المختصر في صفة العمرة وأحكامها

المختصر في صفة العمرة وأحكامها

TAƘAITACCEN BAYANI A KAN SIFFAR UMARAH DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCENTA

Language: lang_ha
Prepared by: Kwamitin ilimi na Cibiyar hidimar abinda Musulunci ya ƙunsa a cikin harsuna daban daban.
Version: 3.0
Translations 56
Amharic Assamese Azerbaijani Bambara +52
Attachments 7
PDF
Audio
Video
+3

TAƘAITACCEN BAYANI A KAN SIFFAR UMARAH DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCENTA

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Annabimmu Muhammad, da alayensa da sahabbansa bakiɗaya.

Bayan haka:

Wannan taƙaitaccan bayani ne a kan siffar aikin Umarah da hukunce-hukuncenta da kuma ladubbanta, mun yi kwaɗayi a kawo bayanin galibin abinda mai yin Umarah yake da buƙatuwa zuwa gare shi.

Allah muke roƙo Ya sanya shi tsarkakakke don zatinSa mai girma, kuma Ya amfanar da dukkanin musulmai da shi.

Kwamitin ilimi na Cibiyar hidimar abinda Musulunci ya ƙunsa a cikin harsuna daban daban.

Shimfiɗa

Na farko: Sharuɗɗan karɓar ibada

Ibada ba ta kasancewa karɓaɓɓiya a wurin Allah - Maɗaukakin sarki - sai da sharuɗɗa biyu:

Ikhlasi, hakan shi ne ya nufi zatin Allah da kuma gidan lahira da ita, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi, mãsu karkata zuwa ga addinin gaskiya}[1]. [al-Bayyinah: 5]. Wato: Suna masu fuskantowa gareShi da kuma bautarSa, suna masu bijirewa wanda ba Shi ba. Ta fsirin al-Sa'adi (shafi na 538)

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Dukkan ayyuka ba sa ingantuwa sai da niyyoyi, kuma kowane mutum ana ba shi ladan abinda ya niyyata ne». [2] Bukhari ne ya rawaito shi, a lamba ta (1), da Muslim, a lamba ta (1907).

Bin Annabi a ciknta (bautar) a faɗa da kuma aikatawa, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: «Duk wanda ya farar da wani abu a cikin wannan Addinin namu wanda ba ya ciki, to shi abun mayarwa ne» A cikin wata riwayar ta Muslim (1718): «Duk wanda ya yi wani aiki wanda babu umarninmu a cikinsa to wannan aikin abun mayarwa ne». [3] Bukhari ne ya rawaito shi, a lamba ta (2697), da Muslim, a lamba ta (1718). [4] Muslim ne ya ruwaito, a lamba ta (1718).

***

Na biyu: Hukuncin neman sanin siffar aikin Umarah da kuma hukunce-hukuncenta

Yana kamata ga wanda ya yi nufin ya bautawa Allah - Maɗaukakin sarki - da wata ibada to ya nemi sanin karantarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinta; dan aikinsa ya zama ya dace da sunnah, haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana kwaɗaitar da mutane akan binsa da kuma karantarwarsa da shiriyarsa; daga Malik ɗan Huwairis - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ku yi sallah kamar yadda kuka ga ina yin sallah» [5] Bukhari ne ya ruwaito shi, a lamba ta (6008).

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: "Na ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin jifa akan dabbarsa a ranar babbar sallah yana cewa: Domin Ku riƙi ayyukan ibadunku; domin cewa ban sani ba wataƙila ba zanƙara yin hajji ba bayan wannan hajjin nawa" [6] Muslim ne ya ruwaito, a lamaba ta (1297).

***

Na uku: Falalar Umarah.

Umarah tana da falala biyu: Mai gamewa da kuma keɓantacciya

Mai gamewa:

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Umarah zuwa Umrah mai kankare abinda ke tsakaninsu ne, kuma kuɓutaccen aikin Hajji ba shi da wani sakamako sai aljanna». [7] Bukhari ne ya rawaito shi, a lamba ta (1773), da Muslim, a lamba ta (1349).

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku bibiyi tsakanin Hajji da Umarah, domin cewa su suna kore talauci da kuma zunubai kamar yadda zugazagi[2] yake kore dattin ƙarfe, da zinariya, da azirfa, kuma kuɓutaccen Hajji ba shi da wani sakamako sai aljanna". Gurin wutar maƙeri ne da kuma mai yin sana'a. al-Tamhid na Ibnu Abdil Barr (15/102) [9] Tirmizi ne ya ruwaito shi, a lamba ta (810), da Nasa'i, da lamba ta (2631).

Keɓantaccen kuma shi ne a cikin watan Ramadan: Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Umarah a cikin (watan) Ramadan ta yi daidai da aikin hajji tare da ni [3]» Wato: Ta yi daidai da aikin hajji tare da ni, kamar yadda ya zo a cikin wata riwayar daban.

***

SIFFAR UMARAH

Na farko: Hukunce-hukunce miƙatai

Miƙatai: Sune wuraren da Anabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ayyanasu dan wanda ya yi nufin yin hajji da Umarah ya yi harama daga garesu.

Duk wanda ya wuce ta ɗaya daga cikinsu yana mai yin niyyar hajji ko Umarah: To ya wajaba a kansa ya yi harama daga wurin, kuma bai halatta gare shi ya ƙetare shi, ba tare da harama ba.

Wanda ya kasance mafi kusa ga Makka daga waɗannan miƙatan: To lallai cewa miƙatinsa shi ne gurinsa: Sai ya yi harama daga wurin dan Hajji da kuma Umarah .

Amma mutanen Makka da wanda ya yi niyar yin harama daga gareta: To sai su yi haramar hajji daga Makka, amma Umarah kuwa: To lallai cewa zasu fita ne zuwa wajen harami sai su yi harama daga can, kamar Tan'im da makamancinsa.

Wanda ya kasance a cikin jirgi: To shi idan ya zo daura da miƙatai, sai ya yi shiri ya sanya tufafin harama kafin ya zo daura da miƙatin, idan ya zo daura da shi sai ya yi niyyar harama a lokacin, kuma ba ya halatta gare shi ya jinkirta daukar niyya har sai ya sauka filin jirgi, kuma zai iya kewayo sai ya yi talbiyyah kafin ya zo daura da miƙatin dan jin tsoron kuccewar wurin talbiyyar; saboda saurin jirgin.

Na biyu: Siffar harama da kuma hukunce-hukuneta:

An shara'antawa mai harama abinda ke tafe:

Wanka, shi sunna ne mai ƙarfi a haƙƙin maza da mata har mai al’ada da mai jinin biƙi.

Shafa tirare da mafi daɗin abinda ya samu na mai, mai ƙanshi ko waninsa a kansa da gemunsa, wanzuwar hakan baya cutar da shi, amma mace to shafa abinda yake da ƙanshi ba ya halatta a gare ta; dan kada maza ajnabai su shaƙi ƙanshinta.

Sanya tufafin harama, su ne gwafso da mayafi, kuma sunnah shi ne su zama farare masu tsafta ko sababbi, kuma mace zata yi harama ne a abinda ta so na tufa, kada ta yi tabarruji da ado, saidai cewa ita zata nisanci sanya niƙabi da safar hannu, kuma ta rufe fuskarta da hannayenta da wanin haka.

Yin harama bayan sallar da aka shara'anta, ta kasance farilla ce ko nafila, amma hakan ba wajibi ba ne.

Sai ya ce: (Labbaika Allahumma Umratan (AmsawarKa ya Allah Umarah, wato: Ya Allah ka amsa min wannan Umarah), idan ya kasance mai yi wa waninsa Umarah ne sai ya ce: (Labbaika Allahumma Umratan an fulanin (AmsawarKa ya Allah Umarah ga wane, wato: Ya Allah ka amsawa wane Umarah)).

Idan mai nufin yin harama ya kasance yana jin tsoron wani abu mai hana cika ibadarsa ta Hajji ko Umarah to yana kamata gare shi ya sharɗanta a lokacin harama sai ya ce: (Labbaika Allahumma Umratan, wa'in habasani habisun fa mahalli haisu habastani (AmsawarKa ya Allah Umarah, idan wani abu mai tsarewa ya tsareni to wurina shi ne inda ya tsareni)) aduk lokacin da ya sharɗanta kuma abinda zai hana shi cika ibadarsa ya faru, to cewa shi zai warware haramarsa kuma babu komai akansa.

Sannan ya yawaita yin Talbiyyah: (Labbaika Allahumma labbaika, labbaika la sharika laka labbaika, innal hamda wan ni'imata laka wal mulka la sharika laka labbaika[4] (AmsawarKa ya Allah amsawarKa, amsawarKa ba Ka da abokin tarayya amsawarKa, lallai godiya da ni'ima naKa ne haka mulki naKa ne baKa da abokin tarayya)), namiji ya ɗaga muryarsa da hakan, haka nan mace; muddin dai bata zama a gaban maza ajnabai ba. Kuma yana kamata ga mai harama ya yawaita Talbiyyah musamman ma dai a lokacin canza halaye da lokuta, misali idan ya hau tudu, ko ya sauka gangare, ko ya fuskanci dare ko rana. Ma'anar faɗin mutum: (Labbaika) wato amsawarKa ya Ubangiji, amsawa bayan wata amsawar, kuma ma'anarta: Amsawar mutum ga Ubangijinsa da kuma tsayuwarsa akan biyayyarSa. "Innal hamda wan ni'imata laka wal mulk" al-Hamd: Ita siffa ce abar godiya da cika tare da soyayya da kuma girmamawa, idan ya maimaita to ya zama yabo. Wan ni'imata: Ita ce abinda Allah Yake falala da shi ga bayinSa na samun abin nema da tunkuɗe abin ƙi, da faɗinsa: (almulk) yana nufin mulki ma naKa ne, Allah - alhrinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Shi ne Mamallaki Shi kaɗai, da faɗinsa: (BaKa da abokin tarayya) wato babu wani da zai yi tarayya da Kai a cikin abinda Ya keɓanci Allah - Mai girma da ɗaukaka - na siffofinSa cikakku wanda a cikin hakan akwai kaɗaitakarSa da mulki da kuma halitta da jujjuya al'amura da kuma Allantaka. Majmu'u fatawa wa rasa'il Ibni Usaimin (22/96) a taƙaice.

Talbiyya an shar’anta ta ne a Umarah tun daga harama har zuwa lokacin da zai fara ɗawafi.

Yana wajaba akan mai harama ya kiyaye faɗawa cikin wani abu daga abubuwan da harama take haramtawa har sai ya kammala aikinsa.

Na uku: Siffar ɗawafi.

Da Idan mai harama ya shiga masallaci mai alfarma an sunnanta masa ya gabatar da ƙafarsa ta dama kuma ya faɗi addu'ar shiga masallaci, yana daga mafi ingancin abinda ya zo a cikin hakan ya ce: "Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa", kuma wannan addu'ar zai faɗeta ne a lokacin shiga kowanne Masallaci, bata keɓanci masallaci mai alfarma kadai ba.

Idan ya yi nufin fara ɗawafi to shi zai dakatar da Talbiyyah, kuma ya yi ibɗida'i, siffar yin ibɗida'i shi ne: Ya sanya tsakiyar mayafinsa cikin hammatarsa ta dama kuma geffansa akan kafaɗarsa ta hagu, idan ya gama ɗawafi sai ya dawo da mayafinsa zuwa ga halin da yake kafin ɗawafin; domin ibɗiba'i inda ake yin sa ɗawafi ne kadai.

Sannan ya fuskanci al-Hajarul aswad (bakin dutse) sai ya taɓa dutsen da hannunsa na dama ya kuma sumbace shi, idan sunbatar tasa ba ta yi wu ba sai ya taɓa shi da hannunsa, kuma ya sumbaci hannunsa, idan taɓa shin da hannunsa ba ta yi wu ba, sai ya taɓa shi da wani abinda ke tare da shi kamar sanda da makamancinta sai ya sumbaceta, idan hakan bai yi wu ba to sai fuskanci dutsen kuma ya yi nuni zuwa gare shi nuni kawai kada ya sunbace shi, amma abinda ya fi shi ne kada ya yi turereniya domin hakan sai ya cutar da mutane shima ya cutu da su.

Kuma a lokacin taɓa dutsen ko nuni zuwa gare shi sai ya ce: (Allahu Akbar (Allah ne Mafi girma)).

Sannan sai ya yi dama kuma ya sanya Ɗakin a hagunsa, idan ya kai Rukunul Yamani sai ya taɓa shi ba tare da sumbata ba, idan hakan bai samu ba to kada ya yi turereniya a kansa, kuma kada ya yi nuni zuwa gare shi.

Kuma tsakanin Rukunul Yamani da Hajarul aswad zai ce: (Ya Ubangijinmu Ka bamu mai kyau a duniya haka ma a lahira Ka bamu mai kyau kuma Ka karemu daga azabar wuta).

A duk lokacin da ya wuce Hajarul aswad sai ya yi nuni zuwa gare shi kuma ya ce: (Allahu Akbar (Allah ne Mafi girma)).

A ragowar ɗawafinsa zai faɗi abinda ya so na zikiri da addu'a da kuma karatun Alƙur'ani.

Kuma sunnah ita ce ya yi sassarfa a kewaye ukun farko kawai, sassarfa ita ce: Gaggawar tafiya tare da kusanto da taku, amma ragowar kewaye huɗun to babu sassarfa a cikinsu, kawai zai yi tafiya ne kamar al'adarsa.

Idan ya cika ɗawafin sai ya zo Maƙamu Ibrahim sai ya karanta: {Kuma ku riƙi Maƙamu Ibrahim wurin yin sallah} [al-Baƙara: 125] Sai ya yi sallah raka'a biyu a bayansa idan hakan ya sawwaƙa, inba haka ba sai ya sallacesu a kowane guri a Masallaci, yana karantawa a raka'a ta farko bayan Fatiha: {Ka ce: "Ya kũ kãfirai!} [al-Kafirun:1] A raka'a ta biyu bayan Fatiha sai ya karanta: {Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci}. [al-Ikhlas: 1]

Na huɗu: Siffar Sa'ayi.

Idan ya gama ɗawafi da raka'o'insa biyu to cewa shi zai fita zuwa wurin Sa'ayi, idan ya kusanto Safa sai ya karanta: {Lalle ne Safã da Marwa suna daga wurãren ibãdar Allah}. [al-Baƙara: 158]. Sannan ya ce: "Zan fara da abinda Allah Ya fara da shi". «Abda'u bimā bada'al Lāhu bihī». Ma’ana: (Zan fara da abinda Allah Ya fara da shi) [12]. [12] Muslim ne ya ruwaito, a lamaba ta (1218).

Sannan ya hau Safa har sai ya ga Ka'abah ko ɓangarenta sai ya fuskanceta, sai ya kaɗaita Allah, ya girmamaShi, sai ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai yake ba Shi da abokin tarayya, mulki naSa ne godiya ta tabbata a gare Shi, kuma Shi Mai iko ne akan dukkan komai, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai, Ya zartar da alƙawarinSa, Ya taimaki bawanSa, kuma Ya tarwatsa ƙungiyoyin ƙawance Shi kaɗai). Zai maimaita hakan sau uku, kuma zai yi addu'a tsakanin hakan. «‌Lā'ilāha illallāhu wahdahu lā sharika lahu, lahul mulku walahul hamdu, wahuwa alā kulli shai'in Ƙadīr, lā'ilāha illallāhu wahdahu, anjaza wa'dahu, wa nasara abdahu, wa hazamal ahzāba wahdahu». Ma’ana: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, mulki naSa ne kuma godiya ma taSa ce, kuma Shi mai iko ne akan komai,, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai, Ya zartar da alƙawarinSa, kuma Ya taimaki bawanSa, kuma Ya tarwatsa ƙungiyoyin ƙawance Shi kaɗai). Sannan ya yi addu'a tsakanin haka. Ya faɗi kwatankwacin haka sau uku [7]. [13] Muslim ne ya ruwaito, a lamaba ta (1218).

Sannan ya sauka daga Safa zuwa Marwa yana mai tafiya a ƙasa, idan ya isa koriyar alama sai ya yi gaggawa mai tsanani, idan ya isa koriyar alama ta biyu sai ya yi tafiya kamar al'adarsa, kuma ba'a shara'anta gaggawa mai tsanani ga mata ba.

Idan ya isa Marwa an shara'anta masa ya aikata abinda ya yi akan Safa (sakin layi mai lamba 2).

Sannan ya sauka daga Marwa zuwa Safa yana mai tafiya, idan ya isa koriyar alama sai ya yi gaggawa mai tsanani, idan ya isa koriyar alama ta biyu sai ya yi tafiya kamar al'adarsa.

Haka nan har sai ya cika kewaye bakwai. Tafiyarsa daga Safa zuwa Marwa kewaye ne, kuma dawowarsa daga Marwa zuwa Safa ma wani kewayan ne daban.

Ya fadi abinda ya so na zikiri da addu'a da karatu a cikin Sa'ayinsa.

Na biyar: Siffar aski ƙwal-ƙwal da kuma saisaye:

idan mai Umarah ya cika ɗawafinsa da Sa'ayinsa to ya wajaba akansa ya aske kansa ƙwal-ƙwal ko ya yi saisaye, idan ya kasance namiji ne, sunnah kuma ita ce ƙwal-ƙwal ɗin ko saisayen ya zama ya game dukkanin kai.

Amma ƙwal-ƙwal ɗin ya fi saisayen, sai dai idan ya kasance lokacin Hajji ya kusa, ta inda lokacin tsirowar gashin kai ba zai yalwatu ba; to abinda ya fi shi ne ya taƙaita akan saisayen kawai.

Amma mace to ita zata rage gwargwadan kan ɗan yatsa daga gefen gashinta.

ABUBUWAN DA AKA HANA MAI IHRAMI YA AIKATA.

Abubuwan da shiga harama (da Hajji ko Umarah) yake hanawa sune:

Aske gashi ko saisaye shi ko cizge shi daga kowane wuri na jikinsa.

Rage farata gabaɗayansu ko wasu daga cikinsu na ƙafafuwa ko hannaye.

Rufe kai da abinda yake ɗanfare da shi, misali: Hula da shimag, da rawani, da kuma ɗora mayafi akan kansa, ko sanya hankici, ko bargo, ko kwali, ko wanin haka daga abinda ake nufin rufewa da shi. To wannan ya keɓanci namiji ne banda mace.

Sanya tufafi na al'ada wanda aka yayyanka gwargwadan jiki; da siffarsa ta al'ada, misali: Tufafin da aka yayyanka, da wanduna, da riga, da jaurabi, da safa. To wannan ya keɓanci namiji ne banda mace; kawai ita an hanata ne daga:

Sanya niƙabi ko burga ko rufe fuska da abu mai kama da niƙabi, yana wajaba akanta ta rufe fuskarta a wajen maza ajnabai (wadanda ba maharamai ba) da mayafin da aka saba rufe fuska da shi; ko da mayafin ya shafi fuskarta, kuma ba'a shara'anta mata sanya bandeji - ko makamancinsa - akan fuskarta ba dan manufar rashin gogar mayafin ga fuska; dan rashin abinda yake nuni akan halaccin hakan.

Sanya safar hannu a hannayenta, kuma yana wajaba akanta ta rufe hannayenta a wajen maza da ba maharamai ba ta hanyar sanyasu a cikin mayafinta.

Shafa tirare a cikin jiki, ko tufafin harama.

Kashe abin farauta na sarari (tudu), ko farautarsa ko da bai kasheshi ba.

Nemawa kansa aure ko waninsa.

Ɗaura aure.

Rungumemeniya a abinda ba farji ba; kamar sumbata, da shafa mace da sha'awa.

Jima'i, shi ne tarawa a cikin farji.

Rairaye bayanan ayyukan Umarah (zasu kasance a bango ko a ƙarshen shafin)

Yin wanka

Shafa tirare.

Sanya tufafin harama.

Harama, ita ce niyyar shiga cikin ibadar (Hajji ko Umarah).

Talbiyyah.

Ɗawafi a ɗaki.

Sallah raka'a biyu a bayan Maƙamu Ibrahim.

Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa.

Aski ƙwal-ƙwal ko saisaye. Allah shi ne Mafi sani, Allah Ya yi daɗin tsira ga Annabinmu Muhammad.