GABATARWA Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga wanda aka aiko shi rahama ga talikai, da alayensa da sahabbansa da wanda ya bi sunnarsa, ya kuma nemi shiryuwa da shiriyarsa har zuwa ranar sakamako. Bayan haka: Wannan wani taƙaitaccen saƙo ne, wanda ya ƙunshi mafi muhimmancin abinda Musulmi yake buƙatarsa a falalar goman farko na Zul Hijja, mun tattarashi ga masu ziyartar Masallatan Harami biyu masu daraja, maza da mata; domin su kasance cikin sani da fahimta akan al'amurran addininsu. Muna roƙon Allah mai karamci da Ya anfanar da shi, Ya kuma sanya shi…
Harshe: lang_ha
Shiryawa: Kwamitin ilimi na Ƙungiyar hidimtawa Musulunci da yaruka daban daban.
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga wanda aka aiko shi rahama ga talikai, da alayensa da sahabbansa da wanda ya bi sunnarsa, ya kuma nemi shiryuwa da shiriyarsa har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:
Wannan wani taƙaitaccen saƙo ne, wanda ya ƙunshi mafi muhimmancin abinda Musulmi yake buƙatarsa a falalar goman farko na Zul Hijja, mun tattarashi ga masu ziyartar Masallatan Harami biyu masu daraja, maza da mata; domin su kasance cikin sani da fahimta akan al'amurran addininsu. Muna roƙon Allah mai karamci da Ya anfanar da shi, Ya kuma sanya shi mai kyau, kuma saboda Allah ne kaɗai; lallai Shi ne mafi alherin wanda ake roƙo, kuma mafi karamcin wanda ake fata.
Kwamitin ilimi na Ƙungiyar hidimtawa Musulunci da yaruka daban daban.
Falalar goman farko na Zul-Hijjah:
Kwanaki goma na farkonZulhijjah, falalarsu babba ce, Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya bayyana shi a cikin LittafinSa, kuma ManzonSa Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana shi a cikin Sunnarsa, su ne kwanakan da Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya rantse da su a cikin LittafinSa da faɗinSa:(Inã rantsuwa da alfijiri*Da darũruwa gõma)[al-Fajr: 1-2].Su ne goman farko na Zulhijjah kamar yadda Ibn Abbas, da Ibn Zubair, da Mujahid, da Ibn Kathir, da Ibn al-Ƙayyim, da wasu daga cikin salaf da khalaf suka faɗa [1].[1] Tafsirin Ibnu Kathir (4/106), da Zad al-Ma'ad (1/56).
Su ne kwanakan da aiki a cikinsu yafi alheri fiye da jihadi domin Allah - Maɗaukakin Sarki -; saboda hadisin Ibn Abbas - Allah Ya yarda da su -, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:«Babu wasu kwanakan da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soyuwa a wurin Allah sama da waɗannan kwanakin goma", Suka ce: Ya Ma’aikin Allah, Har jihadi domin ɗaukaka addinin Allah? Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Har Jihadi domin ɗaukaka addinin Allah, sai dai mutumin da ya fita da kansa da dukiyarsa, kuma bai dawo da komai ba» [2].[2] Bukhari ne ya ruwaito shi, da Tirmizi kuma lafazin nasa ne.
FALALAR AYYUKA A GOMAN FARKO NA ZUL-HIJJA:
1. Aikin Hajji da Umra, suna daga mafifitan ayyuka a cikin wannan goman; saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:«Wanda duk ya ziyarci wannan ɗaki (Ka'abah), bai yi kwarkwasa ba, kuma baiyi fasiƙanci ba; zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haifeshi».A cikin wani lafazi na Muslim:«Wanda duk ya ziyarci wannan ɗakin, bai yi kwarkwasa ba, kuma bai fasiƙanci ba; zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haifeshi» [3].Faɗinsa: (Duk wanda ya zo wannan ɗãki) yana ɗauke da ma'anar aikin Hajji da Umra, kuma godiya ta tabbata ga Allah. Wanda tsira da aminci suka tabbata a gareshi ya ce:«Umra zuwa Umra kaffara ce ga abinda ke tsakaninsu, kuma Hajji kuɓutacce ba shi da wani sakamako face Aljanna» [4].[3] Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.[4] Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
2.: Azimin kwanaki tara, ko abin da ya sawwaƙƙa daga cikinsu; saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:«Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soyuwa a wurin Allah sama da waɗannan kwanaki goman».Kuma azumi yana daga cikin mafi girman ayyukan alheri, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kwaɗaitar akansa, kuma ya yi kira zuwa gare shi, daga hakan akwai faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:«Babu wani bawa da zai yi azumin yini ɗaya a tafarkin Allah face Allah Ya nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) kaka saba'in».[5] Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
3. Ana shar'anta yin hadaya a ranar babbar sallah da kuma kwanakin Tashriƙ, haƙiƙa ya tabbata cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:«Ya yi layya da raguna biyu masu farar fuska da baƙi-baƙi masu ƙaho, ya yanka su da hannunsa, ya ambaci Allah kuma ya yi kabbara, kuma ya ɗora ƙafarsa akan fatun wuyayensu». [6].[6] Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:«Babu wani aiki da ɗan Adam zai yi a ranar layya da yafi soyuwa ga Allah fiye da zubar da jini, kuma za'a kawo shi ranar alƙiyama da ƙahonninsa da gashinsa da kofatunsa, kuma lallai jinin yana faɗuwa a wajen Allah a wani wuri kafin ya faɗi a ƙasa, don haka ku daɗaɗa rai da shi» [7].[7] Tirmizi ne ya rawaito shi.
Kuma idan goma ga watan Zul-Hijjah ya shiga; wanda yake son yin layya ya dakatar da cirar wani abu daga gashinsa da fatar jikinsa; saboda hadisin Ummu Salamah - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, cewa shi ya ce:«Idan kun ga jinjirin watan Zul-Hijja kuma ɗayanku yana son ya yi layya; to ya kame daga (cirar) gashinsa da faratansa».Kuma a cikin wani lafazin:«...Kada ya cire wani abu daga gashinsa ko faratansa har sai ya yi layya» [8].[8] Muslim ne ya rawaito shi.
4. Kabbara, da Hailala, da ambaton Allah a cikin waɗannan kwanaki goman da kwanukan Tashriƙ; saboda hadisin Abdullahi Ibnu Umar -Allah Ya yarda da su- daga Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce:«Babu wasu kwanaki da suka fi girma a wurin Allah kuma mafi soyuwa a gare Shi daga aiki a cikinsu kamar waɗannan kwanaki goman, don haka ku yawaita: Hailala, da Kabbara, da Hamdala a cikinsu» [9].[9] Ahmad ne ya ruwaito shi.
Kabbara kashi biyu ne kamar haka:
Sashe na farko: Kabbara kai tsaye, wadda ba ta ƙayyaduwa da bayan salloli; bari dai ana shar'anta ta a kowane lokaci.
Ana fara kabbara kai tsaye a idin layya daga farkon goman Zulhijja zuwa ƙarshen yinin kwanukan Tashriƙ: A dukkanin lokuta, a dare, da rana, da hanya, da kasuwanni, da masallatai, da gidaje, da kuma duk wurin da ya halatta a ambaci Allah - Maɗaukakin Sarki -.
Sashe na biyu: Kabbara abar ƙayyadewa: Ita ce wadda ake ƙayyadeta da bayan salloli a idin layya musamman. Lokacinta da kuma sifarta kamar haka ne:
Na farko: Kabbara abar ƙayyadewa tana farawa bayan sallar Asuba ranar Arfa, kuma tana ƙarewa bayan sallar La'asar a rana ta uku na kwanukan Tashriƙ. Wannan ga wanda ba mahajjaci ba, amma mahajjaci kabbara abar ƙayyadewa a haƙƙinsa tana farawa ne daga Azzahar ɗin ranar layya.
Na biyu: Siffar Kabbara: (Allahu Akbar, Allahu Akbar, La'ilaha illallahu, Allahu Akbar Allahu Akbar walillahil hamd (Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma, babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma, kuma godiya ta tabbata ga Allah)[10].[10] Ka duba: "al-Mughni na Ibn Ƙudama" (3/290), da "al-Sharh al-Kabir tare da al-Muƙni' da al-Insaf" (5/380).
5. Kwaɗaitarwa akan yin sallar idi ga wanda ba mahajjaci ba, da zuwa da wuri, da sauraron huɗuba; domin tana daga cikin mafi girman alamomin Musulunci; kuma saboda girman al'amarinta ne aka umarci mata su fita zuwa gare ta har ma da budurwowi da masu haila; daga Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita - ta ce:«Mun kasance ana umartar mu da mu fito ranar idi, harma mu fito da budurwowi daga ɗakunansu, har da masu haila ma mu fito da su sai su zama a bayan mutane, sai suyi kabbara tare da kabbarar masu sallah suyi addu`ah da addu`ar su, suna masu fatan samun albarkar wannan yini da kuma tsarkinsa».Kuma a cikin wani lafazin:«Ya umarci mata masu haila da su nisaci wuraren sallar musulmai» [11].[11] Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
6. Yawaita ayyuka na gari, daga cikin nafiloli na ibada: Kamar sallah da sadaka, da karãtun Al-ƙur'ani mai girma, da umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna, da kyautatawa maƙwabta, da sãda zumunci da sauran ayyuka na gari, saboda faɗin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:«Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soyuwa a wurin Allah sama da waɗannan kwanakin goma». Suka ce: Ya Manzon Allah, har jihadi domin ɗaukaka addinin Allah? Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Har jihadi domin ɗaukaka addinin Allah, sai dai mutumin da ya fita da kansa da dukiyarsa, kuma bai dawo da komai ba» [12].[12] Bukhari ne ya rawaito shi, da Tirmizi.
Allah ne Abun roƙo, Ya amfane mu da abun da muka sani, kuma Ya sanar da mu abun da zai amfane mu, lallai cewa Shi Mai yawan kyauta ne mai karamci, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammad da iyalansa da aminci, aminci mai yawa.
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin ƙai. Shin ka tambayi kanka: Wa ya halicci sammai da ƙasa da abinda yake cikinsu, na halittu masu girma? Wa ya ƙera wannan ƙwararran tsari nagartacce a cikin su?
Ɗabbaƙawa a aikace a taƙaice na kaifiyyar aiwatar da sallah, domin mu bauta wa Allah bisa basira kuma sallarmu ta kasance mai cikar rukunai da sharuɗɗa. Sifar Sallah Idan muna son yin sallah to ya wajaba mu yi tsarki daga ƙaramin hadasi da kuma babban hadasi. Kuma mu yi sallah da tufafi masu tsarki masu suturce al'aurarmu. Kuma jikinmu da wurin sallarmu su kasance masu tsarki daga najasa. Mu fuskanci alƙibla Kuma mustahabbi ne mu yi sallah zuwa ga sutura.
Littafin Hanyoyi masu amfani don samun rayuwa mai daɗi na Shaikh Abdurrahman bn Nasir al-Sa’di - Allah Ya yi masa rahama - yana magance sabubban tabbataccen jin daɗi na haƙiƙa daga mahangar imani mai zurfi, yana shiryar da mai karatu zuwa nutsuwar zuciya ta hanyar imani da aiki na gari, da zikirin Allah, da gamsuwa da abin da Allah Ya bayar, da tafakkuri a kan ni’imomi, da kyautatawa, da dogaro ga Allah, da haƙuri, da kyakkyawan ƙimanta al’amura, da salo mai kyau. Yana sanya taswira ga rayuwa mai natsuwa a gabanka, madaidaiciya, kuma mai daɗi duk da juyin-juya-halin rayuwa.