الدروس المهمة لعامة الأمة
يهدف الكتاب إلى تعليم المسلمين أساسيات دينهم بطريقة مبسطة وشاملة. يتناول مجموعة من الدروس المهمة مثل قراءة الفاتحة وقصار السور، وأركان الإسلام والإيمان، وأقسام التوحيد والشرك، وشروط وأركان وواجبات الصلاة، بالإضافة إلى مبطلاتها، مع بيان مختصر لشروط الوضوء وفروضه ونواقضه. كما يسلط الضوء على التحلي بالأخلاق الإسلامية والآداب الشرعية، ويقدم إرشادات لطيفة حول تجهيز الميت والصلاة عليه ودفنه.
MUHIMMAN DARUSSA GA DUKKANIN AL'UMMA
Na Babban Malami
Abdul-Azeez Bn Abdullahi Bn Baaz-Allah Ya yi masa rahama-
Allah Ya yi masa rahama
Gabatarwar Mawallafi
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangjin talkai, kyakkyawan ƙarshe ya tabbata ga masu tsoran Allah, Allah Yayi tsira da aminci ga bawanSa kuma manzonSa annabinmu Muhammadu, da alayensa da sahabbansa baki ɗaya .
Bayan haka:
Waɗannan wasu taƙaitattun kalmomine, akan bayanin sashin abinda ya wajaba kowa ya san shi dangane da addinin musulunci, na ambacesu da: (Mahimman darussa ga dukkanin al'umma).
Kuma ina roƙon Allah Ya amfanar da musulmai su, kuma Ya karɓesu daga gareni, hakika Shi Mai yawan kyautane, kuma Mai yawan karamci.
AbdulAzeez Bn Abdullahi Bn Baaz Muhimman darussa ga dukkanin al'umma [1] [1] Majmu'u Fataawa, da maqaloli mabanbanta (3/288-298).
DARASI NA FARKO: SURATUL FATIHA DA KUMA GAJERUN SURORI
Suratul Fatiha da abinda ya sawwaƙa daga gajerun surori, daga suratul Zalzala zuwa Suratun Nas, laƙƙanawa, da gyara karatu, da haddatarwa, da kuma bayani ga abinda fahimtarsa take wajaba.
DARASI NA BIYU: RUKUNAN MUSULUNCI
BAYANIN RUKUNAN MUSULUNCI BIYAR, NA FARKONSU KUMA MAFI GIRMANSU: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, da kuma cewa Muhammadu manzon Allah ne, da sharhin ma'anoninta, tare da bayanin sharuɗɗan la'ilaha illallah. Ma'narta: (La'ilaha) tana mai kore dukkan abinda ake bautawa da ba Allah ba, (Illallah) tana tabbatar da bauta ga Allah Shi kaɗai, ba Shi da abokin tarayya. Amma sharuɗɗan (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah) sune: Sani mai kore jahilci, da tabbatarwa mai kore kokwanto, da ikhlasi mai kore shirka, da gaskiya mai kore ƙarya, da soyayya mai kore ƙiyayya, da miƙa wuya mai kore bari, da karɓa mai kore juyarwa (ƙin karɓa) da kuma kafircewa duk abinda ake bautawa koma bayan Allah. Haƙiƙa an dunƙulesu acikin baitoci biyu masu zuwa:
Sanin yaƙini da ikhlasi da gaskiyarka tare da... soyayya da jawuwa da karɓarsu. An ƙara na takwas ɗinsu kafircewa daga gareka ga abinda... ba Allah ba daga abubuwan da aka allantar da su.
Tare da bayanin shaidawa cewa: (annabi) Muhammad manzan Allah ne, abinda kuma ta hukunta; gasgata shi cikin abinda Ya bada labari, da kuma yi masa biyayya cikin abinda Yayi umarni, da nisantar abinda yayi hani a kansa, kuma ya tsawatar, kuma kada ya bautawa Allah sai da abinda Allah- Mai girma da ɗaukaka- da manzanSa suka shar'anta shi. Sannan a bayyanawa ɗalibi ragowar rukunan musulinci biyar, sune: Sallah, zakka, azumi, ziyartar Ɗakin Allah mai alfarma, ga wanda ya sami ikon zuwa gare shi.
DARASI NA UKU: RUKUNAN IMANI
Su guda shida ne: Ka yi imani da Allah da mala'ikunSa, da littattafanSa, da ranar lahira, kuma ka yi imani da ƙaddara, alkhairinta da sharrinta daga Allah - Maɗaukakin Sarki - suke.
DARASI NA HUƊU: RABE-RABEN TAUHIDI, DA RABE-RABEN SHIRKA
Bayanin rabe-raben Tauhid: su uku ne: Tauhidi Rububiyya (Ubangijintaka), da Tauhidi na Uluhiyya (Allantaka), da Tauhidi na sunaye da siffofi.
1- Tauhidin rububiyya: Shi ne Imani da cewa haƙiƙa Allah- tsarki ya tabbatar maSa- (Shi ne) mahaliccin komai, kuma mai tasarrufi a dukkan wani abu, ba Shi da abokin tarayya a cikin haka.
2- Tauhidin Uluhiyya: Shi ne Imani da cewa haƙiƙa Allah- tsarki ya tabbatar maSa- Shi ne abin bautawa da gaskiya, ba Shi da abokin tarayya a cikin haka, shi ne ma'anar La'ilaha illallah. Haƙiƙa ma'anarta ba bu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dukkanin Ibadu na daga sallah da azumi, da wanin haka, yana wajaba a tsarkake su ga Allah Shi kaɗai, kuma ba ya halatta a juyar da wani abu daga garesu ga waninSa.
3- Tauhidin sunaye da siffofi: shi ne Imani da dukkan abinda ya zo a a cikin Alƙur'ani mai girma, ko a cikin Hadisai ingantattu, na sunayen Allah da siffofinSa, da tabbatar da su ga Allah, Shi kaɗai, a bisa fuska mai dacewa da Shi, ba tare da canzawa, ko korewa, ko misaltawa, ko kamantawa da (halittarSa) ba; don yin aiki da faɗarSa - tsarki ya tabbatar maSa -: {Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci. (1) "Allah wanda ake nufin Sa da buƙata". (2) "Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba." (3) "Kuma babu ɗaya da ya kasance kini a gare Shi.} [al-Ikhlas: 1-4] Da kuma faɗinSa - Mai girma da ɗaukaka -: {Wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani.} {Al-shura: 11}. Haƙiƙa shashin wasu ma'abota ilimi ya sanya su nau'i biyu, ya shigar da Tauhidin sunaye da siffofi a cikin Tauhidin Rububiyya, babu jayayya a lafazi a cikin haka; domin abin nufi bayyanan ne a dukkan rabe-raben biyu.
Rabe-raben shirka uku ne: Babbar shirka, da ƙaramar shirka, da kuma ɓoyayyiyar shirka.
Babbar shirka: tana wajabtar da sarayar (ɓacin) aiki, da dawwama a cikin wuta ga wanda ya mutu a akanta, kamar yadda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Da sun yi shirka da abinda suka kasance suna aikatawa ya lalace.} [al-An'am: 88], kuma Allah -Tsarki ya tabbatar maSa Ya ce: {Bã ya kasancewa ga mãsu shirka su rãya masallatan Allah, alhãli kuwa sunã mãsu bãyar da shaida a kan rãyukansu da kafirci, waɗannan ayyukansu sun ɓãci, kuma a cikin wutã sũ madawwama.} {al-Tauba: 17}, kuma haƙiƙa wanda ya mutu a kanta, ba za a gafarta masa ba, kuma Aljanna ta haramta a gare shi, kamar yadda Allah - Mai gairma da ɗaukakka - Ya ce: {Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan, ga wanda Yake so.} [al-Nisa'i: 48], kuma Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce: {Lalle ne shĩ, wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne, Allah Yã haramta masa Aljanna. Kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai.} [al-Ma'ida: 72].
Kuma yana daga nau'o'inta: Roƙon mamata, da gumaka, da neman agajinsu, da bakance a gare su, da yanka a gare su, da abinda ya yi kama da haka.
Amma ƙaramar shirka: Ita ce abinda ambatanta shirka ya tabbata da nassosi na Alƙur’ani da Sunna, saidai ita karamar shirka ba ta zamo daga jinsin babbar shirka ba, kamar riya a cikin sashin wasu ayyuka, da rantsuwa da wanin Allah, da faɗar: Allah Ya so kuma wane ya so, da abinda ya yi kama da haka; saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "Abu mafi tsoratarwa dana ke ji muku tsoro: shi ne ƙaramar shirka, sai aka tambaye shi mece ce ita, sai ya ce: "Riya". [2] Imamu Ahmad ne ya rawaito shi, da Ɗabarani, da Baihaƙi, daga Mahmud bn Labid al'Ansary-Allah Ya yarda da shi- da Isnadi kyakkyawa, kuma Ɗabari ya rawaito shi da Isnadai kyawawa, daga Mahmud dan Labid, daga Rafi'u ɗan Khadij, daga Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. [2] Imamu Ahmad ya fitar da shi (5/428), da Ɗabarany a cikin Alkabir (4/338), da Baihaƙi a cikin Al-Shu'ab (14/355), ya ce a cikin Majma'u al-zawa'id (1/121), Ahmad da wasu mazajen Al-sahih sun rawaito shi.
Da kuma faɗarsa-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- "Wanda ya rantse da wani abu koma bayan Allah to haƙiƙa ya yi shirka". [3] Imamu Ahmad ya rawaito shi da Isnadi ingantacce, daga Umar ɗan Khaɗɗab- Allah Ya yarda da shi- Kuma Abu Dawud ya rawato shi, da Tirmizi da ingataccen Isnadi, daga Hadisin ɗan Umar- Allah Ya yarda da su- daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- cewa shi ya ce: "Wanda ya rantse da wanin Allah to haƙiƙa ya kafirta ko ya yi shirka". [4] Da kuma faɗarsa-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-: "Kada ku ce : Allah Ya so, wane ma ya so, sai dai ku ce: Allah ne Ya so, sannan wane ma ya so". [5] Abu Dawud ya rawato shi da Isnadi ingantacce, daga Huzaifa ɗan Yamani- Allah Ya yarda da shi -. [3] Imamu Ahmad ya fitar da shi (1/47). [4] Abu Dawud ya ftar da shi, a lamba ta (3251) da Tirmizi a lamba ta (1535). [5] Abu Dawud ne ya fitar da shi a lamba ta (4980), da Ahmad (5/384).
Wannan nau'i ba ya wajabta Ridda (fita daga Musulinci), ba ya kuma sa a dawwama a wuta, sai dai shi yana kore cikar Tauhidi (kaɗaita Allah) na wajibi.
Nau'i na uku: Ɓoyayyar shirka; dallinta faɗar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "Shin ba na baku labari da abinda na fi muku jin tsoron sa ba, fiye da Masihul Dajjal? suka ce: Eh ya manzon Allah, ya ce: Ɓoyayyar shirka, mutum ya ta shi ya yi sallah sai ya ƙawata sallarsa, saboda abinda ya gani na kallon mutum zuwa gare shi". [6] Imamu Ahmad ne ya rawato shi, a cikin Musnad ɗinsa, daga Abu Sa'idi Khudry- Allah Ya yarda da shi -. [6] Ibnu Majah ya fitar da shi a lamba ta (4204) da Imamu Ahmad (3/30).
Kuma za’a iya a raba shirka zuwa nau'i biyu kawai:
Babba da ƙarama, amma ɓoyayyar shirka, ita tana gamesu; Takan faru a shirka babba, kamar shirkar munafukai; domin su, suna ɓoye aƙidunsu ɓatattu, suna bayyanar da Musulinci a fili, don riya (dan a gani) dan kuma tsoro ga kawunansu.
Tana kuma kasancewa a ƙaramar shirka, kamar riya, kamar (yadda ya tabbata) a cikin Hadisin Mahmud ɗan Labeed al- Ansary da ya gabata, da kuma Hadisin Abu Sa'id wanda ya gabata. Allah Shi ne Mai datarwa.
DARASI NA BIYAR: KYAUTAYI.
Rukunin kyautayi, shi ne: Ka bautawa Allah kamar kana ganinSa, domin kai in ba ka ganinSa, to Shi Yana ganinka.
DARASI NA SHIDA : SHARUƊƊAN SALLAH.
Su tara ne:
Muslunci, Hankali, Ganewa, Ɗauke kari (alwala ko wanka), Gusar da najasa, Shigar lokaci, Fuskantar alƙibla, da Niyya.
DARASI NA BAKWAI: RUKUNAN SALLAH.
Su sha huɗu ne:
Tsayuwa tare da iko, da kabbarar harama, da karatun Fatiha, da ruku'u, da daidaituwa bayan ruku'u, da sujjada a kan gaɓɓai bakwai, da ɗagowa daga gare ta, da zama tsakanin sujjada biyu, da nutsuwa a cikin dukkanin ayyukan, da jerantawa tsakanin rukunai, da tahiyar ƙarshe, da zama domin ta, da salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- da sallama biyu.
DARASI NA TAKWAS : WAJIBABBUN SALLAH.
Su takwas ne:
Dukkanin kabbarori banda kabbarar harama, da faɗar: (sami'a Allahu liman hamidahu) ga Liman da mai sallah shi kaɗai, da faɗar(Rabbana walakal hamd) ga kowa, da kuma faɗar (Subhana rabbiyal al-Azeem) a cikin ruku'u da kuma faɗin: Subhana rabbiyal al-Aala) a cikin sujjada, da faɗar (Rabbi igfirli) tsakanin sujjada biyu, da tahiyyar farko, da zama dominta.
DARASI NA TARA : BAYANIN TAHIYYA.
Shi ne ya ce:
"Attahiyyatu Lillahi, Wassalawatu, Waɗɗayyibatu, Assalamu Alaika Ayyuhan Nabiyyu, Warahmatullahi Wabarakatuhu, Assalamu Alaina Wa’ala Ibadillahis Salihina, Ash-hahadu An la’ilaha Illah Lahu, Wa Ash-hahadu Anna Muhammadan AbduHu Wa-rasuluHu". (Dukkan gaisuwa da addu'a da kyawawan abubuwa sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare ka, ya Annabi, da rahamar Allah da albarka. Amincin Allah ya tabbata a gare mu da bayin Allah salihai. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaidawa Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne.)
Sannan sai ya yi salati ga annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya yi albarka a gare shi sai ya ce: (Allahumma Salli Ala Muhammad, Wa’ala Aali Muhammad, kama Sallaita Ala Ibrahim, Wa ala Aali Ibrahim, Innaka Hamidun Majid. Allahumma Barik Ala Muhammad, Wa’ala Aaali Muhammad, Kama Barakta Ala Ibrahim, Wa’ala Aali Ibrahim, Innaka Hamidun Majid).
Sannan ya nemi tsarin Allah a cikin Tahiyya, daga azabar ƙabari, da kuma fitinar rayuwa da mutuwa, da ftinar masihul Dajjal, sannan ya zaɓi abin da ya so daga addu'a, musammama waɗanda aka ruwaito cikinsu, yana daga cikinsu:
(Ya Ubangiji Ka taimakeni a bisa ambatanka, da gode maka, da kyan bautarKa. Ya Allah ni na zalunci kaina zalunci mai yawa, babu mai gafarta zunubai sai Kai, Ka gafarta min gafara daga gareKa, Kajiƙaina, haƙiƙa Kai Mai yawan gafara ne Mai yawan jin ƙai).
Amma a tahiyya ta farko sai ya ta shi, bayan shaidawa biyu, zuwa (raka’a) ta uku a Azahar da La'asar da Magariba da Isha'i, idan ya yi salati ga annabi-tsira da amincin Allah su tabba a gare shi- to shi ya fi; saboda gamewar Hadisai a kan hakan, sannan ya ta shi zuwa ta uku.
DARASI NA GOMA : SUNNONIN SALLAH.
Yana daga cikin su:
1- Buɗewa
2- Sanya tafin hannun dama a kan na hagu, a kan ƙirji, yayin da zai ta shi tsaye, kafin ruku'u da bayan ruku'u.
3- Ɗaga hannaye, yana mai dunƙule yatsu da miƙe su, dai-dai da kafaɗu, ko kunnuwa ya yin kabbarar farko, da ya yin ruku'u da ɗagowa daga gare shi, hakanan ya yin tasowa daga tahiyyar farko zuwa ta uku.
6- Abinda ya ƙaru akan tasbihi ɗaya a cikin ruku'u da sujjada.
5- Abinda ya ƙaru a kan faɗar (Rabbana walakal hamdu) bayan ɗagowa daga ruku'u, da abinda ya ƙaru sama da ɗaya a addu'ar neman gafara tsakanin sujja biyu.
6- Sanya kai daidai da gadan baya a ruku'u.
7- Buɗa damatsa biyu daga gefe biyu, ciki daga kuma cinyoyi, da cinyoyi daga maƙyangyamai a cikin sujjada.
8-Ɗage sandunan hannaye daga ƙasa ya yin sujjada.
9- Zaman mai sallah a kan ƙafarsa ta hagu tana shinfiɗe, da kuma kafa ta dama a tahiyyar farko, da tsakanin sujjadu biyu.
10- Zaman (tawarruki) a tahiyyar ƙarshe, a cikin (sallah) mai raka'a huɗu da mai raka'a uku, shi ne zama akan mazauninsa, da sanya ƙafarsa ta hagu a ƙarƙashin ta dama da kuma kafa ta dama.
11- Yin nuni da ɗanyatsa manuni a tahiyyar farko da ta biyu, tun daga lokacin zama zuwa ƙarshen tahiyyar, da kuma motsa su ya yin addu'a.
12- Yin salati da addu’ar albarka ga (Annabi) Muhammad, da alayansa hakanan ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim a tahiyyar farko.
13- Addu'a a tahiyyar ƙarshe.
14- Bayyanar da karatu a sallar Asuba, da sallar Juma'a, da sallar Idi biyu, da sallar roƙon ruwa, da kuma raka'o'i biyun farkon sallar Magariba da Isha'i.
15- Boye karatu a Azahar, da La'asar, da kuma raka'a ta uku ta sallar Magariba, da raka'o'i biyun ƙarshe na sallar Isha'i.
16- Karatun a binda ya ƙaru akan Fatiha daga Alƙur’ani, tare da kiyaye abinda ya ragu na daga sunnoni a cikin sallah banda abinda muka ambata, yana daga haka: Abinda ya ƙaru akan faɗar mai sallah: (Rabbana walakal hamdu), bayan ɗagowa daga ruku'u, a haƙƙin limam da mai bi, da mai sallah shi kaɗai, cewa hakan sunna ce, kuma yana daga cikin Sunnar, ɗora hannaye a kan gwiwoyi biyu yatsunsu a warware yayin ruku'u.
DARASI NA SHA DAYA: ABUBUWA MASU ƁATA SALLAH.
Su takwas ne:
1- Magana da gangan tare da yana sane kuma ya san hukunci, amma mai mantuwa da wanda bai sani ba, sallarsa ba ta ɓaci da haka.
2- Dariya.
3- Cin (abin ci)
4- Shan (abin sha).
5- Yayewar al'aura.
6- Bauɗewa mai yawa, daga ɓangaren alƙibla.
7- Wasa mai yawa mai jerantuwa a cikin sallah.
8- Warwarewar tsarki.
DARASI NA SHA BIYU: SHARUƊƊAN ALWALA.
Su goma ne:
Musulinci, da hankali, da ganewa da niyya, da kasantuwa cikin hukuncinta, wato kada yayi niyyar yanketa har alwalarsa ta cika, da yankewar abinda ke wajabta al'wala, da tsarkin ruwa ko na hoge kafin shi, da ruwa mai tsarki da halarcinsa, da gusar da abinda ya ke hana kaiwarsa zuwa fata, da shigar lokacin sallah, a haƙƙin wanda karinsa dawwamamme ne.
DARASI NA SHA UKU: FARILLAN ALWALA.
Su shida ne:
Wanke fuska,akwai kuskurar baki da shaƙa ruwa suna daga cikin shi, da wanke hannaye tare da gwiwar hannaye, da shafar dukkanin kai, kunnuwa suna daga cikin shi, da wanke ƙafafuwa tare da idanuwan sawu, da jerantawa da bibbiya. Ana son maimaita wanke fuska, da hannaye, da ƙafafuwa sau uku, hakanan kuskurar baki, da shaƙa ruwa, (wankewa) sau ɗaya ita ce farillah a hakan, amma shafar kai ba'a son mai-maita shi, kamar yadda hadisai ingantattu suka yi nuni a bisa haka.
DARASI NA SHA HUƊU: ABUBUWAN DA SUKE WARWARE ALWALA.
Su shida ne:
Abinda ke fita daga hanyoyi biyu, da abinda ke fita mai muni, najasa daga jiki, da gushewar hankali, da bacci ko waninsa, da shafar farji da hannu, ya kasance gaba ne ko baya (dubura) ba tare da kariya (tufafi) ba, da cin naman raƙumi, da fita daga Musulinci, Allah Ya tsare mu da musulmai daga haka.
Faɗakarwa mai mahimmanci: Amma wanke mamaci: ingantacciyar (magana) cewa shi ba ya warware alwala, ita ce maganar mafi yawan ma'abota ilimi, saboda rashin wani dalili a bisa haka, sai dai da ace hannun mai wankan zai shafi al'aurorin mamacin ba tare da kariya ba, to alwala ta wajaba a kansa.
Abinda ke wajibi a kansa, kada ya shafi al'aurorin mamacin sai ta bayan kariya (kamar safar hannu), haka nan kuma shafar mace ba ta warware alwala a sake, daidai ne hakan ya kasance da sha’awa ne, ko ba tare da sha'awa ba, a mafi ingantacciyar maganganu biyu na malamai, matuƙar dai wani abu bai fito daga gare shi ba, domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya sumbaci sashin matansa sannan ya yi sallah bai yi alwala ba.
Amma faɗar Allah - Maɗaukakn sarki - a cikin ayoyi biyu na (Suratun) Nisa’i da Ma’idah: (ko kuka shafi Mata) [al-Nisa’i: 43] [al-Ma'ida: 6-], Abin nufi da shi: Iima'i, a mafi ingancin faɗar malamai, shi ne faɗin Ibnu Abbas- Allah Ya yarda da su -, da wasu jama'a daga (salaf) magabata da (Khalaf) mamaya. Allah Shi ne Majiɓincin datarwa.
DARASI NA SHA BIYAR: YIN ADO DA ƊABI'U ABABAN SHAR'ANTAWA GA KOWANNE MUSULMI.
Yana daga cikin su: Gaskiya da amana, da kamewa, da kunya. da sadaukantaka, da karamci, da cika alƙawari, da tsarkaka daga dukkan a binda Allah Ya haramta, da kyakkyawan maƙwabtaka, da taimakawa ma'abota buƙata gwargwadan iko, da wanin haka na daga ɗabi'u waɗanda Alƙur'ani ko Sunna suka yi nuni abisa shar'antuwarsu.
DARASI NA SHA SHIDA: LADABTUWA DA LADUBBAN MUSULUNCI.
Yana daga cikin laduban Musulinci : Sallama, da sakin fuska, da ci da dama da kuma sha da ita, da yin Bismillah ya yin farawa, da godiya ga Allah a ya yin gamawa, da godiya bayan yin atishawa, da yi wa mai atishawa barka (addu'a) idan ya godewa Allah, da gaida mara lafiya, da bin jana'iza don yi mata sallah da binne ta, da laduban shari'a lokacin shiga masallaci ko gida da (lokacin) fitowa daga cikin su. Haka kuma yayin tafiya, da (yin ladabi) tare da mahaifa da makusanta da maƙwabta, da manya da ƙanana, da taya murna na abin haihuwa, da addu’ar albarka a aure da bada haƙuri a masifu, da wanin haka na daga ladubban Musulunci a wajen sa tufafi da cirewa, da sa takalmi.
DARASI NA SHA BAKWAI: GARGAƊI AKAN SHIRKA DA NAU'O'IN SAƁO.
Yana daga cikin su; Abubuwa bakwai masu halakarwa, sune: Yi wa Allah tarayya da wani, da tsafi, da kashe ran da Allah Ya haramta sai da gaskiya, da cin riba, da cin dukiyar maraya, da juyawa ranar garkon yaki, da yi wa katangaggun mata rafkanannu mu'uminai ƙazafi.
Kuma yana daga cikin su: Saɓawa iyaye, da yanke zumunci, da shaidar zur (ƙarya) da rantse-rantse na ƙarya, da cutar da maƙwabci, da zaluntar mutane a jinane da dukiyoyi da mutunci, da shan abu mai sa maye, da caca, da yi da wani, da annamimanci, da wanin haka, daga abinda Allah-Mai girma da ɗaukaka Ya yi hani a kansa ko manzanSa-tsra da amincin Allah su tabbata a gare shi-.
DARASI NA SHA TAKWAS: SHIRYA MAMACI DA YI MASA SALLAH DA BINNE SHI.
Ga bayanan kamar haka:
Na farko: An shar'anta laƙƙanawa mai gargara: (Laa ilaha illah); saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - (ku laƙƙanawa matattunku: Laa ilaha illallah.) [7] Muslim ne ya rawaito shi a cikin Sahih ɗin sa. Abin nufi da matattu a cikin wannan Hadisin: Masu gargara, su ne waɗanda alamomin mutawa suka bayyana a gare su. [7] Muslim ne ya fitar da shi, a lambobi na (916-917).
Na biyu: idan mutuwarsa ta tabbata, sai a rufe idanuwansa, a kuma a daure gemunsa, saboda tabbatuwar sunna da hakan.
Na uku: Yi wa mamaci musulmi wanka yana wajaba, sai dai idan ya kasance shahidi ne da ya mutu a wurin yaki, haƙiƙa shi ba'a yi masa wanka, kuma ba'a yi masa sallah, a'a ana binne shi ne a tufafinsa, domin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai wanke waɗanda aka kashe a Uhudu ba, kuma bai yi musu sallah ba.
Na huɗu: Siffar wanke mamaci: A suturce al'aurarsa, sannan a ɗago shi kaɗan, ana tatso cikinsa, tatsa mai sauƙi (wato a hankali), sannan mai yin wankan ya naɗa kyalle ko waninsa a hannunsa, sai ya yi masa tsarki, sannan ya yi masa alwala, irin alwalar sallah, sannan ya wanke kansa da gemunsa da ruwa da magarya, ko makamancinsa, sannan ya wanke tsaginsa na dama, sannan na hagu, sannan ya wanke shi kamar haka na biyu da na uku, yana tafiyar da hannunsa a kan cikinsa a kowacce wankewa, idan wani abu ya fito daga gare shi sai ya wanke shi, ya kuma toshe wurin da audiga ko waninta, idan kuma bai kame ba, to da baƙar laka, ko da wasu hanyoyi na likitancin zamani, kamar gam, ko makamancinsa.
Ya sake yi masa alwala, idan kuma bai tsarkaka ba da (wankewa) uku, sai a ƙara zuwa biyar, ko zuwa bakwai, sannan ya tsane shi da wani tufafi, ya sanya turare a wuraran da ruwa ba ya zuwa gare su, da gaɓɓan sujjadarsa, idan kuma ya sanya turare a dukkan jikinsa, hakan yana da kyau, ana yi wa linkafanansa turaren hayaƙi, idan kuma gashin bakinsa ko faratansa masu tsawo ne, sai a rage su, kuma babu laifi idan anbarsu a yadda suke, ba a sakin (taje) gashinsa, ba a kuma aske mararsa, ko yi masa kaciya (shayi) saboda rashin dalili a bisa haka, mace kuma ana tufke gashinta tufka uku, a sake su a bayanta.
Na biyar: Sa wa mamaci likkafani
Abinda ya fi falala a yi wa namji linkafani a tufafi uku farare, babu riga ko rawani a cikinsu, kamar yadda akayiwa Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- ana shigar da shi a cikinsu shigarwa, idan kuma aka yi masa likkafanin a riga da kwarjalle da lifafa to babu laifi.
Mace kuma anayi mata likkafani a tufafi biyar: Riga, da mayafi, da kwarjalle, da lifafai biyu. Ana yiwa yaro likkafani a tufafi ɗaya zuwa uku, ana yi wa yarinya kuma likkafani a riga da lifafi biyu.
Abinda ya ke wajibi a haƙƙin dukkannin (mamatan) tufafi guda ɗaya, da zai suturce dukkan mamacin, sai dai idan mamacin ya kasance mai harama ne da (Hajji ko Umra) to haƙiƙa shi ana wanke shi da ruwa da magarya, a yi masa likkafani a kwarjallensa da mayafinsa, ko da waninsu, ba za a rufe kansa ko fuskarsa ba, ba za a sa masa turare ba, domin za a tashe shi ranar Alƙiyama yana Talbiyya, kamar yadda ya inganta da haka daga Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -. Idan kuma mai haramar ta kasance mace ce ana yi mata likkafani kamar waninta, sai dai ba a sa mata turare, ba a kuma rufe fusksrta da Nikabi, ko hannayemta da safa, sai dai ana rufe fuskarta da hannayenta da likafanin da aka sata a cikinsa, kamar yadda bayanin siffar yi wa mace likafani ya gabata.
Na shida : Mafi cancantar mutane a yi wa mamaci wanka da sallah da binne shi.
Wasiyyinsa (wato wanda ya yi wasiyya da ya yi masa wanka), a haka, sannan Uba, sannan Kaka, sannan mafi kusanci daga Asibai (dangin uba) a haƙƙin namiji.
Kuma mafi cancanta da yi wa mace wanka: (Wasiyyiyarta) wacce ta yi wasiyya da ta yi mata wanka, sannan uwa, sanan kaka (mace), sannan mafi kusanci sai mafi kusanci cikin mata. Kuma ya halatta ga ma'aurata biyu ɗayansu ya wanke ɗayan, domin Siddiƙu (wato sayyidina Abubakar) - Allah Ya yarda da shi - matarsa ce ta yi masa wanka, kuma domin cewa (Sayyidina) Aliyu - Allah Ya yarda da shi - shi ya wanke matarsa Nana Faɗima - Allah Ya yarda da ita -.
Na Bakwai: Siffar Sallah ga mamaci:
Zaiyi kabbara huɗu, ya karanta Fatiha a bayan ta farko, idan ya karanta gajeriyar sura ko aya ɗaya ko biyu tare da ita to abune mai kyau; saboda ingattaccen Hadisin da yazo akan hakan daga Ibn Abbas-Allah Ya yarda da su-, sannan yayi kabbara ta biyu yayi salati ga annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- kamar salatinsa a tahiyyah, sannan ya yi kabbara ta uku, ya ce: (Ya Allah Ka gafartawa rayayyunmu da mamatanmu, da mahalartanmu waɗanda suke anan, da waɗanda basa nan, da ƙaramin mu da babban mu, da namijin mu da macen mu, ya Allah wanda zaKa rayashi daga cikinmu to ka rayashi akan Musulunci, wanda zaKa karɓi ransa daga gare mu, Ka karɓe shi a bisa imani, Allah Ka gafarta masa, Kaji ƙansa, Ka kare shi, Ka yafe masa, Ka girmama masaukinsa, Ka yalwata mashigarsa, ka wanke shi da ruwa da ƙanƙara, ka tsarkake shi daga kurakurai, kamar yadda ake tsarkake farin tufafi daga datti, Ka canza masa gida mafi alkhairi daga gidansa da ahali (iyali) fiye da Ahalnsa, ka shigar da shi Aljanna, ka tsare shi daga azabar kabari, da azabar wuta, ka yalwata masa a kabarinsa, ka haskaka masa cikinsa, ya Allah kada ka haramta mana ladansa kada kuma ka batar damu a bayansa). Sannan ya yi kabbara ta huɗu, ya yi sallama, sallama ɗaya a damarsa.
Ana son ya ɗaga hannayensa a kowacce kabbara, idan mamacin ya kasance mace ce ana cewa: (Allahumma ighfir laha ...) har izuwa ƙarshe, idan kuma jana'izar ta kasance ta mutane biyu ce, ana cewa: ( Allahumma ighfir lahuma...) zuwa ƙarshe, zai yi amfani da lafazin jam'i idan jana'izar tafi haka yawa, ana cewa: (Allumma ghfir lahum) har zuwa ƙarshe, amma idan ya kasance yaro ne, maimakon yi masa addu'a da neman gafara sai ace: (Ya Allah Ka sanya shi lada magabaci, kuma ajiya ga mahaifansa, kuma mai ceto abin amsawa, ya Allah Ka nauyaya ma'aunansu da shi, Ka girmama ladansu da shi, kuma Ka riskar da shi da managartan magabatan muminai, Ka sanya shi a cikin rainon (Annabi) Ibrahim-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, Ka kare shi da rahamarKa daga azabar Jahannama).
Abinda yake sunna shi ne limami ya tsaya daura (daidai) da kan namiji, mace kuma a tsakiyarta, idan kuma mamatan sun haɗu (maza da mata) sai namji ya kasance shi zai biyo liman, mace kuma ta biyo alƙibla. Idan kuma akwai yara tare da su, sai a gabatar da yaro (namiji) akan babbar mace, sannan babbar mace, sannan yarinya, kan yaron yana kasancewa daura da kan babban namiji, tsakiyar mace kuma daura da kan namiji, haka nan kuma kan yariya yana kasancewa ne daura da kan mace, tsakiyarta kuma ya kasnce daura da kan namiji. Dukkanin masu sallah suna kasancewa a bayan liman, sai dai idan wani bai sami wuri a bayan liman ba, to shi zai tsaya ne a damarsa.
Na Takwas: Siffar binne mamaci:
Abin shar'antawa shine zurfafa ƙabari zuwa tsakiyar namiji, kuma Lahad ya kasance a cikinsa daga ɓangaren (bangon) alƙibla, kuma a sanya mamaci a cikin Lahad ta ɓangaran gefansa na dama, sai a warware ƙulle-ƙullen likkafani, amma kada a zare su, a'a a barsu, ba'a kuma yaye fuskarsa, daidai ne mamacin ya kasance namiji ne ko mace ce, sannan a kafa tubalai a kansa, a yaɓe da taɓo, har sai ya tsaya ya kuma kare shi daga (zubar) turɓaya, idan kuma tubalan basu samu ba, to, sai a canza hakan da waninsu na daga alluna, ko duwatsu ko katako da zai kare shi daga turɓaya, sannan a zuba ƙasa a kansa, kuma ana so a ce yayin hakan :(da sunan Allah kuma akan addinin manzan Allah). Ana daga kabarin kamu daya, kuma ana sanya tsakkuwa akansa in hakan ya saukaka, ana kuma yayyafa masa ruwa.
Ana shar'antawa ga masu rakiya da su tsaya a wajen ƙabarin su yi addu'a ga mamacin, domin Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kasance idan ya gama binne mamaci yana tsayawa a kansa, kuma ya ce: (Ku nemawa ɗan uwanku gafara, ku roƙa masa tabbatuwa (ya yin amsa tambaya), domin shi yanzu za'a tambaye shi.) [8]. [8] Abu Dawud ya fitar da shi, a lamba ta (3221), da Hakim (3/399).
Na Tara; Kuma an shar'anta ga wanda bai yi sallah a gare shi ba, da ya yi sallah a gare shi bayan binnewa;
Domin Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya aikata haka, a bisa cewa hakan ya kasance kamar wata (ɗaya) ko ƙasa da haka, idan lokacin ya kasance yafi haka, ba'a shar'anta sallah a kan ƙabari ba, domin cewa ba a ruwaito daga Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- cewa yayi sallah ga wani ƙabari bayan wata (ɗaya) da binne mamacin ba.
Na Goma: Ba ya halatta ga ‘yan uwan mamaci su yi abinci ga mutane; Saboda faɗar Jarir ɗan Abdullah al-Bajali sahabi mai girma-Allah Ya yard da shi-: "Mun kasance muna lissafa taruwa ga iyalan mamaci, yin abinci bayan binne (mamaci) yana daga kukan mutuwa". [9] Imamu Ahmad ne ya rawaito shi da sanadi kyakkyawa. [9] Ibnu Majah ya fitar da shi, a lamba ta (1612) da Imamu Ahmad (2/204).
Amma yi musu abin ci su (ahalin mamacin) ko ga baƙinsu babu laifi, kuma an shar'anta ga makusantansa da maƙwabtansa da suyi abinci su kai musu; domin Annabi-tsira da amincin Allah su tabbabata a gare shi- yayin da labarin mutuwar Ja’afar ɗan Abi Ɗalib -Allah Ya yarda da shi- yazo masa a Sham ya umarci iyalinsa da su yi abinci ga iyalan Ja’afar, kuma ya ce: (Haƙiƙa abinda zai shagaltar da su ya zo musu) [10]. [10] Muslim Al-jana'iz (976), Nasa'i, Aljana'iz (2034), Abu Dawud Aljana'iz (3234), Ibnu Majah, abinda ya zo a cikin Al-jana'iz (1569), Ahmad (2/441).
Kuma babu laifi ga iyalan mamacin da su kirawo maƙwabtansu, ko waninsu don cin abincin da aka kawo musu, babu lokaci iyakantacce ga hakan cikin abinda muka sani na shari'a.
Na sha ɗaya: Ba ya halatta ga mace ta bar ado (don mutuwar) wani mamaci sama da kwana uku sai ga mijinta.
Lalle yana wajaba tabar ado (don mutuwar mijinta) wata huɗu da kwana goma, sai dai in ta kasance mai ciki ce, to (zata bar adon) zuwa haife cikinta, saboda tabbatar sunna ingattacciya daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da hakan.
Amma namji to baya halatta ya bar ado (don mutwar) wani daga makusantansa ko waninsu.
Na sha Biyu; Ana shar'antawa ga maza ziyarar kabarurruka (maƙabarta), lokaci zuwa lokaci, don yin addu'a a gare su, da nema musu jin ƙai, da tuna mutuwa da abinda ke bayanta;
Saboda faɗar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "Ku ziyarci ƙabarurruka (maƙabarta), domin suna tunatar da ku Lahira". [11] Muslim ne ya fitar da shi a cikin ingantaccen littafinsa. [11] Ibnu Majah ya fitar da shi, a lamba ta (1569), kuma Albani ya inganta shi.
Annabi-tsira da aminciin Allah su tabbata a gare shi-ya kasance yana koyawa sahabbansa idan sun ziyarci ƙabarurruka (maƙabarta) da su ce: "Assalamu Alaikum ahlad diyar minal mu'uminin wal muslimin, wa innā in Shaa Allahu bikum lāhiƙun, nas'alullāha lanā wa lakumul afiyah, yarhamul lāhul mutaƙaddimina minna wal musta'akhirin." (Aminci ya tabbata a gare ku ma'abota gidaje daga muminai da musulmai, mu ma in Allah Ya so masu riskuwa ne da ku, muna roƙon Allah yafiya mu da ku, Allah Ya jiƙan magabata daga gare mu da masu jira.) [12] [12] Muslim ne ya fitar da shi, a lamba ta (975).
Amma mata, ziyarar kabarurruka (maƙabarta) ba ta halatta a gare su, domin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya tsinewa mata masu ziyartar maƙabarta, kuma domin cewa su, ana tsoron fitina da ƙarancin haƙuri a ziyararsu, hakanan kuma bin jana'iza zuwa maƙabarta ba ya halatta a gare su, domin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana su yin hakan. Amma yin sallah ga mamaci a cikin masallaci, ko a filin sallah, ita abar shar'antawa ce, ga maza da mata baki ɗaya.
Wannan shi ne ƙarshen abinda tattarashi ya sawwaƙa. Allah Ya Yi tsira da aminci ga annabinmu Muhammadu, da alayansa da sahabbansa.