Mafi Yawan Bincike
A KAN LADUBBA DA HUKUNCE-HUKUNCEN ZIYARATR MASALLACIN ANNABI
A KAN LADUBBA DA HUKUNCE-HUKUNCEN ZIYARATR MASALLACIN ANNABI
These files are generated automatically from the book's text; their layout may differ from the printed edition.
A KAN LADUBBA DA HUKUNCE-HUKUNCEN ZIYARATR MASALLACIN ANNABI
Bukhari ne ya ruwaito shi (1189), da Muslim (827) kuma lafazin nasa ne.
Bukhari ne ya ruwaito shi (1190) da Muslim (1394).
Bukhari ne ya ruwaito shi (1195) da Muslim (1390).
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammad da alayansa da sahabbansa baki ɗaya.
Bayan haka:
Wannan wani saƙo ne a taƙaice a kan ladubban ziyartar Masallacin Annabi da hukunce-hukuncesu, mun yi kwaɗayin kawo bayanin mafiyawancin abin da mai ziyartar Masallacin Annabi yake buƙatuwa zuwa gare su.
Allah muke roƙo Ya sanya shi tsarkakakke ne don zatinSa mai girma, kuma Ya amfanar da dukkanin musulmai da shi.
Kwamitin ilimi na Cibiyar hidimar abinda Musulunci ya ƙunsa a cikin harsuna daban daban.
TAKAITACCEN BAYANI
An so ziyartar Masallacin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma ziyarar bata da wani ƙayyadajjen lokaci, kuma bata cikin ayyukan Hajji, ziyartar ƙabarin Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ko (ziyartar) Baƙi'a ba wajibi bane ga mahajjata - maza ko mata -.
Ɗaura sirdi (nikar gari) da tafiya saboda ziyarar ƙabrin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya halatta, domin ɗaura sirdi ta fuskar ibada ba ya kasancewa dan ziyatar ƙaburbura, yana kasancewa ne dan masallatan nan uku ne kawai, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: (Kada ku ɗora sirdi sai ga masallatai uku: Wannan masallacin nawa, da Masallaci mai alfarma, da kuma Masallaci mafi nisa (Kudus))
Wanda ke nesa da Madina bai halatta ya ɗaura sirdi da nufin ziyarar ƙabari ba, sai dai an shara'anta masa ɗaura sirdi da nufin ziyarar masallacin Annabi mai daraja, idan ya isa gare shi sai ya ziyarci ƙabarin na annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da ƙaburburan sahabbansa, sai ziyarar ta shiga ƙabarinsa dan bi ga ziyarar masallacinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Ba'a shar’antawa mace ziyartar ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ko ƙabarin waninsa; domin shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya la'anci mata masu yawan ziyartar ƙaburbura, dan abin da zai iya faruwa garesu na kukan mutuwa da tabarruji da waninsu na abubuwan saɓawa shari'a, saidai an so garesu su yawaita salati da sallama ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci da waninsa, sai hakan ya isarwa Annabi - tsira da amincin Allah su ta tabbata agare shi - alhali ita tana kowanne wuri; saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (Kada ku maida gidajanku ƙaburbura, kuma kada ku maida ƙabarina idi, ku yi salati a gareni; domin salatinku a gareni yana isomin a duk inda kuke). kuma Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: (Allah Yana da wasu mala'iku waɗanda suke yawo a ƙasa, suna isar min da sallamar al'ummata).
Idan ya shiga masallacin Annabi mai daraja an so gare shi ya fara gabatar da ƙafarsa ta dama a lokacin shiga sai ya ce: (Allahummaf tah li abwaba rahmatiKa). Ma’ana: (Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa)). kamar yadda zai ce a yayin shiga sauran masallatai.
Kuma babu wani keɓantaccen zikiri dan shiga masallacinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Sannan ya yi sallah raka'a biyu sallar gaishe da (Ubangijin masallaci).
Idan lokacin ba lokacin hana nafila ba ne to zai iya yin sallar nafila yadda ya so, raka'a biyu-biyu; Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: (Sallah a cikin masallacina wannan (ita ce) mafi alheri daga sallah dubu a cikin waninsa sai dai Masallaci mai alfarma).
Yana kamata ya kintaci yin sallah a cikin Raudah - ita ce abin da ke tsakanin minbarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma ɗakinsa - idan hakan ya sawwaƙa a gare shi; saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: (Tsakanin gida na da minbari na, dausayi ne daga cikin dausayan aljanna).
Idan hakan bai sawwaƙa gare shi ba, to sai ya yi sallah a kowane ɓangare na Masallacin, wannan in ba a sallar jam’i ba ne, amma a sallar jam’i to ya kiyaye akan (yin sallah a) sawun farko wanda ke biye da liman; saboda gamewar dalilan da suka zo a kan hakan.
Idan ya yi nufin ziyartar ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da ƙaburburan sahabbansa biyu:
Sai ya tsaya a gaban ƙabarinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da ladabi, da natsuwa, da ƙasa-ƙasa da murya, sannan ya yi masa sallama - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana mai cewa; (Assalamu alaika ya rasulallahi wa rahmatullahi wa barakatuhu). Wato: (Aminci ya tabbata a gareka ya Manzon Allah da rahamar Allah da albarkarSa)); idan ya ce: (Ashhadu annaka rasulullahi haƙƙan, wa'annaka ƙad ballagtar risalh, wa addaital amana, wa jahadta fil lahi haƙƙa jihadihi, wa nasahtal ummah, fa jazakal lahu an ummatika afdala ma jaza nabiyyan an ummatihi. Wato: (Ina shaida cewa lallai kai Manzon Allah ne haƙiƙa, kuma lallai cewa kai haƙiƙa ka isar da saƙo, kuma ka bada amana, kuma ka yi yaƙi saboda Allah haƙiƙanin yaƙi, kuma ka yi wa al'umma nasiha, saboda haka Allah Ya yi maka sakayya ga al'ummarka mafificin abin da ya sakawa Annabi ga al'ummarsa)) to babu laifi.
Sannan ya yi dama kaɗan sai ya yi sallama ga Abubakar al-Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi -.
Sannan kuma ya yi dama kaɗan sai ya yi wa Umar bin Khaɗɗab sallama, Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su - ya kasance idan zai yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sallama da sahabbansa biyu galibi ba ya ƙarawa akan faɗinsa: (Assalamu alaika ya rasulallah, assalamu alaika ya Ababakar, assalamu alaika ya abatah. Wato: (Aminci ya tabbata agareka ya Manzon Allah, aminci ya tabbata agareka ya Abubakar, aminci ya tabbata agareka ya babana)) sannan ya juya.
Ba ya kamata a tsawaita tsayuwa ko addu'a a ƙabarin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tababata agare shi - da ƙabarin sahabbansa biyu, haƙiƙa Imamu Malik ya ƙi hakan, kuma ya ce: Hakan bidi'a ce, magabata ba su aikata hakan ba, kuma babu abin da zai gyara ƙarshen wannan al'ummar sai abin da ya gyara na farkonta.
Amma abin da wasu daga cikin masu ziyara suke aikata wa na ɗaga murya a wurin ƙabarinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da tsawaita tsayuwa a wurin to saɓanin abin da aka shara'anta ne, (Allah) Maɗaukakin sarki Ya ce: (Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku ɗaukaka saututtukanku bisa sautin Annabi, kuma kada ku bayyana sauti gare shi a magana, kamar bayyanãwar sãshenku ga sãshe, dõmin kada ayyukanku su ɓãci, alhãli kuwa kũ ba ku sani ba. Lalle waɗanda ke runtsẽwar saututtukansu a wurin Manzon Allah waɗannan ne waɗanda Allah Yã, jarrabi zukãtansu ga taƙawa. Sunã da wata irin gãfara da ijãra mai girma) [al-Hujurat: 2-3] Kuma domin tsawaita tsayuwa a ƙabarin nasa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, da yawaita yi masa sallama, yana kawo cunkoso da yawan hayaniya da ɗaga murya a ƙabarin sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, to hakan ya saɓawa abinda Allah Ya shara'antawa musulmai a cikin waɗananan ayoyin masu kyawun ma'anoni, kuma shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - abin girmamawa ne halin kasancewarsa a raye ko a bayan rasuwa ne, dan haka ba ya kamata ga mumini ya aikata abinda ya saɓawa ladabin shari'a a ƙabarin sa.
Haka nan abinda wasu daga masu ziyara da wasunsu suke aikatawa na kintatar addu'a a ƙabarinsa, yana mai fuskantar ƙabari yana mai ɗaga hannayensa yana yin addu'a, to dukkanin wannan ya saɓawa abinda magabata na ƙwarai suke a kansa daga sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da masu binsu da kyautatawa, kai shi yana daga fararrun bidi'o'i.
Haka nan abinda wasu daga cikin masu ziyara suke aikatawa a yayin yi masa sallama tsira da amincin Allah su tabbata agare shi, na ɗora hannun damarsu akan hannunsu na hagu a saman ƙirjinsa ko a ƙarƙashinsa kamar yanayin mai yin sallah, to wannan yanayin ba ya halatta a lokacin yi masa sallama, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi; domin hakan sifface ta ƙanƙan da kai da kuma kara ƙanƙar da kai din, da kuma ibadar da bata inganta (ga kowa) sai ga Allah, kamar yadda Hafiz Ibnu Hajar - Allah Ya yi masa rahama - ya hakaito a cikin (Fathul Bari) daga malamai.
Kuma ba ya halatta ga wani ya nemi kusanci ga Allah ta hanyar shafa ɗaki, ko yi masa ɗawafi, kuma kada ya roki Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - biyan buƙatarsa, ko warkar da mara lafiyarsa, da makamantan haka; domin ba'a neman dukkanin wadannan sai a wurin Allah Shi kaɗai.
An so ga wanda ya ziyarci Madina a lokacin da yake a can ya ziyarci Masallacin ƙuba, kuma ya yi sallah a cikinsa; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana zuwa Masallacin na Kuba akan abin hawa da kuma a ƙasa, kuma yana yin sallah raka'a biyu a cikinsa, daga Sahl ibnu Hunaif ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: (Duk wanda ya yi tsarki daga gidansa sannan ya taho Masallaci ƙuba sai ya yi sallah a cikinsa to yana da ladan Umarah).
Kuma an sunnata masa ziyartar ƙaburburan Baƙi'a - ita ce maƙabrtar Madina - da ƙaburburan shahidai, da ƙabarin Hamza - Allah Ya yarda da shi -; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ziyartarsu, kuma yana yi musu addu'a, kuma saboda faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: (Na kasance na haneku daga ziyartar ƙaburbura, to ku ziyarcesu domin zasu tunatar da ku lahira)
Idan zai ziyarcesu sai ya faɗi irin abin da yake faɗa idan ya ziyarci ƙaburbura: (Assalamu alaikum ahlad diyari minal mu'uminina wal muslimina, wa inna insha Allahu bikum lahiƙun, wa yarhamul lahul mustaƙdimina minna wal mustaakhirina, nas'alullah lana walakumul afiya. Ma’ana: (Aminci ya tabbata agareku yaku mutanen wannan gida, daga muminai da musulmai, lallai mu in Allah Ya so masu riskarku ne, kuma Allah Ya jiƙan waɗanda suka gabata daga cikinmu da waɗanda suka jinkirta, muna roƙa mana Allah mu da ku lafiya)).
Babu kokwanto cewa abin da ake nufi da ziyartar ƙaburbura shi ne tina lahira da kuma kyautatawa mamata ta hanyar yi musu addu'a, da kuma bin sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, wannan ita ce ziyara ta shari'a.
Amma ziyartarsu dan nufin addu'a a wurin ƙaburburansu, ko roƙon Allah saboda su, ko da alfarmarsu da makamancin haka to wannan ziyarar ta bidi'a ce abar ƙyama, Allah ko ManznSa basu shara'antata ba, kuma magabata na gari basu aikatata ba, amma roƙonsu biyan buƙatu, ko warkar da marasa lafiya, da makamancin haka to wannan yana daga cikin babbar shirka.
Ya kai mai karatu ga wani abu daga cikin hadisan ƙarya akan wannan babin; don ka sansu kuma ka kiyaye ruɗuwa da su:
Na farko: (Wanda ya yi Hajji bai ziyarce ni ba, to haƙiƙa ya yi mini wauta).
Na biyu: (Wanda ya ziyarce ni bayan rasuwata, to kamar ya ziyarceni ne a halin rayuwata).
Na uku: (Wanda ya ziyarce ni kuma ya ziyarci babana Ibrahim a cikin shekara ɗaya zan lamunce masa aljanna ga Allah).
Na huɗu: (Wanda ya ziyarci ƙabarina, to cetona ya wajaba gare shi).
To waɗannan Hadisan da makamantansu babu wani abu da ya tabbata a cikinsu daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Hafiz al-Uƙaili ya ce: Babu wani abu da ya inganta a cikin wannan babin. Kuma Hafiz Ibnu Hajar ya faɗa a cikin al-Talkhisa - Bayan ya ambaci mafi yawancin waɗannan riwayoyin -: Dukkan hanyoyin wannan hadisin masu rauni ne. Ziyartar masallacin Annabi kafin Hajji ko Umarah ko bayansa ba ya daga cikin sunnonin Hajji ko Umarah ko kuma cikarsu; domin cewa ziyarar Masallacin Annabi abar so ce kai tsaye; idan mai Hajji ko mai Umarah bai ziyarce shi ba to babu laifi a kansa, kuma babu wata alaƙa tsakanin Hajji ko Umarah da kuma ziyarar Masallacin Annabi ita wata ibada ce a rabe take, wanda ya yi Hajji ko ya yi Umarah ziyartar Masallacin Annabi ba ta wajaba a kansa ba, haka nan wanda ya ziyarci Masallacin Annabi aikin Hajji ko Umarah ba su wajaba akansaba, idan ya haɗa tsakanin Hajji da Umarah da ziyarar Masallacin Annabi a cikin tafiya ɗaya to babu laifi.
Abubuwan da suka saɓawa shari'a (da ake yi) a ziyarar Masallacin Annabi
Shafar bangwaye da itatuwa da ƙarfe a wurin ziyarar ƙabarin Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da ɗaura zare da makamancinsa a tagogin dan neman tabarruki.
Albarka tana tabbata ne a cikin abin da Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah suka shara'anta ne kawai ba'a cikin bidi'o'i ba.
Tafiya zuwa koguna a cikin dutsen Uhud da makamancin haka kogon Hira da kogon Saur a Makkah da ɗaura gyale a wurinsu da kuma yin addu'a da addu'o'in da Allah bai yi izini da su ba da kuma shan wahala a cikin hakan.
Dukkanin waɗannan bidi'o'i ne basu da wani asali a cikin shari'a tsarkakakkiya.
Ziyartar wasu daga cikin guraren da suke da'awar cewa suna daga cikin wuraran tarihi na Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kamar inda taguwarsa ta durƙusa da rijiyar zobe, ko rijiyar Usman, da ɗibar ƙasa daga waɗannan guraren dan neman albarka.
Kiran mamata a wurin ziyar maƙabartun Baƙi'a da maƙabartun shahidan Uhud da jefa kuɗi a wurin dan neman kusanci zuwa garesu da kuma neman albarka daga wadanda ke kwance a wurin.
Waɗannan abubuwan suna daga cikin manyan kurakurai, kai suna daga cikin babbar shirka kamar yadda ma'abota ilimi suka ambatar, kuma Littafin Allah da sunnar ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suka yi nuni a kansa; domin cewa bauta tana tabbata ne ga Allah Shi kaɗai juyar da wani abu daga gareta ga wanin Allah ba ya halatta, kamar yin addu'a da yanka da bakance da makamancin haka; saboda faɗinsa: {Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi} [al-Bayyinah: 5].
Allah ne Mafi sani, Allah Ya yi tsira Ya yi aminci ga Annabinmu Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki ɗaya.
Related books
All books
ZIYARAR MASALLACIN ANNABI MAI AL-FARMA TARE DA FADAKARWA DA KUMA NUSARWA GAMAI ZIYARAR14 harsunaZIYARAR MASALLACIN ANNABI MAI AL-FARMA TARE DA FADAKARWA DA KUMA NUSARWA GAMAI ZIYARAR
Wallafar Dr. Abdullahi Bn Naji Al-mikhlafi Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai Gabatarwar Godiya ga Allah wanda ya sanya Ziyarar Masallacin Annabinsa -tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- daga cikin Manyan Ayyukan Ibada, kuma ya sanya Salati ga Annabi a cikinsa karin Darajoji, Kuma Sati da Aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammad Mafi tsarkin Halittu, Kuma haka ga Alayansa da Sahabbansa da duk wadanda suka bisu da kyautaye har zuwa Ranar Mutuwa
FALALA DA LADUBBAN MASALLACIN ANNABI DA HUKUNCE-HUKUNCEN ZIYARAR ƘABARIN ANNABI -TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARE SHI- DA ƘABURBURAN SAHABBANSA BIYU -ALLAH YA YARDA DA SU-52 harsunaFALALA DA LADUBBAN MASALLACIN ANNABI DA HUKUNCE-HUKUNCEN ZIYARAR ƘABARIN ANNABI -TSIRA DA AMINCI SU TABBATA A GARE SHI- DA ƘABURBURAN SAHABBANSA BIYU -ALLAH YA YARDA DA SU-
Littafin yana bayanin falalar Masallacin Annabi da ladubban ziyartarsa, haka kuma yana gabatar da ladubban ziyartar ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da na sahabbansa guda biyu - Allah Ya yarda da su -, yana mai jaddada muhimmancin natsuwa da tsarki da kuma nisantar ayyukan bidi'a a lokacin ziyarar.
TAƘAITACCEN BAYANI A KAN SIFFAR UMARAH DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCENTA65 harsunaTAƘAITACCEN BAYANI A KAN SIFFAR UMARAH DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCENTA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Annabimmu Muhammad, da alayensa da sahabbansa bakiɗaya. Bayan haka: Wannan taƙaitaccan bayani ne a kan siffar aikin Umarah da hukunce-hukuncenta da kuma ladubbanta, mun yi kwaɗayi a kawo bayanin galibin abinda mai yin Umarah yake da buƙatuwa zuwa gare shi. Allah muke roƙo Ya sanya shi tsarkakakke don zatinSa mai girma, kuma Ya amfanar da dukkanin musulmai da shi.
TABBATACCAN BAYYANI A KAN YAWANCIN MAS'ALOLIN HAJJI DA UMRA DA KUMA ZIYARA A KAN DORON LITTAFI DA SUNNAH54 harsunaTABBATACCAN BAYYANI A KAN YAWANCIN MAS'ALOLIN HAJJI DA UMRA DA KUMA ZIYARA A KAN DORON LITTAFI DA SUNNAH
Littafin yana yin sharhin hukunce-hukuncen Hajji da Umra da Ziyara akan doron Littafi da Sunnah, yana bayyana wajiban Hajji da Umra, da abubuwan da aka haramta a lokacin harama, da kuma ladubban ziyarar Masallacin Annabi, yana mai gargaɗi a kan bidi'o'i a cikin waɗannan ibadu.