كيفية صلاة النبي - صلى الله عليه وسلم -
SIFFAR SALLAR ANNABI
SIFFAR SALLAR ANNABI
Shehin Malami
AbdulAziz ɗan Abdullah ɗan Baaz
Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai
Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah Shi kaɗai, tsira da aminci su tabbata ga bawanSa kuma manzonSa Annabimmu Muhammad da alayansa da sahabbansa. Bayan haka:-
Waɗannan wasu taƙaitattun kalmomi ne akan bayanin siffar sallar annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ina son in gabatar da su ga dukkanin musulmi da musulma, domin duk wanda ya gani ya yi ƙoƙarin koyi da shi a cikin hakan, saboda faɗin sa -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: (Ku yi sallah kamar yadda kuka ga ina yin sallah) ([1]) Ga bayanin hakan ga mai karatu: () Bukhari ne ya ruwaito, a lamba ta (605).
1. Zai kyautata alwala, shi ne yayi alwala kamar yadda Allah Ya umarce shi, don yin aiki da faɗinSa - Tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -: {Ya ku waɗanda suka yi imani, idan kun tashi za ku yi sallah, to, ku wanke fuskokinku da hannayenku zuwa gwiwoyi, kuma ku shafi kawunanku, kuma (ku wanke) ƙafafunku zuwa idon sawu} ([2]) [al-Ma'ida: 6]. Zuwa ƙarshen ayar.
Da faɗin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: (Ba’a karɓar sallah ba tare da tsarki ba) ([3]). () Muslim ne ya ruwaito, a lamba ta (224).
Da faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ga wanda ya ɓata sallar sa: Idan ka tashi za ka yi sallah, to ka kyautata alwala([4]) () Bukhari ya ruwaito, a lamba ta (5782).
2- Wanda zai yi sallah zai fuskanci alƙibla, ita ce Ka’abah, duk ta inda yake da dukkanin jikinsa, yana nufin yin sallar da zaiyi ta da zuciyarsa ta farilla ko nafila, ba zai furta niyya da harshensa ba, domin ba a shar’anta furta niyya ba, bari ma dai yin hakan bidi’a ne, saboda Annabi - tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi - bai furta niyya ba haka nan sahabbansa - Allah Ya yarda da su -, sai ya sanya sutura da zai yi sallah gare ta idan ya kasance liman ne ko shi kaɗai yake sallah. Fuskantar alƙibla sharaɗi ne a sallah, saidai a wasu mas’alolin da aka togance kuma sanannu da a ka yi bayaninsu a littattafan malamai.
3. Yana yin kabbarar harama yana cewa: Allahu Akbar, yana mai kallon inda zai yi sujjada da idanuwansa zuwa bigiren sujjadarsa.
4. Yana ɗaga hannuwansa daura da kafaɗunsa ko daidai da kunnuwansa.
5. Ya sanya hannuwansa a ƙirjinsa, na dama akan tafin sa na hagu, da wuyan hannu da damtse, saboda tabbatuwar hakan daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.
6. An sunnanta, (mai sallah) ya karanta addu’ar buɗe sallah, ita ce: (Ya Allah Ka nisantar da ni da laifuka na kamar yadda Ka nisantar da gabas da yamma, Ya Allah Ka tsaftace ni daga kurakuraina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti, ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwa da ƙanƙara da ruwa mai sanyi) ([5]) [4] Bukhari ne ya rawaito shi, a lamba ta (744), da Muslim, a lamba ta (598).
Idan kuma ya ga dama maimakon hakan sai ya karanta: (Tsarki ya tabbata a gareKa Ya Ubangiji haɗi da gode maKa, kuma sunanKa ya daukaka, kuma ikonKa ya burunƙasa, babu abin bautawa in ba Kai ba) ([6]). Idan ya yi wani lafazin na buɗewar sallah da ya tabbata daga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - babu laifi. Abinda yafi, ya aikata wannan a wani lokaci ya kuma yi waccan a wani lokacin; domin hakan ya fi cika wurin bi, sannan sai ya ce: Ina neman tsarin Allah daga shaiɗan jefaffe. Da sunan Allah Mai yawan rahama Mai yawan jinƙai, sannan ya karanta Fatiha, saboda faɗinsa (tsira da amincin Allah su tabbata agare shi): (Babu sallah ga wanda bai karanta Fatiha ba)(7]) Sai ya ce : Amin, bayan (ya karanta ta) a bayyane a cikin sallar da ake karatu a bayya ne, kuma a sirrance idan sallar a ɓoye ake yinta, sannan ya karanta abinda ya sawwaƙa gare shi na AlKur’ani. Abinda ya fi ya karanta bayan Fatiha a sallar Azahar da La’asar da Issha cikin tsakatsakin Mufassal, a Asuba cikin dogayan Mufassal, a Magariba kuma wani lokacin cikin dogayan Mufassal, wani lokacin kuma cikin gajerun Mufassal, don yin aiki da hadisan da suka zo akan hakan . ()Muslim ne ya rawaito shi, a lamba ta (399). () Bukhari ya ruwaito shi, a lamba ta (756).
7. Zai yi ruku’i yana mai yin kabbara kuma yana ɗaga hannayansa daura da kafaɗunsa ko kunnuwansa, yana mai sanya kansa daidai da gadon bayansa, yana ɗora hannayansa akan gwiwowinsa, yana mai wara yatsunsa, ya kuma nutsu a ruku’insa, yana mai cewa: Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mai girma. Abinda yafi shine ya maimaita faɗinta sau uku ko sama da haka, kuma an so ya ce tare da hakan: (Tsarki ya tabbata gareKa Ya Allah Ubangiji haɗi da gode maKa, Ya Ubangiji Ka gafarta min)([8]). () Bukhari ne ya ruwaito shi, a lamba ta (817), da Muslim, a lamba ta (484).
8. Yana ɗago kansa daga ruku’i yana mai ɗaga hannayansa zuwa kafaɗunsa ko daura da kunnuwansa, yana mai cewa: (Allah Yana jin wanda ya gode maSa) Idan ya kasance liman ko shi kaɗai ne sai ya ce a yayin da yake tasowa: (Ya Ubangijimmu godiya taka ce, godiya mai yawa daddaɗa mai albarka, cikin sammai da cikin ƙassai, da cike duk abinda Ka so bayan haka) ([9]). Bukhari ya ruwaito shi, a lamba ta (711), da Muslim, a lamba ta (598).
Amma idan ya kasance mamu ne, to a lokacin ɗagowa daga ruku'u sai ya ce: "Rabbana walakal Hamd”, zuwa ƙarshen abinda ya gabata, idan kuma kowannan su ya ƙara- wato liman da mamu da mai sallah shi kaɗai- (Ahlus Thaná’i wal majd, a haƙƙu má ƙálal abdu, wakulluná laka abdun. Allahumma Lá máni’a limá aaɗaita walá mu’uɗiya limá mana’a ta, walá yanfa’u zal jaddi minkal jaddu)([10]). To hakan yana da kyau, saboda tabbatar hakan daga gare shi. () Muslim ne ya ruwaito shi, a lamba ta (477).
Kuma an so ga kowannen su - wato liman da mamu da mai sallah shi kaɗai - an so ya sanya hannayansa a ƙirjinsa kamar yadda ya yi kafin tasowa daga ruku’i, saboda tabbatuwar abinda yake nuni akan hakan daga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cikin hadisin Wa’il ɗan Hujr da Sahal ɗan Sa’ad - Allah Ya yarda da su -.
9. Yana yin sujjada tare da kabbara, yana sanya gwiwowinsa kafin hannayansa, idan hakan ya sawwaƙa a gare shi, idan kuma yayi masa wahala, sai ya fara gabatar da hannayansa kafin gwiwowinsa, yana mai fuskantar da yatsun ƙafafuwansa da hannayansa zuwa alƙibla, yana mai haɗe yatsun hannuwansa yana miƙar da su, kuma (sujjudar) ta kasance akan gaɓɓai bakwai: goshi tare da hanci, da hannuwa da gwiwowi, da cikin yatsun ƙafafuwa, kuma ya ce: Subhana Rabbiyal Aalá. An sunnanta ya faɗi hakan sau uku ko sama da haka , kuma an so ya faɗa a tare da hakan: (Subhána Kallahumma wabi hamdiKa, Allahumma ghfirlí), Ya yawaita yin Addu’a, saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: (Amma a ruku’i to ku girmama Ubangiji a cikinsa, amma a sujjada to ku yi ƙoƙarin addu’a domin ya cancanci a amsa muku) ([11]) () Muslim ne ya ruwaito, a lamaba ta (479).
Ya roƙi Ubangijin sa alkhairan duniya da lahira, Daidai ne sallar ta kasance ta farilla ce ko ta nafila, ya kuma buɗe damattsansa daga ɓarin jikinsa, cikinsa kuma daga ɓarin cinyoyinsa, cinyoyinsa kuma daga ɓarin ƙwaurinsa, ya kuma ɗago hannayansa su bar ƙasa, saboda faɗin sa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - (Ku daidaita a sujjada, kada ɗayanku ya shinfiɗa hannuwan sa irin shinfiɗawar kare) ([12]) () Bukhari ne ya rawaito shi, a lamba ta (788), da Muslim, a lamba ta (493).
10. Yana ɗago kansa tare da kabbara, ya kuma shinfiɗa diddigensa na hagu sai ya zauna a kansa, ya kuma kafe ƙafarsa ta dama, ya ɗora hannayensa akan cinyoyinsa da gwiwowinsa, sai ya ce: (Ya Allah Ka gafarta mini, Ka ji ƙaina, Ka shiryar da ni, Ka azurtani, Kayi min afuwa, Ka gyara ni) ([13]) Ya kuma natsu a wannan zaman. () Tirmizi ne ya ruwaito shi a lamba ta (284), da Abu Dawud a lambta ta (850), da Ibnu Majah a lamba ta (898).
11. Yana yin sujjada ta biyu tare da kabbara, ya kuma yi hakan kamar yadda yayi a sujjada ta farko.
12- Yana ɗago kansa tare da kabbara, sai ya zauna zama ƙanƙani kamar zaman dake tsakanin sujjada biyu, ana kiransa da zaman hutu, wannan zaman mustahabbi ne, idan ya bari babu wani laifi akansa, babu wani zikiri ko wata addu’a a cikinsa, sannan ya yunƙura ya tashi tsaye zuwa raka’a ta biyu yana mai dogara akan gwiwowinsa idan hakan ya yiwu a gare shi, idan kuma yayi masa wahala ya dogara akan ƙasa, sannan ya karanta Fatiha da abinda ya sawwaƙa a gare shi na AlKur’ani bayan Fatihar, sannan ya yi kamar yadda ya yi a raka’a ta farko.
13. Idan sallar ta kasance mai raka’a biyu ce kamar sallar Asuba da Juma’a da Idi biyu, to sai ya zauna bayan ya ɗago kansa daga sujjada ta biyu yana mai kafa ƙafarsa ta dama yana kuma shimfiɗa ƙafarsa ta hagu, yana ɗora hannun sa na dama akan cinyarsa ta dama, yana naɗe yatsunsa baki ɗaya sai dai manuniya, sai yayi nuni da ita akan Tauhidi, idan ya naɗe ƙaramin yatsansa da wanda yake biye da shi na dama ya kuma lanƙwasa babban yatsa da na tsakiya yayi nuni da manuniya (kaɗai) hakan ma yayi kyau, saboda tabbatuwar duka siffofin biyu daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, abinda ya fi shi ne ya yi wannan a wani lokaci kuma ya yi wancan, sai ya ɗora hannun sa na hagu akan cinyarsa ta hagu da gwiwarsa, sannan sai ya karanta tahiya a wannan zaman, ita ce kuma: "Manyan gaishe-gaishe sun tabbata ga Allah, da salloli da tsarkakan abubuwa, aminci ya tabbata agareka ya kai wannan annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata a garemu da bayin Allah salihai, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ina shaida cewa (Annabi) Muhammadu bawanSa ne kuma manzanSa ne). Sannan ya ce: (Ya Allah Kayi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Kayi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai Kai abin yabo ne Mai girma, kuma Kayi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad kamar yanda Kayi albarka ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai Kai abin yabo ne Mai girma)([14]) () Bukhari ne ya ruwaito shi, a lamba ta (797), da Muslim a lamba ta (402).
Kuma ya nemi tsarin Allah akan abubuwa huɗu, sai ya ce: (Ya Allah ina neman tsarinKa daga azabar Jahannama da azabar ƙabari da fitinar rayuwa da ta mutuwa da fitinar Masihul Dajjal (Jujal)([15]) () Bukhari ne ya ruwaito shi a lamba ta (1311), da Muslim a lamba ta (588).
Sannan ya roƙi abinda yake so na alkhairan duniya da lahira, idan kuma yayi wa iyayansa addu’a ko wasunsu cikin al’ummar musulmai babu wani laifi, daidai ne sallar ta farilla ce ko ta nafila, saboda gamewar faɗin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a hadisin Ibn Mas’ud - Allah Ya yarda da shi-, lokacin da ya koya masa tahiya: (Sannan ya zaɓi addu’ar da ya fi so, sai ya yi)([16]). A cikin wani lafazin daban: (Sannan ya zaɓi abinda yake so sai ya roƙa)([17]). () Nasa’i ne ya ruwaito shi a lamba ta (1298). () Muslim ne ya ruwaito shi a lamba ta (402).
Wannan yana game dukkan abinda zai amfani bawa na alhairan duniya da lahira. Sannan yayi sallama a damansa da kuma hagunsa, yana cewa: Assalámu alaikum wa rahmatullah. Assalámu alaikum wa rahmatullah.
14. Idan sallar ta kasance mai raka’a ukuce kamar magariba, ko mai raka’a huɗu kamar Azahar da La’asar da Issha to sai yayi Tahiyar da aka anbata a ɗazu da kuma salati ga annbi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sannan ya yinƙura ya yashi yana mai dogara akan gwiwowinsa yana ɗaga hannayansa zuwa kusa da kafaɗunsa ko kunnuwansa, yana mai cewa: Allahu Akbar. Yana kuma ɗora hannuwan nasa akan ƙirjinsa kamar yadda ya gabata. Sai kuma ya karanta Fatiha kaɗai, idan kuwa ya karanta a raka’a ta uku da ta huɗu a Azahar ƙari akan Fatiha a wasu lokutan babu laifi, saboda tabbatuwar abinda yake nuni akan hakan daga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin hadisin Sa’id - Allah Ya yarda da shi -, idan kuma ya bar yin balati ga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a Tahiyar farko babu laifi, domin hakan mustabbi ne ba wajibiba ne a Tahiyar farko. Sannan yayi Tahiya bayan raka’a ta uku a sallar Magariba da kuma bayan raka’a ta huɗu a Azahar da La’asar da Issha’i kamar yadda ya gabata a sallah mai raka’a biyu. Sannan ya yi sallama a damansa da kuma hagunsa, ya kuma nemi gafarar Allah sau uku, sannan ya ce: (Ya Allah Kai ne aminci, daga gareKa aminci yake, alherinKa ya yawaita ya Ma’abocin girma da karamci) ([18]) Kafin ya juya ya fuskanci mutane idan ya kasance liman ne, sannan ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai Yake, ba Shi da abokin tarayya, mulki naSa ne, godiya ma taSa ce, kuma Shi Mai iko ne akan dukkan komai. Babu wata dabara babu wani ƙarfi face da (taimakon) Allah. Ya Allah babu mai hana abinda Ka bayar kuma babu mai bayar da abinda Ka hana, kuma ƙwazon mai ƙwazo baya anfani a wurinKa. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ba ma bautawa kowa sai Shi, ni’ima ta Sa ce da falala, da yabo mai kyau, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, muna masu tsarkake addini gare Shi, ko da kafirai sun ƙi) ([19]), () Muslim ne ya ruwaito shi, a lamaba ta (591). ()Muslim ne ya ruwaito shi, a lamba ta (402)
Sai ya yi tasbihi (Subhanallah,) talatin da uku, ya gode maSa (Alhamdulillah) kwatankwacin hakan, ya yi maSa kabbara (Allahu Akbar) kwatankwacin hakan, a cikon na ɗarin sai ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba Shi da bokin tarayya, mulki naSa ne, kuma godiya taSa ce, kuma Shi Mai iko ne akan dukkan komai. Kuma ya karanta Ayatul Kursiyy, da ƙulhuwallahu Ahad da Falaƙi da Nasi a bayan kowacce sallah, kuma an so a maimaita waɗannan surorin uku, sau uku bayan sallar Asuba da Magariba, saboda hadisan da suka zo akan haka daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Dukkanin waɗannan zikiran sunna ne ba farilla ba ne.
Kuma an shar’anta ga kowanne musulmi da musulma yin sallah (nafila) kafin sallar Azzahar raka’a huɗu, bayanta kuma raka’a biyu, da raka'a biyu bayan Magariba, da raka'a biyu bayan sallar Issha, da raka'a biyu kafin sallar Asuba, idan aka haɗa ya kama raka’a goma sha biyu. Waɗannan raka’o'in ana kiransu da Rawatib, domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana kiyaye su a halin zaman gida. Amma a halin tafiya, ya kasance ba ya yin su sai dai na sunnar alfijir da wuturi, domin - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana kiyaye su a halin zaman gida da kuma tafiya, abinda ya fi, a sallaci waɗannan (nafilfilin) Rawatib ɗin da wuturi a gida, idan yayi su a masallaci babu wani laifi, saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - (Mafificiyar sallar mutum a gidansa saidai ta farilla) ([20]) () Bukhari ne ya ruwaito shi, a lamba ta (6860).
Kiyayewa akan waɗannan raka’oin yana daga cikin sabubban shiga aljanna, saboda faɗin annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- (Wanda ya sallaci raka’o'i goma sha biyu a kowanne yini da dare, to za'a gina masa gida a aljannah sabo da su)([21]) () Muslim ne ya ruwaito shi a lamba ta (728).
Idan ya yi sallah raka’a huɗu kafin La’asar da biyu kafin sallar Magariba da kuma biyu kafin sallar Issha hakan yayi kyau, domin abinda yake nuni akan hakan ya inganta daga annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-. Idan kuma ya yi raka’a huɗu bayan Azahar da huɗu kafin ita (Azahar) shi ma abu ne mai kyau, saboda faɗinsa -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-: (Duk wanda ya kiyaye raka’a huɗu kafin Azahar da huɗu bayan ta, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya haramta masa wuta)([22]) Abin nufi, yana ƙara raka’ah biyu akan sunnah Ratiba bayan Azahar; domin abinda yake a Sunnah Ratiba raka’o'i huɗu ne kafin Azahar da raka’o'i biyu a bayanta. Idan ya ƙara raka’a biyu bayan haka, to abinda aka ambata a hadisin Ummu Habiba -Allah Ya yarda da ita - ya tabbata. () Ahmad ne ya ruwaito shi, a lamba ta (25547), da Tirmizi a lamba ta (393), da Abu Dawud a lamba ta (1077).
Allah Shi ne majiɓincin datarwa, tsira da amincin Allah su tabbata ga annabimmu Muhammad ɗan Abdullah da alayensa da sahabbansa da mabiyansa da kyautatawa har izuwa ranar sakamako,,,