Sahihut Tirmizi, 3/153.
107- ((Ya Allah da Iliminka na gaibu, da IkonKa a bisa halitta, Ka rayani matukar Ka san rayuwa ce mafi alkhairi a gare ni, Ka karbi raina matukar Ka san mutuwa ce mafi alkhairi a gare ni, ya Allah ni ina rokanka tsronKa a boye da sarari, ina kuma rokanKa kalmar gaskiya a halin yadda da fushi, ina rokanKa tsakaitawa a cikin wadata da talauci, ina kuma rokanKa ni'mar da bata karewa, ina kuma rokanKa sanyin ido da ba ya yankewa, ina rokanKa yarda bayan kaddara, ina rokanKa hutu bayan mutuwa, ina kuma rokanKa dadin duba zuwa fuskarKa, da begen haduwa da Kai, batare da wata cuta mai cutarwa ba, ko fitina mai batarwa ba, Ya Allah Ka kawata mu da adon Imani, kuma Ka sanya mu shiryayyu masu shiryarwa)){70}. Nasa’i, da lamba 1305, da Ahmad, 4/264, kuma Albani ya inganta shi a cikin Sahihun Nasa’i, 1/280, da 1/281.
108- ((Ya Allah Ka azurtani sanKa, da san wanda sansa zai amfanar dani a gurinKa, ya Allah abinda Ka azurtani na abinda nake so, Ka sanya shi karfi a gare ni cikin abinda Ka ke so, ya Allah abinda Ka juyar da shi daga gare ni na abinda nake so, Ka sanya shi dalilin (samun dama) a gare ni cikin abinda Ka ke so)){71}. Tirmizi ya fitar da shi, da lamba 3491, kuma ya kyautata shi, Sheikh Abdulkadir Al'arna'ud ya ce: ((shi kamar yadda ya ce ne)), duba Tahkikinsa ga jAMI'UL AL'USUL,4/341.
109-((Ya Allah Ka tsarkakeni daga zunubai da kurakurai, Ya Allah Ka tsarkakeni daga garesu, kamar yadda ake tsarkake farin tufafi daga datti, ya Allah Ka tsarkakeni da kankara da ruwan sanyi)){72}. Muslim ne ya fitar da shi, a lamba ta: ta: 476, da Nasa’i, da lamba ta: 400.
110- ((Ya Allah ni ina neman tsarinka daga rowa, da ragwantaka, da mummunar rayuwa, da fitinar kirji (hassada, kulli..) da azabar kabari)){73). Nasa’i a lamba 5469, Lafazinsa: (Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kasance yana neman tsari daga abubuwa biyar: Daga rowa, da ragwantaka, da mummunar rayuwa, da fitinar kirji da azabar kabari)). kuma Abu Dawud ya fitar da shi, da lamba 1539, Arna'uudh ya kyautata shi a Takhrijinsa ga Jami'ul Usul, 4/363.
111- ((Ya Allah Ubangijin Jibril, da Mika'il, Ubangijin Israfil, ina neman tsarinka daga zafin wuta, da azabar kabari)){74}. Nasa’i ya fitar da shi, a lamba 1344. da Ahmad 6/61, da Baihaki a cikin Adda'wat, a lamba ta: 109, kuma Albani ya inganta shi a acikin Sahihun Nasa’i 3/1121, da Silsilatul Al-ahadis Assahiha, a lamba ta: 1544.
112- (( Ya Allah Ka kimsa mini shiriyata, kuma Ka kare ni daga sharrin kaina)){75}. Nasa’i ya fitar da shi, Lafazin nasa ne, 5/519 a lamba 3483, Ahmad ya fitar da shi da makamancinsa 33/197, a lamba 19992, da Hakim 1/ 510, shima da makamancinsa, kuma Zahabi ya inganta shi, Masu tahkikin Musanad sun ce dangane da Hadisin Ahmad, 33/197: (( IsnadinSa ingantacce ne a bisa sharadin Bukhari da Muslim)), amma lafazinTirmizi ne , Albani ya raunana shi a cikin Dha'ifut Tirmizi, shafi na 397.
113-((Ya Allah ina rokanKa Ilimi mai amfani ina kuma neman tsarinKa daga Ilimin da baya amfanarwa)){76}. Nasa'i ya fitar da shi, a cikin Alkubra, a lamba ta: 3843, kuma Albani ya inganta shi a acikin Sahihu Sunani ibnu Majah, 2/327. Lafazinsa: ((ku roki Allah Ilimi mai amfani, kuma ku nemi tsari daga Ilimin da baya amfanarwa)).
114- ((Ya Allah Ubangijin sammai {bakwai} Ubangijin ƙasa, kuma Ubangijin Al'arshi mai girma, Ubangijinmu, kuma Ubangijin kowane abu, Maƙagin ƙwayar hatsi da kwalfar gurtsu, Wanda Ya saukar da Attaura da Linjila da Alfurƙan, ina neman tsarinKa daga sharrin dukkan abinda Kake riƙe da makwankwaɗarsa, ya Allah Kaine na farko, babu wani abu kafinKa, kuma Kaine na ƙarshe babu wani abu a bayanKa, Kaine zahiri babu wani abu a birbishinKa, Kaine baɗini babu wani abu koma bayanKa, Ka biyamana bashi kuma Ka wadatamu daga talauci)){77}. Muslim ne ya fitar da shi, a lamba ta: 2713, daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi.
115- ((Ya Allah ! Ka hada zukatanmu, Ka gyara tsakaninmu, Ka shiryar da mu tafarkin aminci, Ka tserar da mu daga duffai zuwa ga haske, Ka kuma nisantar damu daga Munana abinda ya bayyana daga garesu da abinda ya buya, Ka yi albarka ga kunnuwanmu da idanuwanmu, da zukatanmu, da matayenmu, da zurriyarmu, Ka karbi tubanmu, lalle Kai Mai yawan karbar tuba ne mai yawan jin kai, Ka sanyamu masu godiya ga ni'imominKa, masu yabonKa akansu, masu karbarsu, Ka kuma cikasu a garemu)){78}. Abu Dawud, da lamba ta: 969, da Hakim, Lafazin nasa ne 1/265, kuma ya ce: ((Ingattacce ne a bisa sharadin Muslim)), Zahabi ya yi masa muwafaka, 1/26, Albani ya inganta shi a cikin Sahihu Adabul Al-Mufrad, da lamba 630.
166-((Ya Allah ! ina rokanka mafificin roko, da mafificiyar Addu'a, da mafificiyar nasara, da mafificin aiki, da mafificin lada, da mafificiyar rayuwa, da mafificiyar mutuwa, ka kuma tabbatar dani, Ka nauyaya ma'aunaina, Ka tabbatar da Imanina, Ka daukaka darajata, Ka karbi sallata, Ka gafarta kuskurena, kuma ina rokanKa darajoji madaukaka na daga Aljanna, ya Allah ni ina rokanKa mabudan alkhairi da kuma cikarsu, da matattaransu, da farkonsa da sararinsa da boyansa, da darajoji madaukaka na daga Aljanna, Allah Ka amsa, ya Allah ina rokanKa mafificin abinda zan zo da shi da mafi alkhairin abinda zan aikata, da mafi alkhairin abinda ya boyu, da mafi alkhairin abinda ya bayyana, da darajoji madaukaka na daga aljanna, Allah Ka amsa, Ka gyara lamarina, Ka tsarkake zuciyata, Ka katange al'aurata, Ka haskaka zucyata, Ka gafarta min zunubina, ina rokanKa darajoji madaukaka na aljanna, (Ya) Allah Ka amsa, Ya Allah ina rokanKa Ka yi albarka a kaina, da ji na, da ganina, da raina da halitta ta da dabi'una, da iyalaina, da rayuwata, da mutuwata, da aikina, Ka karbi kyawawan ayyukana, kuma ina rokanKa darajoji madaukaka na daga aljanna Allah Ka amsa,)){79}. Hakim ne ya fitar da shi, daga Ummu Salamah mar'fu'i, 1/520, Zahabi kuma ya inganta shi, 1/520, da Baihaki a cikin Adda'awat, da lamba 225, da Dabarani a cikin Alkabir, 23/326, a lamba 717.
117-((Ya Allah Ka nisantar dani dabi'u ababan ki, da soye-soyen zuciya, da ayyuka, da cututtuka)){80}. Hakim ne ya fitar da shi, 1/523, kuma ya ce: ((Ingattacce ne a bisa sharadin Muslim)). Zahabi ya yi masa muwafaka, 1/532, kuma Dabarani a cikin Al-mu'ujamul-Alkabir, 19/19 da lamba 36, kuma Albani ya inganta shi a ckin Zilalil Al-jannah da lamba 13.
118- ((Ya Allah Ka wadatar dani da abinda Ka azurtani, Ka yi mini albarka a cikinsa, Ka maye min dukkan abinda ya faku a gare ni da alkhairi))[81]. Hakim ne ya fitar da shi, 1/532 ya kuma inganta shi Zahabi, 1/510, daga Ibnu Abbas -Allah ya kara yarda da su - da Baihaki a cikin Al’adab, da lamba 1084, a cikin Adda'wat, 211, Alhafiz Ibnu Hajar ya kyautata shi a cikin Alfutuhat al-rabbaniyya, 4/383.
119- ((Ya Allah Ka yi mini hisabi hisabi mai sauki)){82}. Ahmad ne ya rawaito shi, 6/48, da Hakim, 1/255, kuma ya ce: ((Ingattace ne a bisa sharadin Muslim)), kuma Zahabi ya yi masa muwafaka, 1/55, Nana Aisha-Allah ya kara ya yarda da ita- ta ce: ya yin da ya juyo sai na ce: Ya Manzan Allah menene Hisabi mai sauki? sai ya ce: (( Ya yi duba littafinsa sai ya yafe masa, hakika duk wanda aka tattauna hisabinsa zai halaka, dukkan abinda yake samun mumini Allah Yana kankare masa shi har kayar da ya taka)). Babban malami Albani ya fada akansa, a cikin Mishkatul Al-misbah:(Isnadinsa kyakkyawa ne)).
120- ((Ya Allah Ka taimaka mana a bisa ambatanKa, da godiyarKa, da kyakkyawar bautarKa)){134}. Ahmad ne ya fitar da shi, 2/299, da Hakim, 1/499, kuma ya inganta shi, kuma Zahabi ya yi masa muwakafa, shi lamar yadda suka ce ne, shi a gurin Abi Dawud, da lamba 1524, da Nasa’i a cikin Alkubra, da lamba 9973, kuma Albani ya inganta shi a cikin Sahihul Al-mufrad, da lamba 534.
121-((Ya Allah ina rokanka Imanin da ba ya juyawa (ridda), da ni'imar da bata karewa, da zama tare da (Manzan Allah) Muhammad-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- a cikin madaukakiyar Aljanna ta dawwama)){84}. Ibnu Hibban ne ya fitar da shi (Mawarid) shafi 604, a lamba 2436, daga Ibnu Mas'ud- Allah ya yarda da shi-Maukufi, kuma Ahmad ya ruwaito shi daga wata hanyar daban, 1/386,400, da Nasa’i a cikin Aikin wuni da dare, da lamba 869, kuma Albani ya kyautata shi a cikin Silsilatu al-ahadisu Al-sahiha, a karkashin lamba ta 2301.
122- ((Ya Allah Ka kareni sharrin kaina, Ka karfafeni da mafi shiriyar lamarina, Ya Allah Ka gafarta min abinda na boye, da abinda na bayyana, da abinda na yi kuskure, da abinda na yi da gangan, da abinda na sani da abinda ban sani ba)){85}. Nasa’i ne ya fitar da shi a cikin Alkubra, 6/246. da lamba 10830, da Hakim, 1/510, ya kuma inganta shi, kuma Zahabi ya yi masa muwafaka, Ahmad ya fitar da shi, 4/444, Hadisin yana cikin Al-musnad da aka yi tahakikinsa, 33/ 197 da lamba ta: 1992, kuma Hafiz a ckin Al'Isabah ya ce (( Isnadinsa inagattacce ne)) kuma Albani ya inganta shi a cikin Takhrijin Riyadhus Salihin, a ta'alikinsa akan hadisin da lamba ta: 1495.
123-((Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga rinjayar bashi, da rinjayar maƙiyi, da dariyar maƙiya)){86}. Nasa’i ya fitar da shi, da lamba ta: 5475, da Ahmad, 2/173, kuma Albani ya ingantashi a cikin Sahihun Nasa’i, 3/1113.
124-((Ya Allah Ka gafarta min, Ka shiryardani, Ka azurtani, Ka bani lafya, ina neman tsarin Allah daga kuncin matsaya ranar Alkiyama)){87}. Nasa’i, da lamba ta 1617, da ibnu Majah, da lamba1356, kuma Albani ya inganta shi a cikin Sahihu Sunanu Nasa’i, 1/356, da kuma Sahihu Ibnu Majah.1/226
125- ((Ya Allah Ka jiyar dani dadi da jina da ganina, Ka sanyasu masu wanzuwa a gareni, Ka taimakeni akan wanda ya zalunceni, Ka karbarmin fansa daga gare shi)){88}. Tirmizi ya fitar da shi, da lamba ta: 3681, da Bukhari a cikin Al-adbul Al-mufrad, da Lamba ta 650, da Hakim, 1/523. kuma Zahabi ya ingantashi, kuma Albani ya kyautata shi a cikin Sahihul Tirmizi, 3/188.
126- ((Ya Allah ina rokanKa tsarkakakkiyar ruywa, da mutuwa madaidaiciya, da makoma (zuwa lahira) ba mai kaskanci ba, ko kunyata ba)){89}. Hakim ne ya fitar da shi 1/541, da Zawa’idu Musnadul Bazzar 2/442 mai lamba ta: 2177, da Dabarani a Addu’a mai lamba 1435, Haisumi ya ce a Majma'il Zawa'id 10/179: (Isnadin Dabarani mai kyau ne).
127-(( Ya Allah dukkan godiya ta tabbata a gareKa, babu mai damkewa (kuntatawa) ga abinda ka shinfida (yalwata) kuma babu mai shimfidawa ga abinda ka damke (kuntatata), babu mai shiryarwa ga wanda Ka batar babu kuma mai batarwa ga wanda ka shiryar, babu mai bayarwa ga abinda ka hana, babu kuma mai hanawa ga abinda ka bayar, babu mai kusantowa ga abinda ka nisantar, babu kuma mai nisantarwa ga abinda ka kusantar, ya Allah Ka yalwata mana daga albarkatunka, da jin kanka, da falalarka, da arzikinka, ya Allah ina rokanka ni'ima madawwamiya, wacce bata camzawa kuma bata gushewa, ya Allah ina neman tsarinka daga sharrin abinda ka bamu da sharrin abinda ka hanamu, ya Allah ka soyarmana da imani ka kuma kawata shi a zukatanmu, ka sa mana kiyayyar kafirci da fasikanci, da sabo, ka sanyamu da cikin shiryayyu, ya Allah ka karbi ranmu muna muslimai, ka rayamu muna muslimai, ka riskar damu ga salihai ba masu kunyataba ko ababan fitinarwa ba, ya Allah ka tsinewa kafirai wadanda suke karyata manzanninka, suke kuma toshe tafarkinka, ka sanya azabarka a kansu, ya Allah ka tsinewa kafirai wadanda aka bawa littafi, ya Ubangijin gaskiya {Allah ka amsa})){141}. Ahmad da lafazinnsa 3/424, 24/246 da lamba ta: 15492 da abinda ke tsakanin na Hakim, 1/507, 3/23,24. Bukhari ya fitar da shi a cikin Al-adabul al-Mufrad, da lamba 699, kuma Albani ya inganta shi a acikin Takhrij Fiqhus Seerah, shafi na 284, da kuma cikin Sahihul al-adabul al-mufrad na Bukhari, da lamba 538 shafi 259.
128-((Ya Allah ka gafartamin, kajikaina, ka shiryar dani, ka bani lafiya, ka azurtani)){91}. Muslim, da lamba 2696, da lamba ta: 2697, a cikin wata ruwaya ta muslim: ((lalle wadannan zasu tattarama duniyarka da lahirarka)) a cikin Sunanu ya ce Dawud, da lamba 850: ya ce: (( lokacin da balaraban kauyen ya juya Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:((Hakika ya cika hannayensa da alkhairi)).
((... Ka gyarani, Ka daukakani)){92}. ka duba Sunanu Ibnu Majah, da lamba ta: 898. da Sunan Tirmizi, da lamba 284, Ibnu Majah ya inganta shi 1/148. da Sahihut Tirmizi, 1/90.
129- ((Ya Allah Ka kara mana kada Ka rage mana, Ka girmamu, Kada Ka wulakantamu, Ka bamu kada Ka hanamu, Ka zabemu kada Ka zaba akanmu, Ka yarda da mu ka sa a yarda da mu)){93}. Tirmizi, 5/326, da Hakim, 2/98. kuma ya inganta shi, Shekh Abdulkadr Al-arna'uud a Tahkikinsa na Jami'ul Al-usul, 11/282. da lamba 8847.
130- ((Ya Allah Ka kyautata halittata, Ka kyautata dabi'una)){145}. Ahmad ya fitar dashi 6/68, da 155, da 1/406, da Ibnu Hibbana ( 2423-Mawarid) da Al-Dayalisi, 374, da Musnadu Abi Ya'ala, da lamba 5075, kuma Albani ya ingantashi a Irwa'ul Ghaleel, 1/115, da lamba 74.
131-((Ya Allah Ka tabbatar dani, Ka sanyani shiryayye abin shiryarwa)){95}. Addu'ar Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-ta yi nuni akansa, ka duba: Bukhari, da lamba 6333, haka nan kuma da lambobin 3020, 3936, da waninsu.
132- ((Ya Allah, ni ina roƙonKa tabbata a cikin al'amari, da ƙudirin niyya akan shiriya, ina roƙonKa abubuwan da suke wajabta rahamarka, da ayyukan da suke tababtar da gafararKa, ina roƙonKa godewa ni'imarKa, da kyakkyawar ibadarKa, kuma ina rokanKa zuciya kubutacciyya, da harshe mai gaskiya, ina roƙonKa daga mafi alkhairin abinda Ka sani, kuma ina neman tsarinKa daga sharrin abinda Ka sani, kuma ina neman gafararKa ga abinda Kake sani, lallai cewa Kaine Masanin abinda ke fake){96}. Ahmad, 28/338 da lamba 17114, da 28/356, da lamba, da Tirmizi, da lamba 3407, da Al-Dabarani, a cikin Al-mu'ujam Alkabir da lafazinsa, da lamba 7135, da lamba,7157, da 7175, da lamba7176, da 7177, da 7178, da 7179, da 7180, kuma ibnu Hibban ya fitar da shi, 3/ 215. da lamba 935, da 5/310, da lamba 1975, Al-arna'uud ya kyautata shi a cikin Sahihu Ibnu Hibban 5/312, kuma masu Tahkikiin Al-musnad, sun kyautata shi da hanyoyinsa, 28/338, kuma Albani ya ambace shi a Silsilatul al-ahadisu al-sahiha a cikin mujalladi na bakwai, da lamna ta: 3228. haka nan a cikin Sahihul Mawarid Al-zam'an, da lamba 2416, kuma ya ce: ((ingantacce ne dan waninsa)).
133- ((Ya Allah ni ina rokanKa (Aljannar) firdausi mafi daukakar Aljanna)){97}. An ciro shi ne daga fadar Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ((...Idan za ku roki Allah, to ku roke shi Alfirdausi, domin ita ce mafi alkhairin aljannah, kuma mafi daukakar Aljannah, samanta Al'arshen Rahman yake kuma daga gareta ne koramun Aljanna suke ketowa)). Bukhari a lamba 2790/ da lamba ta: 7423
134- (( Ya Allah ka sabunta Imani a zukatanmu)){98}. An ciro shi ne daga Hadisin Abdullahi bn Umar-Allah ya yarda da su-, ya ce: Manzon Allah -tsra da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya ce:((Hakika Imani yana tsufa a cikin (zuciyar) dayanku, kamar yadda tufafi yake tsufa, ku roki Allah ya sabunta Imani a zukatanku)), Hakim, 1/4, Zahabi ya yi masa muwafaka kuma ya inganta shi,, Haithami ya ce a cikin Majma'u Al-Zawa’id 1/52: (Dabarani ya ruwaito shi a cikin Alkabir, Isnadinsa kyakkyawa ne)). Albani kuma ya kyautata shi a cikn Silsilatul Al-ahadsil Al-sahiha, 4/113. da lamba ta: 1585.
135- ((Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga sallar da bata amfanarwa)){99}. Abu Dawud, da lamba 1549, kuma Albani ya inganta shi a ckin Sunanu Abi Dawud, 1/424.
136-((Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga mummunan makwabci, daga kuma mata wacce zata sani furfura kafin lokacin furfurar ya yi, ina kuma neman tsarinKa daga Da wanda zai kasance uban gida a gare ni, daga kuma dukiya wacce zata zama azaba a gareni, daga kuma aboki makiri, Idonsa yana kallona (kallon badadi) zuciyarsa kuma tana kiyon (cutar dani), in ya ga kyakkyawa (dana aikata) sai ya binne shi, idan kuma ya ga mummuna (dana aikata) sai ya yada shi)){100}. Dabarani a cikin Addu'a, 3/1425, da lamba ta: 1339, Albani ya ce a cikin Silsilatul al-ahadis Al-sahihah, 7/377, da lamba ta: 3137: (( Na ce: wannan Isnadin kyakkyawa ne, mazajensa dukkaninsu daga mazajen Zahabi ne...)).
137-((Ya Allah kada Ka kunyatar dani ranar Alkiyama)){101}. Ahmad a cikin Al-musnad: ((Isnadinsa I ngattacce ne)), kuma Dabarani ya fitar da shi a cikin Al-mu'ujamul Alkabir, 3/20. da lamba ta: 2524, da lafazin ((Ya Allah kada Ka kunyatar dani ranar Alkiyama, kada Ka kunyatar dani ranar debe kauna)).
138- ((Ya Allah ni ina rokanKa lafiya a duniya da lahira)){102|}. ibnu Majah da lamba ta: 3851, kuma Albani ya inganta shi a cikin Sahihu Ibnu Majah, 3/259, haka kuma a cikin Silsilatul Al-ahadisil Al-sahihihah da lamba 1138.
139-(( Ya Allah ni ina neman tsarinka daga Ilimin da ba ya amfanarwa, da aikin da ba'a daga shi, da zuciyar da bata kaskantuwa ga (ambaton Allah) da Addu'ar da ba'a amsawa)){103}. Ibnu Hibban ya fitar da shi, da lamba 2440 (mawarid), Albani kuma ya inganta shi a cikin Sahihu mawaridil Al-Zam'an, 2/454, da lamba 2066.
140- ((Ya Allah ina neman tsarinKa daga bacin rai ,da bakin ciki, da gajiyawa, da kasala, da rowa da ragwantaka, da rinjayar Mazaje)){104}. Bukhari, a lamba 6363, Anas- Allah ya yarda da shi ya ce: ((Na kasance ina yi wa Manzon Allah-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - hidima duk sa'adda zai sauka, na kasance ina jinsa yana yawaita fadin: ((Ya Allah ina neman tsarinKa...)).
141-((Ya Allah ina neman tsarinka daga azabar wuta, ina kuma neman tsarinKa daga azabar kabari, kuma ina neman tsarinKa daga fitintinu wadanda suka bayyana daga cikinsu da wadanda suka buya, kuma ina neman tsarinKa daga fitinar Jujal)){105}. Muslim, a lamba 2867, a cikinsa: ((ku nemi tsarin Allah daga azabar wuta))... {ku nemi tsarin Allah daga azabar kabari...} zuwa karshensa.
142-((Ya Allah ina rokanKa (mutuwar) shahada a tafarkinka)){106}. Muslim, da lamba ta: 1909, an ciro shi daga fadinsa- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: ((wanda ya roki Allah shahada da gaskiya, Allah zai isar da shi matsayin shahidai, koda ko ya mutu akan shinfidarsa )).
143-((Ya Allah Ka gafarta min kurakuraina ranar Alkiyama sama da yawan haluttunKa cikin mutane, ya Allah Ka gafarta min zunubina, Ka shigar dani ranar Alkiyama mashiga ta karamci)){107}. Bukhari da lamba ta: 4323, da Muslim da lamba ta: 2498, an ciro ne daga Addu'ar Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ga Ubaid Abi Amir, yana daga cikin Addu'arsa-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ga Abi Bardata-Allah ya yarda da su.
144-((Ya Allah Ka shiryar dani cikin wadanda ka shiryar, Ka bani lafiya cikin wadanda Ka bawa lafiya, Ka jibinci (lamarina) cikin wadanda Ka jibinta, Ka yi albarka cikin abinda Ka bani, Ka kare ni sharrin abinda Ka kaddara, yadda lamarin yake, wanda Ka so ba ya kaskanta, AlherinKa ya yawaita, Ubangijinmu, kuma girmanka ya daukaka)){109}. Ahmad a cikin Al’Musnad, 3/249, da lamba1723, kuma masu Tahkikin Al- musnad suka ce: 3/249 ((Isnadinsa ingattacce ne)). wannan riwayar sakakkace bata da wami dabaibayi da wuturi, kamar yadda ya zo a cikin wata ruwayar daban, a cikin wannan ruwayar, Anas Allah ya yarda da shi ya ce: ((kuma ya kasance yana koya mana wannan addu'ar...)).
145- ((Ya Ubangijina! Ka gafartamin kurakuraina ranar sakamako))[109}. Muslima, da lamba 214, an ce da annabi-tsira da amincinAllah su tabbata a gare shi- ya Manzan Allah, lalle ibnu Jud'an ya kasance a jahiliyya, yana sada zumunci, yana ciyar da miskianai, shin hakan mai anfani ne ? ya ce: ((Ba zai amfane shi ba, domin shi ba wata rana da ya taba cewa Ubangijina Ka gafarta min kura kuraina ranar sakamako)).
146-((Ina neman gafarar Allah Maigirma wanda babu wani Ubangiji da ya cancanci a bauta masa da gaskiya sai shi, Rayayye tsayayye da kansa, kuma ina tuba a gare shi)){110}. Tirmizi, da lamba ta: 3577, kuma Albani ya inganta shi, a cikin Sahihut Tirmizi, 3/469: ((wanda ya fade shi Allah zai gafarta masa koda a ce ya gudu daga garkon yaki)).
147-((Ya Allah Ka gafarta min zunubina, Ka tafiyar da fushin zuciyata, Ka tserar dani daga fitunu masu halakarwa)){111}. An ciro su daga Addu'o'in annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ga Nana Aisha- Allah ya yarda da ita- : (( Ya Allah Ka gafarta mata zunubinta, Ka tafiyar da fushin zuciyarta, Ka kareta daga fitunu masu halakarwa)) Ibnu Asakir ya fitar dashi da Isnadinsa a cikin (Al'arba'ina fi Manakibi Ummahatil Al- Mu'uminin)), shafi na 85 daga Nana Aisha Allah ya yarda da ita-kuma ya ce: wannan Hadisin kyakkyawa ne daga hadisin Ibnu Al-walid)), a cikin wani bugu kuma na da ban ya ce;((ka tserar dani da shaidan)) maimakon ((daga fitunu masu halakarwa)). Ka duba Takhrijinsa a gurin Albani acikin al-Dhaa'ifah, da lamba ta: 4207, yana da shahidi daga Ummu Salama- Allah ya yarda da ita- a gurin Ahmad, da lamba ta: 26576, 2/44 da makamancinsa, Lafazinsa: ((Ki ce ya Ubangijin Muhammad wanda yake annabi ka gafarta min zunubina, ka tafiyar da fushin zuciyata, ka tserar dani daga fitunu masu halakarwa, matukar Ka rayamu)). Kuma Haithami ya kyautata shi a cikin Majma'u Al-zawa'id,10/27, da lamba kuma shi a wurin Dabarani acikin Mu'ujamul Alkabir, 23/338, da lamba 785, ba tare da lafazinsa ba,((mutukar ka rayamu)). Kuma yana da shahid daga Ummu Hani Allah ya yarda da ita ta ce: ((ya manzan Allah, sanar da ni wata addu'a da zan yi, ya ce: ((Ki ce Allah ka gafartamin zunubina..)). Alkharadhi ya fitar da shi da lamba 52, Masawi’ul Akhlak, da lamba ta: 323.
148- ((Ya Allah Ka rayani akan sunnar annabinKa-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- Ka karbi raina a kan addininsa, Ka tsareni daga fitintunu masu halakarwa)), {112}. Baihaki ya fitar da shi a cikin AlKubra 5/95 daga addu'ar Ibnu Umar maukufi a gare shi, ibnu Mulakkin a cikin Al-badarul Al-munir, 6/309, ya fada yana mai cirowa daga Dhiya’u. (Isnadusa mai kyau ne)). Ibnu Mas'ud -Allah ya yarda da shi ya ce: ((kada dayanku ya ce: ya Allah ni ina neman tsarinka daga fitna, babu wani face yna kunshe da fitna, domin Allah yana cewa: Kadai dukiyoyinku da yayanku fitina ce {Taghabun:15}. dukkanin wanda zai nemi tsari ya nemi tsarin Allah daga fitunu masu halakarwa)). Ibnu Jarir, ya fitar da shi a Tafsirnsa, 13/475, da lamba 15912, kuma Ibnu Baddal ya ambace shi a cikin sharhinsa a Sahihul Bukhari, 4/13.
149- ((Ya Allah Ka yi Salati ga Muhammad, da Alayen Muhammad, kamar yadda Ka yi Salati ga Ibrahim, da alayen Ibrahim, Hakika Kai abin godewa ne kuma abin girmamawa ne. Ka yi albarKa ga annabi Muhammad, da alayen Muhammad kamar yadda ka yi albarka a bisa annabi Ibrahim da alayen Ibrahim a cikin talkai (hakika kai abin godewa ne kuma abin girmamawa ne)){113}. Bukhari da lamba ta: 3370, da abinda ke tsakanin baka biyu na Hadisin Abi huraira-Allah ya yarda da shi [ a gurin Muslim 405.
Godiya ta tabbabata ga Allah Ubangijin talikai, kamar yadda yake dacewa da girmansa, da girman milkinsa, Ya Allah Ka yi salati da aminci ga annabinmu Muhammad da Alayensa, da sahabbansa, da mabiyansa da kyautatawa zuwa ranar sakamako.
MAGANI DA RUK’YA (TAWAIDA)
DAGA AL’KUR’ANI DA HADISI
Mabukaci zuwa ga Allah-madaukakin sarki
DR. Sa'id Bn Ali Bn Wahf AlKahdhani.
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai.
Gabatarwa: Muhimmancin yin magani da Alkur'ani da kuma Hadisi.
Lalle godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrukan kawunanmu, kuma daga munanan ayyukanmu, wanda Allah ya shiryar da shi to babu mai batar da shi, wanda kuma ya batar, to babu mai shiryarwa a gare shi. Kuma ina mai shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kadai yake, ba shi da abokin tarayya, ina kuma shaida cewa annabi Muhammad bawansa ne kuma manzansa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da alayensa da sahabbansa, da wanda ya bi bayansu da kyautatawa zuwa ranar sakamako, da aminci da amincewa masu yawa, Amma bayan haka:
Babu kokwanto cewa, yin magani da Alkr'ani mai girma, da kuma abinda ya tabbata daga annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, na daga Tawaida: shi magani ne mai amfani, kuma waraka ne cikakke, Allah mai girma da buwaya ya ce: {Ka ce shi shiriya ne da waraka ga wadanda suka yi Imani}. Suratu Fussilat, aya ta: 44 Kuma Allah Tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka Ya ce: {Kuma Munã sassaukarwa daga Alƙur'ãni, abin da yake waraka ne da rahama ga mũminai. Kuma bã ya ƙãra wa azzãlumai (kõme) fãce hasãra) Suratul Isra'i: Aya ta: 82 {Min} a nan dan bayanin Jinsi ce, hakika Alkur'ani warkane dukkaninsa, kamar yadda yake cikin ayar da ta gabata{1}, kuma Allah mai girma da daukaka Ya ce: {Ya ku mutãne! Lalle wa'azi yã jẽ muku daga Ubangijinku, da waraka ga abin da yake a cikin ƙirãza, da shiriya da rahama ga muminai}. Suratu Yunus, aya ta: 57
Shi AlKur'ani shine cikakkiyar waraka daga dukkan cututtuka na zuciya, dana jikj, da cututtukan duniya da kuma na lahira, ba kowanne mutum ba ne yake cancanta ko ake datar da shi ga neman waraka da Alkur'an ba, idan mara lafiya ya kyautata yin magani da shi, ya magance rashin lafiyarsa da shi da gaskiya da Imani, da cikakkiyar yarda, da kudirce yankakkiyan yakini, da cika sharuddansa, babu wata cuta da zata yi gogayya da shi, ta yaya cututtuka za su yi gogayya da zancan Ubangijin kasa da sama, wanda da zai sauka akan duwatsu da ya tarwatsasu, ko akan kasa da ya yanketa, babu wata cuta cikin cututtukan zukata, da jiki face acikin alkur'ani akwai tafarkin nuni a kan magance shi, da sababinsa, da kariya daga gare shi ga wanda Allah Ya azurta da shi fahimta a littafinsa, Allah mai girma da daukaka ya ambaci cututtukan zukata da na jukkuna a cikin Alkur'ani, da likitancin zukata da kuma jiki. (1). Ka duba, Aljawabul Kafi liman sa'ala an dawa'ul al-shafi, Na Ibnu Kayyim, shafi 20.
Amma cututtukan zukata, to nau’uka biyu ne: cutar Shubha da kokonto, da cutar sha'awa da bata. Allah tsarki ya tabbatar masa ya ambaci cututtukan zukata, a rarrabe, ya kuma ambaci dalilin cututtukansu, da maganinsu,(2} Allah madaukakin sarki ya ce: {Shin bai ishe su ba cẽwa lalle Mũ, Mun saukar da Littãfin akanka, anã karanta shi a kansu? Lalle a cikin wancan haƙĩƙa akwai rahama da tunãtawa ga mutanen da ke yin ĩmãni}. Suratul Ankabut, Aya ta: 51 Imam Ibnu Kayyim Allah ya yi masa Rahama ya ce: ((Wanda Alkur'ani bai warkar da shi ba, kada Allah ya warkar da shi, wanda bai Ishe masa ba, kada Allah Ya ishe masa)){3} {1} Zadul-ma'ad na Ibnu kayyum, 4/6, da 4 / 352. Zaad Al'Ma'ad, 4/352.
Amma su cututtukan gangar jiki, Hakika Alkur’ani ya shiryar zuwa asalin maganinsu, da matattararsa da ka'idojinsa, hakan kuwa ka'idojin likitancin jiki dukkaninsu suna cikin Alkur'ani mai girma, su uku ne: Kiyaye lafiya, da kariya daga abu mai cutarwa, da fitar da abubuwa lalatattu masu cutarwa, da kafa dalili akan haka abisa ragowar dai-daikun wadannan nau'oi{4}. (4) Zaad Al'ma'ad 4/352, da4/ 6.
Da bawa zai kyautata yin magani da Alkur'ani, da ya ga tasiri mai girma na gaggawar waraka da hakan.
Imam Ibnu Kayyim Allah ya yi masa Rahama ya ce: ((Wani lokaci ya shude min ina Makkah da na yi rashin lafiya a ckinsa, kuma ban sami wani likita ba, ko wani magani, na kasance ina yi wa kaina magani da (Suratul) Alfatiha, sai nake ganin tasirinta mai ban mamaki: ina daukar ruwan Zam-Zam ina karanta ta (fatiha) acikinsa sau dayawa, sannan insha shi, sai na sami cikakkiyar waraka da hakan, sannan sai na zamo ina dogara da haka akan mafi yawan cututtuka, sai na amfanu da shi matukar amfani, na kasance ina bayanin hakan ga wanda yake kukan wani radadi (ciwo), mafi yawaicinsu sun kasance suna warkewa da sauri)){5}. (5) Ka duba: Zād Al'ma'ad,4/178, da Aljawaabul Al-kaafi, shafi na 21.
Haka nan kuma yin magani da tawaidar annabi tabbatacciya, na daga mafi amfanin magunguna, idan addu'a ta kubuta daga abubuwan da suke hana (amsarta) na daga mafi amfanin dalilai a wajen kawar da abin ki, da tabbatar da abin nema, ita (rukya) tana daga mafi amfanin magunguna, musamman ma tare da naci a cikinta, ita (addu'a) makiyar bala'i ce, tana kawar da shi, kuma tana gogayya da shi, tana hana saukarsa, ko ta saukaka shi, idan ya sauka(6) saboda fadinsa-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ((Addu'a tana amfanarwa ga abinda ya sauka da abindama bai sauka ba, ina umartarku da addu'a ya ku bayin Allah)){7}. da kuma faɗinsa - annabi tsira da amncin Allah su tabbata su tabbata agare shi -: ((Babu abinda yake juyar da kaddara sai addu'a, babu kuma abinda yake kara rayuwa sai biyayya)){8} Saidai a nan akwai wani lamari da ya kamata a lura da shi: shine cewa lalle Ayoyi, da zikirai da Addu'o'i da neman tsari, wadanda ake neman waraka dasu, ake kuma tawaida dasu, su akan kansu masu amfani kuma masu warkarwa ne, saidai suna neman karbuwa da karfi mai yi su da tasirinsa, a duk sa'adda waraka ta yi jinkiri, hakan ya kasance ne saboda raunin tasirin mai yin su, ko dan rashin karbuwar, ko dan wani abu mai hanawa mai karfi a cikinsa, da yake hana maganin ya yi amfani a cikinsa, hakika magani da tawaida yana kasancewa ne da al'amura biyu: (6) Ka duba: Aljawabul Alkaafi, shafi na 22-25. (7) Tirmizi, da lamba 3548, da Hakim, 1/670 da Ahmad, a lamba ta: 22044, Albani ya kyautata shi, ka duba Sahihul Al-jami'i, 3/151, da lamba 3403. (8) Alhakim, 1/670, da Tirmizi, a lamba 2139, kuma Albani ya kyautata shi, a cikin Silslatul Al'ahadis Al-sahiha, 1/76. da lamba, 157.
Al'amari na farko: Ta bangaren mara lafiya, yana kasancewa da karfin zuciya, da gaskiyar fuskantarsa zuwa Allah madaukakin sarki, da kudircewarsa yankakkiya, cewa lalle Alkur'ani waraka ne, kuma jinkai ne ga muminai, da neman tsari ingatacce, wanda zuciya da harshe suka hadu a kansa, hakika wannan nau'in yaki ne, shi kuma mayaki nasara bata cika a gare shi, akan makiyinsa saida al'amura biyu:
Makamin ya kasance ingattacce mai kyau shi akansa, kuma damtse ya kasance mai karfi, a duk sa'adda daya daga cikinsu ya yi baya, makami ba zai wadatar da wata fa'ida mai yawa ba, to ta yaya kuma idan aka rasa Al’amura biyun baki daya: zuciya zata zama ta wofanta daga tauhidi da dogaro ga Allah, da tsoran Allah da fuskanta, kuma ba makami a gare shi.
Al'amari na biyu: daga bangaran mai yin magani da Akur'ani da Sunnah, da ya kasance kuma wadannan Al'amura biyu suna tare da shi {9}, saboda wannan ne Ibnut Teen -Allah Ya yi masarahama- ya ce: Tawaida da (surorin) da ake neman tsari da su, da waninsu na daga sunayen Allah, shi liktanci ne na zuciya, idan ya kasance a bisa harshen masu biyayya ga Allah daga halitta, waraka tana samuwa da izinin Allah madaukakin sarki)){10}. (9) Ka duba Zād Al'ma'ad 4/68, da Aljawabul alkaafi shafi na 21. (10) Fathul Albari na Ibnu Hajar, 10/196.
Kuma hakika malamai sun hadu akan halarcin tawaida (RUK’YA), a yayin da sharudda uku suka hadu:
Sharadi na farko: Ta kasance da zancen Allah madaukakin sarki ko, sunayensa da suffofinsa, ko zancen manzansa- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Sharadi na biyu; ta kasance da harshen larabci, ko da abinda za a san ma'anarsa, daga waninsa.
Sharadi na uku: ya kudirce cewa, lalle tawaidar (RUK’YAR) ba ta tasiri da kanta, a'a (tana tasiri ne) da ikon Allah madaukakin sarki { 15}, ita tawaida kadai sababi ce daga sababai. (11) Ka duba, Fathul al'bari 10/ 195, da Fataawa Allama Ibnu Baaz, 2/384.
saboda wannan mahimmanci mai kai matuka, na takaita bangaran tawaida na daga littafina:((Zikiri da Addu’a da yin magani da Tawaida daga AlKur’anin da Sunna)), na kuma kara fa'idoji masu amfani- in Allah Ya so- a kansa, ina rokon Allah mai girma da daukaka da sunayensa kyawawa, da siffofinsa madaukaka, da ya sanya shi domin fuskarsa mai girma kadai, kuma Ya amfanar dani da shi, ya amfanar da wanda ya karanta shi, ko ya buga shi, ko ya zama daliln yada shi, da dukkan musulmai, lalle shi tsarki ya tabbatar masa majibincin haka ne, kuma mai iko ne akansa, Allah Ya yi tsira da aminci da albarka a bisa annabinmu Muhammad da alayensa, da sahabbansa, da wadanda suka biyo su zuwa ranar sakamako.
Mabukaci zuwa Allah-madaukakin sarki
Dr. Sa'id Bn Ali Bn Wahf AlKahdani
An kammala shi a 18/6/1414 H
1- Magance Asiri.
Magaani na Ubangiji ga asiri kashi biyu ne:
Kashi na farko: abinda ake kare asiri dashi kafin afkuwarsa (rigakafi).
1- Tsayuwa da dukkan wajibai, da barin dukkan abubuwan da aka haramta, da tuba daga dukkan munanan ayyuka.
2- Yawaita karatun Alkur'ani mai grma, ta yadda zai sanya wuridi da gare shi, ko wacce rana.
3 - Neman tsari da addu'o'i da surorin neman tsari, da zikirai ababan shar'antawa, yana daga cikin haka: "Da sunan Allah wanda wani abu ba ya cutarwa a cikin kasa ne ko a sama, shi mai ji ne kuma masani ne". sau uku, safe da yamma{12}. Da karanta Ayatul kursiyyi a bayan kowacce sallah, da lokacin barci, da kuma safe da yamma"{13}. Da kuma karanta {Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci}, Da ababan neman tsari ( Falaki da nasi) sau uku, da asuba da kuma yamma, da lokacin barci. Da fadar "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ba shi da abokin tarayya, mulki da godiya sun tabbata a gare shi, shi mai iko ne abisa komai". sau dari a kowacce rana{14}. Da kuma kiyayewa a bisa zikiran safiya da na yammaci, da zikiran bayan salloli, da zikiran barci da farkawa daga gare shi, da zikiran shiga gida, da fita daga gare shi, da zikiran hawa (abin hawa) da zikiran shiga masallaci da fitowa daga gare shi, da addu'ar shiga bandaki, da fitowa daga gare shi, da addu'ar wanda ya ga wanda aka jarraba, da wanin haka. Kuma hakika na ambata da yawa daga haka a cikin ((Hisnul muslim)) a bisa gwargwadan halaye, da yanayi, da gurare, da lokatai, babu kokonto cewa kiyayewa a bisa haka, yana daga dalilai wadanda suke hana gamuwa da asiri da kanbun baka, da aljan da izinin Allah madaukakin sarki, kuma su suna daga mafi girman magunguna bayan gamuwa da wadannan aibuka, da waninsu{15}. (12) Tirmizi, da lamba 3388, da Abu Dawud, da lamba 5088, da Ibnu Majah, da lamba 3869, kuma Albani ya inganta shi a cikin Sahihu Ibnu Majah, 2/332. (13) Hakim, kuma Zahabi ya inganta shi, 1 /562. Albani ya inganta shi a cikin Sahihul Altargiib wattarhiib 1 /273 da lamba 658. (14) Bukhari, 4/95, a lamba 3293, da Muslim, 4/ 2071, a lamba 2691. (15) Ka duba Zādul Ma’adi, 4/126, da Majmu'ul Alfatawa Allama Ibnu Baaz, 3 /277, kuma ka duba, dalilai goma wadanda ake kawar da sharrin Hassada da asiri da su, a cikin kashi na uku na magance kambun baka, daga wannan littafin.
4- Cin dabinai bakwai AJWA akan yawu, da safe idan ya samu, saboda fadin annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. "Duk wanda ya karya kumallo da Dabinon AJWA guda bakwai, a wannan ranar babu wata guba ko asiri da zai cutar da shi"{16}. Mafi cika ya kasance daga dabinon Madina, na daga wanda ke tsakanin unguwanni biyu, kamar yadda yake a cikin riwayar Muslim, babban malaminmu mai yawan sani Abdul'aziz Ibnu Abdullahi Ibnu Baaz yana ganin cewa, dukkanin dabinon Madaina ana samun wannan siffar a tare da shi, saboda fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi "Wanda ya ci dabinai bakwai daga abinda ke tsakanin unguwannin ta biyu (Madina) {17} lokacin da ya wayi gari...)). Hadisi {18}. (16) Bukhari tare da Alfathu, 10/247 a lamba 5445, da Muslim, 3/1618, da lamba 2047. (17) Labataiha: Ita ce (unguwanni), wato kasa ma'abociyar bakaken duwatsu, kai ka ce an konasu da wuta, yana nufi dasu anan: Harrataini da suka kewaye Madinar Annabi, ka duba faithur Alkadir na almunawy, 2/514. (18) Muslim, 3/1618, da lamba 2047..
Kamar yadda- Allah ya jikansa- yake ganin cewa hakan ana kauna ga wanda ya ci dabinai bakwai, ba dabinan Madina ba a sake. .
Kashi na biyu: magance tsafi bayan afkuwarsa, shima nau'ika ne:
Nau'i na farko: kwakulo (asirin) da bata shi, idan aka san gurin da yake, ta hanyoyin da suka halatta, a shara'ance, wannan yana daga mafi kaiwa matukar abinda za'a yi wa wanda aka yi wa tsafi magani da shi {19} (18) Ka duba Zaadul al-ma’ad, 4/124, da Bukhari tare da Alfathu, 10/137, da lamba 5765, da Muslim, 4/1917, da lamba 2189, da Majmu'ul fatawa ibn Baaz
Nau'i na biyu: tawaida ta shari'ah, yana daga cikin ire-irenta abinda zai zo {20}: (20) Ka duba Fathul Al-hakkul Mubin, a kan maganin faduwa da tsafi da kuma kambun baka, shafi 138.
Na farko:((ya dandaka (nika) ganyen magarya bakwai koraye a tsakanin duwatsu biyu, ko makamancinsu, sannan ya zuba ruwan da zai ishe shi wanka, ya karanta a acikinsu:
Ina neman tsarin Allah daga Shaidan abin jefewa, {Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai tsayuwa da kõme, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa. Wane ne wanda yake yin cẽto a wurinSa, fãce da izninSa? Yana sanin abin da yake a gaba gare su da abin da yake a bãyansu. Kuma bã su kẽwayẽwa da kõme daga ilminSa, fãce da abin da Ya so. KursiyyunSa ya yalwaci sammai da ƙasa. Kuma tsare su bã ya nauyayarSa. Kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma}. Suratul Baƙarah, aya ta: 225.
{Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa: "Ka jẽfa sandarka." Sai gã ta tanã lãƙumar abin da suke ƙarya da shi(117) Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci(118) Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu(119) Kuma aka jẽfar da matsafan, sunã mãsu sujada(120) Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta (121) Ubangijin Mũsã da Harũna){26} Suratul al-A’arāf, ayoyi na: 117-122.
(Kuma Fir'auna ya ce: "Ku zo mini da dukan masihirci, masani (79) To, a lõkacin da masihirta suka je, Mũsã ya ce musu,"Ku jẽfa abin da kuke jẽfãwa {80} To, a lõkacin da suka jẽfa, Mũsa ya ce: "Abin da kuka zo da shi sihiri ne. Lalle ne Allah zai ɓãta shi. Haƙĩƙa Allah bã Ya gyãra aikin maɓarnata (81) Kuma Allah Yanã tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kõ dã mãsu laifi sun ƙi. Suratu Yunus, ayoyi na 79-82.
{Suka ce: "Ya Mũsã! Imma ka jefa, ko kuma mu kasance farkon mai jẽfawa (65) Ya ce: "Ã'a, ku jẽfa." Sai gã igiyoyinsu da sandunansu anã sũranta su a gare shi, daga sihirinsu, lalle sunã tafiya da sauri (66) Sai Mũsã ya ji tsõro a cikin ransa.(67) Muka ce: "Kada ka ji tsõro. lalle kai ne mafi ɗaukaka (68) Kuma ka jẽfa abin da ke a cikin hannun dãmanka, ta cafe abin da suka aikata. Lalle ne abin da suka aikata mãkircin masihirci ne kuma masihirci bã ya cin nasara a duk inda ya je (69) Sai aka jẽfar da masihirtan sunã mãsu sujada, suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin Hãrũna da Mũsã} {28} Suratu Ɗāha, ayoyi na: 65-70
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinƙai. {Ka ce: "Ya kũ kãfirai (1) Bã zan bautã wa abin da kuke bautã wa ba (2) Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba (3) Kuma nĩ ban zama mai bautã wa abin da kuka bautã wa ba (4) Kuma kũ, ba ku zama masu bauta wa abin da nake bautã wa ba (5) Addininku na garẽ ku, kuma addinina yanã gare ni)
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai. {Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci (1) Allah shi ne abun nufi da buƙata (2) Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba (3) Kuma babu ɗaya da ya kasance kini a gare Shi}.
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai. Ka ce ina neman tsari daga Ubangijin safiya (1) Daga sharrin abin da Ya halitta (2) Da sharrin dare, idan ya yi duhu (3) Da sharrin mãtã mãsu tõfi a cikin kuduri (4) Da sharrin mai hãsada idan ya yi hasada).
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai. {Ka ce ina neman tsari daga Ubangijin mutane(1) Mamallakin mutane (2) Abin bautãwar mutãne (3) Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa (4) Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane(5) Daga aljannu da mutane}
Bayan karanta abinda aka ambata a cikin ruwa, sai ya debi ruwan ya sha, sau uku. Sai kuma ya yi wanka da ragowar, da hakane cutar zata gushe-insha Allah madaukakin sarki- idan kuma da bukata ta mai-maita hakan sau biyu ko sama da haka, babu laifi, har rashin lafiyar ya gushe, kuma hakika an jarraba sau dayawa, sai Allah ya amfanar da shi, kuma shi mai amfani ne ga wanda aka tsare ga barin matarsa} {21}. (21) Ka duba Fataawa Ibnu Baaz, 3/ 279, da Fathul Majid, shafi na 346, da Al-sarimul battar fi tasaddi lissharah, da Al'asrar na wahid Abdussalam, shafi na 109-117, akwai tawaida mai amfani- in Allah madaukakin sarki Ya so- da Musannif Abdurrazak, 11/13, da fathul albary, na ibn Hajar, 10/ 233.
Na biyu: Sai a karanta Suratul Fatiha, da Ayatul Alkursiyyi, da ayoyi biyu na karshen suratul Bakara, da suratul Ikhlasi, da falaki da Nasi, sau uku ko sama da haka tare da tofawa da kuma shafar (wurin) ciyo da hannun dama{22}. (23) Muslim 4/ 1728, da lamba 2202.
Na Uku: Neman tsari da tawaida (RUK’YA) da gamamman addu'o'i: (22) Ka duba Bukhari tare da Alfathu, da lamba 5016, da Muslim, 4/1723, da lamba 2192, da Bukhari tare da Alfathu 10/ 208.
1-Ina rokon Allah mai girma, Ubangijin Al'arshi mai girma, Ya baka lafiya (warkar da kai) (sau bakwai){23} Abu Dawud, 3/167 a lamba 3106, da Tirmizi, , 2/410, da lamba 2083, kuma Albani ya inganta shi a cikin Sahihul aljamiu, 5/ 180, da 322 da kuma Sahihul Sunanu Abi Dawud, 2/ 276.
2- Maralafiya yana sanya hannunsa akan inda yake yi masa radadi a jikinsa, sai ya ce: ((Bisimillah)) sau uku, kuma ya ce: (( Ina neman tsarin Allah da ikonsa daga sharrin abinda nake ji kuma nake tsoro)). (sau bakwai( {24} (27) Muslim 4 /1728, da lamba 2709.
3- "Ya Allah, Ubangijin mutane Ka tafiyar da tsananin, Ka warkar, Kai ne Mai warkarwa, babu waraka sai warakarKa, warakar da ba ta barin wata larura"{25} {68} Bukhari tare da Alfathu, 10/206, a lamba 5745, da Muslim, 4/ 1794, da lamba 2194.
4- "Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, daga dukkan wani shaidani da kwari, (masu cutarwa da dafi) daga kuma dukkan Idanu mai cutar da abinda ya kalla"{26}. (26) Bukhari tare da Alfathu, 6 /408, da lamba 3371.
6- "Ina neman tsari daga kalmomin Allah cikakku: daga fushinsa, da ukubarsa, da sharrin bayinsa, daga kuma zungurar (rudarwar) shaidanu, ko su halartoni"{28}. (28) Abu Dawud, da lamba 3893, da Tirmizi, da lamba 3528, kuma Albany ya kyautata shi, a cikin Sahihul Tirmizi, 3 /171.
7- "Ina neman tsari daga kalmomin Allah cikakku, wadanda mai biyayya ko fajiri basa ketaresu, daga sharrin abinda ya halittia ya kaga ya samar, kuma daga sharrin abinda yake sakkowa daga sama, da sharrin abinda yake hawa cikinta, da sharrin abinda ya samar a cikin kasa, da sharrin abinda yake fita daga cikinta, kuma daga sharrin futunun dare da rana, da sharrin abinda yake afkowa da daddare sai mai afkowa da zai afko da alkhairi ya mai Rahama"{29}. (29) Musnadu Ahmad, 3 /119, da lamba 15461, da Isnadi ingantacce, da ibn sunni, da lamba 637, ka duba: majma'u al-zawa'id 10 /127, kuma Albani ya inganta shi a cikin Silsiltul al'ahadisi Al'assahiha, 7 /196.
8- "Ya Allah Ubangijin sammai {bakwai} Ubangijin ƙasa, kuma Ubangijin Al'arshi mai girma, Ubangijinmu, kuma Ubangijin kowanne abu, Maƙagin ƙwayar hatsi da kwalfar gurtsu, Wanda Ya saukar da Attaura da Linjila da Alfurƙan, ina neman tsarinKa daga sharrin dukkan abinda Kake riƙe da makwankwaɗars, ya Allah Kaine na farko, babu wani abu kafinKa, kuma Kaine na ƙarshe babu wani abu a bayanKa, Kaine zahiri babu wani abu a birbishinKa, Kaine baɗini babu wani abu koma bayanKa..."{30}. (30) Muslim, 4 / 2084, da lamba 2713.
9- "Da sunan Allah nake maka ruƙya, daga dukkan wani abu da zai cutar da kai, daga sharrin kowanne irin rai ko idon mai hassada, Allah Ya warkar da kai, da sunan Allah nake maka ruƙya"{31}. (31) Muslim ya fitar da shi daga Abu Sa'id - Allah Ya yarda da shi - a lamba ta 4/1718, da lamba.
10- Da sunan Allah Ya warkar da kai, daga dukkan cuta Ya warkar da kai, daga sharrin mai hassada idan zai ya yi hassada, daga dukkan sharrin dukkan mai kambun baka" {32} (32) Muslim daga Aisha-Allah ya yarda da ita, 4/ 1718. da lamba 2185.
11- Da sunan Allah nake maka rukya, daga dukkan wani abu da zai cutar da kai, daga hassadar mai hassada, kuma daga dukkan ma'abocin kambun baka, Allah Ya warkar dakai"{33}. (33) Sunanu Ibnu Majah, da lamba 3527, daga Ubaidah bn Al-samit- Allah ya yarda da shi, Albany ya ingantashi a cikn Sahihu Ibn Majah, 2 /268.
Wadannan Addu'o'in na tsari, da rukya da ake magani da su daga asiri, da kambun baka da shafar aljani, da dukkan cututtuka, hakika su rukya ce wacce ta tattaro abubuwa masu amfani da izinin Allah madaukakin sarkin.'
Nau'i na uku: yin kaho a wurin ko gabar da alamar asirin ya bayyana a kansa, idan hakan ya samu, idan kuma bai samu ba, to abinda aka yi bayaninsa ya isa, na daga magani da godiyar Allah madaukakin sarkin [34}. (34) Ka duba: Zaad al'ma'aad, 4/125, akwai nau'uka na magance asiri bayan afkuwarsa, da babu laifi da su, idan aka jarrabasu suka amfanar, Ka duba: Musannaf ibn Abi Shaibah, 7 / 386-387. da fathu albary, 10 /233-234. da musannaf Abdurrazak, 11 /13, da Sarimul al-battar, shafi na 194- 200. da Assihru hakikatuhu wa hukmuhu na dokta shafi na 66.
Nau'i na hudu: magunguna na dabi'a (na gida), akwai wasu magunguna na dabi'a masu amfani, da Alkur'ani da Sunnah mai tsarki suka yi nuni a gare su, idan mutum ya rike su da yakini da gaskiya ya fuskanta, tare da kudirce cewa amfanin daga gurin Allah yake, Allah yana amfanarwa da su, idah Allah madaukakin sarki Ya so, kamar kuma yadda cewa akwai wasu magunguna wadanda ake hada su daga ganyayyaki da abinda ya yi kama dasu, su abin ginawa ne abisa gwaji, to, babu wani hani daga fa'idantuwa da su a shar'ance, matukar ba sukasance haramun ba {35}. (35) Ka duba Fathul Al-hakkul mubin, a magance kayi da tsafi da kambun baka, shafi 139. (46) Ka duba abinda ya gabata a nau'i na biyu na magance asiri a wannan littafin.
Yana daga magunguna na dabi'a masu amfani da izinin Allah madaukakin sarki, Zuma{36}, da Habbatus saudaa{37}, da ruwan zam-zam{38}, da ruwan sama, saboda fadinsa madaukakin sarki: {kuma Mun saukar da ruwa mai albarka daga sama}. Suratu Kaaf, aya ta: 9 {36} ka duba: Fathul hakkul mubiin, shafi na 140, magani da zuma zai zo a cikin wannan littafin. (37) Ka duba Fathul hakkil al'mubin, shafi na 141. magani da Habbaul al'saudaa zai zo a cikin wannan littafin. {38} Ka duba Fathul hakkul mubiin, shafi na 144, magani da Ruwan zam-zam zai zo, a cikin wannan littafin.
da man zaitun,, Saboda faɗar Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- "Ku ci zait ku yi mai da shi (ku shafa shi), domin shi yana daga bishiya mai albarka"{39}. Kuma hakika ya tabbata daga gwaji a aikace, da aiki, da karatu cewa shine mafificin Mai (zait), kuma yana daga magunguna nadabi'a, yin wanka, da tsaftatuwa, da sa turare}{41}. {39} Ahmad a cikin Musnad, 3/ 497, da lamba 16055, da Tirmizi, da lamba 1851, da ibn Majah da lamba 3319, kuma Albani ya inganta shi a cikin Sahihul Tirmizi, 2 /166. {40} Ka duba Fathul hakkul mubiin a cikin magance kayi, da tsafi da kambun baka, shafi 142. {41} Ka duba: marja'in daya gabata, shafi na 145.
2- Maganin kambun baka
Magance kamuwa da kambun baka kashi-kashi ne;
Kashi na farko; kafin kamuwa, shima nau’uka ne:
1- rigakafi (katangantuwa) da tsare (katange) wanda ake tsoro daga gare shi, ta hanyar zikirai da addu'o'i da neman tsari ta abubuwan da aka shar'anta, kamar yadda yake a kashin farko na magance asiri {42}. (42) Ka duba abinda ya gabata, a magance asiri a wannan littafin.
2- wanda yake tsoro ko yake tsoran shafar (wani) da kambun bakarsa-idan ya ga kansa, ko dukiyarsa, ko dansa, ko dan uwansa, ko wanin haka, na daga abinda yake kayatar da shi- da albarka, sai ya ce: ((MASHA ALLAHU LA KUWWATA ILLA BILLAH, ALLAHUMMA BARIK ALAIHI)). saboda fadin Annabi tsra da amincin Allah su tabbata a gare shi: ((Idan dayanku ya ga abinda yake kawatar da shi daga dan uwansa, to ya yi addu'a a gare shi da albarka)){43}. (43) Muwadda Malik, 2/938, da ibnu Majah, 2/1160, a lamba ta: 3509, da Ahmad, 4 /447 a lamba 15700, kuma Albani ya inganta shi a cikin Sahihu Ibnu Majah, 2 /265, da Zād al'maad, 4/ 170, da Assarimul al-battar fi tasadddi lilsahrati wa Ashrar, na Sheikh Wahid Abdussalam, shafi na 229-252.
3- Suturce kyawawan (halittar) wanda ake tsoran kambun baka daga gare shi,{44}. (44) Ka duba sharhin Sunnah na Bagawy, 13 /116, da Zaad alma'aad 4/173.
Kashi na biyu: bayan kamuwa da kambun baka, shima nau’uka ne:
1- Idan aka san mai kambun bakan, sai a umarce shi da ya yi alwala, sannan wanda ya kamu da kambun bakan ya yi wanka daga gare shi (shi ruwan Alwalal){45}. (45) Ka duba Sunananu Abi Dawud, 4 /9, a lamba ta 5056, kuma Albani ya inganta shi a cikin Silsilati Al'ahadis Al-ssahiha , 6 /61, da Zād alma'aad , 4 /163, ka duba Alwikaya wal'ilaaj minal kitab wassunna, na Muhammad Ibnu Shaya’u 144-147.
2- Yawaita karanta: {Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci} Da falaki da nasi, da fatihatul kitabi, da ayatul kursiyyi, da ayoyin karshe na suratul Bakara, da addu'o'i da aka shara’anta a rukya tare da tofawa, da kuma shafar gurin dake radadi da hannun dama, kamar yadda yake cikn nau'i na biyu a magance tsfi karanta ((j)) a lamba 1-11 {55}. {57} ka duba: nau'i na biyu daga magance tsafi daga wannan littafin,
3- ((Yana karantawa a cikin ruwa tare da tofawa (nunfasawa) sannan mara lafiyar ya sha daga gare shi, a zuba ragowar akansa, {47}, ko ya karanta a cikin mai ya shafa shi)){48}, idan karatun ya kasance a cikin ruwan zam-zam shine mafi cika in ya samu, ko a ruwan sama {50}. (47) Sunan Abi Dawud, 4/10, da lamba 3885, Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya aikata haka ga Sabit bn Kais, kuma Albani ya raunana shi a cikin Dha’ifu Abi Dawud a lamba 836. (48) Musnad Ahmad 3/497, da lamba 16055, Albani ya inganta shi a Silsilatul Al'ahadis al'sahiha, 1/108, a lamba 379. (49) Ka duba: abinda ya gabata a nau'i na hudu cikin magance asiri a wannan littafi. (52) Ka duba: nau'i na biyu na magance asiri, a cikin wannan littafi.
4- Babu laifi a rubutawa mara lafiya ayoyi daga Alku'ani, sannan a wanke ya sha su{51}, yana daga cikin haka, Alfatiha, da Ayatul kursiyyi, da ayoyi biyu na karshen surar Bakara, da {Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci}. Kul huwa. Da falaki da nasi, da addu'o'in rukya, kamar yadda yake a nau'i na biyu na na magance asiri, ya karanta ((b)), da ((j)) daga lamba 1-11{61} (51) Ka duba Zād Ma’ad na ibn Kayyim, 4/170, da Fatawa ibn Taimiyya, 64/19, (50) Ka duba: abinda ya gabata a nau'i na hudu daga magance asiri a wannan littafi.
Kashi na uku: aikata dalilai wadanda zasu ingije (kawar) da idon mai hassada, su ne kamar yadda zasu zo:
1- Neman tsarin Allah daga sharrinsa.
2- Tsoran Allah da kiyaye shi wajan umarninsa da haninsa, tsarki da daukaka sun tabbatar masa: "Ka kiyaye Allah zai kiyaye ka"{53}. (53) Tirmizi, da lamba 2516, Albani ya inganta shi a cikin Sahihul Tirmizi, 2/309.
3- Hakuri da mai hassada, da yi masa afuwa, kuma ka ya yi fada da shi, ko yakai kararsa, ko ya dame shi a zuciyarsa da cutar da shi.
4- Dogaro ga Allah, wanda ya dogara da Allah, shi ya isar masa,
5- Ba zai ji tsoron mai hassada ba, ko ya cika zuciyarsa da tunani a kansa ba, wannan yana daga mafi amfanin magunguna.
6- Fuskantar Allah, da tsarkakewa a gare shi, da neman yardarsa, tsarki ya tabbatar masa.
7- Tuba daga zunubai, domin suna dora makiyan mutum a kansa {Kuma abin da ya sãme ku na wata masifa, to, game da abin da hannãyenku suka sana' anta ne kuma (Alah) Yanã Yafẽwar (waɗansu laifuffuka) mãsu yawa}. Suratus Shurah, aya ta: 30
8- Sadaka da kyautatawa gwargwadan iko, domin hakan yana da tasiri mai ban mamaki, a wajen kawar da bala'i, da kambun baka da sharrin mai hassada.
9- Kashe wutar mai hassada, da azzalumi, da mai cutarwa, ta hanyar kyautata masa, a duk sa'adda ya kara cuta da zalunci da hassada a gareka, kai kuma sai kara kyautata masa., wannan ba'a datarwa a gare shi sai wanda rabonsa daga Allah ya girmama.
10-Kadaitar da Tauhidi, da tsarkake shi ga (Allah) Mabuwayi gwani, wanda wani abu ba ya cutarwa ko amfanarwa saida izininsa, tsarki ya tabbatar masa, shi mai tattarowa ne ga hakan dukkaninsa, wadannan sabuban suna gudana ne a kansa ne, Tauhidi ganuwar Allah ce mafi girma, wanda ya shigeta zai kasance daga cikin amintacce.
Wadannan sune sabuba goma da ake kare sharrin mai hassada, da mai kambun baka, da matsafi da su,{54}. Ka duba: Bada'i'ul Fawa'id na ibn Kayyim, 2 /238-245.
3- Magance cudanya ta Aljani da mutum
Magance wanda aljani ya shigeshi, wanda Aljani yake shigarsa yake kuma cudanyuwa da shi, kashi biyu ne:
Kashi na farko: kafin ya kamu:
Yana daga kariya, kiyayewa a bisa dukkanin farillai, da wajibai, da nisantar dukkanin abubuwan da aka haramta, da tuba daga dukkanin munanan (ayyuka), da katangantuwa da zikirai, da addu'o'i, da ababan neman tsari wadanda aka shar'anta.
Magani bayan shigar Aljani:
Yana kasancewa da karatun musulmi, wanda zuciyarsa ta dace da harshensa, da Ruqyarsa (tawaidarsa) ga wanda aka kayar, kuma mafi giman magani, yin Ruk’ya da Fatihatil kitabi{55}, da Ayatul kursiyyi, da ayoyi biyu na karshen suratul Bakara, da Kulhuwa {Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci}, da Falaki {Ka ce ina neman tsari ga Ubangijin safiya}, da kuma Nasi {Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne}, Tare da tofawa (nunfasawa) akan wanda ya fadi, da mai-maita hakan sau uku, ko sama da haka, da wanin haka na daga ayoyin Alkur'ani, domin AlKur’ani acikinsa akwai waraka ga abinda ke cikin kiraza, kuma (shi) wariaka ne, shiriya ne jin kai ne, ga muminai,{56} da addu'o'in ruk’ya, kamar yadda suke acikin nau’i na biyu na daga maganin tsafi, ka karanta ((b)), da ((j)){67}. babu makawa a wannan maganin daga al'amura biyu: (55) Ka duba: Sunanu Abi Dawud, 4/13-14, da lanba 3896, da Ahmad 5 / 210. da lamba 21835, kuma Albani ya inganta shi a cikin Silslatul al-ahads assahiha, da lamba 2028. {56} ka duba: Alfathul al-rabbani tartib Musnad al-mam Ahmad 17/183.
Na farko daga bangaren wanda aka kayar, da karfin ransa, da gaskiyar fuskantarsa zuwa ga Allah, da neman tsari ingantacce, wanda zuciya da harshe suka hadu a kansa.
Al'amari na biyu: daga bangaren mai yin Maganin, ya kasance kamar haka, domin Makami (yana tasiri ne da tasirin) mai dauke da shi {58}. [58| Ka duba: Ruk’ya Mudawwala Mufida, a cikin Al-ssarimul al-battar shafi na 109-117, na Sheikh Waheed Abdussalam, ka duba Zaad alma'aad, 4/ 66-69, da Izaahul hak fi dukhulil aljinni bil insaany, warrad ala man ankar zalika, na babban malami Abdul’Aziz bn Abdullahi bn Baaz, shafi na 14, da Fataawaa ibn Taimiyya, 19/9-65 da 24/ 276, da Alwiqayah wal Ilaaj minal alkitab wassuna, na Muhammad bn Sabi'i, shafi na 66-69, Ka duba kaifiyyatu dardi jinni minal bait, Alwikayah wal Ilaaj, na Muhaammad bn sabi;i, shafi 59, da Alamul al-jinni wasshayadin shafi na 130.
Idan aka yi kiran sallah a kunnan wanda aljanin shiga jikinsa, to abu ne mai kyau: domin Shaidan yana gudu daga haka{59}. [59} Ka duba Fathul hakkul Al-mbiin fi ilaaj sar'i wassihir wal'ain, shafi na 112, da Bukhari, da lamba 574.
4- Magance cututtukan damuwa:
{60} ka duba hakan: Asbabu sharhi Al-sadri, a Zaad alma'ad, 2/23-28, da Kitabu alwasaa'il almufida lilhayati al-sa'ida na babban malami Abdurraman bn Nasir al-sa'ady Allah Ya jikansa.
Mafi girman magani na cutuutukan damuwa{60}, da kuntatar kirji a takaice shi ne abinda zai zo:
1- Shiriya, da Kadaita Allah, kamar yadda cewa bata, da shirka na daga mafi girman dalilai na kuncin kirji.
2- Hasken Imani na gaskiya, wanda Allah Yake jefa shi a cikin zuciyar bawa,. tare da aiki na kwarai.
3- Ilimi mai amfani, aduk sa'adda ilimin bawa ya yalwata, kirjinsa zai yalwata.
4- Komawa zuwa ga Allah, tsarki ya tabbatar masa, da sonsa da dukkan zuciya, da fuskantuwa a gare shi, da ni'imantuwa da ibadarsa.
5- Dawwamar ambaton Allah, a bisa dukkan hali, hakanan a kowanne guri, ambaton Allah yana da tasiri mai ban mamaki wajen yalwar kirji, da ni'mar zuciya, da gushewar bakin ciki da bacin rai.
6- kyautatawa halitta da nau'o'in kyautatawa, da amfanar da su, da abinda zai yiwu, mai karamci mai kyautatawa, mafi yalwar mutane kirji, mafi dadinsu a rai, mafi ni'imtuwarsu zuciya.
7- Sadaukantaka, hakika sadauki mai yalwar kirji ne, mai yalwar zuciya.
8- fitar da aibukan zuciya (61), daga suffofi ababan kyama, wadanda suke wajabtar da kuntatarsa da azabarsa, kamar hassada, da kiyayya da kulli, da gaba, da zalunci, hakika Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-an tambaye shi dangane da mafificin mutane? sai ya ce: ((Dukkan mai tsarkin zuciya, mai yawan gaskiyar harshe)) sai suka ce: mun san mai yawan gaskiyar harshe, wanene ‘Makhmumumil alkalb? sai ya ce: ((shine mai tsoran Allah, tsarkakke ba zunubi a cikinsa, ko kulli ko hassada)){62}. {61} Da'alu al-shai'i :wani aibu a cikinsa da zai bata shi. {62} Ibn Majah ya fitar da shi, da lamba 4216, kuma Babban malami Albany ya inganta shi a cikin Sahihu ibn Majah, 2/411.
9- Barin kallo mara amfani, da zance, da sauraro, da cudanya, da ci da sha, domin barin haka, na daga dalilan yalwatar kirji, da mi'imar zuciya, da gushewar bacin rai da bakin ciki
10- Shagaltuwa da wani aiki daga ayyuka, ko wani Ilmi daga nau’ukan ilimi masu amfani, domin suna shagaltar da zuciya ga barin abinda zai samata damuwa.
11-Himmatuwa (bada kulawa) ga aikin wunin da ake ciki, da kuma yankewarsa ga damuwa da lokacin da zai zo, ko bakin ciki a bisa lokacin da ya wuce, shi bawa yana yin kokari ne a cikin abinda zai amfanar dashi a Addini da Duniya, kuma ya roki Ubangijinsa nasarar manufarsa, ya dinga neman taimakonsa a bisa haka, lalle hakan zai dinga mantar da shi bacin rai da bakin ciki.
12-Duba zuwa ga wanda ke kasa da kai, kada ka kalli wanda ke sama da kai, a lafiya, da abubuwan da suke tare da ita, da arziki da mabiyansa.
13- mantawa da abinda ya wuce a gare shi na daga abubuwan ki, wadanda ba zai yi wu a gare shi ba ya dawo da su, kada ya dinga tunani akansu kwata-kwata.
14- Idan wata musifa ta faru a bisa bawa cikin musifu, sai ya yi kokarin saukakata, ta hanyar kaddara mafi munin tsammani wadanda lamarin zai tuke a gare shi, ya kawadda su gwargwadan ikonsa.
15- karfin zuciya, da rashin damuwarsa, da tsananin bakin cikinsa da rashin fahimta, da tunani iri daban daban, wadanda munanan tunanai suke jawo su, da rashin fushi, kuma kada ya dinga tsammanin gushewar abubuwan so, da faruwar abubuwan ki, a'a ya mika lamarinsa zuwa Allah- mai girma da daukaka- tare da tsayawa da sababai masu amfani, da rokan Allah rangwami da lafya.
16- kudircewar zuciya a bisa Allah, da dogaro a gare shi, da kyautata masa zato-tsarki da daukaka sun tabbatar masa- domin mai dogaro ga Allah wahamai basa tasiri a gare shi. {65} Abu Dawud, 4/324, da lamba, da Ahmad, 5/42, da lamba 0430, kuma Albani, ya ingantashi a cikin sahihul al-jami'i -da lamba 3388, kuma ya kyautata shi a cikin sunanu Abi Dawud, 251/3
17-Mai hankali yana sanin cewa ingantacciyar rayuwarsa, rayuwar farin ciki da nutsuwa, kuma cewa ita (rayuwarsa) gajera ce kwarai, kada ya gajarta ta da bacin rai, da sakinta tare da gurbace-gurbace, domin hakika hakan kishiyar ingantacciyar rayuwa ce.
18- Idan wani abin ki ya same shi, sai ya gwama tsakanin ragowar tsantsar ni'momi na sa, na addini, ko na duniya, da kuma tsakanin abinda ya same shi na daga abin ki, a yayin gwamawar, yawan abinda yake cikinsa na daga ni'momi za su bayyana a gare shi, hakanan kuma ya gwama tsakanin abnda yake tsoransa na faruwar cuta a garea shi, da kuuma tsakanin da kuma abubuwa masu yawa da yake tsammaninsu a aminci, kada ya bar tsammanin rauni ya rinjayi yawa, yawan tsammani masu karfi, da haka ne bakin cikinsa da tsoransa za su gushe.
19- yasan cewa cutarwar mutane ba za ta cutar da shi ba, musammam a maganganu munana, a'a za su cutar da su ne, kada ya damu da su, ko tunaninsu, don kada su cutar da shi.
20- Ya sanya tunaninsa akan abinda zai dawo masa da amfani, a cikin addini da duniya.
21- kada ya nemi godiya a bisa kyautatawar da ya yi ta, sai dai daga Allah, kuma ya san cewa wannan wata ma'amalace daga gare shi, tare da Allah, kada ya damu da godiyar wanda ya yi masa wata ni'ima: {Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya} Suratul al-insaan: aya ta 9.
22- sanya al'amura masu amfani agaban idansa, da kuma yin aiki a bisa tabbatar da su, da kuma rashin waiwayawa zuwa al'amura masu cutarwa, kada ya shagaltar da kwakwalwarsa, ko tunaninsa da su.
23- Gamawa (kawad da) ayyuka a nan take, da kadaituwa dan abinda zai zo nan gaba, har ya iya zuwa da wasu ayyukan na nan gaba, da karfin tunani da aiki.
24- Yana zaban mafi mahimmanci daga ayyuka masu amfani, da ilimi masu amfani, sannan wadanda suke biye da su a mahimmanci, musammama abinda kwadayi a cikinsa yake tsananta, kuma yana neman taimakon Allah a bisa haka, sannan neman shawara, idan maslaha ta tabbata, kuma ya kudri niyya sai ya dogara ga Allah mai girma da buwaya.
bayar da bayanin ni'imomin Alllah na sarari da na boye, domin saninsu, da bayar da labarin su, Allah Yana ingigije (kawar) da bakin ciki da bacin rai da shi,Yana kuma kwadaitar da bawa a bisa godiya.
26- Mu'amalantar iyali, da makusanci, da abokin mu'amala, da dukkan wanda tsakanin ka da tsakaninsa, akwai wata dangantaka, idan ka sami wani aibi tare da shi, (ka yi masa ma'amala) da sanin abinda ke gare shi na daga kyawawa, da kuma gwama hakan, ta hanyar hararo hakan ne abotaka zata dawwama, kirji kuma ya yalwata, saboda wannann ne Annabi-tsra da mincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ((Mumini ba ya ƙin mumina, in ya ƙi wata ɗabi’ar daga gareta, zai so wata ɗabi’ar daga gareta)){63}. [62} Muslim, 2/1091, da lamba 1469.
27-Addu'a da ingantar al'amura dukkaninsu, mafi girman hakan: ((Ya Allah ka gyara min addini na, wanda shi ne kashin bayan al’amari na, ka gyara min duniya ta wacce na ke rayuwa a cikinta, ka kuma gyara min lahira ta wacce ita ce makoma ta, ka sanya rayuwa ta zamo Karin duk wani alheri a gare ni, mutuwa kuma ta zamo hutu ce a gare ni daga dukkan wani sharri)){64}. Hakanan kuma: ((Ya Allah Rahanarka nake kauna, kada ka barni da kai na, kiftawar ido, ka gyara min sha'anina dukkaninsa, babu abin bautawa da gaskiya sai kai)){65}. {64} Muslim, 4/2087, a lamba 2720. {88”9} Abu Dawud, 4 /324, 5092, da Ahmad, 5/42, da lamba 20430, kuma Albany ya kyautata shi, a cikin irwaul al-galil, 3/ 357,
28- Jihadi akan tafarkin Allah, saboda fadinsa- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: ((Ku yi jihadi a kan tafarkin Allah, hakika jihadi a kan tafarkin Allah kofa ce daga kofofin Aljanna, Allah yana tserarwa da shi daga bacin rai da bakin ciki)){66}. {66} Ahmad, 5/314, 316, 330 326, da lambobi 21624, 22680, 22732, da Hakim zahabi kuma ya inganta shi, 2/75, Albani ya ingantashi a cikin Silsilatul ahadis al- sahiha, 2/ 274.
Wadannan sabuban da hanyoyi: magani ne mai fa'ida ga cututtukan damuwa, kuma suna daga mafi girman magani ga damuwa ta zuciya, ga wanda ya bibbiyesu, kuma ya yi aiki da su, da gaskiya da ikhlasi, hakika wasu sashin malamai masu yawa sun yi magani da su, daga halaye da cututtuka na damuwa, sai Allah ya amfanar dasu amffani mai girma{67}. {67} ka duba: Mukaddimatul Al'wsa'ilil almufida bugu na biyar: shafi: 6.
5- Magance gyambo da rauni
Manzan Allah- tsira da ammincin Allah su tabbata a gare shi- ya kasance idan mutum ya kai kuka, ko ya kasnce yana da gyambo, ko rauni, yana yin haka da dan yatsansa, Sufyanu ya sanya manuniyarsa a kasa, sannan ya daga ta ya ce: ((Da Sunan Allah, Turbayar Kasarmu, da Yawun sashinmu , ake warkar da Mara lafiyarmu, da Izinin Ubangijinmu)){68}. (25) Bukhari tare da Alfathu, 10/206, da lamba 5750, da Muslim, 4/1721 da lamba 2191.
{83}Ana cewa Al-sukdu da al-sakadu: sabanin yarda, ‘wakad sakhida’ (da Larabci) ai ya yi fushi, shi mai fushi ne, ‘wa askhadahu’, wato ya sahi fushi
Ma’anar Hadisin: cewa shi yana dibar yawunsa a kan dan yatsansa manuniya, sannan ya sanya shi a kan kasa, sai wani abu ya hade da shi, sai ya shafi gurin raunin ko ciwon, ya fadi wannan zancen a halin shafar{69} {69} Ka duba Sharhin Al-nawawi na Muslim 14/184, da Fathul Bari na ibn Hajar, 10/208, kuma ka duba cikakken sharhin hadisin Zaad alma'ad, 4 186-187. {84} wato mutum Musulmi.
6-Magance Masifa
{Wata masifa bã zã ta auku ba a cikin ƙasã kõ a cikin rayukanku fãce tanã a cikin littãfi a gabãnin Mu halitta ta. Lalle wannan, ga Allah, mai sauƙi ne {22}. Dõmin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi mumar alfahari da abin da Ya bã ku. Kuma Allah bã Ya son dukkan mai tãƙama, mai alfahari} Suratul Hadid ayoyi biyu: 22-23
2- {Wata masĩfa bã zã ta sãmu ba fãce da iznin Allah. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, Allah zai shiryar da zuciyarsa. Kuma Allah, ga dukan kõme, Masani ne} Suratut Taghabun, aya ta: 11
3- ((Babu wani bawa da wata musifa zata same shi, sai ya ce: inna lillahi wa inna ilaihir raji'un, ya Allah Ka bani lada a musifata, Ka maye min mafi alkhairi daga gareta. Face sai Allah ya ba shi lada a musifarsa, kuma Ya maye masa mafi alkhairi daga gare ta)){70}. {70} Muslim, 2/633, a lamba 918
4- ((Idan dan bawa ya rasu, sai Allah madaukakin sarki ya ce da mala'ikunsa: Kun karbi dan bawa na? sai su ce: na'am, sai ya ce kun karbi dan itaciyar zuciyarsa? sai su ce, na'am, sai ya ce: me bawana ya ce: sai su ce: ya gode maka, ya yi istirja'i (inna lillahi wa inna ilaihir raji'un) {71}, sai ya ce: ku ginawa bawa na gida a cikin Aljanna, ku kira shi da gidan godiya"{72}. (71). wato ya ce: Alhamdu lillahi, inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un. {72} Timizi, a lamba 11021, kuma Albani ya kyautata shi a cikin Sahihul Tirmizi, 1/298.
5- ((Allah madaukakin sarki yana cewa: bawana mumini ba shi da wani sakamako a gurina, idan na karbi zababbansa, daga ahalin duniya sannan ya nemi ladansa sai Aljanna"{72}. [73} Bukhari tare da Fathu, 11/242, da lamba 6424.
6- Annabi- tsra da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce da wani mutum da dansa ya mutu: "Shin baka so ka jewa wata kofa ba cikin kofofin Aljanna face sai ka sameta tana jiranka}{74}. {74} Ahmaad, da lamba 15595, da Nasa'i 4/23, a cikin Al-jana'iz, babun umarni da neman lada da hakuri, lokacin saukar musiba, da lamba, 1870, sanadinsa ingantacce ne a bisa sharadin al-sahih, ibnu Hibban ya inganta shi, 8/209, kuma Albani ya inganta shi a cikin sahihul Targib wattarhib, da lamba 207, ka duba fathul albary 11/243.
7- ((Allah mai girma da buwaya yana cewa: idan na jarrabi bawana da masoyansa biyu, sai ya hakura, [ko ya nemi lada} ina canza masa su da Aljanna)) yana nufin Idanuwansa"{75}. {74} Bukhari tare da fathu, 10 /116, da lamba 5653, da abinda ke tsakanin baka biyu da lamba 2400, daga Sunan Tirmizi ne, ka duba: Sahihu Tirmizi, 2 /286.
8- ((Babu wani Musulmi da wata cuta zata same shi, daga rashin lafiya da abinda yake irinta, face sai Allah Ya sarayar masa da munanan ayyukansa da shi, kamar yadda bishiya take kade ganyanta"{76}. {76} Bukhari tare da fathu, 10/ 120, da lamba 5648, da muslim 4 /1991, da lamba 2571,
9- Babu wani Musulmi da zai taka kaya da abinda ke sama da ita, face sai an rubuta daraja a gare shi sanadiyyarta, kuma a goge kura-kuransa da ita"{77}. {77} Muslim, 4 /1991, da lamba 2572.
10- "Wata rashin lafiya (78), ko wahala (79), ko rashin lafiya, ko bakin ciki, har bacin rai da yake da munsa (80) ba za su sami mumini ba face an kankare masa daga munanan ayyukansa"{81} {78} Alwasabu: ciwo mad yake tare da mutum, yana daga gare shi fadarsa Allah madaukakin sarki: (azaba tabbatacciya ta abbabata a gare su) ka duba sharni al-Nawawi 16/ 130. {79} Al-nasabu: wahala {80} aka ce da yi wa alya'u fatha da yiwa al-ha'u damma "ya hummuhu" kuma aka ce "yuhammahu" da yi wa alya'u damma da fatha ga alha'u, wato yake bakanta masa, dukkaninsu su biyun sun inganta, ka duba sharhin Al-nawawi na Muslim, 16/130. {81} Muslim, 4/1993 da lamba 2573.
11- "Lallai cewa Gwaggwaben lada yana tare da Girman Bala'i, kuma Allah Mai girma da Daukaka idan ya so Mutane, to sai ya Jarrabesu, to duk wanda ya yarda da Jarrabawar to sai ya sami yardar Allah, kuma duk wanda yayi fushi to shi ma sai Allah yayi fushi da shi{82}{83}. {85} Tirmizi, da lamba 2698, da ibnu Majah, da lamba 4023, kuma sheikh Albani ya inganta shi a cikin Sahihul Tirmizi, 2/286.
12- "... Bala'i ba zai gushe ba ga bawa{84} har sai ya barshi yana tafiya akan kasa, babu wani kuskure a tare da shi"{85}. {82} Tirmizi, a lamba ta 2396, da ibnu majah, da lamba 4031, kuma Albani ya inganta shi a cikin Sahihul Tirmizi, 2/286.
7- Maganin damuwa da bakin ciki
1- ba wani bacin rai da zai sami bawa ko bakin ciki sai ya ce: "Ya Allah ni bawanka ne dan bawanka ne, dan baiwarka, makwarkwada ta na ga hannunka, hukuncin ka mai zartuwa ne a gare ni, kaddararka adalci ce a gagare ni, ina rokanka da dukkan wani suna da yake naka ne, da ka ambaci kanka da shi, ko ka saukar da shi a cikin littafinka, ko ka sanar da wani daga halittarka, ko ka kebantu da shi a ilimin gaibu a gurinka, ka sanya Alkur'ani yabanyar zuciyata, da hasken kirjina, da yayewar bakin cikina, da tafiyar da abinda ke damuna. Face sai Allah ya tafiyar da bakin cikisa da bacin ransa, ka canja farin ciki a bagiransa"{86}. {86} Ahmad, 1/ 391, da lamba 3712, kuma Albani ya inganta shi a cikin Sahihut Targhib wal-wattarhib, da lamba 182
2- "Ya Allah ina neman tsarinKa daga bacin rai ,da bakin ciki, da gajiyawa, da kasala, da rowa da ragwantaka, da rinjayar Mazaje"{87}. {87} Bukhari, 7/158, da lamba 2893, manzan Allah- tsira da ammincin Allah su tabbata a gare shi- yana yawaita wannan addu'ar, ka duba Bukhari tare da fathu, 11/173.
Maganin bakin ciki
1- "Babu wani abin bautawa face Allah Mai girma Mai hakuri, babu wani abin bautawa face Allah Ubangijin Al’arshi mai girma, babu wani abin bautawa da gaskiya face Allah Ubangijin sammai kuma Ubangijin kasa kuma Ubangijin Al’arshi mai yawan baiwa"{88}. {88} Bukhari, 7 /154, da lamba 6346, da Muslim, 4 /2092, a lamba 2730.
2-
"Ya Allah rahamarKa na ke fata, kar Ka bar ni da kaina daidai da ƙiftawar ido, Ka gyara min al’amura na dukkan su, ba bu wani abin bautawa da gaskiya sai Kai"{89}.
3- "Babu abin bautawa da gaskiya Sai Kai, tsarki ya tabbata a gareKa, lallai ni na kasance cikin azzaluma"{90} {90} Tirmizi, 5/ 529, da lamba 3505, da Hakim, Zahabi kuma ya inganta shi, 1 /505, Albany ya inganta shi a cikin Sahihul al-Tirmizi, 3/168.
4- ((Allah, Allah Ubangiji na ba zan hada shi da wani ba)){91}. [90} Abu Dawud, 2/87, da lamba 1525, kuma Albany ya inganta shi,a cikin Sahihul ibn Majah, 2/335, kuma Tirmizi ya inganta shi, 4 /196.
9-Yadda mara lafiya zai yi wa kansa magani
"Ka sanya hannunka akan wurin da kake jin raɗaɗin a jikinka, ka ce: Da sunan Allah sau uku, kuma ka ce sau bakwai: “Ina nema tsarin Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji kuma nake tsoro"{92}. {92} Muslim, 4/1728, a lamba 2202.
10- yi wa mara lafiya magani lokacin duba shi
" Babu wani bawa musulmi da zai duba wani mara lafiya, da Aljalinsa bai yi ba, sai ya ce sau bakwai:” ina rokon Allah mai girma, Ubangijin al'arshi mai girma Ya warkar da kai. Face sai ya sami lafiya"{93}. {92} Tirmizi, da lamba 2083, da Abu Dawud, da lamba 3893, kuma Albany ya inganta shi a cikin Tirmizi, 2/210, da Sahihl Jami'u 5/ 180.
11- Magance damuwa da firgita a cikin barci
"Ina neman tsari daga kalmomin Allah cikakku: daga fushinsa, da ukubarsa, da sharrin bayinsa, daga kuma zungurar (rudarwar) shaidanu, ko su zo inda nake "{94}. {94} Abu Dawud, 4/12, da lamba 3893, kuma Albani ya kyautata shi a cikin Tirmizi, 3/171.
12- magance zazzabi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Zazzabi yana daga cikin Hucin wutar Jahannama, ku sanyaya shi da ruwa"{95}. {95} Bukhari tare da fathi, 10/174, da lamba3264, daMuslim, 4/1733, da lamba 2210.
13. Magance cizo da sara
1- Ana karanta Fatihatul Kitab tare da tattara buzaak da ciratarsa akan cizon {95}. " {96} Bukhari tare da Fathul Bari, 10/208, Kitabuld Dubb, babu rukya al-nabiyy-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
2- Yana shafa ruwa da gishiri a kanta, tare da karanta: ((Ka ce: "Ya kũ kãfirai!)) Da Falaki da Nasi {97}. {97} Dabarani a cikin Al'mu'ujami'i al-sagir 2/830, Haithami kuma ya kyautata Isnadisa a cikin majama'u al-zawa'id, 5/111, kuma Albani ya inganta shi a cikin Silsilatul ahadis alsahiha, da lamba 548.
14- Magance fushi
Magance fushi yana kasancewa ne da hanyoyi biyu:
Hanya ta farko: kariya
Yana faruwa da nisantar dalilan fushi, yana daga cikin wadannan dalilan: giriman kai da jiji da kai, alfahari, da kwadayi abin riyawa, da kakaci ba a inda ya dace ba, da abinda ya yi kama dahaka.
Hanya ta biyu: magani idan fushin ya afku
Yana takaituwa a nau'uka hudu:
Neman tsarin Allah daga shaidan abin jefewa.
Alwala.
Canza halin da mai fushi yake akan shi: da zama ko kishingida, ko fita , ko kamewa ga barin magana ko wanin haka.
Halarto da binda ya zo akan hadiye fushi, na daga lada, da kuma abinda ya zo na karshen fushi na daga tabewa{98} {98} ka duba wannan rarrabewar da dalilansu ingantattu a cikin AAFAATUL AL-LISAN, SHAFI NA 110-112, DA ALHIKMA FI DDA'AWAH ILAL aallah, shafi na 64-66 na mawallafin.
15- Magani da Habbatus saudaa
Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce: "A kwai waraka daga dukkan cuta a habbatus saudaa sai dai mutuwa" Ibnu Shihab ya ce; Assamu: mutuwa, habbatus saudaa kuma Assuneez {99} Habbatus saudaa mai yawan amfani ce kwarai, fadarsa kuma: ((waraka daga dukkan cuta)) misalin fadarsa Allah madaukakin sarki: {Tana rusa kowanne abu da umarnin Ubagijinta} Suratul Ahkaaf, aya ta: 25, wato kowanne abu yana karbar rusawa da kininsa{100} {99} Bukhari tare da fathu, 10/143, da lamba 5688, da Muslim, 1735, da lamba 2215. {100} ka duba: Zaad alma'aad 4/297, da a-ldubbi minal kitab Was Sunnah, na babban malami Muwaffaq al-deen a wajen alladiif albagadadi, shafi na 88.
16. Magani da zuma
1- Allah mai girma da daukaka a ambaton kudan zuma ya ce: {Wani abin sha mai sassabawar laukansa, yana fita daga cukkunansu, acikinsa akwai waraka, ga mutane, lalle a cikin hakan akwai aya ga mutane masu tunani} Suratul al-nahl aya ta :69.
2- Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
((Waraka tana cikin abubuwa uku: Kaho, shan zuma, ko lalas da wuta, ni ina hana al'umata lalas"{101}. (101). Bukhari da Fathul Bari, 10/137, Lamba ta 5681, kuma a duba Fawa’idul Asal, a cikin Zādul Ma’ād 4/50-62, da Addibbu Minal Kitab Was Sunnah, na Muwaffakud Deen Abdullatif Albaghdadi , shafi na 129 - 136.
17. Magani da ruwan Zam-zam
1- Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce akan ruwan zamzam. " lalle shi (zamzam ruwa ne) mai albarka ne, kuma hakika shi abinci ne {da warakar cuta{102}. {102} Muslim, 4/1922, da Baihaki a cikin Sunan Kubra, 5/147, da Dabarani a mu'ujamul al'awsad, 3/ 247, isnadisa ingantacce ne, ka duba majma'u zawaad, 3/286
2 kuma Hadisin Jabir yana daga shi: Ruwan Zam-zam dan abinda aka ne domin shi"{103} {103} Ibn Majah, 3062, da waninsa, kuma Albani ya inganta shi a cikin sahihul ibn majah, 2/183, da Irwa'ul galil, 4/320.
3- Ya tabbata daga gare shi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi cewa shi: "ya kasance yana daukar ruwan zamzam ya kuma kasance yana zuba wa akan marasa lafiya{105} Imam Dan Kayyim Allah ya yi masa Rahama ya ce Hakika ni da wanina mun jaraba al'amura masu ban mamaki na neman waraka da ruwan Zamzam, na nemi waraka da shi daga cututtuka masu yawa, sai na warke{106} da Izinin Allah{107}. {103} Al'idawa: jam'inta Al'adawy, Mukhtaru al-sihah, 11/1 {105} Tirmizi, 1/180, da lamba 963. da Baihaky, 5/202, Albani ya inganta shi a cikin Sahihut Tirmizi, 1/284, da Silsilatul ahadisi, 2/572, da lamba 883, da Zādul Ma’ād, 4392. {106} wasun mutanen Hijaz suna cewa: "fabari'itu" al-nihaya fi garibil hadith, 1/111. {107} Zaad al'ma'ad, 4/393, da 178.
18-Magance cututtukan zukata
Zukata nau'i uku ne:
1- Zuciya kubutacciya: Ita ce ba wanda zai tsira ranar alkiyama, sai wanda ya zowa Allah da ita, Allah madaukakin sarki ya ce: {A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi (88) Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki) Suratul al-shu'arah, ayoyi biyu: 88-89.
{Zuciya mai tsarki ita ce wacce ta kubuta (tsarkaka) daga dukkan sha'awa da take sabawa umarnin Allah da haninsa, daga kuma dukkan sha'awa da take bijirewa alkhairinsa, sai ta kubuta daga dukkanin bautar abinda ya wanin shi, kuma ta kubuta daga kai hukunci ga wanin manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,
A dunkule zuciya tsarkakakkiya ingantacciya ita ce wacce ta tsarkaka daga cewa acikinta wanin Allah yana da tarayya acikinta ta kowacce fuska, a'a hakika bautarta ta tsarkaka ga Allah, a nufi da soyayya, da dogaro, da komawa, da kankan da kai , da tsoransa, da fata, kuma ya tsarkake aikinsa dan Allah, idan zai so yana so dan Allah, idan kuma zai ki yana ki dan Allah, idan zai bada yana badawa dan Allah, idan zai hana yana hanawa dan Alllah, damuwarsa dukka ga Allah take, hakanan soyayyarsa dukkanta ga Allah take, kuma nufinsa ga Allah yake jikinsa da ayyukansa da barcinsa da farkensa na Allah ne, zance akan lamarin Allah, ya fi sha'awa a gare shi fiye da dukkan wani zance, tunaninsa yana shawagi, a bisa yardarsa da soyayyarsa, muna rokan Allah madaukakin sarki wannan zuciya. {107} ka duba: igathatu lahfan min masa'idu shaidan na ibnu Kayyum- rahimahullah, 1/ 77, da 73.
2- matacciyar zuciya: ita kishiyar ta farko ce, ita ce wadda bata san Ubangijin ta ba, ba ta bauta masa da umarninsa, da abinda yake sonsa kuma yake yarda da shi, a'a ita tana tsaye tare da sha'awe-shawansa, da jn dadinsa, koda ta kasance cikin abinda fushin Ubangijinta, ita mai bautawa wanin Allah ne, a soyayya da toro da fata, da yarda, da fushi, da girmamawa, da kankan da Kai, idan ya yi yana fushi ne dan san ransa, idan kuma ya hana yana hanawa ne dan san ransa, san rai shi ne jagoransa, sha'awa kuma ita ce jagorarsa, jahilci matukinsa, rafkana abin hawansa,{109] muna neman tsarin Allah daga wannan zuciya. {109} ka duba: igasatul lahfan min msa'id shaidan. 1/9.
3- zuciya mara lafiya: Ita ce da take da rayuwa, kuma a tare da ita akwai cuta, tana da lamura biyu wannan ta kare ta a wani lokaci dayar kuma wani lokacin daban, ita a abinda ya rinjaya akanta daga gare su, acikin ta daga soyayyar Allah madaukakin sarki da imani da shi, da tsarkakewa a gare shi, da dogaro a gare shi, abinda shi lamarin rayuuwarta ne, acikinsa kuma akwai son sha'awa da kwadayi akan tabbatar da ita, da hassada, da girman kai, da jiji da kai da son daukaka, da barna a kasa da shugabanci, da munafinci da riya, da kwauro, da rowa, daga abinda shi lamarin halakarsa ce da kasawarsa{110}. Muna neman tsrin Allah daga wannan zuciyar. {110} ka duba igasatul allahfan, 1/9.
Magance zuciya daga dukkanin cututtuka, lalle Alkur'ani mai girma ya kunshe shi hakan.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ya ku mutãne! Lalle wa'azi yã jẽ muku daga Ubangijinku, da waraka ga abin da yake a cikin ƙirãza, da shiriya da rahama ga muminai.} Suratul Yunus, aya ta: 57 kuma Allah mai gima da buwaya ya ce: {Kuma Munã sassaukarwa daga Alƙur'ãni, abin da yake waraka ne da rahama ga mũminai. Kuma bã ya ƙãra wa azzãlumai (kõme) fãce hasãra} Suratul l'isra, aya ta: 82
Cututtukan zukata nau'i biyu ne:
Nau'in da mai shi, ba ya jin radadi a take, ita ce cutar jahilci, da shubhohi da kokonto, wannan shine mafi girman nau'ika biyu, a radadi, sai dai saboda lalacewar zuciya ba ya jinsa.
da kuma nau'in cuta mai radadi a take, kamar bacin rai da bakin ciki, da da fushi, wannan cutar takan gushe da magunguna na dabi'a ta hanyar gusar da dalilansa, da wanin haka{111}. {111} ka duba igathatul allahfan 1/ 44
Magance zuciya yana kasancewa ne da al'amura hudu:
Al'amari na farko: da Alkur'ani mai girma, domin shi waraka ne ga abinda ke cikn kiraza, na daga kokonto, yana kuma gusar da abinda ke cikinsa na daga shirka, da dattin kafirci, da cututtukan shubhohi, da sha'awa, shi shiriya ne ga wanda ya san da gaskiya, da aiki da shi, da jinkai, ga abinda yake tabbatuwa da shi ga muminai na lada magaggauci da majirkinci, Allah madaukakin sarki ya ce: {Shin, kuma wanda ya kasance matacce sa'an nan Muka rãyar da shi, kuma Muka sanya wani haske dõminsa, yanã tafiya da shi, yanã zama kamar wanda misãlinsa yanã cikin duffai, shĩ kuma ba mai fita ba daga gare su? Kamar wancan ne aka ƙawãta wa kãfirai abin da suka kasance sunã aikatãwa}. Suratul An'am, aya ta: 122
Al'amari na biyu: zuciyar da take bukatuwa zuwa al'amra uku.
1- abinda zai kiya ye masa karfinsa a gare shi, hakan kuwa yana kasancewa ne da imani da aiki na gari, da kuma aikata abubuwa na biyayya.
2-kariya daga abubuwan cutarwa, hakan kuwa da nisantar dukkan sabo, da nau'uka na sabawa.
3- rabuwa daga dukkan abubuwa masu cutarwa, hakan kuwa ta hanyar tuba da neman gafara.
Al'amari na uku: magance cutar zuciya da mamayewar rai damuwa gareta
Yana da magani biyu, yi mata hisabi, da saba mata, hisabi nau'i biyu ne:
nau'i na farko: kafin aikin, yana da matakai guda hudu:
1 shin wannan akin zai yi wu a gare shi?
shin wannan akin aikata shi, shi ya fi alheri a gare shi akan barinsa?
3- shi wannan aikin yana nufin fuskar Allah da shi?
4- shin wannan aikin abin taimako akansa ne, kuma yana da mataimaka da za su taimaka masa, kuma su taimakamasa idan aikin ya kasance yana bukatuwa zuwa mataimaka? idan amsar ta kasance akwai, to, sai ya ci gaba a bisa aikata shi, idan kuma (amsar) a'a ce to ba zai ci gaba da aikata shi ba har abada
nau'i na byu; bayan aiki, shi kuma nau'i uku ne:
1. Yi wa kansa hisabi abisa wata biyayya da bai iya cika ta ba a kan daga hakkin Allah madaukakin sarki, ba'a cikata ta ba a bisa fuskar da ake nema, yana daga cikin hakkokin Allah madaukakin sarki: tsarkake aiki, da nasiha da bibiya da halartar mahallarta ta kyautatawa, da shaidar da baiwar Allah a gare shi, da kuma shaida kasawa a bayan haka dukkaninsa.
2. Yi wa kansa hisabi a bisa dukkan wani aiki da barinsa ya fi alkhari akan aikata shi,
3 yi wa kansa hisabi a bisa wani al'amari na halal, ko wanda aka saba, da bai aikata shi ba, kuma shin ya nufi Allah da shi da gidan karshe, sai ya kasance mai cin riba, ko kuma nufinsa da shi duniya, sai ya zama mai hasara,
Abinda ya kunshi haka shine ya yi wa kansa hisabi da farko akan farillai sannan ya cika su in sun kasance ba su cika ba, sannan ya yi wa kansa hisabi akan abubuwan da aka hana, idan ya san ya aikata wani abu daga gare su sai ya riske su da tuba, da neman gafara, sannan a bisa abinda gabbansa suka aikata, sannan kuma a bisa rafkan{112} {112} ka iga satul allahfan 1/ 136.
Al'amari na hudu magance cutukan zuciya da mamayewar shaidan akanta.
shaidan makiyin mutum ne, rabuwa da shi, shine da abinda Allah ya shar'anta shi na neman tsari, hakika annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tattara tsakanin neman tsari daga sharrin zuciya da sharrin shaidan, Manzon Allah- tsira da mincin su tabbata a gare shi ya ce: ((Ka ce: Ya Allah Ubangijin sammai da kassai, masanin fake da sarari, Ubangijn kowanne abu kuma mamallakinsa, na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai kai, ina neman tsarinka daga sharrin kaina, da sharrin shaidan, da shirkarsa, ko in aikata mumuna akaina, ko in janyo shi zuwa musulmi”. Ka fadi hakan idan ka wayi gari , haka idan yamma ta yi , da kuma lokacin da zaka kwanta. {113}Tirmizi, da lamba 3392, da Abu Dawud, da lamba 5058, kuma Albany ya inganta shi a cikin Tirmizi, 3/142, da Sahihl Jami'u 5/
da neman tsari, da dogaro, da tsarkakewa, yana karya karfin shaidanu. {114} ka duba Igasatul allahfan 1/145-162.
Allah ya yi tsira da aminci ga bawansa kuma manzansa (annabi) Muhammad da alayensa da sahbbansa baki-daya daya, da wanda ya biyo su da kyautatawa zuwa ramar sakamako.
Related books
All books
TABBATACCAN BAYYANI A KAN YAWANCIN MAS'ALOLIN HAJJI DA UMRA DA KUMA ZIYARA A KAN DORON LITTAFI DA SUNNAH54 harsunaTABBATACCAN BAYYANI A KAN YAWANCIN MAS'ALOLIN HAJJI DA UMRA DA KUMA ZIYARA A KAN DORON LITTAFI DA SUNNAH
Littafin yana yin sharhin hukunce-hukuncen Hajji da Umra da Ziyara akan doron Littafi da Sunnah, yana bayyana wajiban Hajji da Umra, da abubuwan da aka haramta a lokacin harama, da kuma ladubban ziyarar Masallacin Annabi, yana mai gargaɗi a kan bidi'o'i a cikin waɗannan ibadu.
Hisnul muslim (Garkuwar Musulmi) daga zikirorin Alƙur’ani da Sunnah57 harsunaHisnul muslim (Garkuwar Musulmi) daga zikirorin Alƙur’ani da Sunnah
Littafin yana tattaro zikirai daga Alƙur'ani da kuma Sunnah domin sauƙaƙa maimaita karanta su a lokuta da yanayi daban-daban, kuma yana ƙunsar addu'o'i na farkawa daga bacci, da alwala, da sallah, da tafiya, da sauransu, wanda hakan zai taimaki musulmi wajen yi wa kansa garkuwa domin ya kasance a cikin kiyayewar Allah da kuma kulawarSa.
HANYOYI MASU AMFANI DON SAMUN RAYUWA MAI DAƊI85 harsunaHANYOYI MASU AMFANI DON SAMUN RAYUWA MAI DAƊI
Littafin Hanyoyi masu amfani don samun rayuwa mai daɗi na Shaikh Abdurrahman bn Nasir al-Sa’di - Allah Ya yi masa rahama - yana magance sabubban tabbataccen jin daɗi na haƙiƙa daga mahangar imani mai zurfi, yana shiryar da mai karatu zuwa nutsuwar zuciya ta hanyar imani da aiki na gari, da zikirin Allah, da gamsuwa da abin da Allah Ya bayar, da tafakkuri a kan ni’imomi, da kyautatawa, da dogaro ga Allah, da haƙuri, da kyakkyawan ƙimanta al’amura, da salo mai kyau. Yana sanya taswira ga rayuwa mai natsuwa a gabanka, madaidaiciya, kuma mai daɗi duk da juyin-juya-halin rayuwa.
TSARI GA WANDA YAKE SON YIN UMARAH DA HAJJI17 harsunaTSARI GA WANDA YAKE SON YIN UMARAH DA HAJJI
Littafin "Tsari ga wanda yake son yin Umarah da Hajji" na Sheikh Muhammad bn Saleh al-Uthaimeen, shi jagora ne da ya tartar kuma karbabbe ne ga dukkanin musulmin da yake tsinkaye don yin ayyukan Hajji da Umarah. Littafin yana gabatar da wani sharhi cikakke ne don ladubban tafiya, da hukunce-hukuncen harama, da abubuwan da suka wajaba ga mai yin Hajji da Umarah, yana mai dogara ga Alƙur'ani mai girma da Sunnar Annabi, kamar yadda littafin yake bayanin miƙatan Hajji a rarrabe, da Nau’ukan ibadu, da hukunce-hukuncen sallar matafiyi, yana mai bayyana yadda ake yin kowane rukuni daga cikin rukunan…