Mafi Yawan Bincike
SIFFAR AIKIN HAJJI
RUBUTUN MAI GIRMA BABBAN MALAMI Allah Ya yi masa gafara da mahaifansa da musulmai Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, ina salati da salllama ga Annabinmu Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki ɗaya. Bayan haka: Lallai ni zan gabatar da abinda ya sawwaƙa na daga magana akan wani abu na aikin Hajji dangane da zuwan lokacinsa, ina mai fatan Allah Ya sanya aikin kowa da kowa ya zama tsarkakakke ga fuskarSa, kuma mai amfanarwa da kusantarwa zuwa gare Shi; lallai Shi Mai yawan kyauta ne Mai karamci.
These files are generated automatically from the book's text; their layout may differ from the printed edition.
SIFFAR AIKIN HAJJI
RUBUTUN MAI GIRMA BABBAN MALAMI
MUHAMMAD BIN SALIH AL-UTHAIMEEN
Allah Ya yi masa gafara da mahaifansa da musulmai
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, ina salati da salllama ga Annabinmu Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki ɗaya. Bayan haka:
Lallai ni zan gabatar da abinda ya sawwaƙa na daga magana akan wani abu na aikin Hajji dangane da zuwan lokacinsa, ina mai fatan Allah Ya sanya aikin kowa da kowa ya zama tsarkakakke ga fuskarSa, kuma mai amfanarwa da kusantarwa zuwa gare Shi; lallai Shi Mai yawan kyauta ne Mai karamci.
Magana akan aikin Hajji tana taƙaita ne a abinda ke tafe:
1- Hukunce-hukuncen da ke da alaƙa da tafiya.
2- Yaushe ne aka farlanta Hajji? kuma akan wa wajabcinsa ya wajaba?
3- Daga ina ne mai nufin yin aikin Hajji ko Umrah zai yi harama?
4- Nau’ukan aikin Hajji, da kuma mafificinsu.
6- Siffar Tamattu'i tun daga fara harama da Umrah har zuwa ƙarewar aikin Hajji a siffa taƙaitacciya.
6- Ɗawafin ban kwana.
7- Abubuwan da ihrami yake hanawa.
8- Hukuncin wanda ya aikata waɗannan abubuwan da aka hana.
9- Ziyarar masallacin Annabi.
HUKUNCE-HUKUNCEN DA KE DA ALAƘA DA TAFIYA
A yayin da ya zamana babu makawa yin Hajji sai da tafiya, bari ma dai shi kansa tafiya ce, ya zamo yana daga muhimman abubuwa mu yi magana dangane da sashen hukunce-hukuncen tafiya a nan. Akwai hukunce-hukunce da ke da alaƙa da tafiya, mafi muhimmancin su su ne masu saduwa da sallah, kuma suna taƙaita kamar haka:
(A)- A tsarki:
Yana wajaba ga mai tafiya ya yi tsarki da ruwa - in ya sameshi - a alwalarsa da sallarsa da kuma wankansa, idan bai sameshi ba to yayi taimama a bigire mai tsarki. Sai ya shafi fuskarsa da hannuwansa daga gare shi, sai ya bigi ƙasa bugu ɗaya, sannan ya shafi fuskarsa gaba ɗayanta da tafukansa, daga gefen 'yan yatsunsa zuwa wuyan hannunsa, shine mararrabar tafinsa daga zira'insa.
Da wannan zai kasance mai tsarki tsarki cikakke, ba ta ɓaci sai da abinda tsarkin ruwa yake ɓaci da shi, ko da samuwar ruwa. Idan ya yi taimama a sallar Azahar, kuma ya wanzu akan tsarkinsa har zuwa La'asar, sai ya yi sallar La'asar ba tare da taimama ba, hakan nan da ya wanzu akan tsarkinsa har zuwa Magariba da Isha'i, ya sallace su akan tsarkinsa ba tare da taimama ba.
Idan janaba ta kama mai tafiya, bai samu ruwa ba sai ya yi taimama, to janabar ta ɗauke, idan ya samu ruwa to janabar ta dawo, kuma wanka ya wajaba a kansa. Idan ya yi kari saboda fitsari ko bayan gida, kuma bai samu ruwa ba ya yi taimama, to karinsa ya ɗauke, idan ya samu ruwa karinsa ya dawo, kuma alwala ta wajaba a kansa; saboda hadisin: «Bigire mai tsarki shi ne ruwan alwalar musulmi, ko da bai sami ruwa ba (tsawon) shekara goma, idan ya sami ruwa to ya ji tsoron Allah ya shafi fatarsa da shi». A cikin wani hadisin daban: «Shi ne abin tsarkin musulmi». Ahmad ne ya rawaito shi, kuma Tirmizi ya ce: Hadisi ne kyakkyawa ingantacce[1]. Matafiyi zai yi shafa a huffunansa (tsawon) yini uku da dararensu saɓanin mai zaman gida, to shi yini ɗaya ne da dare ɗaya. [1] Abu Dawud ne ya fitar da shi a cikin littafin ɗahara, babin mai janaba ya yi taimama, lamba ta (332), da Tirmizi a cikin littafin ɗahara, babin abinda ya zo a taimama ga mai janaba, lamba ta (124), da Nasa'i a littafin ɗahara, babin yin salloli da taimama ɗaya, lamba ta (323), da Ahmad (5/146) daga hadisin Abu Zarrin. Wannan lafazin da aka ambata na farko na Bazzar ne (9/387) a lamba ta (3973).
(B)- A cikin sallar farilla:
Matafiyi zai yi sallah mai raka'o'i huɗu - su ne -: Azzahar, La'asar da Isha'i ta ƙarshe - raka'o'i biyu kaɗai, daga sanda ya fita daga garinsa har ya dawo, daidai ne tafiyar mai tsawo ce ko gajeriya. Ya zo cikin (Sahihul Bukhari) daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi -, ya ce: "Mun fita tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - daga Madina zuwa Makkah (ma'ana: a Hajjin ban kwana), ya kasance yana yin salloli raka'o'i biyu-biyu, har sai da muka dawo zuwa Madina. Na ce: Shin kun zauna a Makkah ne ɗan wani lokaci? Ya ce: Mun zauna (tsawon) kwana goma?"[2]. [2] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin yin ƙasaru babin abinda ya zo a yin ƙasaru, lamba ta (1081), da Muslim a littafin sallar matafiya da yi mata ƙasaru, lamba ta (693).
Ya zo kuma a cikinsa daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: "Allah Ya farlanta sallah sanda Ya farlantata, raka'o'i biyu-biyu, a lokacin zaman gida da kuma tafiya, sai aka tabbatar da sallar tafiya, aka yi ƙari a sallar zaman gida"[3]. [3] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin sallah, babin yaya aka farlanta sallah a Isra'i? Lamba ta (350), da Muslim a cikin littafin sallar matafiya da yi mata ƙasaru, lamba ta (685).
A wata riwayar tasa: "An farlanta sallah raka'o'i biyu, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi hijira, sai aka farlanta (raka'o'i) huɗu, aka bar sallar tafiya akan na farkon"[4]. [4] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin darajoji, babin daga ina suka fara rubuta tarihi? lamba ta (3935).
A Muslim kuma: "Sai aka tabbatar da sallar tafiya akan farillar farko"[5]. [5] Muslim ne ya fitar da shi a littafin matafiya, lamba ta (2/685).
Ba'a kiyaye daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba cewa ya cika (sallah) a tafiyarsa ko sau ɗaya, saboda haka ne mafi yawan malamai suka tafi akan cewa yin ƙasarun matafiyi a sallah mai raka'o'i huɗu zuwa raka'o'i biyu dole ne. Ya zo cikin (Sahihul Bukhari) daga Abdurrahman ɗan Yazid, ya ce:
"Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - ya yi mana sallah a Mina raka'o'i huɗu, sai aka faɗawa Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - hakan, sai ya yi istirja'i (ya ce Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un), sannan ya ce: Na yi sallah tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a Mina raka'o'i biyu, kuma nayi sallah tare da Abubakar - Allah Ya yarda da shi - a Mina raka'o'i biyu, kuma nayi sallah tare da Umar ɗan al-Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - a Mina raka'o'i biyu, kaicon rabo na inama dai ace raka'o'i biyu ne karɓaɓɓu canjin raka'o'i huɗu"[6]. Sai Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya sanya cikawar Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - cikin musibu; yayin da ya yi istirja'i gare shi, kuma ya bayyana cewa sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da sahabbansa biyu (Abubakar da Umar) akan saɓaninsa ne. [6] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin yin ƙasaru, babin sallah a Mina, lamba ta (1084), da Muslim a cikin littafin sallar matafiya, babin ƙasarun sallah a Mina, lamba ta (695).
Kuma lallai Usman - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana yin ƙasaru a Mina (tsawon) shekaru shida ko shekaru takwas na halifancinsa, sannan ya cika, kamar yadda ya zo a (Sahihu Muslim) daga hadisin Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ce: "Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi sallah a Mina sallalr matafiyi da Abubakar da Umar da Usman (tsawon) shekaru takwas - ko cewa ya yi: shekaru shida"[7]. Cikawarsa - Allah Ya yarda da shi - ta kasance saboda wani tawili ne da ya ganshi, kuma ruwayoyi da maganganun malamai sun saɓa a wancan tawilin. [7] Muslim ne ya fitar da shi a littafin sallar matafiya, babin ƙasarun sallah a Mina, lamba ta (18/694).
Amma idan matafiyi ya yi sallah a bayan limamin da yake cika sallah, to ya zama wajibi a kansa ya cika, ya zo cikin (Sahihu Muslim) daga Musa ɗan Salamah Al-Huzali, ya ce: "Na tambayi Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su : Ya ya zan yi sallah idan na kasance a Makkah, idan ban yi sallah tare da liman ba? sai ya ce: Raka'o'i biyu, sunnar baban Alƙasim - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -"[8]. [8] Muslim ne ya fitar da shi a littafin sallar matafiya, babin sallar matafiya da ƙasarun ta, lamba ta (688).
A cikinsa kuma daga Nafi'u, ya ce: "Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya kasance idan zai yi sallah tare da liman sai ya yi raka'o'i huɗu, idan kuma zai yi shi kaɗai sai ya yi raka'o'i biyu" [9]. [9] Muslim ne ya fitar da shi a littafin sallar matafiya, babin ƙasarun sallah a Mina, lamba ta (17/694).
Daidai ne ya shiga tare da liman tun daga farkon sallar ko daga tsakiyarta; saboda gamewar maganar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Abinda ku ka riska to ku sallata, kuma abinda ya kuɓuce muku to sai ku cika»[10]. [10] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin kiran sallah, babin kada ya yi gaggawa zuwa sallah, lamba ta (636), da kuma babin faɗar mutum: Sallah ta kuɓuce mana, lamba ta (635), da Muslim a littafin masallatai, babin an so zuwa sallah cikin kawaici da nutsuwa, lamba ta (602) (603) daga Hadisin Abu Huraira da Abu Ƙatadah.
Amma haɗa Azzahar da La'asar ko Magariba da Isha'i sunnah ne idan ya kasance a kan tafiya, wato idan ya kasance matafiyi; saboda abinda ya zo a (Sahihul Bukhari) daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: "Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance ya na haɗa sallar Azzahar da La'asar idan yana kan abin hawa, kuma yana haɗa Magariba da Issha'i" [11]. [11] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin yin ƙasaru, babin haɗa Magariba da Issha'i a tafiya, lamba ta (1107) da isnadi Mu'allaƙi.
Amma idan ya kasance ya sauka ne to sunnah ita ce kada ya haɗa; saboda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai kasance yana haɗa sallah a Mina ba; saboda shi ya kasance ya sauka ne, idan mutum ya haɗa to babu laifi, musamman ma idan ya buƙaci hakan; saboda wani aikin da zai yi ko bacci da zai huta a cikinsa, ya zo cikin (Bukhari da Muslim) daga Hadisin Abu Juhaifah - Allah Ya yarda da shi -,
cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fita daga wata ƙubbah da yake da ita a nan al-Abɗah a Makkah, Abu Juhaifah ya ce: Ya fita da garjin rana - ma'ana: Lokacin tsananin zafi - zuwa al-Baɗha'u, sai ya yi alwala, sannan ya sallaci Azzahar raka'o'i biyu, da La'asar raka'o'i biyu, hadisi[12]. [12] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin darajoji, babin siffar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, lamba ta (3553), da Muslim a littafin sallah, babin suturar mai yin sallah, lamba ta (503).
Ya zo cikin (Sahihu Muslim) daga Sa'id ɗan Jubair daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su -, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya haɗa (salloli) a wata tafiya da ya yi a yaƙin Tabuka, sai ya haɗa Azzahar da La'asar, Magariba da Isha'i, Sa'id ya ce: Sai na ce da Ɗan Abbas: Me yake nufi da hakan? ya ce: «Ya na nufin don kada ya ƙuntatawa al'ummarsa» [13]. Kuma yana da irin wannan Hadisin a cike daga Mu'az ɗan Jabal - Allah Ya yarda da shi - [14]. [13] Muslim ne ya fitar da shi a littafin sallar matafiya, babin haɗa salloli biyu a zaman gida, lamba ta (51/705). [14] Muslim ne ya fitar da shi a littafin sallar matafiya, babin haɗa salloli biyu a zaman gida, lamba ta (706).
Ma'anar «ƙuntatawa al'ummarsa» ya jefa ta cikin ƙunci da takura.
(C)- A sallar nafila:
An shar'antawa matafiyi yin taɗawwu'i da nafiloli kamar yadda mai zaman gida yake yi, zai yi sallar dare, da wutiri, da sallar walha, da Tahiyyatul masjid da sallar khusufi. Ya zo cikin (Sahihul Bukhari) daga Abdullahi ɗan Umar - Allah ya yarda da su -, ya ce:
"Na ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - idan yana halin tafiya sai ya jinkirta Magariba ya yi ta (raka'o'i) uku, sannan ya yi sallama, sannan zai zauna kaɗan har sai ya tayar da Issha'i, sai ya sallaceta raka'o'i biyu, sannan ya yi sallama, ba zai yi tasbihi (nafila) ba har sai ya tashi a tsakiyar dare" [15]. [15] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin yin ƙasaru, babin shin zai yi kiran sallah ko iƙama idan ya haɗa Magariba da Issha'i? lamba ta (1109), kuma Muslim ya fitar da shi a taƙaice a littafin sallar matafiya, babin halaccin haɗa salloli biyu a tafiya, lamba ta (703).
Ya zo cikin (Sahihaini - Bukhari da Muslim) daga Sa'id ɗan Yasar, ya ce: Na kasance ina tafiya tare da Abdullahi ɗan Umar a hanyar Makkah, sai Sa'idu ya ce: Yayin da na ji tsoron Asubah, sai na yi wutiri, sannan na haɗu da shi, sai Abdullahi ɗan Umar ya ce: A ina ka kasance? sai na ce: Na ji tsoron Asubah ne sai na sauka na yi wutiri, sai Abdullahi ya ce: Shin baka da kyakkyawan koyi ne daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -? sai na ce: ƙwarai wallahi, ya ce: To lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana yin wutiri akan raƙumi [16]. [16] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin wutiri, babin yin wutiri akan dabba, lamba ta (999), da Muslim a littafin sallar matafiya, babin halaccin sallar nafila akan dabba a halin tafiya, lamba ta (36/700).
A cikinsu kuma, daga Abdurrahman ɗan Abu Lailah, ya ce: Babu wanda ya taɓa faɗa min cewa ya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya na sallar walaha sai Ummuhani; domin cewa ita ta zantar cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiga ɗakinta a ranar Fathu Makkah, sai ya yi sallah raka'o'i takwas [17]. [17] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin yin ƙasaru, babin wanda ya yi (sallar) taɗawwu'i a tafiya ba'a bayan salloli (na farilla) ba, lamba ta (1103), da Muslim a littafin sallar matafiya, babin mustahabbancin sallar walaha, lamba ta (80/336).
A cikinsu kuma, daga Abu Ƙatadah - Allah Ya yarda da shi -, cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Idan ɗayanku ya shiga masallaci, to kada ya zauna har sai ya yi sallah raka'o'i biyu»[18]. [18] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin Tahajjudi, babin abinda ya zo na yin (sallar) taɗawwu'i (raka'o'i) biyu-biyu, lamba ta (1163), da Muslim a littafin sallah, babin mustahabbancin Tahiyyatul masjid, lamba ta (714).
A cikinsu kuma, daga Hadisin Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - a ƙissar sallar kusufi, cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Lallai rana da wata ayoyi ne guda biyu daga cikin ayoyin Allah, ba sa kisifewa saboda mutuwa ko rayuwar wani, to idan kun gan su - ma'ana: sun yi husufu -, to ku gaggauta yin sallah»[19]. [19] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin khusufi, babin huɗubar liman a khusufi, lamba ta (1046), da Muslim a littafin khusufi, babin sallar khusufi, lamba ta (901).
Waɗannan hadisan biyu gamammu ne, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai keɓance wani lokaci a kansu ba banda wani lokacin, haka nan zaman gida banda tafiya.
Ya kuma zo a cikin (Sahihul Bukhari), daga Jabir ɗan Abdullah -Allah Ya yarda da su -, ya ce: "Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana sallar taɗawwu'i alhali yana kan abin hawa, ba tare da ya fuskanci alƙibla ba"[20]. [20] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin yin ƙasaru, babin yin sallar taɗawwu'i akan dabba, lamba ta (1094).
(Al) cikin (al-Taɗawwu'u) tana ɗaukar jinsi, kuma tana ɗaukar gamewa, na biyun ya na ƙarfafa: Cewa asali shi ne wanzuwar taɗawwu'i da nafiloli akan shar'ancinsa har sai dalili ya zo akan barinsa, kuma dalili bai zo akan barin ba a abinda muka sani face a nafilolin bayan Azahar, da Magariba da Issha'i. Ya zo cikin (Sahihu Muslim) daga Hafs ɗan Asim ɗan Umar ɗan al-Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi -, ya ce: Na abokanci Ɗan Umar a hanyar Makkah, ya ce: Sai ya yi mana sallar Azahar raka'o'i biyu, sannan ya fuskanto muma muka fuskanta tare da shi har sai da ya zo masaukinsa, kuma ya zauna muma muka zauna tare da shi. Sai ya juyo da ganinsa inda ya yi sallar, sai ya ga waɗansu mutane a tsaye, sai ya ce: Me waɗannan suke yi? na ce: Suna yin Tasbihi ne - ma'ana: Suna yin sallar nafila -, ya ce: Da na kasance mai yin Tasbihi (wato sallar nafila), da na cika sallah ta, ya ɗan uwana. Lallai ni na abokanci Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a tafiya, bai yi ƙari akan raka'o'i biyu ba har Allah Ya karɓe shi. Kuma na abokanci Abubakar, bai yi ƙari akan raka'o'i biyu ba har Allah Ya karɓe shi, kuma na abokanci Umar, bai yi ƙari akan raka'o'i biyu ba har Allah Ya karɓe shi, sannan na abokanci Usman bai yi ƙari akan raka'o'i biyu ba har Allah Ya karɓe shi. Kuma haƙiƙa Allah Ya ce: (Lallai kuna da kyakyawan abin koyi tare da Manzon Allah) [21]. [al-Ahzab: 21]. [21] Muslim ne ya fitar da shi a littafin sallar matafiya, babin sallar matafiyi da ƙasarun ta, lamba ta (689), kamar yadda Bukhari ya fitar da shi a taƙaice a littafin yin ƙasaru, babin wanda ba ya yin taɗawwu'i bayan sallah a cikin tafiya, lamba ta (1101-1102).
Kuma ya rigaya daga hadinsa a cikin haɗawa tsakanin Magariba da Issha abinda yake nuni akan cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance bayayi musu sallah ratiba[22]. [22] Ambatonsa ya gabata (shafi na: 7).
Abin da Ɗan Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ke nufi da faɗinsa: «Da na kasance mai yin nafila da na cika». Ai: Da na kasance mai yin (sallar) taɗawwu'i da abinda farilla ta zata cika da shi daga nafiloli da na cika ta; da dalilin: cewa ya inganta daga gare shi - Allah Ya yarda da shi - cewa ya kasance yana (sallar) taɗawwu'i akan dabbarsa, kuma yana yin wutiri a kanta, kuma yana bada labarin cewa lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana yi.
Daga cikin tarjamomin Bukhari - Allah Ya yi masa rahma - a cikin (Sahihinsa): Babin wanda baiyi taɗawwu'i ba a cikin tafiya a bayan sallah da kuma gabaninta», da «Babin wanda ya yi taɗawwu'i a tafiya ba'a bayan sallah ba da kuma gabaninta».
Amma nafilar Alfijir (raka’atal Fajr), to zai sallace ta a halin zaman gida da tafiya; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bai kasance mafi tsananin riƙo akan komai ba daga gare shi na daga nafiloli, sama da raka'o'i biyu na Alfijir, kuma ba ya barinsu har abada, kamar yadda ya zo a cikin (Sahihul Bukhari), daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita (3/42) daga (al-Fathu)[23]. [23] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin Tahajjudi, babin lazimtar raka'o'i biyu na Alfijir, lamba ta (1169), da Muslim a littafin sallar matafiya, babin mustahabbancin raka'o'i biyu na sunnar Alfijir, lamba ta (94/724).
Ya kuma zo a cikin (Sahihu Muslim), daga Abu Ƙatadah - Allah Ya yarda da shi -, Cewa ya kasance tare da Annabi - tsira da aminicin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya ambaci ƙissar baccinsu da ya hana su yin sallar Asubah har rana ta ɓullo, kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce su, sai suka tashi daga inda suke, sannan ya sauka, sai ya yi alwala, sannan Bilalu ya yi kiran sallah, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi sallah raka'o'i biyu, sannan ya yi sallar safiya, sai ya yi kamar yadda ya saba yi a kowace rana[24]. [24] Muslim ne ya fitar da shi a littafin masallatai, babin rama sallar da ta kuɓuce, lamba ta (681).
Kuma daga gareshi daga Hadisin Abu Huraira [25] Muslim ne ya fitar da shi a littafin masallatai, babin rama sallar da ta kuɓuce, lamba ta (680).
Lallai mun tsawaita magana akan taɗawwu'in matafiyi da yin (sallar) nafila; domin wasu mutanen suna ganin cewa babu taɗawwu'i ga matafiyi kai tsaye, kuma haƙiƙa daga abinda muka ambata ya bayyana: Cewa abinda dalili ya nuna ba za a yi taɗawwu'i da nafilolin Azzahar da Magariba da Isha'i, amma wanin wannan daga nafiloli, to mai wanzuwa ne akan shar'artuwarsa, Allah ne Mai datarwa.
Matafiyi zai iya yin sallar taɗawwu'i a tafiya alhali yana kan abin hawansa duk inda fuskarsa take, ko da kuwa ba ya kallon alƙibla. Ya zo cikin (Sahihul Bukhari) daga Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da su -, Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana yin sallah akan dabbarsa tana fuskantar mahudar rana, idan ya yi nufin yin sallar farilla - ma'ana: Ta farilla - sai ya sauka, ya fuskanci alƙibla [26]. Bukhari ne ya fitar da shi a cikin littafin yin ƙasaru, babin mutum ya sauka don yin sallar farilla, lamba ta (1099).
Yana cikin hukunce-hukuncen tafiya: Ya kamata ya kasance matafiyi yana tare da ayari; don ɗebe kewa da tunkuɗe buƙata, bai kamata mutum ya yi tafiya shi kaɗai ba sai don wata buƙata ko maslaha ta Addini, don jihadi a tafarkin Allah da makamancinsa, ya zo a cikin (Sahihul Bukhari) daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -, cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Da mutane sun san abinda yake cikin kaɗaitaka irin abinda na sani, da matafiyi bai yi tafiya da daddare shi kaɗai ba»[27]. Bukhari ne ya fitar da shi a littafin jihadi, babin mutum ya yi tafiya shi kaɗai, lamba ta (2998).
Kuma ya kamata ya kasance a tare da shi akwai abinda zai tabbatar da sunansa da adireshinsa don kada a kasa gane shi idan ya rasu saboda hatsari ko waninsa.
Daga cikin hukunce-hukuncen tafiya kuma: Cewa ba ya halatta ga mace ta yi tafiya ba tare da muharrami ba, daidai ne tafiyar mai nisa ce ko ta kusa, Hajji ne ko waninsa, kuma duk ɗaya ne ta kasance budurwa ce kyakkyawa ko tsohuwa mummuna, tana tare da mata makusantanta da ƙawayenta ko bata tare da su, kuma daidai ne an rinjayar da zaton amincintakarta ko ba'a rinjayar ba, kuma duk ɗaya ne hakan a cikin jirgin sama ne ko waninsa. Ya zo a cikin (Sahihaini) daga Hadisin Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su -, ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana huɗuba, ya na cewe: «Kada wani namiji ya keɓe da wata mace face a tare da ita akwai muharrami, kuma kada mace ta yi tafiya face tare da ita akwai muharrami». Sai wani mutum ya miƙe, sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai matata ta fita Hajji, kuma lallai ni an sanya ni cikin yaƙin kaza-da-kaza, (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ka tafi ka yi Hajji tare da matarka»[28]. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana tafiyar mace ba tare da muharrami ba kai tsaye, kuma bai ƙayyade shi ba da wata tafiyar banda wata, ko wata macen banda wata, ko a wani halin banda wani, kuma mutumin baiyi cikakken bayani game da matarsa ba. Bukhari ne ya fitar da shi a cikin littafin jihadi, babin wanda aka rubutashi zai je yaƙi a cikin rundunar sojoji, sai matarsa ta fita aikin Hajji, lamba ta (3006), da Muslim a cikin littafin Hajji, babin tafiyar mace tare da muharrami, lamba ta (1341).
Muharrami: Mijin mace, da duk wanda aurenta ya haramta a gare shi haramci haramci na har abada saboda kusanci ne ko shayarwa ko surukantaka.
Muharramai na kusanci ko shayarwa su bakwai ne: Uba ko da kuwa ya ɗaukaka (kaka kakan kaka), ɗa koda kuwa ya sauka (Ɗa ɗan ɗa), ɗan uwa da ɗansa ko da kuwa ya sauka, ɗan 'yar uwa ko da kuwa ya sauka, Baffa (Ɗan’uwan uba) ko da kuwa ya ɗaukaka, da kawu (Ɗan’uwan uwa) ko da kuwa ya ɗaukaka.
Muharramai daga surukuta su huɗu ne: Baban mijin mata ko da kuwa ya ɗaukaka, ɗan mijin mata ko da kuwa ya sauka, mijin 'yar mata ko da kuwa ta sauka, na hudu: Mijin uwar mata ko da kuwa ta ɗaukaka, da sharaɗin: Ya kasance an yi dukhuli da ita (matar).
An sharɗanta cewa muharramin ya kasance baligi mai hankali, saboda haka halaccin yin tafiya ba ya isuwa tare da yaro da mahaukaci.
Akan wannan, idan mace bata samu muharrami ba, Hajji bai wajaba a kanta ba; domin ba ta da ikon yin tafiya zuwa gare shi.
Yaushe ne aka farlanta Hajji?
An farlanta aikin Hajji a shekara ta tara ko goma bayan hijira a mafi rinjayen zantukan malamai; domin farlancinsa ya zamo da faɗinsa - Maɗaukakin Sarki -: {Kuma akwai hajjin ɗãkin dõmin Allah a kan mutãne, ga wanda ya sãmi ĩkon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta to lalle Allah Mawadãci ne daga barin tãlikai}. [al-Imran: 97]. Wannan ayar tana farkon Suratu Ali Imran, ta sauka a shekarar tawaga, shekara ta tara daga hijira.
Hikimar jinkirta farlancinsa - Allah ne Mafi sani - cewa Makka - Allah Ya ƙara mata ɗaukaka - ta kasance a ƙarƙashin ikon mushrikain daga Ƙuraishawa kafin wannan shekarar. Don haka ba zai yi wu Annabi da sahabbansa su yi aikin Hajji ta fuska mafi cika ba, kuma lamarin Umrar Hudaibiyyah bai yi nisa ba, sai mushrikai suka hana Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da sahabbansa cika Umrar su a shekara ta shida bayan hijira.
Kuma Hajji farilla ne akan kowanne musulmi baligi, aƙili, mai ikon yin Hajji da dukiyarsa da kuma jikinsa.
Amma wanda bai balaga ba, to aikin Hajji ba ya wajaba a kansa, sai dai yana inganta daga gare shi, kuma yana da ladan Hajjin taɗawwu'i, amma idan ya balaga zai yi na farilla, domin Hajjinsa kafin balagarsa Hajji ne kafin lokacin da aka neme shi da yinsa, don haka kamar ya yi sallar farilla ne kafin lokacinta.
Wanda ya gajiya daga yin aikin Hajji da dukiyarsa - kamar talaka da bawa -, aikin Hajji ba ya wajaba a akansa; saboda faɗinsa - Maɗaukakin Sarki -: {Wanda ya sãmi ĩkon zuwa gare shi}. , kuma wannan ba mai iko ba ne, don haka ba ya wajaba a kansa.
Amma wanda ya kasa saboda jikinsa kaɗai, idan ba'a tsammanin gushewar kasawar ta sa- kamar tsufa da rashin lafiya mai ɗorewa-, to zai wakilta wanda zai masa aikin Hajjin, idan kuma ana tsammanin gushewar gajiyawar ta sa - kamar rashin lafiya da ta afka masa kwatsam -, to za'a jira har ya warke daga gare ta, sannan ya yi aikin Hajjin, idan ya rasu kafin wannan, to waɗanda ya bari su zasu yi masa aikin Hajjin (daga cikin dukiyarsa) da ya bari.
Kuma duk sanda aikin Hajji ya wajaba akan musulmi, to ya wajaba ya gaggauta yin sa; domin lamurran Allah da ManzonSa basu kasance ababen ƙayyadewa da wani lokaci ba, kuma babu wani dalili da ya yi nuni akan jinkirtasu, to sai a gaggauta aiwatar da su, saboda Hadisin Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su -, cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku gaggauta zuwa aikin ajji - ma'ana na farilla -, domin ɗayanku bai san abinda zai bujuro masa ba»[29]. Ahmad ne ya rawaito shi, amma a isnadinsa akwai rauni, sai dai zancen gaggauta yin sa yana da dalilai gamammu da suke ƙarfafa wannnan Hadisin. Ahmad ne ya fitar da shi a cikin al-Musnad (1/314).
Daga ina ne wanda ya yi nufin yin Hajji ko Umarah zai yi harama?
Wanda ya yi nufin yin Hajji ko Umra zai yi harama daga miƙatan da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya iyakance su -, su biyar ne:
Na farkon su: Zul Hulaifah - ana kiransa da: Abyar Ali - ga mutanen Madina da wanda ya wuce ta wurin daga waninsu.
Na biyu: Al-Juhfah - wata alƙarya ce tsohuwa da ta rushe, sai mutane suka sanya Rabigh a madadinta - ga mutanen Sham, da wanda ya biyo ta nan daga waninsu idan bai wuce ta Zul Hulaifah ba kafin ita.
Na uku: Yalamlamu - dutse ne ko wuri a Tihamah, ana kiransa da: As-Si'idiyyah - ga mutanen Yamen da wanda ya biyo ta nan daga waninsu.
Na huɗu: Ƙarnul Manazil - ana kiransa da: As-Sailu - ga mutanen Najd da wanda ya biyo ta wurin daga waninsu.
Na biyar: Zatu Irƙin - ana kiransa da: al-Daribahh - ga mutanen Iraƙi da wanda ya wuce ta wurin daga waninsu.
Wanda ya wuce ta waɗannan miƙatan alhali yana son yin aikin Hajji ko Umarah, ya wajaba a kansa ya yi harama.
Wanda kuma ya zo daura da su ta sararin samaniya (jirgin sama) ko kogi (jirgin ruwa), to ya wajaba a kansa ya yi harama idan ya zo daura da su. Ba ya halatta gare shi ya jinkirta harama har ya sauka a filin jirgin sama ko ya sauka a tashar ruwa; domin wannan yana daga ƙetare dokokin Allah. {Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to waɗannan su ne Azzãlumai}. [al-Baƙara: 229].
Wanda ba ya cikin waɗannan miƙatan a Makkah, to ya yi harama daga inda yake, har waɗanda suke a Makkah za su yi harama ne a Makkah sai fa ga Umrah, to za su yi harama ne a wajen Harami, wato: ta Bayan milamilan Hilli; saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabata a gare shi- ga Abdurrahman ɗan Abubakar: «Ka fita da 'yar uwarka - ma'ana: Nana Aisha - daga Harami, sai ta yi haramar yin Umarah »[30]. Bukhari ne ya fitar da shi a littafin Hajji, babin faɗin Allah - Maɗaukakin Sarki - ﴾Hajji watanni ne sannanu﴿, lamba ta (1560), da Muslim a littafin Hajji, babin bayanin nau'ikan yin harama, lamba ta (123/1211) daga hadisin Aisha - Allah Ya yarda da ita -.
Wanda ya wuce ta waɗannan miƙatan alhali ba yana nufin yin aikin Hajji ko Umarah ba - kamar me nufin yin kasuwanci ko ziyarar wani makusanci ko neman ilimi ko makamantansu - yin harama bai wajaba a kansa ba; domin aikin Hajji ko Umrah basa wajaba sama da sau ɗaya a rayuwa, kuma ba'a yin harama sai a Hajji ko Umrah.
Nau’ikan aikin Hajji, da kuma mafificinsu
Nau'ikan aikin Hajji uku ne: Tamattu'i, Ƙirani da kuma Ifradi.
Tamattu'i: Shi ne ya yi haramar yin Umrah a wattanin Hajji - wato bayan shigar watan Shawwal - kuma ya gama a cikinsu, sannan ya yi haramar yin Hajji a wannan shekarar.
Ƙirani: Shi ne ya haɗa aikin Hajji da Umarah, sai ya yi haramar su duka, ko ya yi haramar yin Umrah ita kaɗai, sannan ya shigar da aikin Hajji a cikinta kafin ya fara ɗawafinta.
Ifradi: Shi ne ya yi haramar yin aikin Hajji shi kaɗai.
Gamayyar malamai sun tafi akan cewa mutum yana da zaɓi tsakanin nau'ikan nan, amma sun saɓa a mafifici daga cikinsu, amma mafi ingancin magana: Mafifici shi ne Tamattu'i; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarci sahabbansa da shi, kuma ya kwaɗaitar da su a kansa, kuma domin shi ya fi zuwa da ayyuka da yawa; domin yana zuwa da ayyukan Umrah gaba ɗaya, da kuma ayyukan Hajji gaba ɗaya, kuma domin shi ya fi sauƙi daga sauran ga wanda ya iso Makkah da wuri; a yayin da zai ji daɗin (yin komai) bayan warware harami a tsakanin Umrah da Hajji.
Kuma yana wajaba a yi hadaya a Tamattu'i saboda godiya, ba saboda gyara ba, daga abinda zai isa a yanka kamar akuya ko ɗaya bisa bakwai na taguwa ko ɗaya bisa bakwai na saniya, zai yanka shi ranar idi ko kwanaki uku bayansa, kuma ya rarraba shi a Mina ko a Makkah, kuma ya ci daga gareshi. Idan bai samu ba to (ya yi) azumin kwana uku a cikin lokutan Hajjin, kada ya wuce kwanaki uku bayan idi da su, da kuma (azumin) kwana bakwai idan ya dawo (gida).
Me yin Ƙirani kamar me yin Tamattu'i ne a wajabcin yin hadaya ko canjinsa.
Siffar yin Tamttu'i daga fara haramar Umrah har zuwa ƙarewar Hajji a siffa taƙaitacciya.
(A) Umrah
1- Idan ya yi nufin yin haramar Umrah, sai ya yi wanka kamar yadda ake wankan janaba ya sanya mafi daɗin turaren da ya samu a kansa da gemunsa, kuma ya sanya kwarjalle da mayafi farare. Mace za ta sanya duk irin tufar da take so sai dai kada ta bayyana ado.
2- Sannan zai yi sallar farilla idan lokacin sallar farilla ne; dan ya yi harami a bayanta, idan ba lokacin farilla bane sai ya yi sallah raka'o'i biyu da niyyar sunnar alwala, bada niyyar sunnar harama ba; domin bai tabbata daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba cewa akwai wata sunnah ga harama.
3- Sannan idan ya idar da sallar, sai ya yi niyyar shiga cikin Umrah, sai ya ce: «labbaikal lahumma labbaika, labbaika la sharika laka labbaika, innalhamda wan ni'imata laka wal mulk, la sharika laka, labbaikl lahumma Umratan (AmsawarKa Ya Allah amsawarKa, AmsawarKa baKa da abokin tarayya amsawarKa, lallai godiya da ni'ima taKa ce, mulki ma naka ne, baKa da abokin tarayya, amsawarka Ya Allah, Umrah)», namiji zai ɗaga sautinsa da wannan, mace kuma zata ɓoye muryar.
An sunnanta yawan yin Talbiya har sai ya fara ɗawafi, sai ya yanke ta.
4- Idan ya je Makkah, sai ya fara ɗawafi daga lokacin da ya isa, sai ya nufi Alhajarul Aswad, ya shafe shi - wato: Ya shafe shi - da hannunsa na dama sannan ya sumbace shi in hakan ya sauƙaƙa ba tare da cunkoso ba, idan kuwa ba haka ba, to ya yi nuni gare shi, ya yi kabbara.
Sannan ya juya, sai ya sanya ɗakin Ka'abah a hagunsa, idan ya wuce ta Arruknul Yamani - shi ne rukuni na ƙarshe da zai wuce bayan Ruknul Hajar - sai ya shafe shi da hannunsa na dama in hakan ya sauƙaƙa ba tare da sumbata ba.
Saannan ya yi ɗawafi kewaye bakwai, namiji zaiyi sassarfa akewaye ukun farko, yayi Ibɗiba'i a dukkanin ɗawafan.
Arramlu: Shi ne gaggawa a tafiya tare da kusanto da taku.
Al-Idɗiba'u: shi ne ya sanya tsakiyar mayafinsa a ƙarƙashin hammatarsa ta dama, da gefen mayafin akan kafaɗarsa ta hagu.
Ya kuma ambaci Allah, ya yi maSa tasbihi a ɗawafinsa, ya roƙi abinda yake so cikin tsoro da halarto da zuciya, duk sadda ya zo Alhajarul Aswad to ya yi kabbara, kuma ya ce tsakanin Arruknul Yamani da Alhajarul Aswad: {Rabbana ãtina fid duniya hasanatan wafil ãkhiarti hasanatan waƙina azaban nãr (Yã Ubangijinmu! Ka bã mu mai kyau a cikin dũniya da mai kyau a cikin Lãhira, kuma Ka tsare mana azãbar wuta)}. [al-Baƙara: 201]. Amma ƙayyade wata addu'a ayyananna a kowanne kewaye, to ba shi da wani asali daga sunnah, bari ma dai bidi'a ce fararriya.
5- Idan ya kammala ɗawafi sai ya yi sallah raka'o'i biyu a bayan Maƙamu Ibrahim ko da ya yi masa nisa, a raka'a ta farko bayan karatun fatiha, zai karanta: {Ƙul yã ayyuhal kafirun (Ka ce: "Ya kũ kãfirai!)}. [al-Kafirun:1] A (raka'a) ta biyu kuma: {Ƙul huwallahu ahad (Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci)}. [al-Ikhlas: 1].
6- Sannan ya yi zagaye (Sa’ayi) a Safa da Marwa - wato: tsakaninsu - kewaye bakwai, zai fara da Safa ya kammala a Marwa.
Sunnah ita ce : Ya hau samansu ya tsaya yana fuskantar alƙibla, yana mai ɗaga hannuwansa, ya ambaci Allah ya roƙeShi.
Sunnah ga namiji ita ce: Yayi gaggawa tsakanin korayen alamu biyu gaggawa mai tsanani.
7- Idan ya gama Sa'ayi sai ya rage gashin kansa gaba ɗaya, mace zata rage gashin gwargwadon kan ɗan yatsa.
Da wannan ne Umrah ta cika, kuma ya warware ihraminsa, sai ya ji daɗi da dukkanin abinda Allah Ya halatta masa kafin harama na sanya tufafi, da shafa turare, da aure da wanin haka.
(B) Aikin Hajji
1- Idan ranar Tarwiya ta zo - ita ce rana ta takwas ga Zul Hijjah - sai ya yi harama da Hajji a inda ya sauka, sai ya aikata irin abinda ya aikata lokacin harama da Umrah na wanka, da shafa turare da sanya tufafin harama.
2- Idan ya gama wannan sai ya yi niyyar shiga aikin Hajji, sai ya ce: «Labbaikal lahumma labbaika, labbaika la sharika laka labbaika, innal hamda wa'inni'imata laka wal mulk, la sharika laka, labbaikal lahumma Hajjan (AmsawarKa Ya Allah amsawarKa, amsawarKa baKa da abokin tarayya amsawarKa, lallai godiya da ni'ima naKa ne mulki ma naKa ne, baKa da abokin tarayya, amsawarKa Ya Allah ga aikin Hajji. Wato: Ya Allah ka amsa mana wannan aikin Hajjin)». Namiji zai ɗaga muryarsa a wannan, mace kuma zata ɓoyeta.
An sunnanta yawan yin Talbiyah har sai ya jefi Jamratul Aƙabah (Babban Shaiɗan) a ranar idi, sai ya katseta.
3- Sannan ya fita zuwa Mina, sai ya yi sallar Azahar, da La'asar, da Magariba, da Issha'i da Asuba a can, zai yi ƙasarun salloli masu raka'o'i huɗu zuwa raka'o'i biyu amma kar ya haɗa su.
4- Idan rana ta ɓullo a ranar tara ga wata sai ya tafi zuwa Arfa, sai ya sauka a Namirah - in hakan ya sauƙaƙa gare shi - har zuwa gushewar rana, idan kuwa ba haka ba, to ya tsaya a Arfa, idan rana tayi zawali, sai ya haɗa sallar Azzahar da La'asar ya yi ƙasarun su da jam'insu (haɗa Azahar da La'asar), sannan ya kaɗaita da ambaton Allah da roƙonSa, yana mai fuskantar alƙibla a wannan - ko da dutsen ya zama a bayansa - har sai rana ta faɗi.
5- Idan rana ta faɗi, sai ya tafi Muzdalifah, sai ya yi sallar Magariba a can raka'o'i uku da Isha'i raka'o'i biyu, ya kwana a can, idan ya yi sallar Asuba ya shagala da ambaton Allah da rokonSa har sai gari ya washe sosai.
6- Idan gari ya waye sosai sai ya tafi Mina, idan ya je sai ya fara da jifan Jamratul Aƙabah (Babban Shaiɗan), shi ne mafi kusancin Jamrorin zuwa Makkah, sai ya jefe ta da tsakuwowi guda bakwai a jere wata na bin wata, kowacce tsakuwa ta fi girman waken garbanzo da kaɗan, kuma ya yi kabbara a kowacce tsakuwa cikin ƙanƙan da kai da girmama Allah - Maɗaukakin Sarki -.
Idan ya gama jifanta, sai ya soke hadayar sa in hakan ya sauƙaƙa, sannan ya aske kansa gaba ɗaya ƙwal-ƙwal ko saisaye, amma ƙwalƙwal ya fi in ba mace bace, to sai ta rage gashinta gwargwadon tsawon kan ɗan yatsa.
Idan ya yi jifan da aski ƙwalƙwal ko saisaye ya warware ihraminsa a karon farko (Tahalluli na farko), sai ya sanya tufafinsa, ya shafa turare, ya yi duk abinda Allah Ya halatta kafin yin harama, amma banda (kusantar) mata, domin duk abinda ya ke da alaƙa da su ba ya halatta gare shi har sai ya warware ihraminsa a karo na biyu (Tahalluli na biyu).
Sannan ya sauka Makkah, sai ya yi ɗawafin aikin Hajji, ya yi Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa a irin siffar da ta gabata a ɗawafin Umrah da Sa’ayin ta, sai dai ba zai yi sassarfa ba a ɗawafin, kuma ba zai yi Idɗiba'i ba (bayaninsa ya gabata); dominsu - ina nufin yin sassarfa da Idɗiba'i - ba'a shar'antasu ba in ba a yin ɗawafi ba lokacin da ya iso.
Idan ya yi ɗawafin da Sa'ayin waɗanda suka gabata da jifan Jamrah da ƙwalƙwal ko saisaye, to yayi tahalluli tahalluli na biyu (ya kammala ihraminsa) a karo na biyu, to duk abinda Allah Ya halatta kafin yin harama ya halatta gare shi har (kusantar) mata.
Taƙaitaccen abinda za'a aikata na ibadu a ranar idi sune kamar haka:
Jifan Jamratul Aƙabah (Babban Shaiɗan).
Soke hadaya.
Aski Ƙwalƙwal ko saisaye.
Ɗawafi da Sa'ayi.
Sunnah ita ce ya jerantasu kamar hakan, idan kuma hakan bai sauƙaƙa gare shi ba, to ya gabatar da sashensu akan sashe, babu laifi.
7- Sai ya kwana a Mina a daren goma sha ɗaya da goma sha biyu.
8- Zai jefi Jamrori uku a waɗannan ranakun biyu bayan rana ta yi zawali, zai fara da Jamrah ta farko, ita ce mafi nisan Jamrah daga Makkah, sai ya jefe ta da tsakwankwani guda bakwai a jere, ya yi kabbara a kowacce tsakuwa. Idan ya gama sai ya yi nesa da ita kaɗan daga cunkoson jama'a, sai ya tsaya yana mai fuskantar alƙibla, yana mai ɗaga hannuwansa, yana mai roƙon Allah - Maɗaukakin sarki - addu'a mai tsawo da duk abinda ya ke so. Sai ya jefi Jamrah ta biyu, ya tsaya bayan ya gama don addu'a kamar yadda ya yi a na farko daidai-wa-daida. Sannan sai ya jefi Jamrah ta uku - ita ce Jamratul Aƙabah wadda ya jefeta a ranar idi - kamar yadda ya jefi Jamrori guda biyu kafin ita, amma kada ya tsaya yin addu'a bayan ya gama.
9-Bayan ya kammala jifan Jamrorin uku a rana ta goma sha biyu, idan ya so ya jinkirta (ya zauna) a Mina har rana ta goma sha uku, ya jefi Jamrorin a cikinsa bayan rana ta yi zawali, hakan shi ya fi; domin shi ne aikin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma akwai ƙarin aiki na gari a cikinsa. Idan kuma ya so ya gaggauta (kammalawa) a kwanukan biyu, sai ya fita daga Mina a rana ta sha biyu kafin faɗuwar rana.
Kuma ya kamata ya yawaita yin kabbara da zikiri a waɗannan ranakun da kuma dararen; saboda faɗinSa - Maɗaukakin Sarki -: {Kuma ku ambaci Allah a cikin kwanuka ƙididdigaggu}. [al-Baƙara: 203]. Da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Ranakun Tashriƙ ranaku ne na ci da sha da ambaton Allah»[31]. Muslim ne ya fitar da shi a littafin azumi, babin haramcin azumi a ranakun Tashriƙ, lamba ta (1141) daga hadisin Nubaishatul Huzali.
Da wannan ne ayyukan Hajji suka kammala.
7- Ɗawafin bankwana.
Idan Alhaji ya gama yin dukkan ayyukan Hajji, kuma ya yi nufin komawa zuwa garinsa, to ba zai fita daga Makkah ba har sai ya yi ɗawafi a ɗakin Ka'abah na bankwana, zai sanya shi a ƙarshen al'amurransa yayin tafiyarsa.
Mai yin jinin al’ada da biƙi ba zata yi ɗawafin bankwana ba; saboda faɗin Ɗan Abbas - Alllah Ya yarda da su -: «An umarci mutane da ƙarshen lazimtarsu ya zama ɗakin Ka'aba ne, sai dai an sauƙaƙawa mai haila»[32]. Bukhari ne ya fitar da shi a littafin Hajji, babin ɗawafin ban kwana, lamba ta (1755), da Muslim a littafin Hajji, babin wajabcin ɗawafin bankwana, lamba ta (380/1328).
Abubuwan da harama take hanawa
Abubuwan da ihrami ya ke hanawa: Su ne abubuwan da aka haramta a ihrami saboda yin harama.
Sune kamar haka a taƙaice :
1- Cire gashin kai saboda aski ko waninsa, jamhur ɗin malamai sun riskar da: Sauran gashin jiki da shi.
2- Yanke farcen hannuwa ko ƙafafuwa, jamhur ɗin malamai sun riskar da gashi da shi; da cewa duka dan nuna wadata ne.
3- Amfani da turare bayan yin harama a jiki ko a kaya ko a abinci ko a abin sha.
4- Sanya al-ƙuffazain, sune safar hannu.
5- Runguma saboda sha'awa.
Fidiya (Fansar) waɗannan abubuwan da aka hana guda biyar akan zaɓi ne, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ambata a cikin Alƙur'ani a sha'anin aske gashin kai, sai aka ƙiyasta ragowar a kansa. Za'a zaɓa tsakanin azumin kwana uku, ko ciyar da miskinai shida, rabin sa'i ga kowane miskini, ko yanka akuya, sai a rarraba abincin da akuyar ga miskinai, ko a cikin Makkah, ko a wurin da ya yi abun da aka hana ɗin.
6- Yin jima'i a farji, idan ya yi a lokacin Hajji kafin warware haramar farko, to al'amurra guda huɗu sun jerantu a kansa:
Ɓacin ibadar da aka yi jima'i a cikinta.
Wajibi ne a ci gaba da ibadar.
Wajibi ne a rama ta a shekarar da zata zo.
Fidiyar soke taguwa, zai rabawa miskinai a cikin Makkah ko a inda ya yi jima'in.
7- Ɗaura aure, babu fitar da fansa (fidiya), sai dai auren ya ɓaci, daidai ne mai yin haramar shi ne mijin ko matar ko waliyyi ko wakilinsa ne.
8- Kashe abin farauta na tudu da daji, kuma akwai sakamakonsa a kansa, shi ne yanka kwatankwacinsa, zai rabawa faƙiran Harami, ko ƙimanta shi da abincin da zai rabawa faƙiran Harami, ko ya yi azumin kwana ɗaya a maimakon ciyar da kowanne miskini.
Waɗannan abubuwan da aka hana guda takwas haramun ne (aikatasu) a kan duk wanda ya yi harama, namiji ne ko mace, an keɓance namiji da abubuwan da aka hana guda biyu:
1- Rufe kai da abin da yake ɗamfaruwa (a jiki), amma wanda baya ɗamfaruwa - kamar tanti da rufin mota da lema - to babu laifi a (amfani) da shi.
2- Sanya abinda aka ɗinka, shi ne duk abinda aka ɗinka gwargwadon jiki ko sashen jiki ko wata gaɓa daga gaɓoɓinsa, kamar riga, wando da huffuna. Amma kwarjalle da mayafi da aka yi masa faci to babu laifi da shi, haka nan babu laifi a sanya zobe, da agogo, da gilashin ido, da abin ji na kunne, jakar sanya kayan amfani da makamantansu.
An keɓance mace a abubuwan da aka haramta da abubuwan da ke tafe:
Rufe fuska a kowacce irin siffa take, sashen malamai sun faɗa: Niƙabi kawai aka hanata, shi ne mace ta rufe fuskarta da abin rufewa, wanda akayiwa huda a cikinsa saboda idanuwanta, abinda ya fi kada ta rufe ta kai tsaye sai dai idan maza da ba muharramanta ba suna ganinta, to ya wajaba ta rufe ta a halin harama da waninsa.
Fansar waɗannan keɓantattun abubuwan da aka hana akan zaɓi ne, kamar dai fansar waɗancan biyar ɗin da suka gabata.
Hukuncin wanda ya aikata waɗannan abubuwan da aka hana
Wanda ya aikata abubuwan da aka hana waɗanda suka gabata yana da halaye guda uku:
Na farko: Ya aikata abubuwan ne ba tare da wata buƙata ba ko uzuri, to wannan mai laifi ne kuma akwai fansa a kansa.
Na biyu: Ya aikata ne saboda wata buƙata, to ba me laifi ba ne amma zai bada fansarsa (fidiya). Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce: {To, wanda ya kasance majinyaci daga cikinku, kõ kuwa akwai wata cũta daga kansa (ya yi aski) sai fansa (fidiya) daga azumi ko kuwa sadaka ko kuwa yanka}. [al-Baƙara: 196], Da zai buƙaci rufe kansa - saboda sanyi ko zafin da yake tsoro - ya halatta ya rufeshi, kuma zai bada fansa (fidiya) akan zaɓi tsakanin abubuwan da suka gabata.
Na uku: Ya aikata alhali yana abin yi wa uzuri saboda jahilci ko mantuwa ko tilastawa ko bacci, to babu laifi a kansa, kuma babu fansa (fidiya), saboda faɗinSa - Maɗaukakin Sarki -: {Yã Ubangijinmu! Kada Ka kãmã mu, idan mun yi mantuwa, ko kuma mun yi kuskure}. [al-Baƙara: 286]. Yazo a cikin hadisi daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa shi ya ce: «Allah ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da abin da aka tilasta su akansa»[33]. Ibn Majah ne ya fitar da shi a littafin saki, babin sakin wanda aka tilastawa da wanda ya yi mantuwa, lamba ta (2043) (2045) daga Abu Zarrin da Ɗan Abbas.
Sai dai duk sanda uzurin ya gushe, kuma ya san abinda aka hana ɗin ko ya tuna shi ko tilastawar tasa ta gushe ko ya farka daga baccinsa, to ya wajaba ya bar wannan abun - wato: Daga abun da aka hana ɗin - cikin gaggawa.
Ziyartar Masallacin Annabi
Masallacin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ɗaya ne daga cikin masallatai uku waɗanda ba'a ɗaura tafiya zuwa kowanne masallaci sai su kaɗai, su ne: Masallacin harami a Makkah, masallacin Annabi a Madina da masallacin al-Aƙsa a Ƙudus. Sallah a masallacin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta fi falala akan sallah sau dubu a waninsa sai fa a masallacin Harami. Da wannan ne aka shar'anta ziyartar masallacin don yin sallah a cikinsa a kowanne lokaci koda ba lokacin aikin Hajji ba, kuma ba shi da alaƙa da aikin Hajji, Hajji yana cika ba tare da shi ba, kuma ba ya tawaya saboda barinsa, sai dai mutane sun sanya shi a tare da aikin Hajji; don tafiya zuwa gare su ta zama guda ɗaya, musamman ga wanda ɗayanta kowanne daga cikinsu zai yi masa wahala a wajen tafiya, kamar mutanen da suke a ƙasashe masu nisa.
Idan ya shiga masallacin sai ya yi sallah a cikinsa gwargwadon yadda Allah Ya so, sannan ya tafi ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsaya a gabansa, ya ce: «Assalamu alaika - ayyuhan nabiyyi - warahmatullahi wabarakatuhu, Allahumma salli ala muhammad wa ala ali muhammad, kama sallaita ala Ibrahim wa ala ali Ibrahim; innaka Hamidun Majid, wabarik ala Muhammad wala ali Muhammad; kama barakta ala Ibrahim wa ala ali Ibrahim; innaka hamidun Majid (Aminci ya tabbata a gareKa - yakai wannan Annabi -, da rahamar Allah da albarkarSa, Ya Allah Ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen Muhammad; kamar yadda Ka yi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen Ibrahim, lallai Kai Abin yabaone Mai girma, kuma Ka yi albarka ga (Annabi) Muhammad da alayen Muhammad; kamar yadda Ka yi albarka ga (Annabi) Ibrahim da alayen Ibrahim; lallai Kai Abin yabone, Mai girma».
Sannan ya yi taku kaɗan a hannunsa na dama; domin ya yi sallama ga Abubakar - Allah Ya yarda da shi -, sai ya ce: Amincin Allah ya tabbata a gareka ya Abubakar, ya halifan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, Allah Ya yarda da kai, Ya kuma saka maka da alkhairi a madadin al'ummar (Annabi) Muhammad».
Sannan ya yi taku kaɗan a hannunsa na dama; domin ya yi sallama ga Umar, Allah Ya yarda da shi, sai ya ce: “Aminci ya tabbata a gare ka Amirul Muminina Umar, Allah Ya yarda da kai, Ya kuma saka maka da alkhairi a madadin al’ummar (Annabi) Muhammad».
Sai ya kuma je Masallacin Ƙuba ya na cikin tsarki (alwala), ya yi sallah a cikinsa.
Ya kuma ziyarci al-Baƙi’a, ita ce maƙabartar Madina. Sai ya yi sallama ga Usman, - Allah Ya yarda da shi -. Ya na tsaye a ƙabarinsa ya na cewa: «Aminci ya tabbata a gareka ya Amirul Muminina Usman, Allah Ya yarda da kai, Ya saka maka da alkhairi a madadin al'ummar (Annabi) Muhammad». Ya kuma yi sallama ga mutanen al-Baƙi’a yana kuma roƙon Allah Ya yi musu gafara da rahama.
Ya kuma tafi Uhud ya ziyarci ƙabarin Hamza, baffan Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da ƙabarin shahidai a wurin, sai ya nema musu yarda, ya na kuma roƙa musu gafara da rahama.
Mace ba ta ziyarar ƙaburbura, ko ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ko ƙaburburan waninsa.
Babu wani abu da aka shara'anta nufatar ziyarta a Madina na daga masallatai ko wasu wurare, sai abin da muka ambata kawai.
Allah ne Mai datarwa, Allah Ya yi salati da aminci ga Annabinmu Muhammadu da alayensa da sahabbansa baki ɗaya.
Mabuƙaci zuwa ga Allah ne ya rubuta.
Muhammad Saleh al-Uthaimeen
Related books
All books
TAƘAITACCEN BAYANI A KAN SIFFAR UMARAH DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCENTA65 harsunaTAƘAITACCEN BAYANI A KAN SIFFAR UMARAH DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCENTA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Annabimmu Muhammad, da alayensa da sahabbansa bakiɗaya. Bayan haka: Wannan taƙaitaccan bayani ne a kan siffar aikin Umarah da hukunce-hukuncenta da kuma ladubbanta, mun yi kwaɗayi a kawo bayanin galibin abinda mai yin Umarah yake da buƙatuwa zuwa gare shi. Allah muke roƙo Ya sanya shi tsarkakakke don zatinSa mai girma, kuma Ya amfanar da dukkanin musulmai da shi.
SIFFAR UMRAH28 harsunaSIFFAR UMRAH
Taƙaitaccen littafin «Siffar Umarah» Na Shehin malami Abdul’Aziz bn Baz - Allah Ya yi masa rahama - yana bayanin ayyukan Umrah akan wani tsari (salo) fayyatacce, kuma mai sauƙi, domin ya zama jagora a aikace da zai taimakawa musulmi akan gudanar da ayyukan sa (na Umrah), cikin ƙanƙan da kai da kuma sauƙi, yana kuma tare da addu’o’i, da zikirai da a aka ruwaito a kowanne mataki.
TAƘAITACCEN BAYANIN SIFFAR AIKIN HAJJI49 harsunaTAƘAITACCEN BAYANIN SIFFAR AIKIN HAJJI
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Annabimmu Muhammad da alayensa da sahabbansa baki ɗaya. Bayan haka: Wannan taƙaitaccen saƙo ne a kan siffar Hajji, mun yi kwaɗayin kawo bayanin mafi yawancin abinda maniyyaci yake buƙatuwa zuwa gare shi. Allah muke roƙo Ya sanya shi tsarkakakke ne don zatinSa mai girma, kuma Ya amfanar da dukkanin musulmai da shi. Shimfiɗa
Siffar alwala (taƙaitaccen sharhi a aikace)79 harsunaSiffar alwala (taƙaitaccen sharhi a aikace)
Sifar Alwala (Sauƙaƙaƙƙen bidiyo) Ɗabbaƙawa a aikace da ke bayanin yadda siffar alwala taka daki-daki, yana da matuƙar muhimmanci saboda alwala sharaɗi ce na ingancin sallah. Kalli bidiyon ka ko yi ingantacciyar Siffar alwala. Siffar Alwala