المنتقى من المتجر الرابح في ثواب العمل الصالح - المعتمد
كتاب جامع لجملة من أحاديث النبي -صلى الله عليه وسلم- الصحيحية في ثواب الأعمال الصالحة كطلب العلم والطهارة والصلاة، وصلاة التطوع، والجمعة والجنائز، والصدقات والصوم والحج والجهاد، وقراءة القرآن، وذكر الرحمن وغيرها.
ABIN ZABOWA DAGA ABIN KASUWANCI MAI RIBA A CIKIN LADAN AIKI NA GARI
LADAN ILIMI DA NA MALAMAI
Daga Mu'awiya - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Duk wanda Allah Ya ke nufin sa da alheri zai fahimtar da shi Addini".
Bukharine ya ruwaito shi (71) da Muslim (1037).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya shiga wata hanya wacce ya ke neman ilimi a cikin ta Allah Zai sauwaƙa masa hanyar zuwa Aljanna da ita, mutane ba za su haɗu a wani ɗaki daga ɗakunan Allah ba, suna karanta littafin Allah, suna dandaƙa karanta shi a tsakaninsu ba, sai nutsuwa ta sauka a gare su, kuma rahama ta lulluɓesu, Mala'iku sun kewaye su, kuma Allah Ya ambace su a cikin waɗanda ke wurin sa".
Muslim ne ya ruwaitoshi (2699).
LADAN SANAR DA ILIMI
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan mutum ya mutu akin sa ya yanke sai dai daga abu uku: Sadaka mai gudana, ko wani ilimi da ake anfanuwa da shi, ko ɗa na gari da ya ke masa addu'a".
Muslim ne ya ruwaitoshi (1631).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya yi kira zuwa ga shiriya yana da lada kwatankwacin ladan wanda ya bi shi, ba za'a rage komai daga ladan su ba, kuma wanda ya yi kira zuwa ga ɓata a kan sa akwai kwatankwacin zunubin wanda ya bi shi, ba za'a rage komai daga zunuban su ba.
Muslim ne ya ruwaito shi (2674).
Daga Abu Mas'ud Al-Ansary - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Duk wanda ya shiryar akan wani aikin alheri, to, yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikata shi".
Muslim ne ya ruwaito shi (1893).
LADAN ALWALA DA CIKATA
Daga Abu huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan bawa musulmi ya yi alwala, ko kuma mumini, sai ya wanke fuskar sa, to, kowane kuskure da ya kalla da idanun sa zai fice daga fuskar sa tare da ruwa, ko kuma tare da ƙarshen ɗigon ruwa, idan ya wanke hannayen sa, kowane kuskure zai fita daga hannayen sa waɗanda hannayen sa suka damƙa da su tare da ruwa ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa, idan ya wanke kafafuwan sa kowane kuskuren da kafafuwan sa suka tafi gareta zasu fita tare da ruwa ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa har sai ya fita tsarkakakke daga zunubai".
Muslim ne ya ruwaito shi (244).
Daga Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi- daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwalar, to, kurakuran sa za su fita daga jikin sa har sai sun fita ta ƙarƙashin faratan sa".
Muslim ne ya ruwaito shi (229).
LADAN CIKA ALAWALA A LOKUTAN DA AKE ƘI
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Shin ba na shiryar da ku ga abin da Allah Ya ke shafe kurakurai da shi ba, kuma Ya ɗaukaka darajoji da shi?" Suka ce: Na'am, ya Manzon Allah, ya ce: "Cika alwala a lokutan da ake ƙi, da yawan taku zuwa masallatai, da jiran sallah bayan sallah, wancanan ku shi ne zaman dako".
Muslim ne ya ruwaito shi (251).
LADAN ASUWAKI
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Asuwaki mai tsarkake baki ne, kuma mai janyo yardar Ubangiji ne".
Al-Nasa'i ne ya ruwaito sh (1/10), Bukhari ya ruwaito shi a matsayin Mu'allaƙi a cikin ingantaccen littafin sa (4/158).
LADAN KIYAYE ALWALA
Daga Sauban - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Ku daidaita, ba zaku iya kiyayewa ba, ku sani cewa lallai mafi alherin ayyukan ku itace sallah, kuma ba mai kiyayewa akan alwala sai mumini".
Ahmad ne ya rawaito shi (22378).
LADAN FAƊIN SHAHADA BIYU BAYAN ALWALA
Daga Umar - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Babu wani mutum a cikinku da zai yi alwala ya kai matuƙa ko ya cika alwalar sannan ya ce: (Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma lallai cewa Muhammadu bawan Allah ne kuma manzansa ne) sai an buɗe masa ƙofofin Aljanna takwas ya shiga ta wadda ya ke so.
Muslim ne ya ruwaito shi (234).
LADAN SALLAH BAYAN ALWALA
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce wa Bilal yayin sallar Asuba:
"Ya Bilal, ka zantar dani da mafi ƙaunar aikin da ka aikata shi a cikin Musulunci, domin ni na ji takun takalman ka a gaba na a Aljanna".
Yace: Ban aikata wani aiki ba mafi ƙauna a wurina: Sai dai cewa ni ban taɓa alwala ba a cikin kowane lokaci da daddare ne ko da rana, sai na sallaci abinda aka rubuta min in sallata da wannan alwalar.
Bukhari ne ya ruwaito shi (1149) da Muslim (2458).
Daga Uƙubah ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Babu wani Musulmin da zai yi alwala ya kyautata alwalar sa, sa'annan ya tashi ya yi raka'a biyu, yana mai mai da hankali a cikinsu da zuciyar sa da fuskar sa, sai Aljanna ta wajaba a gare shi".
Muslim ne ya ruwaito shi (234).
Daga Usman - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ya yi alwala kwatankwacin alwalata wannan, sannan ya yi sallah raka'a biyu, bai zantar da ransa a cikinsu ba, za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa".
Bukhari ya ruwaito shi (164) da Muslim 2267).
LADAN MAI KIRAN SALLAH
Daga Abu Sa'a sa'ah Al-Ansary: Lallai cewa Abu Sa'id Al-khudry - Allah Ya yarda da shi - ya ce masa:
"Lallai ni ina ganin ka kana san tumakai da ƙauye, to, idan ka kasance a cikin tumakan ka da ƙauyan ka, to, ka yi kiran sallah, kuma ka ɗaga muryar ka da kiran domin cewa shi: Ba wani aljani ko wani mutum ko wani abu da zai ji muryar mai kiran sallah sai ya yi shaida gareshi ranar Al-ƙiyama".
Abu sa'id ya ce: Na ji shi daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -.
Bukhari ne ya ruwaito shi (3296).
Daga Dalha ɗan Yahaya, daga baffansa ya ce:
Na kasance a wurin Mu'awiya ɗan Abu Sufyan, sai ladani ya zo masa yana kiran sa zuwa ga sallah sai Mu'awiya ya ce:
Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Ladanai su ne mafiya tsawon wuyaye a ranar Al-ƙiyama".
Muslim ne ya ruwaito shi (387).
Daga Anas ɗan Malik ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana kai hari idan Alfijir ya ɓullo, kuma yakasance yana sauraren kiran sallah, idan ya ji kiran sallah sai ya kame, in ba haka ba kuma sai ya kai hari, sai ya ji wani mutum yana cewa: "Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "(waɗannan suna) a kan ɗabi'a ta Musulunci" sannan ya ce: "Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Ka fita daga wuta" Sai suka yi duba sai ga shi mai kiwon awaki ne.
Muslim ne ya ruwaito shi (382).
LADAN BIN LADANI
Daga Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Idan ladani ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sai ɗayan ku ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan yace: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, yace: Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sannan yace: Ina shaidawa cewa Annabi Muhammadu manzon Allah ne, ya ce: Ina shaidawa cewa Annabi Muhammadu manzon Allah ne, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa ga sallah, ya ce: Babu dabara kuma babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa ga tsira, ya ce: Babu dabara kuma babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, daga zuciyar sa, to zai shiga Aljanna".
Muslim ne ya ruwaito shi (385).
LADAN ZIKIRI DA ADDU'A DA AKA SHARA'ANTA BAYAN KIRAN SALLAH
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Al-Aas cewa shi ya ji Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cawa:
"Idan kun ji ladani, to, ku faɗi irin abin da ya ke faɗa, sannan ku yi salati a gare ni, domin cewa wanda ya yi salati a gare ni salati ɗaya Allah zai yi salati goma a gare shi sabo da shi, sannan ku roƙa min Allah Al-Wasila, domin cewa ita wata daraja ce a cikin Aljannah, ba ta kamata sai ga wani bawa daga bayin Allah, kuma ina ƙaunar in kasance ni ne shi, wanda ya roƙamin Al-Wasilah, to, ceto ya halatta a gare shi".
Muslim ne ya ruwaito shi (384).
Daga Jabir ɗan Abdullahi lallai cewa - Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Duk wanda ya ce yayin da ya ji kiran sallah: (Ya Allah, Ubangijin wannan cikakken kira da sallah da za'a tayar, Ka bai wa [annabi] Muhammad Al-Wasila da Al-Fadila, kuma Ka tashe shi a matsayi abin yabo wanda Ka yi masa alɗawarin sa), ceto na zai halatta a gare shi ranar Al-ƙiyama".
Bukhari ne ya ruwaito shi (614).
Daga Sa'ad ɗan Abu waƙas - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Duk wanda ya ce yayin da ya ji kiran salla: (Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai Ya ke, ba Shi da abokin tarayya, kuma cewa Annabi Muhammad bawan Sa ne kuma Manzon Sa ne, na yadda da Allah Shine Ubangiji, kuma da Muhammad shi ne Manzo, da Musulunci shi ne Addini), za'a gafarta masa zunuban sa".
Muslim ne ya ruwaito shi (386).
LADAN SALLAH
Daga Mi'idan ɗan Abu Dalha Al-Ya'amury ya ce:
Na gamu da Sauban 'yantaccen Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai na ce: Shin ba za ka ba ni labari da wani aikin da zan aikata shi Allah Ya shigar da ni Aljanna da shi ba? ko ya ce, na ce: Da mafi son ayyuka zuwa ga Allah, sai ya yi shiru. Sannan na tambaye shi, Sai ya yi shiru. Sannan na tambaye shi a karo na uku sai ya ce: Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da wannan, sai ya ce: "Na umarce ka da yawan sujjada ga Allah, domin cewa kai ba za kayi wata sujjada ga Allah ba, sai Allah Ya ɗaga darajar ka da ita, kuma Ya sarayar da kuskure daga gare ka da ita".
Mi'idan yace: Sannan na gamu da Abu Al-Darda'i sai na tambaye shi sai ya faɗa mini kwatankwacin abin da Sauban ya faɗa mini.
Muslim ne ya ruwaito shi (488).
Daga Rabi'a ɗan Ka'ab Al-Aslamy ya ce:
Na kasance tare da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai na zo masa da ruwan alwalar sa da buƙatar sa sai ya ce da ni: "Ka yi tambaya" sai na ce: Ina roƙan ka abokantakar ka a cikin Aljanna. Ya ce. "Ko wanin wannan" sai na ce: Shi ne wannan. Ya ce: "To ka taimake ni akan kan ka da yawan sujjada".
Muslim ne ya ruwaito shi (489).
LADAN SALLOLIN FARILLA DA KIYAYEWA A KAN SU
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Shin kuna ganin cewa da ace akwai ƙorama a ƙofar ɗayan ku yana yin wanka a cikin ta kowace rana sau biyar, shin wani abu zai ragu daga dattin sa?" Suka ce: Babu wani abu da zai ragu daga dattin sa, ya ce: "To, haka salloli biyar su ke, Allah yana shafe kurakurai da su".
Bukhari ya ruwaito shi (528)) da Muslim (667).
Daga Amr ɗan Sa'id ɗan Al-Aas ya ce:
Na kasance a wurin Usman sai ya sa a kawo masa abin tsarki, sai ya ce naji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Babu wani mutum musulmi da sallar farilla za ta halarto masa sai ya kyautata alwalar ta da khushu'in ta da ruku'in ta, sai ta kasance kaffara ga abinda ke kafin ta daga zunubai, muddin dai bai zo wa wani babban laifi ba, wannan a zamani ne gaba ɗayan sa".
Muslim ne ya ruwaito shi (227).
LADAN SALLAR ASUBA DA LA'ASAR A TARE
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mala'ikun dare, da Mala'ikun rana suna bibiyar juna a cikin ku, kuma suna taruwa a sallar Asuba, da sallar La'asar, sannan waɗanda suka kwana a cikin ku sai su hau, sai Ubangijin su Ya tambaye su alhali Ya fi kowa sanin su: Yaya kuka bar bayi na? sai su ce: Mun bar su alhalin suna sallah, kuma da ma mun zo musu alhalin suna sallah".
Bukhari ya ruwaito shi (555) da Muslim 6327).
Daga Jabin ɗan Abdullah ya ce:
Mun kasance a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya yi duba zuwa ga wata daren cikakken hasken wata, sai ya ce: "Lallai za ku ga Ubangijin ku, kamar yadda ku ke ganin wannan watan, ba za ku yi cunkoso a cikin ganin sa ba, idan kuna da iko kada a rinjaye ku a kan sallah kafn ɓullowar rana da kafin faɗuwarta, to, ku aikata", sannan ya karan ta: (Ka tsarkake Ubangijin ka da godiya kafin ɓullowar rana da kafin faɗuwarta).
Bukhari ya ruwaito shi (554) da Muslim 6337).
Daga Imarah ɗan Ru'aibah ya ce: Na ji - Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
" Ba zai shiga wuta ba duk wanda ya yi sallah kafin ɓullowar rana, da kafin faɗuwar ta".
Yana nufin Sallar Asuba da La'asar.
Muslim ne ya ruwaito shi (634).
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ya sallaci sanyaya biyu zai shiga Aljanna".
Bukhari ya ruwaito shi (574) da Muslim 6357).
Sanyaya biyu sune: Sallar La'asar da sallar Asuba.
LADAN SALLAR LA'ASAR
Daga Abu Busrah Al-Gifari - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yayi mana sallar La'asar a Mukhammas, sai ya ce: "Lallai wannan sallar an bijirota ga waɗanda ke kafin ku sai suka tozarta ta, wanda ya kiyaye ta, to, yana da ladan sa sau biyu".
Muslim ne ya ruwaito shi (830).
LADAN SALLAR ASUBA
Daga Jundub - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ya yi sallar Asuba, to, yana cikin alƙawarin Allah, to, kada Allah Ya nemeku ga alƙawarin Sa da wani abu, domin cewa duk wanda ya neme shi ga alƙawarin Sa da wani abu zai riskeshi, sannan Ya kifar da shi ta fuskar sa a cikin wutar Jahannama".
Muslim ne ya ruwaito shi (657).
LADAN SALLAR ISHA'I DA ASUBA ACIKIN JAMA'A
Daga Usman - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa:
"Wanda ya sallaci Isha'i a cikin jama'a, kamar ya tsaya rabin dare ne, wanda ya sallaci Asuba a cikin jama'a, to kamar ya sallaci dare ne gaba ɗayan sa".
Muslim ne ya ruwaito shi (656).
LADAN SALLAH A CIKIN LOKACINTA
Daga Ibn Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na tambayi manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: wane aiki ne mafi soyuwa zuwa ga Allah? ya ce: "Sallah a kan lokacin ta".
Bukhari ya ruwaito shi (527) da Muslim (857).
FALALAR FAƊIN AMIN A CIKIN SALLAH
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan liman ya ce: (Ba waɗanda aka yi fushi a kansu ba ba kuma ɓatattuba), to, kuce: Amin; domin cewa shi wanda faɗin sa ya dace da faɗin Mala'iku za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zubin sa".
Bukhari ya ruwaito shi (782) da Muslim (4107).
Daga Abu Musa Al-Ash'ary - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Lallai cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi mana haɗuba sai ya bayyana mana sunnar mu, ya kuma sanar da mu sallar mu. Sai ya ce; "Idan za ku yi sallah, to, ku daidaita sahun ku, sannan ɗayan ku ya yi muku limanci, idan ya yi kabbara, to, ku yi kabbara, idan ya ce: (Ba waɗanda aka yi fushi a kansu ba, ba kuma batattu ba), to, ku ce: (Amin), Allah zai amsa muku".
Muslim ne ya ruwaito shi (404).
FALALAR FAƊIN (YA ALLAH UBANGIJINMU GODIYA TA TABBATA A GAREKA) BAYAN ƊAGOWA DAGA RUKU'U
Daga Abu huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan liman ya ce: (Allah Ya ji wanda ya gode masa), to, ku ce: (Ya Allah Ubangijinmu godiya ta tabbata a gareKa); domin cewa shi wanda faɗin sa ya dace da faɗin Mala'iku, za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zubin sa".
Bukhari ya ruwaito shi (796) da Muslim (409).
Daga Abu Musa Al'ash'ary - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Lallai cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya yi mana huɗuba, sai yabayyana mana sunnar mu ya kuma sanar damu sallar mu. Sai ya ce: "Idan za kuyi sallah, to, ku daidaita sahunku, sannan ɗayanku ya yi muku limanci..., idan ya ce: (Allah Yaji wanda ya gode masa), to, ku ce: (Ya Allah Ubangijinmu godiya ta tabbata a gareKa) Allah zai amsa muku.
Muslim ne ya ruwaito shi (404).
FALALAR FAƊIN (YA UBANGIJINMU GODIYA TA TABBATA A GAREKA GODIYA MAI YAWA... ) BAYAN ƊAGOWA DAGOWA DAGA RUKU'U
Daga Rifa'ah ɗan Rafi'in Al-Zuraƙy ya ce:
"Mun kasance wata rana muna sallah a bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da ya ɗago kan sa daga raka'a ya ce: (Allah Ya ji wanda ya gode maSa), sai wani mutum a bayan sa ya ce: (Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata a gareKa; godiya mai yawa, mai tsarki, mai albarka a cikinta), yayin da ya juya, ya ce: "Waye mai magana" yace: Ni ne, ya ce: "Na ga Mala'iku tamatin da wani abu suna gaggawa waye zai fara rubuta ta".
Bukhari ne ya ruwaito shi (799).
LADAN SALLAR JAM'I
Daga Dan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Sallar jam'i ta fi sallar mutum ɗaya da daraja ashirin da bakwai".
Bukhari ya ruwaito shi (645) da Muslim (650).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
“Sallar mutum a cikin jam'i tana ƙaruwa a kan sallarsa a gidan sa, da sallar sa a cikin kasuwar sa da daraja ashirin da wani abu, saboda idan mutum ya yi alwala ya kyautata alwalar, sannan ya zo masallaci babu abin da ya zaburo da shi sai sallah, ba ya nufin komai sai sallah, ba zai yi wani taku ba sai an ɗaga darajar sa da shi, kuma an sarayar da kuskuran sa da shi, har ya shiga masallaci, idan ya shiga masallaci zai kasance a cikin ladan sallah muddin dai sallar ce ta tsare shi, kuma Mala'iku suna yi wa ɗayan ku addu'a muddin dai ya kasance a mazaunin da ya yi sallah a cikin sa, suna cewa: Ya Allah Ka yi masa rahama, ya Allah Ka gafarta ma sa, ya Allah Ka yi tuba a gare shi, muddin dai bai yi cuta a cikin sa ba, muddin dai bai yi kari a cikin sa ba".
Bukhari ya ruwaito shi (647) da Muslim (649).
LADAN SALLAH A SAHUN FARKO
Daga Abu huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Da mutane sun san abin da ke cikin kiran sallah da sahun farko, sannan ba za su samu ba sai sun yi ƙuri'a a kan sa; to, da sunyi ƙuri'ar".
Bukhari ya ruwaito shi (615) da Muslim 4377).
An-nida'u shi ne kiran sallah.
Shi kuma Istiham shi ne ƙuri'a.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Mafi alherin sahun maza shi ne na farkon su, kuma mafi sharrin su shi ne na ƙarshen su, mafi alherin sahun mata shi ne na ƙarshen su, kuma mafi sharrin su shi ne na farkon su".
Muslim ne ya ruwaito shi (440).
LADAN SALLAH A CIKIN MASALLACIN HARAMI DA MASALLACIN ANNABI
Daga Abu huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Sallah a cikin masallaci na wannan shine mafi alheri daga sallah dubu a cikin wanin sa sai masallacin Harami".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1190) da Muslim (1394).
LADAN WANDA YA GINA MASALLACI SABODA ALLAH - MAI GIRMA DA ƊAUKAKA -.
Daga Usman - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Wanda ya gina masallaci yana mai neman zatin Allah - mai girma da ɗaukaka - da shi Allah zai gina masa gida a cikin Aljanna".
Bukhari ya ruwaito shi (450) da Muslim (533).
LADAN TAFIYA ZUWA MASALLATAI DON YIN SALLAH
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Mafi girman mutane lada a cikin sallah; shi ne mafi nisan su, sai mafi nisan su a tafiya, wanda ya ke jiran sallah har sai ya sallace ta tare da liman, to, shi ne mafi girman lada daga wanda ya ke sallah sannan ya yi barci".
Bukhari ne ya ruwaito shi (651) da Muslim (662).
Daga Abu Huraira daga Annabi - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya yi sammako zuwa masallaci ko ya maraita, Allah zai tanadar masa wani masauki a cikin Aljanna duk lokacin da ya yi sammako ko ya maraita".
Bukhari ne ya ruwaito shi (662) da Muslim (669).
Daga Ubayyu ɗan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Wani mutum ya kasance nesa da masallaci sama da kowa a iya sanina, kuma ya kasance ba wata sallah da take kuskure masa, sai aka ce masa: Ai da za ka sayi jaki, da za ka dinga hawan sa a cikin duhu, da zafin rana, sai ya ce; Ba na son masauki na ya kasance a gefen masallaci, lallai cewa ni ina son a rubuta mini tafiya ta zuwa masallaci, da dawowa ta idan na dawo zuwa iyalaina, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Haƙiƙa Allah Ya haɗa maka wannan gaba ɗayan sa".
Muslim ne ya ruwaito shi (663).
Daga Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Gidajenmu sun kasance nesa da masallaci, sai muka so mu sayar da gidajen mu, don mu kusanto masallaci, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya hana mu sai ya ce: "Lallai cewa ku kuna da lada a kowane taku".
Muslim ne ya ruwaito shi (664).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ya yi tsarki a cikin gidan sa, sannan ya tafi zuwa wani ɗaki daga ɗakunan Allah don ya ba da wata farilla daga farillan Allah, takawar sa biyu sun kasance ɗayan su tana sarayar da kuskure, ɗayar kuma tana ɗaga daraja".
Muslim ne ya ruwaito shi (666).
LADAN WANDA ZUCIYAR SA TAKE RATAYE DA MASALLATAI
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa:
"Mutum bakwai Allah - maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu inuwa sai inuwarSa: Shugaba mai adalci, da matashi da ya taso a cikin bautar Allah, da mutumin da zuciyar sa take rataye da masallatai...".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1423) da Muslim (1031).
LADAN WANDA YA ZAUNA A CIKIN MASALLACI YANA SAURARON SALLAH
Daga Abu huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Bawa ba zai gushe ba acikin sallah, muddin dai ya kasance a wurin sallar sa yana jiran sallah, Mala'iku suna cewa: Ya Allah Ka gafarta masa, ya Allah Ka jiƙansa, har sai ya juya, ko ya yi kari".
Bukhari ne ya ruwaito shi (176) da Muslim (649).
LADAN SALLAR NAFILA A CIKIN GIDA
Daga Jabir ɗan Abbdullahi - Allah Ya ƙara yarda a gare su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan ɗayanku ya gama sallah a cikin masallaci, to, ya sanya wani rabo na sallar sa a gidan sa; domin Allah zai sanya alheri a gidan sa saboda sallar ta sa".
Muslim ne ya ruwaito shi (778).
LADAN KIYAYEWA A KAN SUNNONI MASU JERANTUWA
Daga Ummu Hubibah - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa:
"Babu wani musulmi da zai yi sallah saboda Allah kowace rana raka'a goma sha biyu nafila ba farillah ba, sai Allah Ya gina masa gida a Aljanna, ko sai an gina masa gida a cikin Aljanna".
Ummu Habiba ta ce: Ban gushe ba ina sallatarsu bayan nan
Amr ya ce: Ban gushe ba ina sallatar su bayan nan
Nu'uman shi ma ya faɗi irin haka.
Muslim ne ya ruwaito shi (728).
LADAN RAKA'O'I BIYU NA ALFIJIR
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Raka'o'i biyu na Alfijir su ne mafi alheri daga Duniya da abin da ke cikinta".
A cikin wata riwayar: "Wallahi su ne mafi soyuwa a gareni daga duniya gaba ɗaya".
Muslim ne ya ruwaito shi (725).
LADAN WITIRI A ƘARSƘEN DARE
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Duk wanda ya ji tsoron ba zai iya tashi a ƙarshen dare ba; to, ya yi Wutiri a farkon sa, wanda kuma ya yi kwaɗayin tashi a ƙarshen sa; to ya yi Wutiri a ƙarshen dare; domin sallar ƙarshen dare abar halartowar Mala'ikuce, kuma wannan ya fi".
Muslim ne ya ruwaito shi (755).
LADAN WANDA YA TASHI CIKIN DARE KUMA YA FARKAR DA IYALANSA DON HAKA
Daga Abu Sa'id Al-khudry da Abu Huraira - Allah Ya yarda da su - sun ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya farka cikin dare kuma ya farkar da matar sa, suka yi sallah raka'a biyu gaba ɗayan su, za'a rubuta su daga masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambaton Allah da yawa mata".
Abu Dawud ne ya rawaito shi (1451).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Allah Ya ji ƙan mutumin da ya tashi da daddare, sai ya yi sallah, kuma ya farkar da matar sa, ta yi sallah, idan ta ƙi, to, ya yayyafa ruwa a fuskar ta, kuma Allah ya ji ƙan matar da ta tashi da daddare, ta yi sallah, ta farkar da mijin ta, sai ya yi sallah, idan ya ƙi, to, ta yayyafa ruwa a fuskar sa".
Ahmad ne ya ruwaito shi (7410) da Abu Dawud (1308).
LADAN SALLAR WALAHA
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Kowace gaɓa daga ɗayanku tana wayar gari da sadaka, dukkanin Tasbihi sadaka ne, dukkanin Tahmidi sadaka ne, dukkanin Hailala sada ce, dukkanin Kabbara sadaka ce, horo da aikin alheri sadaka ne, da hani daga abin ƙi sadaka ne, kuma raka'a biyun da mutum zaiyi su na Walaha suna isuwa daga wannan".
Muslim ne ya ruwaito shi (720).
LADAN SALLAR JUMA'A
Daga Abu huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Salloli biyar, da Juma'a zuwa Juma'a, kaffara ne ga abin da ke tsakanin su, muddin dai ba'a zakkewa manyan zunubai ba".
Muslim ne ya ruwaito shi (233).
LADAN WANKA DA SHAFA TURARE DA YIN SHIRU A LOKACIN HUƊUBAR JUMA'A
Daga Salman Al-Farisi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya yi wanka ranar juma'a, ya yi tsarki da abinda zai iya na tsarki, sannan ya shafa mai, ko ya shafa turare, sannan ya tafi bai raba tsakanin mutum biyu ba, sai ya sallaci abinda aka wajabta masa, sannan idan liman ya fito sai ya yi shiru, za'a gafarta masa abin da ke tsakanin sa da tsakanin wata Juma'ar daban".
Bukhari ne ya ruwaito shi (910).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ya yi wanka, sannan ya zowa Juma'a, sai ya sallaci abin da aka ƙaddara masa, sannan ya yi shiru har ya gama huɗubar sa, sannan ya yi sallah tare da shi, za'a gafarta masa abin da ke tsakanin sa da tsakanin wata Juma'ar daban, dama ƙarin kwana uku".
Muslim ne ya ruwaito shi (857).
LADAN YIN SAMMAKO ZUWA SALLAR JUMA'A
Daga Abu huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sannan ya tafi, kamar ya bayar da sadakar taguwa ne, wanda ya tafi a lokaci na biyu, kamar ya bayar da sadakar saniya ne. wanda ya tafi a lokaci na uku kamar ya bayar da sadakar rago ne mai ƙaho. wanda ya tafi a lokaci na huɗu kamar ya bayar da kaza ne, wanda kuma ya tafi a lokaci na biyar kamar ya bayar da ƙwai ne. Idan liman ya fito Mala`iku za su halarto suna sauraron zikiri (Huɗuba)".
Bukhari ne ya ruwaito shi (881) da Muslim (850).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Idan ranar Juma'a ta zo, ya kasance a kowace ƙofa daga ƙofofin masallaci akwai Mala'iku suna rubuta na farko sai na farko, idan liman ya zauna sai su ninke takardun, su zo suna sauraren zikiri, misalin mai tafiya a garjin rana kamar mai bayar da kyautar taguwa ne, sannan kamar mai bayar da kyautar saniya, sannan kamar mai bayar da kyautar rago, sannan kamar mai bayar da kyautar kaza, sannan kamar mai bayar da kyautar ƙwai, idan liman ya fito sai su ninke takardunsu, suna sauraron zikiri (Huɗuba)".
Bukhari ne ya ruwaito shi (929) da Muslim (850).
LADAN KARDADON LOKACIN AMSA ADDU'A RANAR JUMA'A
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Lallai a cikin Juma'a akwai wani lokaci babu wani bawa da zai dace da shi yana roƙon Allah wani alheri a cikin sa sai ya bashi shi".
Yace: Wani lokaci ne ƙanƙani.
Bukhari ne ya ruwaito shi (935), da Muslim (852) kuma lafazin nasa ne.
LADAN WANDA ƘARSHEN MAGANAR SA YA KASANCE (BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH)
Daga Mu'azu - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ƙarshen maganar sa ta kasance babu abin bautawa da gaskiya sai Allah zai shiga Aljanna".
Abu Dawud ne ya ruwaito shi (3116).
LADAN BIN JANA'IZA
Daga Abu huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya bi jana'izar wani musulmi don imani da neman lada, kuma ya kasance tare da shi har aka yi masa sallah, aka gama birne ta, to, zai dawo da lada ƙiraɗi biyu, dukkanin ƙiraɗi kamar dutsen Uhudu ne, wanda ya yi sallah a gare ta, sannan ya dawo kafin a birne ta, to, shi kuma zai dawo da ƙiraɗi ɗaya".
Bukhari ne ya ruwaito shi (47) da Muslim (945).
LADAN WANDA MUTUM ƊARI KO ARBA'IN DAGA CIKIN MUSULMAI SUKAYI MASA SALLAH
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Babu wani mamacin da al'ummar musulmai da adadinsu ya kai ɗari za su yi masa sallah, dukkanin su suna nema masa ceto, sai an ba su ceton sa".
Muslim ne ya ruwaito shi (947).
Daga Kuraib daga Abdullahi ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa wani ɗan sa ya rasu a Ƙudaid ko Usfan, sai ya ce: Ya Kuraib, ka duba yadda mutane suka taru gare shi, ya ce: Sai na fita, sai ga mutane haƙiƙa sun taru gare shi, sai na bashi labari, sai ya ce: Kana zaton su arba'in ne? Ya ce: Na'am, ya ce: Ku fito da shi; Domin ni na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Babu wani mutum musulmi da zai mutu, sai mutum arba'in su tsaya a kan Jana'izar sa, waɗanda ba sa haɗa Allah da komai, sai AllahYa ba su ceton sa".
Muslim ne ya ruwaito shi (948).
LADAN WANDA YA CE (LALLAI MU GA ALLAH MU KE KUMA GA ALLAH ZA MU KOMA) A YAYIN MUSIBA
Daga Ummu Salamah - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Babu wani musulmin da musifa za ta same shi, sai ya faɗi abin da Allah Ya umarce shi: (Lallai mu ga Allah muke, kuma ga Allah za mu koma) Ya Allah Ka ba ni lada a cikin musiba ta, kuma Ka maye min gurbin ta da mafi alheri, sai Allah Ya maye masa mafi alheri daga gare ta".
Tace: Yayin da Abu Salamah ya rasu, na ce: Waye mafi alheri daga Abu Salamah a cikin musulmai? Farkon gidan da yayi Hijira zuwa ga Manzon Allah - tsira da amncin Allah su tabbata a gare shi -, lallai tabbas na faɗe ta, sai Allah Ya maye mini gurbi da Manzon Allah - tsira da amncin Allah su tabbata a gare shi -.
Muslim ne ya ruwaito shi (918).
LADAN WANDA YA MUTU DA ANNOBA
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa:
"Annoba Shahada ce ga kowane musulmi".
Bukhari ne ya ruwaito shi (2830) da Muslim (1916).
Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da annoba, sai ya ba ni labarin cewa wata azaba ce da Allah Yake aiko ta ga wanda Ya so, kuma lallai Allah Ya sanya ta rahama ce ga muminai, babu wani da zai faɗa cikin annoba, sai ya zauna a cikin ƙasar sa yana mai haƙuri da neman lada, tare da sanin cewa babu wani abu da zai same shi sai abinda Allah Ya rubuta masa, sai ya kasance yana da lada irin na shahidi".
Bukhari ne ya ruwaito shi (3474).
LADAN WANDA BIYU KO UKU DAGA 'YA'YAN SA SUKA RASU BA SU BALAGA BA
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Babu wani musulmi daga mutane da 'ya'yan sa uku za su rasu ba su balaga ba; sai Allah Ya shigar da shi Aljanna saboda falalar tausaya musu da ya yi".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1248).
Daga Abu Sa'id -Allah Ya yarda da shi- : Lallai wasu mata sun ce wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- : Ka sanya mana wata rana, sai ya yi musu wa'azi, sannan ya ce; "Duk matar da 'ya'yan ta uku suka rasu, za su kasance mata shamaki daga wuta" Sai wata mace ta ce: Har biyu ma? ya ce: "Har biyu ma".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1249) da Muslim (2633).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Babu wani mutum daga cikin musulmai da 'ya'yansa uku za su rasu sannan kuma wuta ta taɓa shi sai dai hana-rantsuwa".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1251) da Muslim (2632).
LADAN WANDA TSARKAKAKKEN MASOYIN SA DAGA MUTANEN DUNIYA YA RASU SAI YA YI HAƘURIN RASHIN SA
Daga Abu huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Allah Maɗaukakin sarki Yana cewa: Babu wani sakamako ga bawa na mumini idan na karɓi Masoyin sa daga Mutanen Duniya sannan ya yi haƙuri saboda Allah sai Aljanna".
Bukhari ne ya ruwaito shi (6424).
Tsarkakakke: Shine masoyi mai tsarkake soyayya kamar ɗa da ɗan uwa da dukkanin wanda mutum yake son sa.
LADAN SADAKA
Daga Abu huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Sadaka ba ta tauye dukiya".
Muslim ne ya ruwaito shi (2588).
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Abu Dalha ya kasance mafi yawan mutanen Madina dukiya ta dabinai a Madina, kuma mafi soyuwar dukiyoyin sa gare shi ita ce Bairuha'a, kuma ta kasance mai fuskantar Al-ƙiblace, manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana shiga cikin ta kuma yana sha daga ruwa mai daɗi a cikin ta.
Anas ya ce: Yayin da aka saukar da wannan ayar: (Ba za ku samu (sakamakon) nagarta ba har sai kun ciyar da abin da ku ke so) sai Abu Dalha ya tashi zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yana cewa: (Ba za ku samu (sakamakon) nagarta ba har sai kun ciyar da abinda ku ke so) kuma lallai mafi soyuwar dukiyoyi na gare ni ita ce Bairuha'a, lalle (na bayar da) ita sadaka ga Allah, ina fatan (samun) kyautatawar ta da ajiyar ta a wurin Allah, to, ka sanya ta ya Manzon Allah inda Allah Ya nuna maka.
Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Madallah, wannan dukiya ce mai riba, wannan dukiya ce mai riba, haƙiƙa na ji abin da ka ce, kuma lallai ina ganin ka sanya ta ga 'yan uwa", Sai Abu Dalha ya ce: Zan aikata ya Manzon Allah, sai ya rabata a cikin 'yan uwan sa da 'ya'yan baffan sa.
Bukhari ne ya ruwaito shi (1461) da Muslim (998).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
Duk wanda ya yi sadaka da dadai da dabino na halaliyar nema, Kuma ba mai hawa zuwa ga Allah sai mai tsarki; domin lallai Allah zai karɓeta da daman sa, sannan Ya ƙara ta ga mai ita, kamar yadda ɗayan ku yake rainon ɗan bagazan ɗinsa, sai tazama tamkar dutse".
Bukhari ne ya ruwaitoshi (7430) da Muslim1(014).
LADAN MAI AIKI A KAN SADAKA DA MAI GADI IDAN SUN KASANCE AMINTATTU
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Lallai amintaccen ma'aji musulmi, wanda ya ke zartar da - wataƙila cewa ya yi: Ya ke bayar da abin da aka umurce shi da shi cikakke abin yalwatawa, ransa yana mai daɗi da shi, sai ya ba da shi zuwa ga wanda aka umarceshi da shi, to, shi ma ɗaya ne daga masu yin sadakar".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1438)) da Muslim (1023).
LADAN SADAKAR MAI ƘARANTAWA (MARA SHI)
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Dirhami ɗaya ya rigayi Dirhami dubu" Suka ce: Ya Manzon Allah, ta yaya?.
Ya ce: "Mutum ne yake da Dirhami biyu sai ya ɗauki ɗayan su sai ya yi sadaka da shi, da mutumin da yake da dukiya mai tarin yawa sai ya ɗauki dubu ɗari daga kadarar dukiyar sa sai ya yi sadaka da shi".
Ahmad ne ya ruwaitoshi (8929) da Al-Nasa'i (2527).
Daga Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya Manzon Allah, wace sadaka ce ta fi? ya ce: "Ƙoƙarin mai ƙarancin dukiya, kuma ka fara da wanda nauyin su ya lazimce ka".
Ahmad ne ya ruwaito shi (8702) da Abu Dawud (1677).
LADAN SADAKAR ƁOYE
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Mutum bakwai Allah Yana inuwantar da su a cikin inuwar Sa ranar da babu inuwa sai inuwar Sa". daga cikin su ya ambaci: "Da mutumin da ya bayar da wata sadaka sai ya ɓoye ta har hagun sa ba ta san abin da daman sa ta ciyar ba".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1423) da Muslim (1031).
LADAN WANDA AKA AZURTA SHI DA ABU KAƊAN SAI YA WADATU YA YI HAƘURI BAI TAMBAYI WANI BA DAN AMINCEWA DA ALLAH DA DOGARO GARE SHI
Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - lallai Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Haƙiƙa ya rabauta wanda ya miƙa wuya kuma aka azurta shi da abu kaɗan, kuma Allah Ya wadata shi da abin da Ya bashi".
Muslim ne ya ruwaito shi (1054).
Daga Abu Sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wasu mutane daga Mutanen Madina sun roƙi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ba su, sannan suka sake roƙon sa, sai ya basu, sannan suka sake roƙon sa, sai ya ba su har abin da yake wurin sa ya ƙare, sai ya ce: "Abin da ya kasance a wurina na alheri ba zan ɓoye shi gare ku ba, duk wanda ya nemi kamewa; Allah zai ba shi kamewa, duk wanda ya nemi wadatuwa; Allah zai wadata shi, wanda ya yi ƙoƙarin yin haƙuri; Allah zai haƙurƙurtar da shi, ba a taɓa bai wa wani kyauta mafi alheri da yalwa ba sama da hakuri".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1469) da Muslim (1053).
LADAN CIYAR DA ABINCI SABO DA ALLAH MAƊAUKAKIN SARKI
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - zai faɗa a ranar Al-ƙiyama: Ya kai Dan Adam Na yi rashin lafiya ba ka dubaNi ba, sai ya ce: Ya Ubangiji ta yaya zan duba Ka alhali Kai ne Ubangijin talikai?.
Ya ce: Shin ba ka san cewa bawa Na wane yayi rashin lafiya amma ba ka duboshi ba, shin ba ka san cewa da ka dubo shi; da ka same Ni awurin sa ba?.
Ya kai Dan Adam Na nemi ciyarwar ka amma ba ka ciyar da Ni ba, ya ce: Ya Ubangiji ta yaya zan ciyar da Kai alhali Kai ne Ubangijin talikai?.
Ya ce: Shin ba ka san cewa bawa Na wane ya nemi ciyarwar ka amma ba ka ciyar da shi ba? Shin ba ka san cewa da ka ciyar da shi; da ka sami wannan a wuri Na.
Ya kai Dan Adam Na nemi shayarwar ka amma ba ka shayar da Ni ba, ya ce: Ya Ubangiji ta yaya zan shayar da Kai alhali Kai ne Ubangijin talikai?.
Ya ce: Bawa Na wane ya nemi shayarwar ka ba ka shayar da shi ba, amma tabbas da ka shayar da shi za ka sami wannan a wuri Na".
Muslim ne ya ruwaito shi (2569).
LADAN WANDA YA SHAYAR DA DAN ADAM KO DABBA
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:
"Lallai cewa wani mutum ya ga wani kare yana cin ƙasa saboda ƙishirwa, sai mutumin ya ɗauki khuffinsa, sai ya riƙa kanfato masa dashi har ya ƙosar da shi, sai Allah Ya gode masa, sannan Ya shigar da shi Aljanna".
Bukhari ne ya ruwaito shi (173).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -:
"Lallai cewa wata mace karuwa ta ga wani kare a wata rana mai zafi yana kewaye wata rijiya, harshen sa ya na lallagi saboda ƙishirwa, sai ta cire takalmin ta saboda shi sai aka gafarta mata".
Muslim ne ya ruwaito shi (2245).
LADAN WANDA YA SHUKA WATA SHUKA KO YA DASA WANI DASHE
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Babu wani musulmi da zai dasa wani dashe, ko ya shuka wata shuka, sai wani tsuntsu ko mutum ko dabba, su ci daga gare shi sai ya zamo sadaka a gare shi".
Bukhari ne ya ruwaito shi (2320) da Muslim (1553).
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Babu wani musulmi da zai dasa wani dashe sai ya kasance abin da aka ci daga gare shi sadaka ne a gare shi, kuma abin da aka sace daga cikin sa sadaka ne gare shi, kuma abin da namun jeji suka ci daga ciki to, shi ma sadaka ne gare shi, kuma abin da tsuntsu ya ci to, shi ma sadaka ne gareshi, kuma babu wanda zai rageshi sai ya kasance sadaka a gare shi".
Muslim ne ya ruwaito shi (1552).
LADAN CIYARWA A CIKIN FUSKOKIN ALHERI
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Babu wani yinin da bayi za su wayi gari a cikin sa, sai akwai wasu Mala'iku guda biyu da suke sauka, sai ɗayan su ya ce: Ya Allah Ka bada mayewa ga mai ciyarwa, sai ɗayan yace: Ya Allah kaɓatawa mai rikewa".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1442) da Muslim (1010).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gareshi - ya ce:
"Allah Ya ce: "Ya kai Dan Adam ka ciyar; Zan ciyar da kai".
Bukhari ne ya ruwaito shi (5352) da Muslim (993).
LADAN WANDA YA SAUƘAƘA GA WANDA YA KE CIKIN TSANANI KO YA JINKIRTA MASA KO YA SARAYAR MASA
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Wani ɗan kasuwa ya kasance yana ba wa mutane bashi, idan ya ga wanda ke cikin tsanani, sai ya ce wa yaran sa: Ku yafe masa, wataƙila Allah ya yafe mana, sai Allah Ya yafe masa".
Bukhari ne ya ruwaito shi (2078)) da Muslim (1562).
Daga Abdullahi ɗan Abu Qatada: Cewa Abu Qatada ya nemi wani da ya ke bin sa bashi, sai ya ɓuya, sannan ya same shi, sai ya ce: Lallai ina cikin mawuyacin hali ne, sai ya ce: Ka rantse da Allah? ya ce: Ka rantse da Allah?: Domin cewa ni na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Duk wanda ya ke son Allah Ya tseratar da shi daga baƙƙan cikin ranar Al-ƙiyama; to ya yaye baƙin ciki daga wanda ya ke cikin mawuyacin hali, ko ya sarayar masa".
Muslim ne ya ruwaito shi (1563).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
Duk wanda ya yayewa wani mumini baƙin ciki daga baƙƙan cikin Duniya, to, Allah Zai yaye masa wani baƙin ciki daga baƙƙan cikin lahira, wanda ya sawwaƙa ga wanda yake cikin matsuwa, to, Allah Zai sawwaƙa masa a Duniya da lahira, wanda ya suturta wani musulmi, to, Allah Zai suturta shi a Duniya da lahira. Allah Yana cikin taimakon bawa muddin bawan ya kasance a cikin taimakon ɗan uwan sa".
Muslim ne ya ruwaito shi (2699).
Daga Abul Yaseer - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Wanda ya saurarawa wanda yake cikin matsi ko ya sarayar masa, to, Allah Zai inuwantar da shi a cikin inuwar Sa".
Muslim ne ya ruwaito shi (3006).
LADAN AZUMI
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Allah Mai girma da ɗaukaka Ya ce: Dukkanin aikin Dan Adam nasa ne sai azumi, lallai cewa shi nawa ne, kuma Ni ne Zan yi sakayya a kan sa, yana barin sha'awar sa da abincin sa saboda Ni, na rantse da Wanda ran (annabi) Muhammadu yake a hannun Sa, warin bakin mai Azumi shi ne mafi tsarki a wurin Allah a ranar Al-ƙiyama sama da ƙamshin almiski, mai Azumi yana da farin ciki biyu da zai yi farin ciki dasu: Idan ya yi buɗa baki zai yi farin ciki da buɗa bakin sa, kuma idan ya gamu da Ubangijin sa zai yi farin ciki da Azumin sa".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1904) da Muslim (1151).
Daga Sahlu - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Lallai a Aljanna akwai wata ƙofa ana kiran ta Rayyanu, masu Azumi za su shiga ta cikin ta a ranar Al-ƙiyama, ba wanda zai shiga ta nan in ba su ba, za'a ce: Ina masu Azumi? sai su tashi, babu wanda zai shiga ta nan in ba su ba, idan suka shige za'a kulleta, ba wanda zai shiga ta ita".
Bukhari ne ya ruwaitoshi (1896) da Muslim (1152).
LADAN WANDA YA AZUMCI RAMADAN DAN IMANI DA NEMAN LADA
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya azumci Ramadan saboda Imani da neman lada, za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunuban sa".
Bukhari ne ya ruwaito shi (37) da Muslim (759).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan Ramadan ya shigo za'a buɗe ƙofofin Aljanna, za'a kulle ƙofofin Jahannama, za'a ɗaure Shaiɗanu".
Bukhari ne ya ruwaito shi (3277), da Muslim (1079) kuma lafazin na Bukhari ne
LADAN WANDA YA YI TSAYUWAR RAMADAN DAN IMANI DA NEMAN LADA
Daga Abu huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya yi tsayuwar Ramadan saboda Imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubin sa".
Bukhari ne ya ruwaito shi (37) da Muslim (759).
LADAN WANDA YA YI TSAYUWAR LAILATUL QADARI DAN IMANI DA NEMAN LADA
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya tsaya a daren Lailatul Ƙadari don Imani da neman lada, to, za'a gafarta masa abin da ya gabata daga zunubin sa".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1901) da Muslim (760).
LADAN SAHUR
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ku yi Sahur, domin cewa lallai a cikin Suhur akwai Albarka".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1923) da Muslim (1095).
LADAN GAGGAUTA BUƊA BAKI
Daga Sahl ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mutane ba za su gushe cikin alheri ba matuƙar sun gaggauta buɗa baki".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1957) da Muslim (1098).
LADAN WANDA YA YI AZUMIN RAMADAN KUMA YA BI SHI DA SHIDA DAGA SHAWWAL
Daga Abu Ayyub - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya Azumci Ramadan sannan ya bi shi da shida daga Shawwal ya kasance kamar Azumin zamani ne".
Muslim ne ya ruwaito shi (1164).
LADAN AZUMIN RANAR ARAFAH
Daga Abu Qatadah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da Azumin ranar Arafah? Sai ya ce: "Yana kankare shekarar da ta shuɗe da wacce ta rage".
Muslim ne ya ruwaito shi (1162).
LADAN AZUMIN RANAR ASHURA
Daga Abu Qatadah - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - an tambaye shi game da Azumin ranar Ashura? Sai ya ce: "Yana kankare shekarar da ta shuɗe".
Muslim ne ya ruwaito shi (1162).
LADAN AZUMIN WATAN ALLAH AL-MUHARRAM
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Mafificin Azumi bayan Ramadan shi ne watan Allah Al-Muharram".
Muslim ne ya ruwaito shi (1163).
LADAN AZUMIN WATAN SHA'ABAN
Daga Usama ɗan Zaid - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ce ya Manzon Allah! ban ganka kana yin Azumi a wani wata daga watanni ba, kamar yanda kake Azumtar Sha'aban?
Sai ya ce: "Wannan wani wata ne wanda mutane suke rafkana a cikin sa tsakanin Rajab da Ramadan, wani wata ne wanda ake ɗaga ayyuka a cikin sa zuwa Ubangijin talikai, to, sai naso a ɗaga aikina alhali ina Azumi".
Al-Nasa'i ne ya ruwaito shi (2357).
LADAN WANDA YA YI AZUMIN KWANA UKU AKOWANE WATA
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Al-Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce da ni:
"Ka yi Azumin kwana uku a kowane wata, wannan Azumin zamani ne, ko kamar Azumin zamani ne".
Bukhari ne ya ruwaito shi (3419) da Muslim (1159).
a cikin wata ruwayar ta su:
"Lallai haƙiƙa ya isheka ka yi Azumin kwana uku daga kowane wata; domin cewa ga kowace kyakykyawa ɗaya akwai lada goma tamkar ta, wannan shine zamani gaba ɗayan sa".
Bukhari ne ya ruwaito shi (6134) da Muslim (1159).
Daga Abu Qatada - Allah Ya yarda da shi - yac e: Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Azumin kwana uku daga kowane wata, da Ramadan zuwa Ramadan, Azumin zamani ne".
Muslim ne ya ruwaito shi (1162).
LADAN AZUMIN RANAR LITININ
Daga Abu Qatada Al-Ansary - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - an tambaye shi game da Azumin ranar Litinin? sai ya ce: "Wannan rana ce wacce aka haife ni a cikinta, kuma rana ce wacce aka aiko ni, ko aka saukar mini (Alƙur'ani) a cikin ta".
Muslim ne ya ruwaito shi (1162).
LADAN AZUMTAR YINI DA BUƊE BAKI A WANI YININ
Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - yace: Manzon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da ni:
"Mafi soyuwar Azumi ga Allah shi ne Azumin Dawud, ya kasance yana azumtar yini kuma yana buɗe baki a wani yinin".
Bukhari ne ya ruwaito shi (3420) da Muslim (1159).
LADAN HAJJI DA UMRAH
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Wanda ya yi Hajji, bai yi kwarkwasa ba, kuma bai yi fasikanci ba, zai dawo kamar ranar da mahaifiyar sa ta haife shi".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1521) da Muslim (1350).
Daga Abu huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Umrah zuwa Umrah kaffara ce ga abin da ke tsakaninsu, kuma Hajji kuɓutacce ba shi da wani sakamako sai Aljanna".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1773) da Muslim (1349).
LADAN UMRAH A CIKIN RAMADAN
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce wa wata mace daga Mutanen Madina ana ce mata Ummu Sinan: "Me ya hanaki ki kasance kinyi aikin Hajji tare da mu? sai ta ce: Wasu raƙuma ne masu ban ruwa guda biyu na Abu wane - mijinta - ya yi Hajji shi da ɗansa a kan ɗayan su, ɗayan kuma ya kasance bawammu yana shayarwa a kansa, sai ya ce; "To, Umrah a cikin Ramadan tana matsayin Hajji, ko Hajji ce tare da ni".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1782) da Muslim (1256).
LADAN AIKI A CIKIN GOMAN ZUL-HIJJAH
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wane aiki ne a wasu kwanakin ya fifita daga waɗannan?" Sai suka ce: ko da yaƙi? Ya ce: "Ko da yaƙi, sai dai mutumin da ya yi ƙarfin halin fita da kansa da dukiyar sa ga halaka, bai dawo da komai ba"
Bukhari ne ya ruwaito shi (969).
LADAN ZAMA A MADINA TA ANNABI
Daga Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Madina ita ce mafi alheri a garesu da sun kasance suna da sani, wani mutum ba zai barta ba don ƙinta ba; sai Allah Ya canza wanda ya fi shi alheri a cikin ta, kuma ba wanda zai jure a kan masifunta da farinta (rashin ruwan sama); sai na kasance mai ceto a gareshi, ko mai shaida a gareshi ranar Al-ƙiyama".
Muslim ne ya ruwaito shi (1363).
LADAN SANIN AL-ƘUR'ANI DA KARANTASHI
Daga Abu Musa Al-Ash'ary - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Kwatankwacin muminin da ya ke karanta Al-ƙur'ani kamar gawasa ne, ƙamshin ta mai daɗi, kuma ɗanɗanon ta mai daɗi, kuma kwatankwacin muminin da ba ya karanta Al-ƙur'ani, kamar dabino ne ba shi da ƙamshi, amma ɗanɗanon sa mai zaƙi ne, kuma kwatankwacin munafikin da ya ke karanta Al-ƙur'ani kamar karankarma (ɗaɗɗoya) ne, ƙamshin sa da daɗi, amma ɗanɗanon ta mai ɗaci ne, kuma kwatankawacin munafikin da ba ya karanta Al-ƙur'ani kwatankwacin guna ce, ba ta da ƙamshi, kuma ɗanɗanon ta mai ɗaci ne.
Bukhari ne ya ruwaito shi (5020) da Muslim (797).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Shin ɗayan ku yana son idan ya koma ga iyalansa ya samu taguwoyi uku masu ciki kuma manya masu ƙiba? sai muka ce: Eh, ya ce: "To ayoyi uku da zai karanta su a cikin sallar sa, sun fi alheri gareshi daga taguwoyin uku masu ciki kuma manya masu ƙiba".
Muslim ne ya ruwaito shi (802).
Daga Uƙuba ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
"Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya fito alhali mu muna cikin Suffah (wuri ne mai inuwa a masallacin Madina) sai ya ce: "Shin ɗayanku yana son ya wayi gari kowace rana zuwa Buɗhan ko zuwa Aƙiƙ, sai ya zo daga can da taguwoyi biyu masu manyan tozo, ba tare da zunubi, ko yanke zumunci ba?, sai muka ce: Ya Manzon Allah muna son haka, sai ya ce: "Shin ɗayan ku ba ya wayi gari zuwa masallaci ba, sai ya nemi sanin, ko ya karanta ayoyi biyu daga Littafin Allah - mai girma da ɗaukaka -, shi ne mafi alheri gareshi daga taguwoyi biyu, uku kuma su ne mafi alheri gareshi daga uku, huɗu kuma sune mafi alheri gareshi daga huɗu, haka kuma daga yawansu daga rakuma".
Muslim ne ya ruwaito shi (803).
Daga Usman - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Mafi Alheirin ku shi ne wanda ya san Alku'ani kuma ya sanar da shi".
Bukhari ne ya ruwaito shi (5027).
Acikin wata riwayar ta sa:
"Lallai cewa Mafificin ku shi ne wanda ya san Al-ƙur'ani kuma ya sanar da shi".
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Gwani a Al-ƙur'ani yana tare da Mala'iku jakadu masu daraja masu biyayya ga Allah, kuma wanda yake karatun Al-ƙur'ani, kuma yake guragura a cikinsa, yana mai shan wuya gareshi, to yana da lada biyu".
Bukhari ne ya ruwaito shi (4937), da Muslim (798), kuma lafazin nasa ne.
Daga Abu Umamah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa:
"Ku karanta Al-ƙur'ani domin zai zo ranar Al-ƙiyama mai ceto ga ma'abotan sa".
Muslim ne ya ruwaito shi (804).
Daga Amir ɗan Wasilatu lallai cewa Nafi'u ɗan Abdul Haris ya gamu da Umar a Usfan, Umar ya kasance ya naɗashi gwamna a Makka, sai ya ce: Wa kasa aiki ga mutanen kwari? sai ya ce: Ɗan Abza, ya ce: Waye Ɗan Abza? Sai ya ce: Wani 'yantaccen bawa ne daga 'yantattun bayin mu, ya ce: Kuma sai ka naɗa musu 'yantaccen bawa? sai ya ce: Lallai cewa shi makaranci ne ga littafin Allah - mai girma da ɗaukaka -, kuma lallai cewa shi masani ne da rabon gado, sai Umar ya ce: Lallai cewa Annabin ku -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - haƙiƙa ya ce: "Lallai Allah Ya na ɗaukaka wasu mutane da wannan littafin, kuma Yana ƙaskantar da wasu".
Muslim ne ya ruwaito shi (817).
Daga Abu huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Wasu mutane ba za su taru a wani ɗaki daga cikin ɗakunan Allah ba, suna karanta littafin Allah kuma suna koyar da shi a tsakanin su ba, sai nutsuwa ta sauka a kansu, kuma rahama ta rufe su, kuma Mala'iku sun kewaye su, kuma Allah Ya ambace su cikin waɗanda suke wurinsa".
Muslim ne ya ruwaito shi (2699).
LADAN KARANTA SURATUL FATIHA
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce:
"Yayin da Jibrilu ya ke zaune a wurin Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ji wata ƙara daga sama, don haka ya ɗaga kansa sama, ya ce: Wannan wata ƙofa ce daga sama da aka buɗeta a yau, ba'a taɓa buɗe ta ba sai yau, sai wani Mala'ika ya sauko daga cikinta, sai ya ce: Wannan wani Mala'ika ne da ya sauko ƙasa, kuma bai taɓa sakkowa ba sai yau, sai ya yi sallama, ya ce: Ka yi albishir da haske biyu da aka ba ka su, wanda ba'a bawa wani Annabi kafinka ba; Ita ce Fatihatul Kitab, da ƙarshen suratul Baƙarah, ba za ka karanta wani harafi daga cikinsu ba sai an ba ka shi".
Muslim ne ya ruwaito shi (806).
LADAN KARANTA SURATUL BAƘARAH
Daga Abu huraira - Allah ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Kada ku mayar da gidajen ku Maƙabartu, lallai cewa Shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Suratul Baƙarah acikin sa".
Muslim ne ya ruwaito shi (780).
Daga Abu Umamah - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa:
"Ku karanta Suratul Baƙarah; domin lallai cewa riƙo da ita albarka ne, kuma barinta nadama ne, kuma matsafa ba zasu iyata ba".
Mu'awiya ya ce: Labari ya isar mini cewa Al-Baɗalah: Sune: Matsafa.
Muslim ne ya ruwaito shi (804).
LADAN KARANTA AYATUL-KURSIYYI
Daga Abu Huraira - Allah Ya ƙara yarda a gare shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya wakilta ni in kula da zakkar Ramadan, sai wani mai zuwa ya zo mini, sai ya fara ɗibar abincin, sai na kamashi, sai na ce: Wallahi sai na kai ka wajen Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -, sai ya karanto hadisin, sannan yace: Idan ka zo shinfiɗarka; to, ka karanta Ayatul Kursiyyi, wani mai kiyayewa daga Allah ba zai gushe tare da kai ba, kuma Shaiɗani ba zai kusance ka ba har ka wayi gari, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Ya faɗa maka gaskiya alhali shi baƙin maƙaryaci ne, ai wancananka Shaiɗan ne".
Bukhari ne ya ruwaito shi (3275).
LADAN KARANTA ƘARSHEN SURATUL BAƘARAH
Daga Abu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Ayoyi biyu daga ƙarshen Suratul Baƙara wanda ya karanta su a cikin dare; to, sun ishe shi".
Bukhari ne ya ruwaito shi (5009) da Muslim 80737).
LADAN KARANTA SURATUL BAKARA DA AL-IMRAN
Daga Abu Umamah Al-Bahili - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa:
"Ku karanta masu hasken nan guda biyu; Al-Baƙara da Al-Imran, domin za su zo ranar Al-ƙiyama kai kace su giza-gizai ne biyu, ko kamar lemomi ne biyu, ko kamar wasu dandazo ne biyu na tsuntsaye waɗanda sukayi sahu-sahu, suna ba da kariya ga ma'abotan su".
Muslim ne ya ruwaito shi (804).
Daga Nawwas ɗan Sam'an Al-kilabi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa:
"Za'a zo da Al-ƙur'ani a ranar Al-ƙiyama da ma'abotan sa waɗanda sun kasance suna aiki da shi, Suratul Baƙara da Al-Imrana suna yi masa jagora" Kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya buga misalai uku ba mu manta su ba bayan nan, ya ce: "Kai kace su giza-gizai ne biyu, ko baƙaƙen lemomi ne biyu a tsakaninsu akwai haske, ko kai ka ce su dandazo ne biyu na tsuntsaye waɗanda suka yi sahu-sahu, suna ba da kariya ga ma'abocin su".
Muslim ne ya ruwaito shi (805).
LADAN SURATUL KAHFI
Daga Al-Bara'u ɗan Azib, ya ce: Wani mutum ya kasance yana karanta Suratul Kahfi, kuma a gefensa akwai wani doki a ɗaure da igiyoyi biyu, sai wani girgje ya lulluɓe shi, sai ya fara kusantowa yana kusantowa, sai kuma dokinsa ya fara zabura, yayin daya wayi gari sai ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ambata masa wannan, sai ya ce: "Waccan nutsuwa ce take sauka tare da Al-kur'ani".
Bukhari ne ya ruwaito shi (5011) da Muslim (795).
LADAN HADDACE AYOYI GOMA DAGA FARKON SURATUL KAHFI
Daga Abu Al-Darda'i - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahfi za'a tsare shi daga fitinar Dujal".
Muslim ne ya ruwaito shi (809).
LADAN KARANTA SURATUL IKHLAS (KA CE ALLAH SHI NE ƘWAL)
Daga Abu Al-Darda'i - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Shin karanta ɗaya bisa uku na Al-ƙur'ani acikin dare ɗaya zai gagari ɗayanku?" Sai sukace: Ta yaya za'a karanta ɗaya bisa uku na Al-ƙur'ani? sai ya ce: "Qul huwallahu Ahad tana daidai da ɗaya bisa uku na Al-ƙur'ani".
Muslim ne ya ruwaito shi (811).
LADAN AMBATON ALLAH MAƊAUKAKIN SARKI
Daga Abu Hurairah- Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya kasance yana tafiya a hanyar Makka, sai ya wuce ta wani dutse ana ce masa: Jamdan, sai ya ce: "Ku tafi, wannan Jamdan ne, masu kaɗaitawa sun rigaya".
Sai su ka ce: Su waye masu kaɗaitawa ya Manzon Allah? Sai ya ce: Maza masu ambaton Allah da yawa, da mata masu ambataon Allah".
Muslim ne ya ruwaito shi (2676).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Allah Yana cewa: Ni Ina wurin zaton bawaNa gareNi, kuma Ni Ina tare da shi idan ya ambace Ni, idan ya ambace Ni a cikin ransa zan ambace shi a cikin raiNa, idan ya ambaceNi acikin wasu jama'a, zan ambace shi a cikin wasu jama'a mafi alheri daga garesu, idan ya yi kusanci zuwa gareNi taku ɗaya zan yi kusanci gareshi zira'i, idan ya yi kusanci gareNi zira'i, zan yi kusanci gareshi gaba guda, idan ya zo mini yana tafiya zan zo masa ina gaggawa".
Bukhari ne ya ruwaito shi (7405) da Muslim (2675).
LADAN MAJALISAN ZIKIRI
Daga Mu'awiya - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya fita zuwa wata halƙa ta sahabban sa, sai ya ce: "Menene ya zaunar da ku?" Sai suka ce: Mun zauna ne muna ambaton Allah, muna gode maSa a bisa shiryar da mu ga musulunci, da kuma baiwar da Ya yi mana da shi, ya ce: Kun rantse da Allah babu abin da ya zaunar da ku sai wannan, suka ce: Mun rantse babu abin da ya zaunar da mu sai wannan, ya ce: "Amma ni ban nemi ku rantse ba don tuhuma a gareku, sai dai cewa Jibrilu ne ya zo min, sai ya ba ni labari cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku".
Muslim ne ya ruwaito shi (2701).
Daga Abu Hurairah da Abu Sa'id Al-Khudry - Allah Ya yarda da su - cewa sun shaida Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wasu mutane ba za su zauna ba suna ambaton Allah - Mai girma da ɗaukaka - sai Mala'iku sun kewayesu, kuma rahma ta lulluɓe su, kuma nutsuwa ta sauka a garesu, kuma Allah Ya amabace su a cikin waɗanda suke wurin Sa".
Muslim ne ya ruwaito shi (2700).
LADAN KALMAR TAUHIDI (BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH)
Daga Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, waye mafi arziƙin mutane da samun ceton ka a ranar Al-ƙiyama? sai ya ce: "Ya kai Abu Hurairah haƙiƙa na yi zaton cewa wani mutum ba zai tambaye ni game da wannan hadisin ba kafin ka; saboda abin da na gani na kwaɗayin ka a kan hadisi, to, mafi arziƙin mutane da samun cetona ranar Al-ƙiyama shi ne wanda ya ce; (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah) yana mai tsarkake zuciyar sa".
Bukhari ne ya ruwaito shi (6570).
LADAN FAƊIN (BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH, SHI KAƊAI YAKE BA SHI DA ABOKIN TARAYYA, MULKI NASA NE, KUMA GODIYA TASA CE, KUMA SHI MAI IKO NE A KAN DUKKAN KOMAI) ACIKIN YINI SAU ƊARI
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah -tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki nasa ne, godiya tasa ce, kuma Shi Mai iko ne a kan dukkan komai) sau ɗari a cikin yini, za'a rubuta masa kyakkyawa ɗari, kuma za'a shafe masa mummuna ɗari, kuma za ta kasance tsari daga shaiɗan a wannan yinin nasa, har sai ya kai maraice, kuma ba wanda zai zo da abin da ya fi wanda ya zo da shi, sai dai wanda ya aikata sama da hakan"
Bukhari ne ya ruwaito shi (3293) da Muslim (2691).
LADAN FAƊIN (TSARKI YA TABBATA GA ALLAH DA GODIYAR SA) A CIKIN YINI SAU ƊARI
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah -tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya ce: (Tsarki ya tabbata ga Allah da godiyar Sa) sau ɗari a yini, za'a kankare masa kurakuran sa, ko da sun kai kwatankwacin kumfar kogi".
Bukhari ne ya ruwaitoshi (6405) da Muslim (2692).
LADAN FAƊIN (TSARKI YA TABBATA GA ALLAH DA GODIYAR SA, TSARKI YA TABBATA GA ALLAH MAI GIRMA)
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah -tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Kalmomi biyu masu sauƙi a harshe, masu nauyi a cikin ma'auni, masu soyuwa zuwa ga Mai jin ƙai: Tsarki ya tabbatar wa Allah da godiyar Sa, tsarki ya tabbatar wa Allah Mai girma)".
Bukhari ne ya ruwaito shi (6406) da Muslim (2694).
LADAN FAƊIN (TSARKI YA TABBATA GA ALLAH, GODIYA TA TABBATA GA ALLAH)
Daga Abu Malik Al-Ash'ary - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Godiya ta tabbata ga Allah tana cika ma'auni, tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah su biyun suna cika ko tana cika abinda ke tsakanin sama da ƙasa".
Muslim ne ya ruwaito shi (223).
LADAN FAƊIN (TSARKI YA TABBATA GA ALLAH, KUMA GODIYA TA TABBATA GA ALLAH, KUMA BABU ABIN BAUTAWA DA GASKIYA SAI ALLAH, KUMA ALLAH NE MAFI GIRMA)
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Da ince: (Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma godiya ta tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah ne mafi girma) Shi ne mafi soyuwa gareni daga abin da rana ta fito a kansa".
Muslim ne ya ruwaito shi (2695).
Daga Samurah ɗan Jundub - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Mafi soyuwar zance zuwa ga Allah huɗu ne: (Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma godiya ta tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah ne mafi girma) ba ya cutar da kai da kowannen su ka fara".
Muslim ne ya ruwaito shi (2137).
LADAN TASBIHI
Daga Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Mun kasance a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ce: "Shin ɗayanku zai gaza wajen samu kyakykyawan aiki dubu a kowace rana?" Sai wani mai tambaya daga mazauna wajen ya tambaye shi: Ta yaya ɗayammu zai samu kyakykyawan aiki dubu? Ya ce: "Ya yi tasbihi sau ɗari, sai a rubuta masa kyakykyawa dubu, ko kuma a sarayar masa da kura-kurai dubu".
Muslim ne ya ruwaito shi (2698).
LADAN FAƊIN (TSARKI YA TABBATA GA ALLAH DA GODIYAR SA, ADADIN HALITTAR SA, DA YARDAR KANSA, DA NAUYIN AL-ARSHIN SA, DA TAWADAR KALMOMIN SA)
Daga Juwairiyya - Allah Ya yarda da ita - lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya fita daga wurinta da sassafe yayin da ya yi sallar Asuba, alhali tana wurin sallarta, sannan ya dawo bayan ya hantsinta, alhali tana nan a zaune, sai ya ce: "Ba ki gusheba a kan halin da na barki a kansa?" Tace: Eh, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Haƙiƙa na faɗi wasu kalmomi huɗu a bayanki, sau uku, da za'a auna su da abin da kika faɗa a yau da sun rinjaye su: (Tsarki ya tabbata ga Allah da godiyar Sa, adadin halittar Sa, da yardar kansa, da nauyin Al-Arshin Sa, da tawadar kalmomin Sa).
Muslim ne ya ruwaito shi (2726).
LADAN FAƊIN: (BABU WATA DABARA KO ƘARFI SAI GA ALLAH)
Daga Abu Musa Al-Ash'ary - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce da ni:
"Shin ba na shiryar da kai ba a bisa wata taska daga taskokin Aljanna? Sa na ce: Eh, sai ya ce: "Babu dabara kuma babu ƙarfi sai ga Allah".
Bukhari ne ya ruwaito shi (7386) da Muslim (2704).
FALALAR SHUGABAN ISTIGFARI
Daga Shaddadu ɗan Aus - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -:
Shugaban Istigfari shi ne ka ce: "Ya Allah Kai ne Ubangijina, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai, Ka halicce ni kuma ni bawanKa ne, kuma ni ina kan wuyayenKa da alƙawarin Ka iya iyawata, ina neman tsarin Ka daga sharrin abin da na aikata, ina iƙirari gare Ka da ni'imar Ka gareni, kuma ina iƙirari gare Ka da zunubi na, to, Ka gafarta min; domin ba mai gafarta zunubai sai Kai".
Duk wanda ya faɗeta da rana yana mai sakankancewa da ita, sai ya mutu a yininsa kafin yayi maraice, to, yana daga 'yan Aljanna, kuma wanda ya faɗeta da daddare alhali shi yana mai sakankancewa da ita,sai ya mutu kafin ya wayi gari, to, yana daga 'yan Aljanna".
Bukhari ne ya ruwaito shi (6306).
LADAN FAƊIN (INA NEMAN TSARIN ALLAH DA KALMOMIN ALLAH CIKAKKU DAGA SHARRIN ABINDA YA HALITTA)
Daga Khawlatu 'yar Hakim Al-sulamiyyah - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Wanda ya sauka a wani masauki sannan ya ce: (Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da Ya halitta) Wani abu ba zai cutar da shi ba, har sai ya tafi daga wannan masaukin nasa".
Muslim ne ya ruwaito shi (2708).
Daga Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi - cewa ya ce:
Wani mutum ya zo wajen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ce: Ya Manzon Allah ban gamu da cuta ba kamar kunamar da na gamu da ita ta harbeni a daren jiya, sai ya ce: "Ina ma dai ka ce yayin da ka yammata: (Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, da ba ta cuce ka ba)".
Muslim ne ya ruwaito shi (2709).
LADAN ABIN DA AKE FAƊA KAFIN BACCI
Daga Al-Bara'u ɗan Azib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Idan ka zowa makwancinka, to, ka yi alwala alwarka ta sallah, sannan ka kwanta a ɓangaren ka na dama, sannan ka ce: (Ya Allah ina miƙa fuskata gareKa, na fawwala al'amarina gareKa, na fakar da bayana gareKa,dan kwaɗayi da tsoro gareKa, babu mafaka kuma babu matsirata sai zuwa gareKa, Ya Allah na yi imani da littafin da Ka saukar, da kuma Annabin da Ka aiko), idan ka mutu a daren naka, to, kai kana kan Sunnah, kuma ka sanya su ƙarshen abin da za ka yi magana da shi".
Bukhari ne ya ruwaito shi (247) da Muslim (2710).
LADAN ABNDA WANDA YA FARKA DA DARE ZAI AIKATA SHI (ABIN DA ZA'A AMBATA)
Daga Ubadah ɗan Samit - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ya farka daga dare, sai ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai Ya ke, bashi da abokin tarayya, mulki nasa ne kuma godiya ta tabbata a gareShi, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai, godiya ta tabbata ga Allah, tsarki ya tabbata ga Allah, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne mafi girma babu dabara, babu ƙarfi sai ga Allah), sannan ya ce: (Ya Allah ka gafarta min), ko ya yi addu'a, to, za'a amsa masa, idan ya yi alwala ya yi sallah za'a karɓi sallarsa".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1154).
"Ta'arra" da yi wa Ra shadda wato: Ya farka.
LADAN ZIKIRAN DA AKE FAƊA A ƘARSHEN SALLOLIN FARILLA
Daga Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa talakawan da sukayi hijira sun zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai suka ce: Masu dukiya sun tafi da darajoji maɗaukaka, da dawwamammiyar ni'ma, sai ya ce: Menene wannan?" Sai suka ce; Suna sallah kamar yadda muke sallah, suna azumi kamar yadda muke azumi, kuma suna sadaka amma bama sadaka, suna 'yantawa amma bama 'yantawa, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Shin bana sanar da ku wani abu ba wanda zaku riski wanɗanda suka rigaye ku da shi kuma ku tserewa waɗanda ke bayan ku da shi, kuma babu wani wanda zai kasance mafifici a kanku, sai wanda ya aikata irin abin da kuka aikata" Suka ce: Eh, ya Manzon Allah, sai ya ce: "Ku yi Tasbihi, ku yi Kabbara, ku yi Hamdala, a bayan kowace sallah sau talatin da uku".
Abu Saleh ya ce: Sai talakawa Muhajirai suka dawo zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -, sai suka ce: 'Yan uwammu masu dukiya sun ji abin da muka aikata, sai suka aikata irinsa, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wannan falalar Allah ce ya ke ba wa wanda yake so".
Bukhari ne ya ruwaito shi (843) da Muslim (595).
Daga Ka'ab ɗan Ujrah - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Masu bibiya a ƙarshe mai faɗinsu ba zai taɓe ba, ko mai aikatasu a bayan kowace sallar farilla, tasbihi talatin da uku, tahmidi talatin da uku, da kabbara talatin da huɗu".
Muslim ne ya ruwaito shi (596).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ya tsarkake Allah a bayan kowace sallah sau talatin da uku, kuma ya gode wa Allah sau talatin da uku, yayi wa Allah Kabbara sau talatin da uku, wancan shi ne casa'in da tara kenan, kuma yace a cikon ɗarin: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Ya ke ba Shi da abokin tarayya, mulki ya tabbata gareShi, godiya ta tabbata gareShi, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai), za'a gafarta masa kurakuran sa, ko da sun kasance tamkar kumfar kogi".
Muslim ne ya ruwaito shi (597).
LADAN ADDU'A
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Lallai Allah Yana cewa: Ni ina inda zaton da bawaNa ya ke da Ni, kuma Ni ina tare da shi idan ya kiraNi".
Muslim ne ya ruwaito shi (2675).
LADAN WANDA YA YI ADDU'A GA ƊAN'UWANSA A ƁOYE
Daga Abu Al-Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Babu wani bawa musulmi da zai yi addu'a ga ɗan'uwan sa a ɓoye, sai Mala'ika ya ce: Kai ma kana da tamkar".
Muslim ne ya ruwaito shi (2732).
LADAN ISTIGFARI
Daga Abu Zarr - Allah ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - daga cikin abin da ya ke ruwaito wa daga Allah - Mai girma da ɗaukaka - cewa Ya ce:
"Ya ku bayiNa lallai ku kuna kuskure dare da rana, kuma Ni ina gafarta zunubai gaba ɗaya, to, ku nemi gafaraTa in yi gafara gareku".
Muslim ne ya ruwaito shi (2577).
LADAN SALATI GA ANNABI - TSIRA DA AMICIN ALLAH SU TABBATA A GARESHI-
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah -tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya yi salati a gareni sau ɗaya, Allah Zai masa salati sau goma".
Muslim ne ya ruwaito shi (408).
LADAN BIN IYAYE
Daga Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - cewa wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - waɗane ayyuka ne mafifita? Sai ya ce: "Sallah a kan lokacin ta, da biyayya ga iyaye".
Bukhari ne ya ruwaito shi (7534) da Muslim (140).
Daga Abdullahi ɗan Amru ɗan Al-Aas - Allah Ya yarda da su - yace:
Wani mutum ya fuskanto zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabata a gareshi - sai ya ce: Zan yi maka caffa a kan Hijira da yaƙi, ina neman lada daga Allah, sai ya ce: "shin daga iyayenka akwai wani ɗaya da yake raye?" Ya ce: Eh, ai su biyun ma, ya ce: "Kuma kake neman lada daga Allah? ya ce: Eh, ya ce: "To ka koma zuwa ga mahaifan ka ka kyuautata zama da su".
Muslim ne ya ruwaito shi (2549).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin" Aka ce: Wa ya Manzon Allah? Ya ce: "Wanda ya riski iyayen sa yayin girma, ɗayan su ko su biyun amma bai shiga Aljanna ba".
Muslim ne ya ruwaito shi (2551).
LADAN SA DA ZUMUNCI
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda yake son a yalwata masa a cikin arziƙin sa, kuma a jinkirta masa a cikin gurbin sa; to, ya sadar da zumuncin sa".
Bukhari ne ya ruwaito shi (5986) da Muslim (2557).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Lallai Allah Ya halicci halitta, har lokacin da ya gama daga halittarSa, sai zumunci ya ce: Wannan shi ne matsayin mai fakewa gareka daga yankewa, ya ce: Eh,shin baka yarda in sadar wa wanda ya sadar maka ba, kuma in yanke wa wanda ya yanke maka? ya ce: Eh, ya Ubangiji, ya ce: To, an yi maka, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Ku karanta in kun so: (Shin kuna ƙauna idan kun juya baya ku yi ɓarna a cikin ƙasa kuma ku yanke zumuncin ku)".
Bukhari ya ruwaito shi (5987) da Muslim (2554).
Daga Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi - cewa wani mutum ya ce: Ya manzon Allah, ina da wasu 'yan uwa ina sadar musu, su kuma suna yanke min, kuma ina kyautata musu, su suna munana wa gareni, kuma ina haƙuri da su, kuma suna yi min wauta, sai ya ce: "Idan ka kasance kamar yadda ka faɗa, to, kamar kana cusa musu toka mai zafi ne a bakin su, kuma wani mai rinjaye a kansu daga Allah ba zai gushe tare da kai ba muddin dai ka kasance a kan haka"
Muslim ne ya ruwaito shi (2558).
"Al-Mall" da yi wa lami Shadda: Shi ne toka mai zafi.
LADAN CIYARWA GA MATA DA IYALI
Daga Abu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Idan mutum ya ciyar da iyalan sa yana mai neman ladan hakan, to, ya zama sadaka ne gare shi".
Bukhari ne ya ruwaito shi (55) da Muslim (1002).
Daga Ummu Salamah - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ce; Ya Manzon Allah, shin ina da lada idan na ciyar da 'ya'yan Banu Salamah, kuma su ɗin 'ya'yana ne? sai ya ce: "Ki ciyar da su, kina da ladan abin da kika ciyar a gare su".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1467) da Muslim (1001).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Dinare da ka ciyar da shi a cikin tafarkin Allah, da dinaren da ka ciyar da shi a 'yanta wuyaye, da dinaren da ka yi sadaka da shi ga miskini, da dinaren da ka ciyar da shi ga iyalan ka; mafi girman su lada shi ne wanda ka ciyar ga iyalan ka".
Muslim ne ya ruwaito shi (995).
Daga Sa'ad ɗan Abu waƙas - Allah Ya yarda da shi - cewa ya ba shi labari cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Lallai cewa kai ba za ka ciyar da wata ciyarwa ba da kake neman zatin Allah da ita; sai an ba ka lada a kanta, har abin da za ka sa a cikin bakin matar ka".
Bukhari ne ya ruwaito shi (56) da Muslim (1628).
LADAN WANDA YAKE DA 'YA'YA MATA BIYU, KO 'YAN UWA BIYU MATA SAI YAYI HAƘURI A KANSU YA KUMA KYAUTATA MUSU
Kuma daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Wata mata ta shigo gareni, a tare da ita akwai 'ya'yan ta mata biyu, sai ta roƙe ni, ba ta samu komai a wurina ba sai dabino guda ɗaya, sai na bata shi, sai ta raba shi a tsakanin 'ya'yanta mata biyun, ba ta ci komai daga ciki ba, sannan ta tashi ta fita da 'ya'yanta mata biyun, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shigo wurimmu, sai na bashi labari, sai ya ce: "Duk wanda aka jarrabe shi da waɗannan 'yan matan da wani abu sai ya kyautata musu, za su zama kariya a gareshi daga wuta".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1418) da Muslim (2629).
Kuma daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Wata miskiniya ta zo wurina tana ɗauke da 'ya'yanta mata biyu, sai na ciyar da ita dabinai uku, sai ta ba wa kowacce ɗaya daga cikinsu su biyun dabinon, sai ta ɗaga dabino zuwa bakinta don ta ci, sai 'ya'yan na ta mata biyun suka nemi su ƙara ci, sai ta raba musu dabinon da ta so ta ci, sai sha'anin ta ya ƙayatar da ni, sai na gaya wa Ma'aikin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - abin da ta aikata, sai ya ce: "Lallai haƙiƙa Allah Ya wajabta mata Aljanna da shi, ko kuma Ya 'yanta ta daga wuta da shi".
Muslim ne ya ruwaito shi (2630).
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ya kula da ɗawainiyar 'ya'ya mata biyu har suka balaga, to, zai zo ranar Al-ƙiyama, ni da shi" ya damƙe 'yan yatsun sa.
Muslim ne ya ruwaito shi (2631).
LADAN MAI KAI KAWO GA MATAR DA MIJINTA YA MUTU DA MISKINI
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mai kai-kawo ga wacce mijinta ya mutu da miskini, kamar mai yaƙi ne a tafarkin Allah, ko mai tsayuwar dare kuma mai azumi da rana".
Bukhari ne ya ruwaito shi (5353) da Muslim (2982).
LADAN KULA DA MARAYA
Daga Sahlu - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Kuma ni da mai kula da maraya a cikin Aljanna kamar haka ne" Sai ya yi nuni da ɗan yatsa na nuni da na tsakiya, ya kuma wara tsakanin su".
Bukhari ne ya ruwaito shi (5304).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Mai kula da maraya na sa, ko na waninsa, ni da shi kamar waɗannan biyun ne a cikin Aljanna" Sai Malik ya yi nuni da ɗan yatsa na nuni da na tsakiya.
Muslim ne ya ruwaitoshi (2983).
Faɗinsa "Nasa ko na wanin sa" yana nufin: Duk ɗaya ne marayan ya kasance makusanci ne gareshi, ko ya kasance na nesa ne gareshi, babu kusanci tsakanin sa da shi.
LADAN WANDA YA ZIYARCI ƊAN UWAN SA A CIKIN LAMARIN ALLAH - MAƊAUKAKIN SARKI -
Daga Abu Hurairah - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, cewa wani mutum ya ziyarci wani ɗan’uwan sa a wani ƙauyen daban, sai Allah Ya sanya wani Mala’ika a kan hanyar sa ya dakace shi, yayin da ya zo masa, sai ya ce: Ina kake nufi? Sai ya ce: Ina nufin wani ɗan uwa ne a cikin wannan ƙauyen, sai ya ce: Shin kana da wata ni'ima ce da ka ke son cikata gare shi? Sai ya ce: A'a, sai dai cewa ni ina sonsa ne saboda Allah - mai girma da ɗaukaka - sai ya ce: Lallai cewa ni Manzon Allah ne zuwa gareka, cewar lallai haƙiƙa Allah Ya so ka kamar yadda ka so shi a cikin lamarin Sa".
Muslim ne ya ruwaito shi (2567).
LADAN WANDA YA BIYA BUƘATUN 'YAN UWAN SA MUSULMAI
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Musulmi ɗan uwan musulmi ne, kada ya zalunce shi, kuma kada ya miƙashi, wanda ya kasance a cikin buƙatar ɗan uwansa Allah Zai kasance a cikin buƙatar sa, wanda ya yaye wani baƙin ciki daga musulmi Allah Zai yaye masa wani baƙin ciki daga baƙƙan cikin ranar Al-ƙiyama, wanda ya suturta wani musulmi Allah Zai suturta shi ranar Al-ƙiyama".
Bukhari ne ya ruwaito shi (2442) da Muslim (2580).
Daga Abu Qatadah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa:
"Wanda yake son Allah Ya tseratar da shi daga baƙƙan cikin ranar Al-ƙiyama, to, ya yaye wa wanda yake cikin wani mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (wani haƙƙi ko nauyin da ya ke kansa)".
Muslim ne ya ruwaito shi (1563).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Duk wanda ya yayewa wani mumini baƙin ciki daga baƙƙan cikin duniya, to, Allah Zai yaye masa wani baƙin ciki daga baƙƙan cikin lahira, wanda ya sawwaƙa ga wanda yake cikin matsuwa, to, Allah Zai sawwaƙa masa a duniya da lahira, wanda ya suturta wani musulmi, to, Allah Zai suturta shi a duniya da lahira. Allah Yana cikin taimakon bawa muddin bawan ya kasance a cikin taimakon ɗan uwan sa".
Muslim ne ya ruwaito shi (2699).
LADAN WANDA YA DUBA WANI MARA LAFIYA
Daga Sauban - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ya duba wani mara lafiya ba zai gushe ba a cikin Khurfah ta Aljanna" Aka ce ya Manzon Allah, mecece Khurfah ta AJanna? sai ya ce: "Ababen tsinkarta".
Muslim ne ya ruwaito shi (2568).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Zai ce a ranar Al-ƙiyama: Ya kai Dan Adam, Na yi rashin lafiya amma ba ka duba Ni ba? Sai ya ce: Ya Ubangiji ta yaya zan duba Ka alhali kai ne Ubangijin talikai? Sai ya ce: Amma ka san cewa bawaNa wane ya yi rashin lafiya ba ka duba shi ba, shin ba ka san cewa da ace ka dubo shi da ka same Ni a wajensa ba? Ya kai Dan Adam Na nemi ka ciyar da Ni amma ba ka ciyar da Ni ba, Sai ya ce: Ya Ubangiji, ta yaya zan ciyar da Kai alhali kai ne Ubangijin talikai?! Sai ya ce: Shin ba ka san cewa bawa Na wane ya nemi ciyarwarka amma ba ka ciyar da shi ba? ba ka san cewa da ace ka ciyar da shi da ka samu wannan a waje Na ba,Ya kai Ɗan Adam Na nemi shayarwar ka amma ba ka shayar da Ni ba, Yace: Ya Ubangiji, ta yaya zan shayar da kai alhali kaine Ubangijin talikai?! Sai ya ce: "BawaNa wane ya nemi ka shayar da shi amma ba ka shayar dashi ba, shin ba ka sani ba cewa da ka shayar da shi za ka samu wancan a wajeNa".
Muslim ne ya ruwaito shi (2569).
LADAN GASKIYA
Daga Hakim ɗan Hizam - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Masu cikini biyu suna da zaɓi muddin dai ba su rabu ba, idan suka yi gaskiya, kuma suka bayyana za'ayi musu albarka a cikin cinikinsu, idan suka ɓoye kuma suka yi ƙarya, to, za'a shafe albarkar cinikin su".
Bukhari ne ya ruwaito shi (2079) da Muslim (1532).
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Na hore ku da gaskiya, saboda gaskiya tana shiryarwa zuwa ga aikin alheri, kuma lallai aikin alheri yana shiryarwa zuwa ga Aljanna, kuma mutum ba zai gushe ba yana yin gaskiya, kuma yana kirdadon gaskiya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai yawan gaskiya ne, kuma na haneku da ƙarya, saboda ƙarya tana shiryarwa ne zuwa ga fajirci, kuma fajirci yana shiryarwa ne zuwa ga wuta, kuma mutum ba zai gushe ba yana yin ƙarya kuma yana kirdadon ƙarya har sai an rubuta shi a wajen Allah mai yawan ƙarya".
Bukhari ne ya ruwaito shi (6094) da Muslim (2607).
LADAN AFUWA DA ƘANƘAN DA KAI
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wata sadaka ba ta taɓa tauye wata dukiya ba, kuma babu wani abu da Allah Yake ƙarawa bawa sabo da rangwame sai ɗaukaka, kuma babu wanda zai ƙanƙan da kai ga Allah sai Allah Ya ɗaukaka shi".
Muslim ne ya ruwaito shi (2588).
LADAN TAUSASAWA A CIKIN AL'AMURA GABA ƊAYANSU
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ya ke Aisha, lallai Allah Mai tausasawa ne Yana son tausasawa, kuma Yana bayarwa a kan sauƙaƙawa, abin da ba Ya bayarwa a kan tsanani, da kuma abin da ba Ya bayarwa a kan waninsa".
Muslim ne ya ruwaito shi (2593).
A cikin wata riwayar ta sa (2594): "Lallai sauƙi ba ya kasancewa a cikin wani abu face sai ya ƙawata shi, kuma ba za'a cire shi daga wani abu ba face sai ya munana shi".
LADAN WANDA YA SUTURTA ƊAN UWAN SA MUSULMI
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Al-ƙiyama".
Muslim ne ya ruwaito shi (2590).
LADAN YIN SULHU TSAKANIN MUTANE
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Kowace gaɓa daga mutane akwai sadake a kanta, kowane yinin da rana ta fito a cikin sa da zai daidaita tsakanin mutum biyu sadaka ne, kuma ya taimaki mutum game da dabbar sa; sai ya ɗora shi a kanta, ko ya ɗora masa kayan sa a kanta, to, sadaka ne, kuma kalma mai daɗi sadaka ce, kuma kowane taku da zai yi zuwa ga sallah sadaka ne, kuma ya kau da ƙazanta daga hanya sadaka ne".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Faɗinsa: "Ya daidaita tsakanin mutum biyu" Wato: Ya yi sulhu a tsakanin su da adalci.
LADAN WANDA YA JUYAR DA GIBAR MUSULMI KUMA YA KARE MASA MUTUNCIN SA
Daga Abu Al-Darda'i - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Duk wanda ya kare mutuncin ɗan uwan sa, Allah Zai kare fuskar sa daga wuta ranar Al-ƙiyama".
Tirmizi ne ya ruwaito shi, kuma ya ce: Hadisi ne kyakkyawa
LADAN SO A CIKIN SHA'ANIN ALLAH - MAƊAUKAKIN SARKI -
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - game da Al-ƙiyama, sai ya ce: yaushe ne Al-ƙiyama? Sai ya ce; "Mai ka tanadar mata" Sai ya ce: Babu komai, sai dai cewa ni ina son Allah da Manzon Sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya ce: "Kai kana tare da wanda ka ke son sa".
Anas ya ce: Ba mu taɓa farin ciki da wani abu ba irin farin cikimmu da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi: "Kai kana tare da wanda kake so".
Anas ya ce: "To, ni ina son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - da Abu Bakar da Umar, kuma ina ƙaunar in kasance tare da su sabo da son da na ke musu, ko da ban aikata irin ayyukan su ba".
Bukhari ne ya ruwaito shi (3688) da Muslim (2639).
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Wani mutum ya zo wajen Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ce: ya Manzon Allah, ya za ka ce a shanin mutumin da ya so wasu mutane amma bai riskesu ba? Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mutum yana tare da wanda ya so".
Bukhari ne ya ruwaito shi (6169) da Muslim (2640).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Lallai Allah Zai ce a ranar Al-ƙiyama: "Ina masu soyayya don girma Na, a yau Zan inuwantar da su a cikin inuwa Ta, ranar da babu wata inuwa sai inuwa Ta".
Muslim ne ya ruwaito shi (2566).
LADAN HAƘURI A KAN BALA'I KO DA KAƊAN NE
Daga Abu Sa'id Alkhudry - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya horar wa kansa haƙuri; Allah zai datar da shi da haƙuri, Allah Bai ba wa wani wata kyauta ba mafi alheri kuma mafi yalwa sama da haƙuri ba".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1469) da Muslim (1053).
Daga Abu Malik Al-Ash'ary - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Haƙuri haske ne".
Muslim ne ya rawaito shi (223).
Daga Aɗa'u ɗan Abu Rabah ya ce: Ibn Abbas ya ce da ni: Shin ba na nuna maka wata mace 'yan Aljanna ba? Na ce: Eh, sai ya ce: Wannan matar baƙa ta zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ta ce: Lallai cewa ni ina farfaɗiya, kuma cewa ni ina yayewa [tsirara], to, ka roƙamin Allah, sai ya ce: "Idan kin so ki yi haƙuri Aljanna ta tabbata gareki, idan kuma kin so in roƙa miki Allah Ya ba ki lafiya" Sai ta ce: Zan yi haƙuri, sai ta ce: Lallai cewa ni ina yayewa [tsirara], to, ka roƙa min Allah da kada na yaye. sai ya roƙa mata Allah. Bukhari ne ya ruwaito shi (5652) da Muslim (2578).
Daga Abu Sa'id da Abu Hurairah - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gre shi - ya ce: "Abin da ya ke samun mumini na gajiya, ko rashin lafiya, ko damuwa, ko takaici, ko baƙin ciki, har ƙayar da zai takata sai Allah Ya kankare masa kurakuren sa da ita" Bukhari ne ya ruwaito shi da Muslim, lafazin sa shi ne, ya ce: "Babu abin da zai samu mumini na rashin lafiya ko gajiya ko masassara ko baƙin ciki, kai har takaici da zai dame shi sai Allah Ya kankare masa munanan ayyukan sa".
"Al-Nasab": Gaajiya, kuma "Al-Wasb": Rashin lafiya.
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu wata musiba da za ta samu musulmi sai Allah Ya kankare masa da ita, har ƙayar da ya taka ta". Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
A cikin wata riwayar ta Muslim: "Wata ƙaya ba za ta samu mumini ba, da abin da ke samanta, sai Allah Ya rage masa daga kuskuran sa da ita".
a cikin wata da ban" sai Allah Ya ɗaga darajarsa da ita, kuma Ya sarayar da kuskurensa da ita".
A cikin wata riwayar ta sa ta da ban, ya ce: Wasu samari daga Quraishawa sun shiga wurin A'isha - Allah Ya yarda da ita - a lokacin tana Mina alhali suna ta dariya, sai ta ce: Me ya ke sa ku dariya? Sai suka ce: Wane ne ya faɗo akan igiyar hema kuma wuyan sa ko idon sa ya kusa ya tafi sabo da`Allah, sai ta ce: Kada ku yi dariya domin cewa ni na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Babu wani musulmi da zai taka wata ƙaya ko sama da ita, sai Allah Ya rubuta masa daraja da ita, kuma an shafe masa kuskure da ita".
Daga Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce; "Babu wani musulmin da wata cuta ta rashin lafiya, ko waninta za ta same shi, sai Allah Ya sarayar da munanan ayyukan sa da ita, kamar yadda bishiya ta ke sarayar da ganyaryakin ta" Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
LADAN ZAZZAƁI
Daga Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiga wajen Ummus Sa'ib, ko kuma Ummul Musayyib sai ya ce: "Me ya same ki ya ke Ummul Sa'ib ko yake Ummul Msayyib kike makyarkata? Ta ce: "Zazzaɓi, kada Allah Ya yi albarka gare shi, sai ya ce: "Kada ki zagi zazzaɓi, domin cewa shi yana tafiyar da kurakuran 'yan Adam, kamar yadda zugazugi ya ke tafiyar da dattin ƙarfe".
Muslim ne ya ruwaito shi (2575).
Daga Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - a cikin rashi lafiyar sa, alhali yana fama da rashin lafiya mai tsanani, sai na ce; Lallai cewa kai ana jarrabar ka da rashin lafiya mai tsanani, kuma na ce: Lallai cewa wannan kana da lada biyu kenan? Ya ce; "Eh, babu wani musulmin da wata cuta za ta same shi sai Allah ya sarayar da kurakuran sa, kamar yadda bishiya take sarayar da ganyayaryakin ta".
Bukhari ne ya ruwaito shi (5647) da Muslim (2571).
LADAN WANDA YA RASA GANINSA SAI YA YI HAƘURI YA NEMI LADA
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce; Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Lallai Allah Ya ce: Idan na jarrabi bawaNa da masoyan sa biyu sai yayi haƙuri, zan canza masa Aljanna da su".
Yana nufin: Idanuwan sa biyu
Bukhari ne ya ruwaito shi (5653).
LADAN GUSAR DA ABU MAI CUTARWA DAGA HANYA
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"An bijiro min da ayyukan al'umma ta, kyawawan su da munanan su, a cikin kyawawan ayyukan su sai na samu abu mai cutarwa da ake gusar da shi daga hanya, kuma a cikin munanan ayyukan su sai na samu kaki a masallaci, wanda ba'a binneshi ba".
Muslim ne ya ruwaito shi (553).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - ya ce:
"Wata rana wani mutum yana tafiya a wata hanya, sai ya samu reshen wata ƙaya a kan hanyar, sai ya kawar da shi, sai Allah Ya yaba masa Ya kuma gafarta masa".
Bukhari ne ya ruwaitoshi (652) da Muslim (1914).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wani mutum ya wuce da wani reshen bishiya a kan doron wata hanya, sai ya ce: Na rantse da Allah sai na nisantar da wannan daga musulmai ba zai cutar da su ba, sai aka shigar da shi Aljanna".
Muslim ne ya ruwaito shi (1914).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Haƙiƙa na ga wani mutum yana juyawa a cikin Aljanna, dan sha'anin wata bishiyar da ya yanketa a kan hanya, ta kasance tana cutar da mutane".
Muslim ne ya ruwaito shi (1914).
LADAN WANDA YA KASHE MICIJIYA KO TSAKA
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya kashe tsaka a farkon duka, za'a rubuta masa kyawawa ɗari, a na biyun ƙasa da haka, a na ukun ma ƙasa da haka".
Muslim ne ya ruwaito shi (2240).
LADAN ƊAN KASUWA MAI YAWAN GASKIYA KUMA AMINTACCE
Daga Hakim ɗan Hizam - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Masu ciniki biyu suna da zaɓi muddin dai basu rabu ba, idan suka yi gaskiya, kuma suka bayyana, za'ayi musu albarka a cikin cinikin su, idan suka ɓoye kuma suka yi ƙarya, to, za'a shafe albarkar cinikin su".
Bukhari ne ya ruwaito shi (2110) da Muslim (1532).
LADAN RANGWAME A CIKIN SAYE DA SAYARWA
Daga Jbir ɗan Abbdullahi - Allah Ya yarda da su - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Allah ya ji ƙan mutum mai rangwame idan zai siyar, kuma idan zai siya, haka idan zai nemi biyan bashi".
Bukhari ne ya ruwaito shi (2076).
LADAN WANDA YA KIYAYE FARJIN SA DON TSORON ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA
Daga Sahlu ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya lamunce min abin da ke tsakanin muƙamuƙan sa guda biyu, da abin da ke tsakanin ƙafafuwan sa guda biyu, to, zan lamunce masa Aljanna".
Bukhari ne ya ruwaito shi (6474).
Abin nufi da abin da ya ke "Tsakanin muƙamuƙan sa biyu": Shi ne harshe. Kuma da abinda ya ke "Tsakanin ƙafafuwan sa biyu": Shi ne farji.
LADAN TUBA
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Allah Shi ne mafi farin ciki da tuban bawan Sa yayin da ya tuba zuwa gareShi daga ɗayan ku da ya kasance a kan taguwar sa a wani sararin daji, sai ta ɓace masa, kuma a kanta akwai abincin sa da abin shan sa, sai ya yanke ƙauna daga gareta, sai ya zo wa wata bishiya, sai ya kwanta a inuwarta, haƙiƙa ya yanke ƙauna daga taguwarsa, yana cikin wannan yanayi sai gashi da ita tana tsaye a wajen sa, sai ya riƙe linzamin ta, sannan ya ce sabo da tsananin farin ciki: "Ya Allah Kai ne bawa na, kuma ni ne ubangijin Ka, ya yi kuskure sabo da tsananin farin ciki".
Muslim ne ya ruwaito shi (2747).
LADAN AIKI NA GARI YAYIN ƁACIN ZAMANI
Daga Ma'ƙil ɗan Yasar - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ibada a cikin fitina kamar Hijira ce zuwa gareni".
Muslim ne ya ruwaito shi (2948).
"Al-Haraj" da yi wa Ra ɗauri, shi ne saɓani da fitintinu.
LADAN TALAKAWA DA MASU RAUNI
Daga Imran ɗan Husain - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
‘’Na yi tsinkaye a cikin Aljannah sai na ga mafiya yawan jama'ar ta talakawa ne, kuma na yi tsinkaye a cikin wuta sai na ga mafiya yawan jama'ar ta mata ne".
Bukhari ne ya ruwato shi (3241) kuma Muslim ya ruwaito shi (2737) daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su -.
Daga Usama - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Na tsaya a ƙofar Aljanna, kuma mafi yawancin waɗanda suka shigeta miskinai ne, kuma masu rabo na dukiya ababen tsarewa ne, sai dai cewa ma'abota wuta haƙiƙa an yi umarni da su zuwa ga wuta, kuma na tsaya akan ƙofar wuta sai ga mafi yawan waɗanda suka shigeta mata ne".
Bukhari ne ya ruwaito shi (5196) da Muslim (2736)
Daga Sauban - yardar Allah ta tabbata a gare shi - ya ce:
Na kasance ina tsaye a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai wani malami daga malaman Yahudawa ya zo, sai ya ce: Na zo ne in tambaye ka, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce masa: "Shin wani abu zai amfanar da kai in na zantar da kai?" Sai ya ce: Zan ji da kunnuwa na biyu, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya daki ƙasa da wata sanda da ke tare dashi, sai ya ce: "Kayi tambaya" Sai Bayahuden ya ce: A ina mutane za su kasance ranar da za'a canja ƙasa banda wannan ƙasar da sammai?".
Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Za su kasance a cikin duhu kafin gada" Sai ya ce: Waye farkon mutane a ƙetarewa? sai ya ce: "Su ne talakawa waɗanda suka yi Hijira".
Muslim ne ya ruwaito shi (315).
Daga Abu Abdul Rahman Al-Habli yace: Wasu mutane uku sun zo wurin Abdullahi ɗan Amr ɗan Al-Aas, alhali ni ina wurin sa, sai suka ce: Ya Abu Muhammadu lallai mu wallahi ba mu da iko a kan komai, babu ciyarwa, babu dabba, kuma babu kaya, sai ya ce da su: Me kuke so, idan kun so ku dawo zuwa wurinmu, sai mu ba ku abin da Allah Ya sawwaƙe gareku, idan kuma kun so mu ambaci al'amarin ku ga sarki, idan kun so kuma kuyi haƙuri; domin cewa ni na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Lallai cewa talakawa waɗanda suka yi Hijira za su riga mawadata ranar Al-ƙiyama zuwa ga Aljanna da shekara arba'in". Sai suka ce: To, mu za muyi haƙuri, ba za mu ƙara tambayar komai ba.
Muslim ne ya ruwaito shi (2979).
"Al-Jad" da yiwa jim Fataha, shi ne rabo da wadata.
LADAN KYAUTATA ZATO GA ALLAH
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Allah - maɗaukakin sarki - Yana cewa: Ni ina wurin zaton bawaNa gareNi".
Bukhari ne ya ruwaito shi (7405) da Muslim (2675).
LADAN YAƊA SALLAMA
Daga Abu Huraira - yardar Allah ta tabbata a gareshi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba za ku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba har sai kun so juna, shin ba na shiryar da ku bisa wani abu wanda idan kun aikata shi za ku so juna ba? Ku yaɗa sallama a tsakanin ku".
Muslim ne ya ruwaito shi (93).
Daga Abdullahi ɗan Salam - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: " Ya ku mutane, ku yaɗa Sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunci, kuma ku yi sallah alhali mutane suna barci; za ku shiga Aljanna cikin aminci".
Tirmizi ne ya ruwaito shi (2485), kuma yace: "Hadisi ne kyakykyawa ingantacce".
LADAN SALLAMA GA MUTANEN GIDA
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce da ni: "Ya kai ɗan ƙaramin ɗana, idan za ka shiga ga iyalanka, to, ka yi sallama, za ta zama albarka gareka,da kuma iyalan gidan ka". Tirmizi ne ya ruwaitoshi, (2698) kuma ya ce: Hadis ne kyakykyawa ingantacce".
LADAN MASU JIN ƘAI
Daga Usama ɗan Zaid - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Lallai Allah Yana jin ƙan masu jin ƙai daga bayin Sa".
Bukhari ne ya ruwaito shi (1284) da Muslim (923).
LADAN ADDU'A A CIKIN LOKACIN AMSAWA
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Lallai a cikin dare akwai wani lokaci, babu wani mutum musulmi da zai dace da shi yana roƙon Allah - maɗaukakin sarki - wani alheri daga al'amarin duniya da na lahira, sai Allah Ya bashi shi, kuma wannan a kowane dare ne".
Muslim ne ya ruwaito shi (757).
LADAN KIRA ZUWA GA ALLAH
Daga Sahlu ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Da ace Allah Ya shiryar da wani mutum ɗaya sabo da kai; shi ne mafi alheri a gareka daga jajayen raƙuma".
Bukhari ne ya ruwaito shi (3009) da Muslim (2406).
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ya yi kira zuwa ga shiriya ya kasance yana da lada kwatankwacin ladan waɗanda suka bi shi, ba tare da an rage musu komai daga ladansu ba, kuma duk wanda ya yi kira zuwa ga ɓata ya kasance a kansa akwai zunubi kwatankwacin waɗanda suka bi shi, ba tare da an tauye musu komai daga zunuban su ba".
Muslim ne ya ruwaito shi (2674).
Daga Jarir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Wanda ya sunnanta wata sunnah kyakykyawa a cikin musulunci, sai ya yi aiki da ita, za'a rubuta masa kwatankwacin ladan wanda ya yi aiki da ita, kuma ba za'a tauye komai daga ladansu ba, kuma wanda ya sunnanta wata sunnah mummuna a cikin musulunci, sai aka yi aiki da ita a baynsa, za'a rubuta masa kwatankwacin laifin wanda ya yi aiki da ita, kuma ba za'a rage komai daga laifukan su ba".
Muslim ne ya ruwaito shi (1017).
LADAN ISAR DA HADISIN ANNABI - TSIRA DA AMICIN ALLAH SU TABBATA A GARE SHI -
Daga Ɗan mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji shi, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji".
Tirmizi ne ya ruwaito shi (2657), kuma ya ce: "Hadisi ne kyakykyawa kuma ingantacce".
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah Yana yarda da bawa da ya ci abinci sai ya gode maSa a kansa, ko ya sha abin sha, sai ya gode maSa a kansa".
Muslim ne ya ruwaitoshi (2734).