نبذة في العقيدة الإسلامية (شرح أصول الإيمان)
رسالة لطيفة تتناول أصول العقيدة الإسلامية بأسلوب مبسط وميسر. تبدأ بمقدمة حول أهمية علم التوحيد، كونه أشرف العلوم وأجلّها، ثم تتناول مفهوم الدين الإسلامي وأركانه الخمسة: الشهادتان، والصلاة، والزكاة، والصوم، والحج. كما يشرح الإيمان بالله، وملائكته، وكتبه، ورسله، واليوم الآخر، ويؤكد على أهمية التوحيد في بناء دين المسلم بشكل سليم. الكتاب يهدف إلى تعزيز الفهم الصحيح للعقيدة الإسلامية وتطبيقها في حياة المسلم اليومية.
TAƘAITACCEN BAYANI A KAN AƘIDAR MUSULUNCI
Da alƙalamin babban malami mai yawan sani.
Muhammad bn Saleh al-Usaimeen
Allah Ya yi masa gafara shi da mahaifansa da musulmai.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
GABATARWA
Haƙiƙa godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna tuba zuwa gare Shi. Muna neman tsarin Allah daga sharrukan rayukanmu, da kuma munanan ayyukanmu. Duk wanda Allah Ya shiryar babu mai ɓatar da shi, kuma wanda Ya ɓatar babu mai shiryar da shi. Ina shaida cewa babu wani abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kaɗai yake, ba Shi da abokin tarayya. Kuma ina shaida cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzanSa ne, Allah Ya yi tsira a gare shi, da alayensa, da sahabbansa, da waɗanda suka biyo su da kyautatawa, Ya yi aminci amincewa.
Bayan haka: Haƙiƙa (Ilimin kaɗaita Allah) (shi ne) Mafi ɗaukakar ilimai, kuma mafi girmansu a daraja, mafi wajabcinsu a nema, domin shi ilimin sanin Allah - Maɗaukakin sarki - ne, da sunayenSa, da siffofinSa, da haƙƙoƙinsa a kan bayinSa, kuma domin shi mabuɗin hanya ne zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, kuma ginshiƙin shari'oinSa ne.
Saboda haka: Manzanni sun haɗu a kan kira zuwa gare shi. Allah - Maɗaukakin sarki - Yace: {Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba a gabãninka fãce Munã yin wahayi zuwa gare shi, cẽwa 'Lalle ne Shi, bãbu abin bautãwa fãce Nĩ, sai ku bauta Mini 25} [al-Anbiya': 25].
Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya shaidarwa kanSa da kaɗaitaka, kuma mala'kunSa sun shaidar maSa da ita, da ma'abota sani. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Allah Ya shaida cẽwa: Lalle ne bãbu abin bautãwa fãce Shi kuma malãiku da ma'abũta ilmi sun shaida, yana tsaye da ãdalci, bãbu abin bautãwa face Shi, Mabuwãyi, Mai hikima 18} [āli-Imran: 18].
Yayin da ya kasance wannan shi ne sha'anin tauhidi (kaɗaita Allah) to ya zama wajibi a kan kowanne musulmi ya kula da shi a koyo da koyarwa, da bibbiya, da ƙudircewa, dan ya gina Addininsa a kan kuɓutaccen ginshiƙi, da nutsuwa da miƙa wuya, har ya azurtu da fa'idodinsa, da kuma sakamakonsa.
Allah Shi ne Majiɓincin datarwa.
Mawallafi
ADDININ MUSULUNCI
Addinin Musulunci: Shi ne Addinin da Allah Ya aiko (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da shi, kuma Allah Ya cika Addinai da shi, Ya cika shi ga bayinSa, Ya kuma cika ni'ima a gare su da shi, Ya yarda da shi a gare su a matsayin Addini, ba ya karɓar wani Addini daga wani in ba shi ba. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Muhammadu bai kasance uban kõwa ba daga mazanku, kuma amma shĩ yã kasance Manzon Allah kuma cikon Annabãwa. Kuma Allah Ya kasance Masani ga kõme 40} [al-Ahzab: 40].
Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {...A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni'imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku...} [al-Ma'ida: 3].
Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Lalle ne, addini a wurin Allah, Shi ne Musulunci...} [āli-Imran: 19].
Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra 85} [āli-Imran: 85].
Kuma haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya farlanta a kan dukkanin mutane, da su bautawa Allah - Maɗaukakin sarki - da shi, sai Ya ce Yana yi wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - magana: {Ka ce: "Yã kũ mutãne! Lalle ne nĩ manzon Allah ne zuwa gare ku, gabã ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã kashewa, sai ku yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa 185} [al-A'araf: 158].
Kuma ya zo a cikin Sahihin Muslim daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa shi ya ce: «Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa, babu wani daga wannan al'umma Bayahude ko Nasara da zai ji wani abu game da ni, sannan ya mutu bai yi imani da abin da aka aiko ni da shi ba, face sai ya kasance daga cikin 'yan wuta» [1]. [1] Muslim ne ya fitar da shi: Littafin Imani, babin wajabcin yin imani da saƙon Annabinmu Muhammadu - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ga dukkan mutane, kuma Addinisa ya soke sauran Addinai, lamba ta (153).
Kuma imani da shi: (shi ne) gasgata abin da ya zo da shi tare da karɓa da miƙa wuya, ba kawai gasgatawa ba. Saboda wannan ne Abu Ɗalib bai kasance mai bada gaskiya da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ba, tare da gasgatawarsa ga abin da ya zo da shi, da kuma shaidawarsa da cewa shi (Musulunci) yana daga mafificin Addinai.
Addinin Musulunci: Mai ƙunsar dukkanin maslahohi ne, waɗanda Addinan da suka gabata suka ƙunsa, mai keɓentuwa ne a kansu da kasancewarsa, shi wanda ya dace ne da dukkan zamani da al'umma. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce Yana mai magana da ManzonSa: {Kuma Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka da gaskiya, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Littãfi (Attaura da Injĩla), kuma mai halartãwa a kansa...} [al-Ma'ida: 48].
Ma'anar kasancewarsa wanda ya yi daidai ne da kowanne zamani da guri da al'umma: cewa riƙo da shi, ba ya kore maslahar al'umma a kowanne zamani, ko gari, a'a shi ne ingantuwarsu. Ma'anar haka, bai zamo cewa shi mai bi ne ga kowanne zamani da guri da al'umma ba, kamar yadda sashin wasu mutane suke nufin shi. (Wato shi ake bi a kowanne Lokaci da wuri).
Addinin Musulunci: shi ne Addinin gaskiya, wanda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya lamincewa wanda ya yi riƙo da shi, riƙo na gaskiya, cewa zai taimake shi Ya kuma ba shi rinjaye a kan waninsa. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Shi ne wanda Ya aiko manzonSa da shiriya da Addinin gaskiya, dõmin ya bayyana shi a kan Addini dukansa, kuma kõ dã mushirikai sun ƙi 9} [as-Saff:9].
Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare. Ku, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zai shugabantar da su a cikin ƙasa kamar yadda Ya shugabantar da waɗanda suke daga gabãninsu, kuma lalle ne zai tabbatar mu su da addininsu wanda Ya yardar musu, kuma lalle ne Yanã musanya mu su daga bãyan tsõronsu da aminci, sunã bauta Mini bã su haɗa kõme da Nĩ. Kuma wanda ya kãfirta a bãyan wannan, to, waɗancan, su ne fãsiƙai 55} [an-Nur: 55].
Addinin Musulunci: Aƙidane da shari'a, shi cikakke ne a aƙidarsa da kuma shari'unsa:
1- Yana umarni da kaɗaita Allah- Maɗaukakin sarki- yana kuma hani ga shirka.
2- Yana umarni da gaskiya kuma yana hana ƙarya.
3- Yana umarni da adalci kuma yana hani daga zalunci. Adalci shi ne daidaitawa tsakanin masu kamanceceniya da kuma rabewa tsakanin masu sassaɓawa. Adalci bai zamo tsantsar daidaitawa ba, kamar yadda wasu sashin mutane suke furuci da shi, yayin da yake cewa: Addinin Musulunci Addinin daidaitawa ne, kuma ya saki (maganar), domin lalle daidaitawa tsakanin abubuwan da suka sassaɓa zalunci ne, Musulunci ba ya zuwa da shi, kuma ba ya yabon mai aikata shi.
4- Yana umarni da amana kuma yana hani daga ha'inci.
5- Yana umarni da cika alƙawari kuma yana hani daga yaudara.
6- Yana umarni da biyayya ga mahaifa kuma yana hani ga saɓa (musu).
7- Yana umarni da sada zumunci, su ne 'yan uwa kuma yana hani daga yanke (zumunci).
8- Yana umarni da kyautata maƙwabtaka, kuma yana hani ga munanata.
Gamammiyar magana ita ce: Haƙiƙa (Musulunci) yana umarni da dukkan ɗabi'a mai falala; yana kuma hani ga dukkan ɗabi'a maƙasƙanciya, yana umarni da dukkan aiki na gari, kuma yana hani daga dukkan mummunan aiki.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Lalle Allah nã yin umurni da ãdalci da kyautatãwa, da bai wa ma'abũcin zumunta, kuma yanã hani ga alfãsha da abin da aka ƙi da rarrabe jama'a. Yanã yi muku gargaɗi, tsammãnin ku, kunã tunãwa 90} [an-Nahl: 90].
RUKUNAN MUSULUNCI
Rukunan Musulunci: Ginshiƙansa waɗanda yake ginuwa a kansu, su biyar ne: An ambata a cikin abin da Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su - ya ruwaito daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa ya ce: «An gina Musulunci a bisa abubuwa biyar: a kan a kaɗaita Allah (kuma a wani ruwaya: a bisa abubuwa biyar): Shaidawa cewa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma (Annabi) Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da azumin Ramadan, da Hajji» Sai mutumin ya ce: Hajji, da azimin Ramadan? Ya ce: «A'a, azumin Ramadan, da Hajji» Haka na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - [2]. [2] Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin imani, lamba ta (8), da Muslim: Littafin imani, Babin faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: An gina Musulunci a kan ginshiƙai biyar, lamba ta (16).
1-Amma shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzanSa ne, shi ne: Ƙudircewa a yanke wacce za'a bayyanar da wannan shahadar da harshe, kamar cewa shi da yankewarsa a hakan mai shaidawa ne a gare shi, kaɗai an sanya wannan shaidawar rukuni guda ɗaya tare da ƙididdigar abin shaidawar da shi.
Ko dai: Cewa Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mai isarwa ne daga Allah - Maɗaukakin sarki -, shaidawa a gare shi da bauta da kuma manzanci yana daga cikar shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah.
Ko kuma dai: Saboda waɗannan shaidawa guda biyu su ne ginshiƙin ingancin ayyuka da kuma karɓarsu, domin babu inganci ga wani aiki ko karɓa sai da ikhlasi ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da kuma biyayya ga ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.
Da ikhlasi ne ga Allah shaidawa take tabbatuwa: Cewa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, kuma da biyayya ga Manzan Allah ne shaidawa take tabbata: Cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne.
Yana daga fa'idodin wannan shaidawar mai girma: 'Yantar da zuciya da rai daga bauta ga ababen halitta, kuma daga bin wanin Manzanni.
2- Amma tsaida sallah: To shi ne bauta ga Allah- Maɗaukakin sarki - da zai aikata ta a bisa fuskar daidaituwa da cika a lokutanta, da kuma yadda take.
Yana daga fa'idodinsa: Yalwatuwar ƙirji, da sanyin ido, da hana alfasha da kuma abin ƙi.
3- Amma ba da zakka: Shi ne bauta ga Allah - Maɗaukakin sarki - da bada gwargwadon wajibi a dukiyoyi na zakka waɗanda suka cancanta.
Yana daga fa'idodinsa: Tsarkake rai daga ƙasƙantacciyar ɗabi'a (rowa) da biyan buƙatar Musulunci da musulmai.
4- Amma kuma Azumin watan Ramadan: Shi ne bauta ga Allah -Maɗaukakin sarki - da kamewa daga abubuwa masu karya (azumi) da rana a Ramadana.
Yana daga fa'idodinsa: Horar da rai a bisa barin abubuwan so, don neman yardar Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
5- Amma ziyartar Ɗakin Allah: Shi ne bauta ga Allah- Maɗaukakin sarki - da nufin Ɗaki mai alfarma,don aikata alamomin (ayyukan) Hajji.
Yana daga fa'idodinsa: Horar da rai a kan bada dukiya da aka tara da ƙarfin jiki a wajen biyayyar Allah - Maɗaukakin sarki - da wannan ne Hajji ya kasance wani nau'i na jihadi a kan tafarkin Allah - Maɗaukakin sarki -.
Waɗannan fa'idodin waɗanda muka ambace su, na waɗannan ginshiƙan, dama waɗanda ba mu ambace su ba, suna sa al'umma (su zamo) al'umma ta Musulunci tsarkakkiya mai tsarkaka, tana yin Addini ga Allah Addini na gaskiya, tana kuma mu'amalantar halitta da adalci da kuma gaskiya. Domin abin da ba su ba daga shari'oin Musulinci, yana ingantuwa ne da ingantuwar waɗannan ginshiƙan, kuma halayen al'umma suna ingantuwa da ingantuwar Addininta, kuma ingantuwar halayensu yana tsere mata ne, da gwargwadan abin da ya tsere mata na daga ingantuwar al'amuran Addininta.
Wanda yake son ƙarin bayanin haka, to ya karanta faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Kuma dã lalle mutãnen alƙaryu sun yi ĩmãni kuma suka yi taƙawa dã haƙĩƙa Mun bũɗe albarkõki a kansu daga sama da ƙasa, kuma amma sun ƙaryata, don haka Muka kãma su da abin da suka kasance sunã tãrãwa 96. Shin, mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbar Mu ta jẽ musu da dare, alhãli kuwa sunã barci? 97 Kõ kuwa mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbarMu ta jẽ musu da hantsi, alhãli kuwa sunã wãsa? 98 Shin fa, sun amince wa makarun Allah? To, bãbu mai amince wa makarun Allah fãce mutãne mãsu hasãra! 99} [al-A'raf: 96-99].
Ya yi duba a tarihin waɗanda suka gabata, haƙiƙa tarihi izina ne ga ma'abota hankula, kuma abin la'akari ne ga wanda shamaki bai tsare zuciyarsa ba, Allah Shi ne abin neman taimako.
GINSHIƘAN AƘIDAR MUSULUNCI
Addinin Musulunci:-Kamar yadda muka bayyana a baya- aƙida ne da shari'a, haƙiƙa munyi nuni zuwa wani abu daga shari'o'nsa, kuma mun ambaci rukunansa waɗanda ake la’akari da su ginshiƙai ga shari'o'insa.
Amma aƙidar Musulunci, ginshiƙanta sune: Imani da Allah, da mala'ikunSa, da littatafanSa da manzanninSa da ranar lahira, da ƙaddara alkhairinta, da sharrinta.
Haƙiƙa littafin Allah da sunnar ManzanSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sun yi nuni a bisa waɗannan ginshiƙan.
A cikin littafin Allah - Allah Maɗaukakin sarki - Yana cewa: {Bai zama addini ba dõmin kun jũyar da fuskõkinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira da malã'iku da Littattafan sama da Annabãwa...} [al-Baƙara: 177]. Yana cewa a kan ƙaddara: {Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri. 49 Kuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido 50} [al-Ƙamar: 49-50].
A cikin sunnar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Yana amsawa Jibril lokacin da ya tambaye shi game da imani: «Imani: (shi ne) ka yi imani da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da ManzanninSa, da ranar lahira, kuma ka yi imani da ƙaddara: alkhairinta da sharrinta» [3]. [3] Muslim ne ya fitar da shi: Littafin Imani, lamba ta (8), da Abu Dawud: Littafin Sunnah, Babi a cikin Ƙaddara, lamba ta (4695).
Imani da Allah - Maɗaukakin sarki -:
Amma imani da Allah, yana ƙunsar abubuwa ne guda huɗu:
Abu na farko: Imani da samuwar Allah - Maɗaukakin sarki -:
Haƙiƙa kyakyyawar ɗabi’a, da hankali da shari'a, da riska ta sarari, sun yi nuni a bisa samuwarSa - Maɗaukakin sarki -.
Amma nunin halitta ta asali a bisa samuwarSa- tsarki da ɗaukaka sun tabbata a gare Shi -: Haƙiƙa dukkan abin halitta an halicce shi ne a kan imani da Mahaliccinsa, ba tare da rigayar tunani ba, ko koyarwa, babu wanda zai juya ya bar abin da wannan halitta ta asali ta hukuntar, sai wanda abin da zai juyar da shi daga gare ta ya ɗarsu a kan zuciyarsa; Saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Babu wani yaro face ana haifarsa a kan turba, sai dai iyayensa su maida shi bayahude, ko su maida shi banasare, ko su maida shi bamajuse» [4]. [4] Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin jana’iza, babin idan yaro ya musulunta sai ya rasu, shin za'a yi masa sallar jana’iza, kuma shin za'a bijirowa da yaro Musulunci, lamba ta (1292), da Muslim: Littafin ƙaddara, babin ma’anar cewa kowane jariri ana haifarsa a kan fitra, da hukuncin mutuwar yaran kafirai da yaran musulmai, lamba ta (2658).
2- Amma nunin hankali a bisa samuwar Allah - Maɗaukakin sarki - domin cewa waɗannan abubuwan halitta: Waɗanda suka gabata da waɗanda za su zo, babu makawa suna da wani Mahalicin da Ya samar da su, domin ba zai yuwu ba, su samar da kansu da kansu, kuma ba zai yuwu su samu haka kwatsam ba.
Ba zai yuwu ba, su samar da kansu da kansu: domin wani abu ba ya halittar kansa, domin kafin samuwarsa rasasshe ne, to ta yaya zai zama mahalicci?!
Ba kuma zai yuwu ba, su samu katsahan, domin dukkan fararre lalle ba makawa akwai wanda ya farar da shi. Kuma domin cewa samuwarsu a kan wannan tsarin mai ƙayatarwa, da jerantuwa mai ɗamfaruwa, da haɗuwa mai cuɗanyuwa tsakanin dalilai da abubuwan da suke haifar da su, da kuma tsakanin kasantattu sashinsu tare da sashi, (hakan) zai hana hani yankakke samuwarsu ta kasance katsahan, domin abin samarwa ta hanyar katsahan ba ya zamowa a kan tsari a asalin samuwarsa, to ta yaya zai kasance tsararre a halin wanzuwarsa da ci gabansa?!
Idan ba zai yuwu ba cewa waɗannan ababen halitta su samar da kansu da kansu ba, ko kuma su samu katsahan ba, to ya tabbata cewa akwai wanda ya samar da su, shi ne Allah Ubangijin talikai.
Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ambaci wannan dalili na hankali, da hujja yankakkiya a cikin surar al-Ɗur; a inda Ya ce: {Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta? 35} [aɗ-Ɗur: 35]. Yana nufin: Cewa su ba'a haliccesu ba ba tare da Mahalicci ba, ba kuma su ne suka halicci kawunansu ba; to ya tabbata cewa Mahaliccinsu Ya kasance shi ne Allah - Mai girma da ɗaukaka -. Saboda wannan ne, ya yin da Jubairu Ibnu Muɗ'im - Allah Ya yarda da shi - ya ji Manzan Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana karanta Surar al-Ɗur sai ya kai ga waɗannan ayoyin: {Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta? 35 Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba. 36 Shin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya? 37} [aɗ- Ɗur: 35-37].
Jubairu ya kasance a wannan lokaci mushiriki ne, ya ce: "Zuciyata ta kusa ta fashe, hakan shi ne farkon abin da ya tabbatar da imani a cikin zuciyata"[5]. [5] Bukhari ne ya fitar da shi: Surar al-Ɗur, a lamba ta (4854).
Mu buga misali da zai bayyanar da haka: Cewa da ace wani mutum zai ba ka labarin wani katafaren gida mai tsawo, da lambuna suka kewaye shi, kuma ƙoramu suke gudana a tsakaninsu, kuma an cika shi da shimfiɗu da gadaje, an kuma ƙawata shi da nau'o'in ado daga masu tabbatar da shi da kuma cika shi, ya kuma ce da kai: Haƙiƙa wannan katafaren gida da abin da yake cikinsa na daga cika, haƙiƙa ya samar da kansa ne, ko ya samu hakannan kwatsam, ba tare da mai samawarwa ba, da ka yi gaggawan musun hakan, da kuma ka ƙaryata shi, kuma ka ɗauki zancensa wauta ta magana. Shin zai yiwu bayan haka, wannan kasantacce mai faɗi ya kasance: Da ƙasarsa da samansa da taurarinsa, da halayensa, da tsarinsa mai ƙayatarwa mai rinjaye, ya samar da kansa, ko ya samu kwatsam ba tare da mai samarwa ba?!
3- Amma dalilai na Shari'a a bisa samuwar Allah - Maɗaukakin sarki -; domin cewa dukkanin littattafan sama, suna furuci da haka: da abin da suka zo da shi na daga hukunce-hukunce na adalci waɗanda suka ƙunshi maslahohin halitta, dalili ne a bisa cewa, su daga Ubangiji Gwani Masani da maslahohin halittarSa suke. Da abin da suka zo da shi na daga labarai na kasantacce waɗanda waƙi'i ya shaida da gaskiyarsu, dalili ne a bisa cewa su daga Ubangiji Mai iko a bisa samar da abin da Ya bada labari da shi suke.
4- Amma dalilan riska ta sarari a bisa samuwar Allah - Maɗaukakin sarki -: To tana daga fuskoki biyu:
Ɗaya daga cikinsu: Cewa mu muna ji kuma muna gani na amsawa masu roƙo da agazawa masu neman ɗauki, abin da yake nuni nuni yankakke a bisa samuwarSa - Maɗaukakin sarki -. Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce: {Kuma Nũhu, a sa'ad da ya yi kira a gabãni, sai Muka karɓa masa...} [al- Anbiya': 76]. Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {A lõkacin da kuke nẽman Ubangijinku taimako, sai Ya karɓa muku...} [al-Anfal: 9].
A cikin «Sahihul Bukhari» daga Anas bin Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: «Haƙiƙa wani balaraben ƙauye ya shigo ranar Juma’a - alhalin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana huɗuba -, sai ya ce: Ya Manzon Allah, dukiya ta halaka, iyalai sun yunwata, ka roƙar mana Allah; sai ya ɗaga hannayensa ya yi addu’a, sai girgije ya ta so ya yaɗu, kamar duwatsu, bai gushe ba a kan mimbarinsa, har na ga ruwan sama yana ɗiga daga gemunsa» [6]. [6] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin Juma'a, babin istisqa'i a huɗubar Juma'a, lamba ta (891).
A cikin kuma Juma'a ta biyu, sai wannan balaraben ƙauyen ya tashi, ko waninsa ya ce: Ya Manzan Allah, gini ya rushe, kuma dukiya ta dulmiye, ka roƙar mana Allah, sai ya ɗaga hannayensa, kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: «Ya Allah a kewayenmu, ba a kanmu ba». «To, duk inda ya yi ishara, sai ya rabu» [7]. [7] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin Juma'a, babin istisƙa'i a huɗuba ranar Juma'a, lamba ta (891), da Muslim a littafin sallar istisƙa'i, babin addu'a a istisƙa'i, lamba ta (897).
Kuma amsawar masu Addu’a bai gushe ba yana wani lamari abin shaidawa (gani) har zuwa wannan zamaninmu, ga wanda ya gasgata fakewa da miƙa lamarinsa ga Allah- Maɗaukakin sarki - ya kuma zo da sharuɗɗan amsawa.
Fuska ta biyu: Haƙiƙa ayoyin Annabawa waɗanda ake kiransu da mu'ujizozi, kuma mutane suke ganinsu, ko suke jin su hujja ce yankakkiya a bisa samuwar Mai aiko su, Shi ne Allah - Maɗaukakin sarki -; domin su wasu al'amura ne da suka fita (wuce) ikon ɗan Adam. Allah - Maɗaukakin sarki - Yana gudanar da su, don ƙarfafawa ga ManzanninSa da kuma taimako a gare su.
Misalin haka: Mu'ujizar (Annabi) Musa- amincin Allah ya tabbata a gare shi - Allah - Maɗaukakin sarki - Ya umarce shi da ya buga sandarsa a kan kogi, sai ya buga ta, sai ya tsage goma sha biyu hanya bushasshiya, ruwa kuma a tsakaninsu kamar duwatsu. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa 'Ka dõki tẽku da sandarka.' Sai tẽku ta tsãge, kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma 63} [ash- Shu'ara': 63].
Misali na biyu kuma: Mu'ujizar (Annabi) Isa - amincin Allah ya tabbata a gare shi - ta yadda yake rayar da matattu, kuma ya fito da su daga ƙabarurrukansu da izinin Allah. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya faɗa game da shi: {...kuma ina rãyar da matottu, da izinin Allah...} [āli- Imran: 49]. Kuma Ya ce: {...kuma a lõkacin da kake fitar da matattu da izinĩNa...} [al- Ma'ida: 110].
Misali na uku kuma: Na (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- lokacin da ƙuraishawa suka nemi mu'ujiza daga gare shi, sai ya yi nuni zuwa ga wata, sai ya tsage tsagi biyu, mutane suka gan shi, a kan haka ne faɗarSa - Maɗaukakin sarki -: {Sã'a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge. 1 Idan sun ga wata ãyã, sai su yi watsi da ita, kuma su ce: sihiri ne mai ci gaba 2} [al-Ƙamar: 1-2].
Waɗannan mu'ujizozin da aka gani, waɗanda Allah - Maɗaukakin sarki - Yake gudanar da su, don ƙarfafawa ga ManzaninSa, da kuma taimako a gare su, suna nuni, nuni yankakke a bisa samuwarsa - Maɗaukakin sarki -.
Al'amari na biyu daga abin da imani da Allah ya ke ƙunshe da shi: Imani da RububiyyarSa, ai cewa Shi kaɗai ne Ubangiji ba Shi da abokin tarayya ko mai taimako.
Ubangiji: Shi ne wanda halitta, da mulki, da umarni, suka tabbata a gare Shi, babu wani mahalicci ko mamallaki sai Shi, babu wani umarni sai gare Shi. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {...To, Shĩ ne da halittar kuma da umurnin...} [al-A'raf: 54]. Kuma Ya ce: {...Wannan Shĩ ne Allah, Ubangijinku, gare Shi mulki yake, kuma waɗanda kuke kira waninSa bã su mallakar kõ fãtar gurtsun dabĩno.} [Faɗir: 13].
Ba a san cewa wani daga halitta ya yi musun Rububiyyar Allah - tsarki ya tabbatar maSa - ba, sai dai in ya kasance mai girman kai ne, ba mai ƙudirce abin da yake faɗa ba, kamar yadda ya faru ga Fir'auna, ya yin da ya ce da mutanansa: {Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka 24} [an-Nazi'at: 24]. Kuma Ya ce: {...Yã ku mashãwarta! Ban san kunã da wani abin bautãwa baicina ba...} [al-Ƙasas: 38], sai dai hakan bai zama daga aƙida ba. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma suka yi musunsu, alhãli zukãtansu sun natsu da su dõmin zãlunci da girman kai...} [an-Naml: 14]. Kuma (Annabi) Musa - aminci ya tabbata a gare shi - ya ce wa Fir'auna, kamar yadda Allah Ya ba da labari game da shi: {...Haƙĩƙa ka sani bãbu wanda ya saukar da waɗannan, fãce Ubangijin sammai da ƙasa dõmĩn su zama abũbuwan lũra. Kuma lalle ne ni, haƙĩƙa, ina zaton ka, yã Fir'auna, halakakke.} [al-Isra': 102]. Saboda wannan ne mushirikai suka kasance suke tabbatar da Rububiyyar Allah - Maɗaukakin sarki -, tare kuma da yadda suke masa tarayya a Uluhiyya. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ka ce: "Wane ne da mulkin ƙasa da wanda ke a cikinta, idan kun kasance kunã sani?"84 Za su ce: "Allah ne." Ka ce: "Ashe, ba ku tunãni? 85 Ka ce: "Wane ne Ubangijin sammai bakwai da Ubangijin Al'arshi mai girma?"86 Za su ce: "Allah ne." Ka ce: "Ashe, ba ku jin tsoronSa?"87 Ka ce: "Wane ne a hannunSa mulkin dukkan kõme, kuma Shi ne ke bayar da kariya, kuma ba a iya bayar da kariya daga gare Shi, idan kun kasance kunã sani?"88 Za su ce: "Allah ne." Ka ce: "To, yaya kuke yin sihiri? 89} [al- Mu'minun: 84-89].
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma lalle ne, idan ka tambaye su, "Wãne ne ya halitta sammai da ƙasa?" Lalle zã su ce, "Mabuwãyi Mai ilmi ne Ya halitta su 9} [az-Zukhruf: 9].
Kuma - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce: {Kuma lalle idan ka tambaye su: 'Wãne ne ya halitta su?' Lalle ne zã su ce Allah ne. To, yãya ake jũyar da su? 87} [az-Zukhruf: 87].
Lamarin Allah - tsarkakken sarki -, mai gamewa ne ga lamari na kasantacce da na shari'a, kamar yadda Shi ne Mai tsara kasantacce mai hukunci a cikinsa, da abin da Yake nufi, gwargwadan abin da hikimarSa take hukuntarwa. To, kuma Shi ne hakanan Mai hukunci a cikinsa da shar'anta ibadu, da hukunce-hukuncen ma'amaloli gwargwadan yadda hikimarSa take hukuntarwa. Wanda ya riƙi wani mai shar'antawa tare da Allah - Maɗaukakin sarki -, ko (ya riƙi) wani mai hukuntawa a mu'amaloli, to haƙiƙa ya yi shirka da Shi, kuma bai tabbatar da imani ba.
Lamari na uku daga abin da imani da Allah yake ƙunsarsa: Imani da Uluhiyyarsa, wato: Cewa Shi kaɗai ne abin bautawa da gaskiya, ba Shi da abokin tarayya, kalmar (Ilāhu) da ma'anar (al-ma'lūh) wato (abin bautawa) don so da kuma girmamawa.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma Ubangijinku Ubangiji Guda ne. Bãbu wani abin bautawa da cancanta fãce Shi, Mai rahama, Mai jin ƙai 163} [al-Baƙara: 163]. Kuma (Allah) Maɗaukakin sarki Ya ce: {Allah Ya shaida cẽwa: Lalle ne bãbu abin bautãwa da cancanta fãce Shi kuma malãiku da ma'abũta ilmi sun shaida, yana tsaye da ãdalci, bãbu abin bautãwa da cancanta face Shi, Mabuwãyi, Mai hikima 18} [āli-Imran: 18]. Duk wanda ya riƙi wani abin bautawa tare da Allah, yake bautawa waninSa, to, Uluhiyyarsa ɓatacciya ce. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Wancan! sabõda lalle ne Allah, shĩ ne Gaskiya, kuma lalle ne, abin da suke kira waninSa shi ne ƙarya. Kuma lalle ne Allah, Shĩ ne Maɗaukaki, Mai girma 62} [al-Hajj: 62]. Kuma ambatonsu Alloli da akayi ba ya ba su can-cantar Allantaka, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce dangane da {Laata, da Uzza, da Manaata}: {Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba...} [an-Najm: 23].
Kuma Ya ce dangane da (Annabi) Hudu - amincin Allah ya tabbata a gare shi - cewa shi ya ce wa mutanensa: {...Shin, kunã jãyayya da ni a cikin wasu sunãye waɗanda kũ ne kuka yi musu sunãyen, kũ da ubanninku, Allah bai saukar da wani dalili ba a gare su...?} [al-A'raf: 71].
Kuma Ya ce dan gane da (Annabi) Yusuf - amincin Allah ya tabbata a gare shi- cewa shi ya ce wa abokansa na kurukuku su biyu: {Yã abõkaina biyu na kurkuku! Shin iyãyen giji dabam-dabam ne mafiya alhẽri kõ kuwa Allah Makaɗaici Mai tanƙwasãwa? Ba ku bauta wa kõme ba, baicin sũnãye waɗanda kuka sanya musu, kũ da ubanninku, Allah bai saukar da wani dalĩli ba game da su...} [Yusuf: 39-40].
Saboda wannan ne manzanni- tsira da amincin Allah su tabbata a gare su- suka kasance, suna cewa mutanansu: {...Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa waninsa...} [al-A'raf: 59] Sai dai mushirikai sun ƙi hakan, suka riƙi alloli koma bayan Allah, suna bauta musu tare da Allah - tsarkakakken sarki kuma Maɗaukaki - suna neman taimakonsu da agajinsu.
Kuma haƙiƙa- Allah - Maɗaukakin sarki- Ya ɓata riƙar waɗannan iyayengjin da hujjoji biyu na hankali:
Na farko: Cewa babu wani abu daga cikin abubuwan da suka keɓanci allantaka a tare da waɗannan allolin da suka riƙe. Su halittarsu aka yi, ba sa halitta, ba sa jawo wani anfani ga masu bauta mu su, kuma ba sa tunkuɗe wata cuta daga gare su, kuma ba sa mallakar rayuwa ko mutuwa a gare su, kuma ba sa mallakar wani abu daga sammai, ba sa kuma tarayya a cikinsa.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma suka riƙi abũbuwan bautawa, baicin Shi, bã su yin halittar kõme alhãli sũ ne ake halittãwa kuma bã su mallakar wa kansu wata cũta ko wani amfãni, kuma bã su mallakar mutuwa kuma bã su mallakar rãyarwa, kuma bã su mallakar tãyarwa 3} [al-Furƙan: 3].
Kuma (Allah) Maɗaukakin sarki Ya ce: {Ka ce: "Ku kirãyi waɗanda kuka riya (cẽwa abũbuwan bautãwa ne) baicin Allah, bã su Mallakar ma'aunin zarra a cikin sammai, kuma bã su Mallakarsa a cikin ƙasa kuma bã su da wani rabon tãrẽwa a cikinsu (sammai da ƙasa), kuma bã Shi da wani mataimaki daga gare su. Kuma cẽto bã ya amfanarwa a wurinSa fãce ga wanda Ya yi izni gare shi...} [Saba'i: 22-23]. Kuma Madaukakin sarki Ya ce: {Shin, sunã shirki da abin da bã ya halittar kõme, kuma sũne ake halittãwa? 191 Kuma bã su iyãwa gare su taimako, kuma bã su taimakon kansu 192} [al-A'raf: 191-192].
Idan wannan ya kasance shi ne halin waɗancan iyayen giji (ababen bauta), to haƙiƙa riƙarsu a matsayin ababen bauta, yana daga mafi girman wauta, kuma ɓarna mafi ɓaci.
Na biyu: Haƙiƙa waɗannan mushirikan sun kasance suna tabbatar da cewa Allah - Maɗaukakin Sarki - Shi kaɗai ne Ubangiji Mahalicci, wanda mulkin kowanne abu ke hannunSa, Shi Yana amintar da wanda Ya so, kuma ba'a amintar da wanda Ya yi nufin azabtarwa; wannan yana lazimta musu su kaɗaita Shi da Uluhiyya, kamar yadda suka kaɗaita Shi da Rububiyya, kamar yadda (Allah) Maɗaukkain sarki Ya ce: {Yã ku mutãne! Ku bauta wa Ubangjinku, Wanda Ya halicce ku, kũ da waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku ku kãre kanku! 21 Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, da sama gini, kuma Ya saukar da ruwa daga sama, Ya fitar da 'ya'yan itãce da shi, arziki a gare ku. Sabõda haka, kada ku sanya wa Allah abõkan tarayya, alhãli kuwa kũ kunã sani 22} [al-Baƙara: 21-22].
Kuma (Allah) Maɗaukakin sarki Ya ce: {Kuma lalle idan ka tambaye su: 'Wãne ne ya halitta su?' Lalle ne zã su ce Allah ne. To, yãya ake jũyar da su? 87} [az-Zukhruf: 87].
Kuma (Allah) - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ka ce: "Wãne ne Yake azurtã ku daga sama da ƙasa? Shin kõ kuma Wãne ne Yake mallakar jĩ da ganĩ, kuma Wãne ne Yake fitar da mai rai daga mamaci, kuma Ya fitar da mamaci daga mai rai, Kuma Wãne ne Yake shirya al'amari?" To, zã su ce: "Allah ne." To, ka ce: "Shin fa, bã zã ku yi taƙawa ba?" 31 Wannan Allah ne Ubangijinku na gaskiya. To, me ke akwai bayan gaskiya fãce ɓata? To, yãya ake karkatar da ku? 32} [Yunus: 31-32].
Lamari na huɗu daga abin da imani da Allah yake ƙunshe da shi: Imani da sunayenSa da kuma siffofinSa:
Yana nufin: Tabbatar da abin da Allah Ya tabbatarwa kanSa a cikin littafinSa, ko sunnar ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - na daga sunaye da siffofi, a bisa fuska da ta dace da Shi, ba tare da canja ko kore ko tambayar ya ya suke ba ko kuma kamanta (siffofi da sunayenSa) ba. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma Allah Yanã da sũnãye mãsu kyau. Sai ku rõƙe shi da su, kuma ku bar waɗanda suke yin ilhãdi a cikin sũnãyenSa: zã a sãka musu abin da suka kasance sunã aikatãwa 180} [al-A'raf: 180]. Kuma (Allah) - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {...Kuma Yanã da misãli wanda ya fi ɗaukaka a cikin sammai da ƙasã kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai hikima} [ar-Rum: 27]. Kuma (Allah) - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {...wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani} [ash-Shura:11].
Haƙiƙa jama'a biyu sun ɓata a wannan lamari:
Na farkonsu: (Masu korewa) waɗanda suka yi musun sunayen da siffofin, ko sashinsu, suna masu riya cewa, tabbatar da su ga Allah zai lazimtar da kamanceceniya, wato: Kamanta Allah - Maɗaukakin sarki - da halittunSa, wannan riyawa ɓatacciya ce, saboda wasu fuskoki, daga cikin fuskokin:
Na farko: Cewa shi yana lazimtar da lazimai ɓatacciya, kamar warwara a cikin zancen Allah tsarkakken sarki, hakan kuwa cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya tabbatarwa kanSa sunaye da siffofi, kuma Ya kore wani abu ya zama tamkarSa. Da a ce tabbatar da su yana lazimtar da kamanceceniya, da tufka da warwara sun tabbata a cikin zancen Allah, da kuma ƙaryata sashinsa da sashi, (tsarki ya tabbata ga Allah).
Na biyu: Cawa haɗuwar abubuwa biyu a suna ko siffa ba ya lazimtar da su kasance masu kamanceceniya, kai kana ganin mutane biyu suna haɗuwa a cewa kowannensu mutum ne mai ji, mai gani mai magana. Ba ya lazimtuwa daga haka su yi kamanceceniya a ma'anoni na mutuntaka, ji, da gani, da magana,
Za ka ga dabbobi suna da hannaye, da ƙafafu, da idanuwa, haɗuwarsu a wannan ba ya lazimtar da hannayensu da ƙafafuwansu da idanuwansu su kasance masu kamanceceniya.
Idan nisan banbanci ya bayyana, tsakanin ababen halitta, cikin abin da suka haɗu a cikinsa, na daga sunaye da siffofi, to nisan bambanci tsakanin Mahalicci da ababen halitta, shi ya fi bayyana kuma ya fi girma.
Jama'a ta biyu: (Masu kamantawa) waɗanda suka tabbatar da sunayen da siffofin, tare da kamanta Allah - Maɗaukakin sarki - da halittarSa. Suna masu riya cewa wannan shi ne hukuncin abin da nassoshi suka yi nuni da shi, domin Allah Yana magana da bayi da abin da za su fahimta, wannan riyawar ɓatacciya ce, saboda wasu fuskoki, daga cikin fuskokin:
Na farko: Cewa kamantuwar Allah - Maɗaukakin sarki - da halittarSa lamari ne da hankali da shria'a za su ɓata su, kuma ba zai yi wu ba, abin da nassosin littafi da sunna suka hukuntar ya kasance lamari ɓatacce.
Na biyu: Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi magana da bayi da abin da za su fahimta daga asalin ma'ana, amma haƙiƙar abin da waccan ma'anar take kansa, to shi yana daga abin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya keɓanta da saninsa cikin abin da yake da alaƙa da zatinSa da kuma siffofinSa.
Idan Allah Ya tabbatarwa kanSa cewa Shi Mai ji ne: To haƙiƙa ji sananne ne ta ɓangaran ma'ana (shi ne riskar sautuka), sai dai haƙiƙar haka dangane da jin Allah - Maɗaukakin sarki - ba abin sani ba ne; domin haƙiƙar ji tana nisantar juna har ga ababen halitta, to nisantarta tsakanin Mahalicci da ababen halitta shi ya fi bayyana kuma yafi girma.
Idan Allah - Maɗaukakin sarki - Ya bada labari game da kanSa cewa Shi Ya daidaita a kan Al'arshinSa, to haƙiƙar daidaituwa ta ɓangaren asalin ma'ana sananniya ce, sai dai haƙiƙar daidaituwa wacce Shi Yake a kanta ba sananniya ba ce a gare mu, dangane da daidaituwar Allah a kan Al'arshinSa, domin haƙiƙar daidaituwa tana bambantar juna a haƙƙin abin halitta. Daidaituwa a kan kujera tabbacciya ba ta zamo ba kamar daidaituwa a kan siddin raƙumi mai wahalarwa mai tirjiya ba, idan ta bambanta a haƙƙin abin halitta, to bambantarta tsakanin Mahalicci da abin halitta shi ya fi bayyana kuma ya fi girma.
Imani da Allah - Maɗaukakin sarki - a bisa abin da muka siffanta yana samarwa mumini fa'idoji masu girma, daga cikinsu akwai:
Ta farko: Tabbatar da kaɗaitakar Allah - Maɗaukakin sarki -, ta yadda ƙauna ko tsoro ba za su ratayu da waninSa ba, kuma ba za'a bautawa waninSa ba.
Ta biyu: Cikar son Allah - Maɗaukakin sarki - da girmama Shi, gwargwadon abin da sunayenSa kyawawa da siffofinSa maɗaukaka suka hukunta.
Ta uku: Tabbatar da bauta maSa da aikata abin da Ya yi umarni da shi, da kuma nisantar abin da Ya yi hani agare shi.
*
IMANI DA MALA'IKU
Mala'iku: Wata duniya ce ta gaibu, ababen halitta, masu bautar Allah - Maɗaukakikn sarki -, ba su da wani abu daga abubuwan da suka keɓanci Rububiyyah ko Uluhiyya. Allah - Maɗaukakikn sarki - Ya halicce su daga haske, Ya kuma ba su cikakken miƙa wuya ga umarninSa da ƙarfi a bisa zartar da shi. Allah - Maɗaukakikn sarki - Ya ce: {...Kuma waɗanda suke wurinSa bã su yin girman kai ga ibãdarSa kuma bã su gajiya, suna tasbĩhi dare da yini bã su kasala} [al-Anbiya': 19-20].
Kuma su adadi ne mai yawa, babu mai ƙididdigesu sai Allah - Maɗaukakin Sarki -. Haƙiƙa ya tabbata a cikin Bukhari da Muslim daga hadisin Anas - Allah Ya yarda da shi - a ƙissar mi'iraji cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - an ɗago masa Baitul Ma'muur a sama, kowacce rana Mala'iku dubu saba'in ne suke yin sallah a cikinsa, idan suka fita ba sa dawowa zuwa gare shi, ƙarshen abin da ke a kansu.
Imani da Mala'iku yana ƙunsar al'amura huɗu:
Na farko: Imani da samuwarsu.
Na biyu: Imani da wanda muka san sunansa daga cikinsu da sunansa, (kamar Jibril) waɗanda ba mu san sunansu ba, mu yi imani da su a dunƙule.
Na uku: Imani da abinda muka sani daga siffofinsu, kamar siffar (Jibril). Haƙiƙa Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya bada labarin cewa shi ya gan shi a siffarsa wacce aka halicce shi a kanta, yana da fuka-fukai ɗari shida, haƙiƙa ya rufe sasannin sama.
Kuma haƙiƙa Mala'ika ya kan iya canzawa da umarnin Allah - Maɗaukakikn sarki - zuwa kamannin wani mutum, kamar yadda ya faru ga (Jibril) a lokacin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya aike shi zuwa ga Nana Maryam, sai ya kamantu da mutum daidaitacce a gare ta, kuma a lokacin da ya zo zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - alhalin shi yana zaune a cikin sahabbansa, ya zo masa da siffar wani mutum mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baƙin gashi, ba a ganin alamar tafiya a gare shi, kuma babu ɗaya daga sahabbansa wanda ya san shi. Sai ya zauna zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya jingina gwiwoyinsa zuwa gwiwoyinsa, ya kuma ɗora tafukan hannayensa a kan cinyoyinsa, ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - dangane da Musulunci, da Imani, da Kyautayi, da tashin al-ƙiyama, da alamominta; sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya amsa masa, sannan ya tafi, sa’an nan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wannan Jibril ne; ya zo muku ne ya sanar da ku Addinink" [8]. [8] Muslim ne ya fitar da shi: Littafin Imani, Babin bayanin Imani da Musulunci da Ihsani da wajabcin yin imani da ƙaddarar Allah - Maɗaukakin Sarki -, lamba ta (8).
Hakanan Mala'iku waɗanda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya aika su zuwa (Annabi) Ibrahim da (Annabi) Luɗu sun kasance ne a bisa surar mutane (mazaje).
Na huɗu daga abin da imani da mala'iku yake ƙunsarsa: Imani da abin da muka sani na daga ayyukansu, waɗanda suke tsayawa da su da umarnin Allah - Maɗaukakin Sarki - kamar tsarkake Shi, da bauta maSa dare da rana, ba tare da ƙosawa ko rauni ba.
Kuma wasunsu yakan kasance suna da wasu ayyuka na musamman.
Misalin: Jibril amintacce ne a bisa wahayin Allah - Maɗaukakin sarki. Allah Yana aika shi da shi (wahayi) zuwa Annabawa da Manzanni.
Kuma misalin: Mika'ilu: wanda aka wakilta shi ga ruwan sama da tsirrai.
Hakanan misalin Isrāfil: Wanda aka wakilta ga busa a cikin ƙaho a lokacin tashin alƙiyama da tasowar halitta.
Kuma kamar Mala'ikan mutuwa: Wanda aka wakilta ga karɓar rayuka a lokacin mutuwa.
Da misalin Malik: Wanda aka wakilta ga wuta, shi ne mai tsaron wuta.
Kuma kamar misalin: Mala'iku waɗanda aka wakilta ga 'yan tayi a cikin mahaifa, idan mutum ya cika wata huɗu a cikin mahaifiyarsa, sai Allah Ya aiko mala'ika zuwa gare shi, ya umarce shi da rubuta arziƙinsa, da ajalinsa, da aikinsa, shaƙiyyi ne ko mai arziƙi ne.
Da misalin: Mala'iku waɗanda aka wakilta su da kiyaye ayyukan 'yan Adam da rubuta su, kowanne mutum yana da mala'iku biyu, ɗayansu a dama, ɗayan kuma a hagu.
Kuma misalin: Mala'iku waɗanda aka wakilta su da tambayar mamaci idan aka sa shi a cikin ƙabari; mala'iku biyu suna zuwar masa, suna tambayarsa, dangane da Ubangijinsa, da Addininsa, da Annabinsa.
Imani da Mala'iku yana haifar da fa'idoji masu girma, daga cikinsu:
Ta farko: Sanin girman Allah - Maɗaukakin sarki -, da ƙarfinSa, da sarautarSa; domin cewa girman ababen halitta yana nuni a bisa girman Mai halitta.
Ta biyu: Godewa Allah- Maɗaukakin sarki- a bisa kulawarSa da 'yan Adam, ta yadda ya wakilta daga waɗannan Mala'ikun, waɗanda suke tsayawa da kiyaye su, da rubuta ayyukansu, da wanin hakan daga maslahohinsu.
Ta uku: Son mala'iku a bisa abin da suka tsaya da shi na bautar Allah - Maɗaukakin sarki -.
Kuma haƙiƙa wasu mutane daga karkatattu sun yi musun kasancewar mala'iku suna da jiki, suka ce: Haƙiƙa su bayani ne a kan ƙarfin alkhairi wanda ya tabbatu a cikin ababen halitta. Wannan ƙaryatawa ne ga littafin Allah- Maɗaukakin sarki- da sunnar ManzanSa -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- da haɗuwar musulmai.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Gõdiya ta tabbata ga Allah, Mai fãra halittar sammai da ƙasã, Mai sanya malã'iku manzanni mãsu fukãfukai, bibbiyu, da uku-uku da hurhuɗu...} [Faɗir: 1].
Kuma (Allah) Maɗaukakin sarki Ya ce: {Kuma dã kã gani, a lõkacin da Malã'iku suke karɓar rãyukan waɗanda suka kãfirta, sunã dukar fuskõkinsu da ɗuwãwunsu...} [al-Anfal: 50].
Kuma (Allah) Maɗaukakin sarki Ya ce: {...Kuma dã kã gani, a lõkacin da azzãlumai suke cikin mãyen mutuwa, kuma malã'iku sunã mãsu shimfiɗa hannuwansu, (sunã ce musu) "Ku fitar da kanku;...} [al-An'am: 93].
Kuma (Allah) Maɗaukakin sarki Ya ce: {...Har a lõkacin da aka kuranye tsõro daga zukãtansu, sai su ce, 'Mẽne ne Ubangijinku Ya ce?' Suka ce: 'Gaskiya', kuma shi ne Maɗaukaki, Mai girma} [Saba'i: 23].
Kuma - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce game da 'yan aljanna: {...Kuma malã'iku sunã shiga zuwa gunsu ta kõwace kõfa, Salãmun alaikum sabõda abin da kuka yi haƙuri. To madalla da ãƙibar gida} [ar-Ra'd: 23-24].
Kuma ya zo a cikin Sahihul Bukhari daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan Allah Ya so bawa sai Ya kira (Mala'ika) Jibril: Lallai Allah Yana son wane to kaima ka so shi, sai Jibril ya so shi, sannan ya yi yekuwa ga 'yan sama: Cewa Allah Yana son wane to kuma ku so shi, sai 'yan sama su so shi, sannan a sanya masa karɓuwa a ƙasa.[9] [9] Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin farkon halitta, Babin bayanin Mala'iku, a lamba ta (3037), da Muslim: Littafin alheri da sada zumunci da ladabi, Babin idan Allah Ya so wani bawa, sai Ya sanya shi abin so ga bayinSa, a lamba ta (2637).
Ya zo kuma a cikinsa daga Abu Huraira-Allah Ya yarda da shi- Ya ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: "Idan ranar Juma'a ta zo, ya kasance a kowace ƙofa daga ƙofofin masallaci akwai Mala'iku suna rubuta na farko sai na farko, idan liman ya zauna (a kan munbari) sai su ninke takardun, su zo suna sauraren zikiri (Huɗuba)" [10]. [10] Bukhari ne ya fitar da shi a littafin Jumu'a, babin sauraron huɗuba, lamba ta (887), da Muslim a cikin littafin Jumu'a, babin falalar yin wuri ranar Jumu'a, lamba ta (850).
Waɗannan nassosi bayyanannu ne a kan cewa Mala’iku jukkuna ne, ba ƙarfi ba ne na ma’ana, kamar yadda karkatattu suka faɗa, kuma a kan abin da waɗannan nassosi suka hukunta musulmai suka haɗu.
*
IMANI DA LITTATTAFAI
Littattafai: Jam'i ne na (littafi) da ma'anar (abin rubutawa).
Abin nufi da su a nan: Littattafai waɗanda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da ga ManzanninSa, don rahama ga halitta da shiryarwa a gare su, don su sadu da su zuwa arziƙi a dunya da lahira.
Imani da littattafai yana ƙunsar al'amura huɗu:
Na farko: Imani da cewa saukarsu daga Allah gaskiya ne.
Na biyu: Imani da abin da muka san sunansa daga gare su da sunansa: Kamar Alƙur'ani da aka saukar ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da Attaura wacce aka saukar ga (Annabi) Musa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da Injiila wacce aka saukar ga (Annabi) Isa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da Zabura wacce aka saukar ga (Annabi) Dauda - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - amma abin da ba mu san sunansa ba, muna imani da shi a dunƙule.
Na uku: Gasgata abin da ya inganta daga labaransu, kamar labaran Alƙur'ani, da labaran abin da ba a canza ko jirkita ba daga littattafan da suka gabata.
Na huɗu: Aiki da hukunce-hukunce a abin da ba a shafe ba daga gare su, da kuma yarda da miƙa wuya da shi, daidai ne shin mun fahimci hikimarsa, ko ba mu fahimce ta ba. Dukkan littattafan da suka gabata waɗanda aka shafe ne da Alƙur’ani mai girma. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma Mun saukar da Littãfi zuwa gare ka da gaskiya, yanã mai gaskatãwa ga abin da yake a gaba gare shi daga Littãfi (Attaura da Injĩla), kuma mai halartãwa a kansa...} [al-Ma'ida: 48]. Wato: Mai hukunci a kansa.
A kan haka ne: Yin aiki da kowanne irin hukunci daga hukunce-hukuncen littattafan da suka gabata ba ya halatta, sai abin da ya inganta daga gare su, kuma Alƙur'ani ya tabbatar da shi.
Imani da lttattafai yana samar da fa'idoji masu girma, daga cikinsu:
Ta farko: Sanin kulawar Allah - Maɗaukakin sarki - ga bayinSa, ta yadda Ya saukarwa kowacce al'umma littafin da yake shiryar da su da shi.
Ta biyu: Sanin hikimar Allah - Maɗaukakin sarki - a shar'antawarSa ta yadda Ya shar'antawa kowacce al'umma abin da yake dacewa da halayensu, Kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce: {...Ga kõwanne daga gare ku Mun sanya sharĩa da hanya (ta bin ta...} [al-Ma'ida: 48].
Ta uku: Godewa ni'imar Allah a bisa haka.
*
IMANI DA MANZANNI
Manzanni jam'i ne na (Manzo) da ma'anar (abin aikowa) wato abin aikowa da isar da wani abu.
Abin nufi a nan: Wanda aka yi wahayi zuwa gare shi daga 'yan Adam, da wata shari'a kuma aka yi umarni da ya isar da ita.
Farkon Manzanni (Annabi) Nuhu - amincin Allah ya tabbata a gare shi -, na ƙarshensu kuma (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Lalle ne Mu, Mun yi wahayi zuwa gare ka, kamar yadda Muka yi wahayi zuwa ga Nũhu da annabãwa daga bãyansa...} [an-Nisa': 163].
A cikin «Sahihul Bukhari» daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - a cikin Hadisin ceto cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: «An ambaci cewa mutane za su zo zuwa (Annabi) Adam, don ya nema musu ceto, sai yai hanzari a gare su, yace: Ku je (wurin) (Annabi) Nuhu farkon Manzon da Allah Ya aiko shi". Sai ya ambaci cikar hadisin [11]. [11] Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin Tauhidi, Babin faɗin Allah - Maɗaukakin Sarki -: ﴾لِمَا خَلَقْتُ بِيَدَيَّ﴿, lamba ta (7410), da Muslim: Littafin Imani, Babin mafi ƙanƙantar matsayin mutumin Aljanna a cikinta, lamba ta (193).
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce a sha'anin (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: {Muhammadu bai kasance uban kõwa ba daga mazanku, kuma amma shĩ yã kasance Manzon Allah kuma cikamakin Annabãwa...} [al-Ahzab].
Kuma babu wata al'umma da ta zamo bata da wani Manzo da Allah - Maɗaukakin sarki - zai aiko shi da wata shari'a keɓantacciyya zuwa mutanensa, ko wani Annabi da zai yi wahayi zuwa gare shi da wata shari'ar waɗanda suka gabace shi, don ya sabuntata. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): 'Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ɗãgũtu...} [an-Nahl: 36].
Kuma (Allah) Maɗaukakin sarki Ya ce: {...Kuma bãbu wata al'umma fãce wani mai gargaɗi yã shũɗe a cikinta} {Faɗir: 24}.
Kuma (Allah) Maɗaukakin sarki Ya ce: {Lalle ne Mu, Mun saukar da Attaura, a cikinta akwai shiriya da haske Annabãwa waɗanda suke sun sallamã, sunã yin hukunci da ita ga waɗanda suka tuba (Yahudu)...} [al-Ma'ida: 44].
Manzanni 'yan Adam ne ababen halitta, ba su da wani abu da ya keɓanci Rububiyyah ko Uluhiyya. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya faɗa dan gane da AnnabinSa Muhammad kuma shi ne shugaban Manzanni, mafi girmansu da ɗaukaka a gurin Allah: {Ka ce: "Bã ni mallaka wa raina wani amfãni, kuma haka ban tunkuɗe wata cũta, fãce abin da Allah Ya so. Kuma dã na kasance inã sanin gaibi, dã lalle ne, nã yawaita daga alhẽri kuma cũta bã zã ta shãfe ni ba, nĩ ban zama ba face mai gargaɗi, kuma mai bãyar da bishãra ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni 188} [al-A'raf: 188] .
Kuma (Allah) Maɗaukakin sarki Ya ce: {Ka ce: "Lalle ne, nĩ bã ni mallakar wata cũta gare ku, kuma bã ni mallakar wani alhẽri." 21 Ka ce: "Lalle ne, bãbu wanda zai tsĩrar da ni daga Allah, kuma bã zan sãmi wani mafaka ba, baicinSa 22} [al-Jinn: 21-22].
Kuma abubuwan da suka keɓanci 'yan Adam suna riskarsu: Na daga rashin lafiya, da mutuwa, da buƙatuwa zuwa abinci da abin sha, da wanin haka. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce dangane da (Annabi) Ibrahim - amincin Allah ya tabbata a gare shi a siffantawarsa ga Ubangijinsa - Maɗaukakin sarki -: {Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni. 79 Kuma idan na yi rashin lafiya, Shĩ ne Yake warkar da ni. 80 Kuma Wanda Yake kashẽ ni, sa'an nan Yake rãyar da ni 81} [ash-Shu'ara': 79-81].
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Kaɗai ni mutum ne kamar ku, ina yin mantuwa kamar yadda ku ke mantuwa, idan na manta ku tunartar da ni» [12]. [12] Bukhari ne ya fitar da shi: Babukan alƙibla, babin fuskantar alƙibla a duk inda aka kasance, lamba ta (392), da Muslim: Littafin masallatai da wuraren sallah, babin mantuwa a cikin sallah, da sujjadar rafkanuwa, lamba ta (572).
Haƙaƙa Allah - Maɗaukakin sarki- Ya siffanta su da yi masa bauta a mafi ɗaukakar matsayinsu, a kuma siyaƙin yabo a gare su; Sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce game da (Annabi) Nuhu - aminci ya tabbata a gare shi -: {...Lalle ne shi ya kasance wani bãwa mai gõdiya} [al-Isra': 3]. Kuma Ya faɗa a sha'anin (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: {Albarka ta tabbata ga wanda Ya saukar da (Littãfi) mai rarrabẽwa a kan bãwanSa, dõmin ya kasance mai gargaɗi ga halitta 1} [al-Furƙan: 1].
Kuma Ya faɗa dangane da (Annabi) Ibrahim, da (Annabi) Ishaƙ, da (Annabi) Ya'aƙub - tsira da amincin Allah su tabbata a gare su -: {Kuma ka ambaci bãyinMu: Ibrahĩm da ls'hãƙa da Ya'aƙũba, ma'abũta ƙarfin (ɗaukar umurnin Mu) da basĩra. 45 Lalle ne, Mun tsarkake su da tsarkakakkiyar tunãtarwa ta gidan (lahira) 46. Kuma lalle ne, su a wurin Mu, tabbas, sunã daga cikin zababbun mãsu alhẽri 47} [Sād: 45-47].
Ya ce a kan sha'anin (Annabi) Isa ɗan Maryam: {Shi (ɗan Maryama) bai zama ba fãce wani bãwa ne, Mun yi ni'ima a gare shi, kuma Muka sanya shi abin kõyi ga Banĩ Isrã'ĩla 59} [az-Zukhruf: 59].
Imani da Manzanni yana ƙunsar al'amura huɗu:
Na farko: Imani da cewa saƙonsu gaskiya ne daga Allah - Maɗaukakin sarki - yake, wanda ya kafirce da saƙon ɗaya daga cikinsu, to haƙiƙa ya kafircewa dukkaninsu, kamar yadda Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce: {Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni 105} [ash-Shu'ara': 105]. Sai Allah Ya sanya su masu ƙaryatawa ga dukkan Manzanni, tare da cewa wani Manzo bai kasance ba ban da shi (Annabi Nuhu), a lokacin da suka ƙarya ta shi. A kan wannan ne Nasara waɗanda suka ƙaryata (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma ba su bi shi ba, su masu ƙaryatawa ne ga (Annabi) Isa ɗan Nana Maryam, kuma su ba mabiyane a gare shi ba, musamman ma cewa shi lallai ya yi musu bushara da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma babu ma'ana da yi musu bushara da shi, sai don cewa haƙiƙa shi Manzo ne zuwa gare su, da Allah zai tsamar da su da shi daga ɓata, Ya kuma shiryar da su zuwa tafarki madaidaici.
Na biyu: Imani da wanda muka san sunansa daga cikinsu da sunansa, misalin: (Annabi) Muhammad, da (Annabi) Ibrahim, da (Annabi) Musa, da (Annabi) Isa, da (Annabi) Nuhu - tsira da amincin Allah su tabbata a gare su -. Waɗannan biyar ɗin sune ma'abota haƙuri da himma maɗaukakiya daga Manzanni. Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ambacesu a guri biyu cikin AlKur'an a cikin faɗarSa: {Kuma a lõkacin da Muka riƙi alƙawarin Annabawa daga gare su, kuma daga gare ka, kuma daga Nũhu da Ibrãhĩm da Mũsa da kuma Ĩsã ɗan Maryama, kuma Muka riƙi wani alƙawari mai kauri daga gare su 7} [al-Ahzab: 7]. Da faɗinSa: {Ya shar'anta muku, game da addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nũhu da abin da Muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da Muka yi wasiyya da shi ga Ibrãhĩm da Mũsã da Ĩsã, cẽwa ku tsayar da addini sõsai kuma kada ku rarrabu a cikinsa. Abin da kuke kira zuwa gare shi, ya yi nauyi a kan mãsu shirki. Allah na zãɓen wanda Yake so zuwa gare Shi, kuma Yanã shiryar da wanda ke tawakkali gare Shi, ga hanyar Sa 13} [ash-Shura: 13].
Amma wanda ba mu san sunansa daga cikinsu ba; to muna imani da shi a dunƙule. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma lalle haƙĩƙa, Mun aika wasu Manzanni daga gabãninka, daga cikinsu akwai wanda Muka ƙissanta maka lãbãrinsa kuma daga cikinsu akwai wanda ba Mu ƙissanta lãbãrinsa ba a gare ka...} [Ghafir: 78].
Na uku: Gasgata abin da ya inganta daga gare su na labarukansu.
Na huɗu: Aiki da shari'ar wanda aka aiko zuwa gare mu daga cikinsu, shi ne cikamakinsu (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda aka aiko zuwa dukkanin mutane. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {To, a'aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmãni ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya sãɓa a tsakãninsu, sa'an nan kuma ba su sãmi wani ƙunci a cikin zukãtansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamãwa 65} [an-Nisa': 65].
Imani da Manzanni yana da fa'idoji masu girma, daga cikinsu:
Ta farko: Sani da rahamar Allah - Maɗaukakin sarki -, da kulawarSa, ga bayinSa, ta yadda Ya aiko Manzanni zuwa gare su; don Ya shiryar da su zuwa tafarkin Allah - Maɗaukakin sarki -; kuma su bayyana musu yaya za su bautawa Allah, domin hankalin ɗan Adam ba zai keɓantu da sanin haka ba.
Ta biyu: Gode maSa - Allah Maɗaukakn sarki - a bisa wannan ni'imar mai girma.
Ta uku: Son Manzanni - tsira da amincin Allah su tabbata a gare su - da girmama su da yabo a gare su da abin da ya dace da su, domin su Manzannin Allah - Maɗaukakin sarki - ne, kuma domin cewa su sun tsaya da bauta maSa, da isar da saƙonSa da kuma nasiha ga bayinSa.
Haƙiƙa masu tsaurin kai sun ƙaryata Manzanninsu, suna masu riya cewa Manzannin Allah - Maɗaukakin sarki - ba za su kasance daga mutane ba! kuma haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ambaci wannan riyawar, kuma Ya ɓata ta da faɗarSa - tsarkakken sarki -: {Kuma bãbu abin da ya hana mutãne su yi ĩmãni, a lõkacin da shiriya ta jẽ musu, fãce sunce, 'Shin, Allah zai aiko mutum ya zamo yana Manzo. 94 Ka ce, 'Dã akwai malã'iku a cikin ƙasa suna tafiya cikin natsuwa, dã mun saukar musu daga sama malã'ika ya zamo yana Manzo 95} [al-Isra': 94-95].
Sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ɓata wannan riyawar da cewa lallai ba makawa Manzo ya kasance mutum; domin shi abin aikowa ne zuwa ahalin ƙasa, su kuma mutane ne, da ace mutanen ƙasa mala'iku ne, da Allah Ya saukar da Mala'ika daga sama a gare su, a matsayin Manzo don ya zama irinsu. Kamar haka Allah - Maɗaukakin sarki - Ya hakaito daga masu ƙaryatawa ga manzanni cewa su sun ce: {...Ba ku zama ba fãce mutãne misãlinmu kuma nufinku ku kange mu daga abin da iyãyenmu suka kasance sunã bautãwa sai ku zo mana da dalĩli mabayyani." Manzannin su suka ce "Mu ba mu zama ba fãce mutãne misãlinku kuma amma Allah Yanã yi wa wanda Ya so daga bãyinSa falala. Kuma bã ya yiwuwa a gare mu mu zo muku da wani dalĩli sai da iznin Allah...} [Ibrahim: 10-11].
*
IMANI DA RANAR LAHIRA
Ranar lahira: Ranar Alƙiyama wacce za a tashi mutane a cikinta, don hisabi da sakamako.
An ambace ta da hakan: domin babu wata rana a bayanta, ta yadda 'yan Aljanna zasu tabbata a cikin gidajensu, 'yan wuta kuma (zasu tabbata) a cikin gidajensu.
Imani da ranar lahira yana ƙunsar al'amura uku:
Na ɗaya: Imani da tashi: Shi ne rayar da matattu lokacin da za a yi busa a cikin ƙaho, busa ta biyu; sai mutane su tashi ga Allah Ubangijin talikai, marasa takalma, ba masu takalma ba, matsiraita, ba masu tufafi ba, masu loba ba masu kaciya ba. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {...Kamar yadda Muka fãra a farKon halitta Muke mãyar da ita. Wa'adi ne a Kanmu. Lalle ne Mun kasance Mãsu aikatãwa} [al-Anbiya: 104].
Tashi: Gaskiya ne tabbatacce, da Alƙur’ani da Sunna sun yi nuni a kan hakan, da haɗuwar musulmai.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne. 15 Sa'an nan kuma ku, a Rãnar Ƙiyãma, za a tãyar da ku 16} [al-Mu'minun: 15 - 16].
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Za'a tashi mutane ranar Alƙiyama marasa takalma tsirara marasa kaciya» [13]. An haɗu a kansa. [13] Muslim ne ya fitar da shi, Littafin Aljanna, da siffofin ni’imarta da mazaunanta. Babi na ƙarewar duniya, da bayanin taruwar mutane ranar AlKiyama, lamba ta (2859).
Kuma musulmai sun haɗu a kan tabbacinsa, kuma shi ne manufar hikima; inda take hukunta cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana sanya wa wannan halittar makoma, da Zai yi musu sakayya a cikinta a kan abin da Ya shara'anta musu a cikin abin da Ya aiko ManzanninSa da su, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba?115} [al-Mu'minun: 115]. Kuma Ya ce da AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: {Lalle ne wanda Ya faralta Alƙur'ãni a kanka, haƙĩƙa, Mai Mayar da kai ne zuwa ga makõma...} [al-Ƙasas: 85].
Na biyu: Imani da hisabi da sakamako: za a yi wa bawa hisabi a kan aikinsa, kuma a saka masa a kansa, haƙiƙa Littafi (Alƙur’ani), da sunna, da haɗuwar musulmai sun yi nuni a kan haka.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take. 25 Sa'an nan, lalle ne, a kan Mu hisãbinsu yake 26} [al-Gashiya: 25-26]. Kuma (Allah) - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Wanda ya zo da kyakkyãwan aiki guda, to, yanã da gõma ɗin misãlansa. Kuma wanda ya zo da mũgun aiki gũda, to, bã zã a sãka masa ba fãce da misãlinsa. Kuma sũ bã a zãluntar su 160} [al-An'am: 160]. Kuma (Allah) - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma Munã aza ma'aunan ãdalci ga Rãnar ¡iyãma, sabõda haka ba a zãluntar rai da kõme. Kuma kõ dã ya kasance nauyin ƙwãya daga kõmayya ne Mun zo da ita. Kuma Mun isa zama Mãsu hisãbi 47} [al-Anbiya': 47].
Daga Ibn Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa - ya ce: «Haƙiƙa Allah Yana kusanto da mumini, sai Ya sanya sittirarSa a kansa, - wato Ya suturce shi -: Sai Ya ce: Shin kana sanin zunubi kaza? shin kana sanin zunubi kaza? Sai ya ce: Eh, ya Ubangiji, har yayin da Ya tabbatar masa da zunubansa, ya tabbatar a kan kansa cewa shi ya halaka, sai (Allah) Ya ce: Na suturta su a gare ka a duniya, a yau Ni kuma zan gafarta su a gare ka, sai a ba shi littafin kyawawan ayyukansa. Amma kafirai da munafikai, sai a yi kira a gaban halittu: (a ce) waɗannan sune waɗanda suka ƙaryata Ubangijinsu, ku saurara, tsinuwar Allah ta tabbata a kan azzalumai." [14] An haɗu a kansa. [14] Bukhari ne ya fitar da shi: Littafin Zalunci, babin Faɗar Allah Maɗaukaki: ﴾أَلَا لَعۡنَةُ ٱللَّهِ عَلَى ٱلظَّٰلِمِينَ﴿، lamba ta (2309), da Muslim: Littafin Tuba, babin Karɓar tubar mai kisa, ko da kuwa ya yi kisa da yawa, lamba ta (2768).
Kuma ya inganta daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa ya ce: «Cewa wanda ya yi nufin (aikata) kyakkyawan aiki, sai ya aikata ta, Allah zai rubuta masa a wurinsa kyawawa goma, zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninke-ninke masu yawa; kuma wanda ya yi nufin (aikata) mummunan aiki, sai ya aikata shi, Allah zai rubuta masa mummuna guda ɗaya." [15] [15] Muslim ne ya fitar da shi: Littafin Imani, Babin idan bawa ya himmantu da kyakkyawan aiki za a rubuta masa, idan kuma ya himmantu da mummunan aiki ba za a rubuta masa ba, lamba ta (131).
Haƙiƙa musulmai sun haɗu a kan tabbatar da hisabi da sakamako a kan ayyuka, kuma shi ne abin da hikima take hukuntarwa (nema). Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya saukar da littattafai, kuma Ya aiko Manzanni, Ya farlanta wa bayi karɓar abin da suka zo da shi, da kuma aiki da abin da aiki yake wajaba da shi daga gare shi, kuma Ya wajabta yaƙar masu bijire masa, Ya halatta jinanansu, da zurriyarsu, da matayensu, da dukiyoyinsu. Kuma da a ce hisabi da sakamako ba za su kasance ba, da hakan ya kasance yana daga wasa, wanda ake tsarkake Ubangiji gwani daga gare shi. Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi nuni zuwa ga haka a faɗarSa: {Sa'an nan lalle ne Munã tambayar waɗanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Munã tambayar Manzannin. 6 Sa'an nan lalle ne Munã bã su lãbãri da ilmi, kuma ba Mu kasance mãsu ɓõyẽwa ba 7} [al-A'raf: 6-7].
Na uku: Imani da aljanna da wuta kuma cewa su makoma ce ta har abada ga halitta.
Aljanna gidan ni'ima ce, wacce Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya tanade ta ga muminai masu tsoron Allah, waɗanda suka yi imani da abin da Allah Ya wajabta a kansu da su yi imani da shi, kuma suka tsaya da biyayyar Allah da ManzonSa, suna masu tsarkake (ayyukansu ga Allah, masu bin manzonSa, a cikinta (Aljanna) akwai daga nau'oin ni'ima. «Abin da ido bai taɓa gani ba, kuma kunne bai taɓa ji ba, kuma bai taɓa ɗarsuwa a zuciyar wani mutum ba» [16]. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Lalle ne waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan su ne mafifita alherin halitta 7. Sakamakonsu a wurin Ubangijinsu shi ne Aljannatun Adnin, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada. Allah Ya yarda da su, kuma sun yarda da Shi. Wannan shi ne ga wanda ya ji tsoron Ubangijinsa 8} [al-Bayyinah: 7-8]. Kuma (Allah) Maɗaukakin sarki Ya ce: {Sabõda haka wani rai bai san abin da aka ɓõye musu ba, na sanyin idãnu, dõmin sakamako ga abin da suka kasance sunã aikatãwa 17} [as-Sajda: 17]. [16] Al-Bukhari ya fitar da shi: Littafin Tafsiri, babin faɗinSa: {Wata rai ba ta sanin abin da aka ɓoye musu na abin da rai yake farin ciki (da shi)}, lamba (4501), da Muslim: Littafin Aljanna da siffofin ni’imarta da mutanenta, lamba (2824).
Amma Wuta: Ita gidan azaba ne wacce Allah - Maɗaukakin sarki - Ya tanade ta don kafirai azzalumai, waɗanda suka kafirce da shi, kuma suka saɓawa manzanninSa, a cikinta akwai nau'ikan azaba da uƙuba waɗanda ba sa ɗarsuwa a zuciya, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma ku ji tsõron wutã wadda aka yi tattali dõmin kãfirai 131} [Aal Imran: 131]. Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma ka ce: 'Gaskiya daga Ubangijinku take.' Sabõda haka wanda ya so, to, ya yi ĩmãni, kuma wanda ya so, to, ya kãfirta. Lalle ne Mũ, Mun yi tattali dõmin azzãlumai wata wuta wadda shãmakunta, sun ƙẽwaye da su. Kuma idan sun nẽmi taimako sai a taimake su da wani ruwa kamar dabzar mai, yanã sõye fuskõki. Tir da abin shansu, kuma wutar ta yi mũnin zama mahũtarsu 29} [al-Kahf: 29]. Kuma (Allah) - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Lalle Allah Yã la'ani kãfirai, kuma Yã yi musu tattalin wata wuta mai ƙũna. 64 Sunã madawwama a cikinta har abada. Bã su sãmu wani majiɓinci ko wani mataimaki ba. 65 A rãnar da fuskõkinsu zã a jũya a cikin wuta, sunã cẽwa, 'Kaitõnmu! Dã mun yi ɗã'a ga Allah, kuma mun yi ɗã'a ga Manzo 66} [al-Ahzab: 64-66].
Imani da ranar lahira yana da fa'idoji masu girma, daga cikin su:
Ta farko: kwaɗayin aikata biyayya, da kwaɗayi a kanta, don ƙauna ga ladan waccen ranar.
Ta biyu: Tsoran aikata saɓo, da yarda da shi; don tsoro daga uƙubar waccen ranar.
Ta uku: Rarrashin mumini, daga abin da yake rasawa na duniya da abin da yake ƙaunarsa na daga ni'imar lahira, da ladanta.
Haƙiƙa kafirai sun yi musun tashi bayan mutuwa, suna masu riya cewa hakan ba mai yuwuwa ba ne.
Wannan riyawar ɓatacciya, shari'a da riska da sarari, da hankali sun yi nuni a bisa ɓacinta.
Amma a shari'a, haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Waɗanda suka kãfirta sun riya cẽwa bã zã a tãyar da su ba. Ka ce: "Ni, inã rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle zã a tãyar da ku haƙĩƙatan, sa'an nan kuma lalle anã bã ku lãbãri game da abin da kuka aikata. Kuma wannan ga Allah mai sauƙi ne 7} [at-Tagabun: 7]. Kuma haƙiƙa dukkanin littattafan sama sun haɗu a kansa.
Amma riska ta sarari: Haƙiƙa Allah Ya nunawa bayinSa rayar da matattu a wannan duniyar, akwai misalai biyar a cikin surar Baƙara a kan haka, su ne:
Misali na farko: Mutanen (Annabi) Musa lokacin da suka ce da shi: {...bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka, sai munga Allah bayyane...} [al-Baqarah:55]. Sai Allah Ya kashe su, sannan Ya rãyar da su. A kan haka ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa, Yana Mai magana da 'ya'yan Isra'ila: {Kuma a lõkacin da kuka ce: 'Ya Musa! Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka, sai munga Allah bayyane,' sabada haka tsãwar nan ta kamaku, alhãli kuwa kuna kallo. 55 Sa'an nan Muka tãyar da ku daga bãyan mutuwarku, tsammãninku, ku gõde 56} [al-Baƙara: 55-56].
Misali na biyu: A ƙissar wanda aka kashe, wanda 'ya'yan Isra'il suka yi husuma a sha'aninsa, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya umarce su da su yanka saniya, su doke shi da shashin ta, don Ya ba su labarin wanda ya kashe shi, a kan haka ne Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ke cewa: {Kuma a lõkacin da kuka yi kisan kai, kuka dinga tunkuɗa wa jũna laifĩ a cikinsa, kuma Allah Mai fitar da abin da kuka kasance kuna ɓõyẽwa ne. 72 Sai Muka ce, 'Ku bugẽ shi da sãshen nan.' Kamar haka Allah Yake rãyar da matattu, kuma Yana nũna muku ãyõyinsa, tsammãninku, zã ku yi hankali 73} [al-Baƙara: 72-73].
Misali na uku: A ƙissar mutanen da suka fita daga gidajensu don gujewa mutuwa su dubunnai ne; sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya kashe su, sannan Ya raya su, a kan haka ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa: {Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suka fita daga gidãjensu, alhãli kuwa sũ dubbai ne, dõmin tsõron mutuwa? Sai Allah Ya ce musu: "Ku mutu." Sa'an nan kuma Ya rãyar da su, lalle ne Allah, haƙĩƙa Ma'abũcin falala a kan mutãne ne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdẽwa 243} [al-Baƙara: 243].
Misali na huɗu: Kissar wanda ya wuce wata alƙarya matacciya, sai ya nisantar da cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Zai (sake) raya ta, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya kashe shi shekara ɗari, sannan Ya raya shi, a kan haka ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa: {Kõ kuwa wanda ya shũɗe a kan wata alƙarya, alhãli kuwa tana wõfintacciya a kan gadãjen rẽsunanta. Ya ce: "Yaya Allah zai rãyar da wannan a bãyan mutuwarta." Sai Allah Ya matar da shi, shẽkara ɗari; sa'an nan kuma ya tãyar da shi. Ya ce: "Nawa ka zauna?" Ya ce: "Na zauna yini ɗaya ko kuwa rabin yini." Ya ce: "A'a kã zauna shẽkara ɗari." To, ka dũba zuwa ga abincinka, da abin shanka, (kõwanensu) bai sãke ba, kuma ka dũba zuwa ga jãkinka, kuma dõmin Mu sanya ka wata ãyã ga mutãne. Kuma ka duba zuwa ga ƙasũsuwa yadda Muke mõtsarda su sa'an nan kuma Mu tufãtar da su, da nãma", To, a lõkacin da (abin) ya bayyana a gare shi, ya ce: "Ina sanin cẽwa lalle Allah a kan dukan kõme Mai ĩkõn yi ne 259} [al-Baƙara: 259].
Misali na biyar: A ƙissar (Annabi) Ibrahim badaɗin Allah, lokacin da ya roƙi Allah - Maɗaukakin sarki - da Ya nuna masa yadda Yake raya matattu. Sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya umarce shi da ya yanka tsuntsaye huɗu, kuma ya rarrabasu a gutsittsire a kan duwatsun da suke kewaye da shi, sannan ya kira su a gutsittsiren za su haɗu shashinsu zuwa shashi, kuma za su zo wurin (Annabi) Ibrahim da sauri, a kan haka ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa: {Kuma a lõkacin da Ibrãhĩm ya ce: 'Ya Ubangijina! Ka nũna mini yadda Kake rãyar da matattu.' Ya ce: 'Shin, kuma ba ka yi ĩmãni ba?' Ya ce: 'Na'am! Kuma amma dõmin zũciyãta, ta natsu.' Ya ce: 'To ka riƙi huɗu daga tsuntsãye, ka karkatar da su zuwa gare ka, ka yanka su, sa'an nan kuma ka sanya juzu'i daga gare su a kan kõwane dũtse, sa'an nan kuma ka kira su zã su zo maka gudãne. Kuma ka sani cẽwa lalle Allah Mabuwãyi ne, Masani 260} [al-Baƙara: 260].
Waɗannan misalai na sarari waɗanda suka faru, suna nuni a bisa yuwuwar rayar da matattu. Haƙiƙa nuni ya gabata zuwa abin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya sanya shi daga mu'ujizozin (Annabi) Isa ɗan Maryam, na rayar da matattu, da kuma fito da su daga ƙabarurrukansu da izinin Allah - Maɗaukakin sarki -:
Amma nunin hankali: Daga fuskoki biyu ne:
Ɗaya daga cikinsu: Cewa Allah - Maɗaukakin sarki - (Shi ne) Mahaliccin sammai da ƙasa, da abin da yake cikinsu, Mahaliccinsu tun farko, kuma Mai iko a kan farar halitta ba ya gajiyawa daga dawo da ita, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma Shĩ ne Wanda Ya fãra halitta, sa'an nan Ya sãke ta kuma sakẽwarta tã fi sauƙi a gare shi...} [ar-Rum: 27]. Kuma (Allah) - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {...Kamar yadda Muka fãra a farKon halitta Muke mãyar da ita. Wa'adi ne a Kanmu. Lalle ne Mun kasance Mãsu aikatãwa} [al-Anbiya: 104]. Kuma Ya ce Yana Mai umarni da maida martani ga wanda ya yi musun rãyar da ƙasũsuwa, alhãli kuwa sunã rududdugaggu: {Ka ce: 'Wanda ya ƙãga halittarsu a farkon lõkaci Shĩ ke rãyar da su, kuma Shi, game da kõwace halitta, Mai ilmi ne 79} [Yasin: 79].
Na biyu: Haƙiƙa ƙasa tana kasancewa matacciya rusasshiya, babu koriyar bishiya a kanta, sai ruwan sama ya sauka a kanta, sai ta yi motsi tana koriya rayayyiya, a kanta akwai daga dukkan nau'i biyu masu ƙayatarwa. Mai iko a bisa rayar da ita, bayan mutuwarta, Mai iko ne a bisa raya matattu. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma akwai daga ãyõyinSa cẽwa lalle kai kanã ganin ƙasã ƙẽƙasasshiya, to, idan Mun saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura. Lalle wannan da Ya rãya ta, haƙĩƙa, Mai rãyar da matattu ne. Lalle Shĩ Mai ĩkon yi ne a kan kõwane abu 39} [Fussilat: 39]. kuma (Allah) - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa. 9 Da itãcen dabĩno mãsu tsawo, waɗanda suke da ƙwai mai ɗaurin juna. 10 Dõmin arziki ga bãyin Allah. Kuma Mun rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar haka ne fitowa 11} [Qaf: 9-11].
Kuma yana shiga cikin imani da ranar lahira yin imani da duk abin da zai kasance bayan mutuwa, misali:
(A) Fitinar ƙabari: Ita ce tambayar mamaci bayan binne shi, dangane da Ubangijinsa, da Addininsa, da Annabinsa; sai Allah Ya tabbatar da waɗanda suka yi imani da magana tabbatacciya, sai ya ce: Ubangijina (shi ne) Allah, Addinina Musulinci, Annabina Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Allah Yana ɓatar da azzalumai, sai kafiri ya ce: Haa, haa, ban sani ba, munafiki ko mai kokanto sai ya ce: Ban sani ba, na ji mutane suna faɗar wani abu sai na faɗe shi.
(B) Azabar ƙabari da ni'imarsa: Tana kasancewa ga azzalumai daga munafukai da kafirai. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {...Kuma dã kã gani, a lõkacin da azzãlumai suke cikin mãyen mutuwa, kuma malã'iku sunã mãsu shimfiɗa hannuwansu, (sunã ce musu) "Ku fitar da kanku; a yau anã sãka muku da azãbar wulãƙanci sabõda abin da kuka kasance kunã faɗa, wanin gaskiya, ga Allah kuma kun kasance daga ãyõyinSa kunã yin girman kai} [al-An'am: 93].
(Allah) - Maɗaukakin Sarki - Yana cewa a cikin mutanen Fir’auna: {Wutã, anã gitta su a kanta, sãfe da maraice, kuma a rãnar da Sa'a take tsayuwa, anã cẽwa, 'Ku shigar da mutãnen Fir'auna a mafi tsananin azãba 46} [Ghafir: 46].
A cikin Sahihin Muslim daga hadisin Zaidu ɗan Sabit - Allah Ya yarda da shi, - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ba don kada ku daina binne mamatanku ba, da na roƙi Allah ya jiyar da ku daga azabar ƙabari wanda nake ji daga gare shi». Sannan ya juyo da fuskarsa, sai ya ce: «Ku nemi tsarin Allah daga azabar wuta». Suka ce: "Muna neman tsarin Allah daga azãbar wutã," ya ce: «Ku nemi tsarin Allah daga azabar ƙabari». Suka ce: Muna neman tsarin Allah daga azaba ƙabari, ya ce: «Ka nemi tsari da Allah daga fitinu, abin da ya bayyana daga cikinsu da abin da ya ɓoye». Suka ce: Muna neman tsarin Allah daga fitintinu, waɗanda suka bayyana da waɗanda suka ɓuya. Ya ce: «Ku nemi tsari da Allah daga fitinar Masihul Dajjal». Sai suka ce: Muna neman tsarin Allah daga fitinar Dajjal [17]. [17] Muslim ne ya fitar da shi: Littafin aljanna da siffar ni’imarta da mazaunanta, babin bijiro da mazaunin mamaci daga aljanna ko wuta a gare shi, da tabbacin azabar ƙabari da neman tsarin Allah daga gare ta, lamba ta (2867).
Amma ni'imar ƙabari: Ta tabbata ga muminai masu gaskiya. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Lalle waɗannan da suka ce: "Ubangjinmu, shĩ ne Allah," sa'an nan suka daidaitu, malã'iku na sassauka a kansu (a lõkacin saukar ajalinsu sunã ce musu) "Kada ku ji tsõro, kuma kada ku yi baƙin ciki, kuma ku yi bushãra da Aljanna, wadda kun kasance anã yi muku wa'adi da ita 30} [Fussilat: 30].
Kuma (Allah) - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa). 83 Kuma kuna kallo a lokacin. 84 Kuma Mu ne mafi kusanci gare shi fiye da ku, amma ba ku gani. 85 To, don me idan ba ku da bashi, ku mayar da shi idan kun kasance masu gaskiya. 87 To, idan yana daga cikin waɗanda aka kusantar. 88 To, jin daɗi da ni'ima da Aljannar ni'ima 89} [al-Waƙi'ah: 83-89].
An karɓo daga al-Bara'u bin Azib - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce a sha'anin mumini idan ya amsawa mala'iku biyu a cikin ƙabarinsa: «Mai kira zai yi kira daga sama: Cewa bawaNa ya yi gaskiya, ku yi masa shimfiɗa daga Ajanna, ku sanya masa (tufafi) daga Aljanna, ku buɗe masa ƙofa zuwa Aljanna, ya ce sai ya zo masa daga ƙanshinta da daɗinta, kuma a yalwata masa ƙabarinsa iyaka ganinsa». Ahmad ne ya rawaito shi da Abu Daud a cikin hadisi mai tsawo [18]. [18] Abu Dawud ne ya fitar da shi: Littafin Sunnah, babin tambaya a ƙabari da azabar ƙabari, lamba ta (4753), da Ahmad: Musnad na mutanen Kufa, hadisin al-Bara bin Azib, lamba ta (18534).
Haƙiƙa wasu mutanan daga ma'abota karkata sun ɓata, da suka yi musun azabar ƙabari, da ni'imarsa, suna masu riya cewa hakan ba mai yi wuwa ba ne, saboda saɓawarsa da abin da yake faruwa, domin da za’a yaye mamaci a ƙabarinsa, da an same shi kamar yadda ya kasance a kansa, ƙabarin kuma bai canza ba da yalwa ko da ƙunci.
Wannan riyawar ɓataccya ce a shari'a da riskar sarari da hankali:
Amma a shari'a: Haƙiƙa nassosi sun gabata masu nuni a bisa tabbatar azabar ƙabari da ni'marsa.
A cikin Sahihul Bukhari daga hadisin Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: "Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fito daga wani sashi na shingayen Madina; sai ya ji sautin mutane biyu ana yi musu azaba a cikin ƙaburburansu", sai ya ambaci hadisin, kuma a cikinsa: «Lallai cewa ɗayansu ya kasance ba ya kiyaye jikinsa da tufafinsa daga fitsari». Kuma a cikin wata riwayar: «Daga fitsarinsa». «Ɗayan kuma ya kasance yana yawo da annamimanci». A cikin wata riwayar ta Muslim kuma: «Ba ya tsarkake kansa daga fitsari» [19]. [19] Bukhari ne ya fitar da shi: Kitab al-Wudu', babin abin da ya zo game da wanke fitsari, a lamba ta (215).
Amma riskar sarari: Haƙiƙa mai barci yana gani a cikin barcinsa, cewa shi ya kasance a wani guri mai faɗi mai kwarjini, yana ni'imtuwa a cikinsa, ko kuma cewa shi ya kasance a wani guri ƙuntatacce mai kewa. Yana jin raɗaɗi daga gare shi, wani lokaci ya kan farka daga abin da ya gani. Kuma duk da haka shi yana kan shimfiɗarsa a cikin ɗakinsa a kan abin da yake a kansa. Bacci ɗan uwan mutuwa ne, saboda wannan ne ma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ambace shi: (mutuwa) Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Allah ne ke karɓar rãyuka a lõkacin mutuwarsu, da waɗannan da ba su mutu ba, a cikin barcinsu. Sa'an nan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa a kansa kuma Ya saki gudar, har zuwa ga ajali ambatacce...} [az-Zumar: 42].
Amma hankali: Haƙiƙa mai barci yana ganin mafarkin gaskiya ne mai dacewa ne da abin da yake faruwa a barcinsa, yakan iya ganin Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- a bisa siffarsa, wanda kuma ya gan shi a bisa siffarsa to haƙiƙa ya gan shi da gaske, amma duk da haka, mai barci yana cikin ɗakinsa a kan shimfiɗarsa nesa da abin da ya gani. Idan har wannan ya zama mai yiwuwa ne a abubuwan duniya, to, shin ba zai yi wu ba a abubuwan lahira?!
Amma kuma dogaransu cikin abin da suka riya shi cewa, da za a tone mamaci a cikin ƙabarinsa, da an same shi kamar yadda aka binne shi, kuma ƙabarin bai canza ba da yalwatuwa ko ƙuntata, to amsarsa a kan haka ta wasu fuskoki ne, ga wasu:
Na farko: Cewa bijirewa abin da shari'a ta zo da shi ba ya halatta, da misalin waɗannan shubhohi ɓatattu rusassu, waɗanda da mai bijre musu, zai lura da abin da shari'ar gaskiya ta zo da shi, da ya san ɓacin waɗannan shubhohin, haƙiƙa an ce:
Da yawa daga mai aibata magana ingattacciya.
Aibukansa na daga mummunar fahimta ne.
Na biyu: Cewa halayen barzahu na daga al'amuran gaibu, waɗanda riska ta zahiri ba ta riskarsu, da a ce ana riskarsu da riska ta sarari, da fa'idar imani da gaibu an rasa ta, da kuma masu imani da gaibu da masu musun gasgata shi sun daidaita.
Na uku: Cewa azaba, da ni'ma, da yalwar ƙabari, da ƙuncinsa, kaɗai mamaci ne ya ke riskarsu banda waninsa, wannan kuwa kamar yadda mai barci yake gani a cikin barcinsa, cewa shi yana wani guri ƙuntatacce mai kewa, ko kuma a wani guri mai yalwa mai ƙayatarwa, alhalin wanda ke kewaye da shi ba ya ganin hakan ba ya kuma jinsa. Kuma haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance ana wahayi zuwa gare shi, alhalin yana tsakanin sahabbansa, sai ya ji wahayi, sahabbai kuma ba sa jinsa, kuma da yawa mala’ika yakan kamantu da mutum sai ya yi masa magana, sahabbai kuma ba sa ganin mala’ikan, ba kuma sa jinsa.
Na huɗu: Cewa riskar halitta abar iyakancewa ce da abin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya tabbatar musu riskarsa, riskar kowanne abu ba zai yi wu ba, sammai bakwai, da ƙasa, da abin da ke cikinsu, kowanne abu suna tsarkake da godewa Allah, tsarkakewa ta haƙiƙa, wani lokaci Allah - Maɗaukakin sarki - Yana jiyar da tsarkakewar ga wanda Ya so daga halittarSa. Tare da haka shi abin tsarewa ne a gare mu, a kan haka ne, Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa: {Sammai bakwai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sunã yi Masa tasbĩhi. Kuma bãbu wani abu fãce yanã tasbĩhi game da gõde Masa, kuma amma ba ku fahimtar tasbĩhinsu...} [al-Isra': 44]. Kuma haka nan shaiɗanu da aljanu suna tafiya a bayan ƙasa, tafiya da dawowa, kuma haƙiƙa aljanu sun halarci Manzon Allah suka ji karatunsa, kuma suka saurara, suka juya zuwa mutanensu suna ma su gargaɗi, tare da wannan su ababen shamakancewa ne a gare mu. A kan haka ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa: {Yã ɗiyan Ãdam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyãyenku, biyu daga Aljanna, yanã fizge tufarsu daga gare su, dõmin ya nũna musu al'aurarsu. Lalle ne shĩ, yanã ganin ku, shi da rundunarsa, daga inda bã ku ganin su. Lalle ne Mũ, Mun sanyaShaiɗan majiɓinci ga waɗanda bã su yin ĩmãni 27} [al-A'raf: 27]. Idan ya kasance halitta ba sa riskar kowanne abu, to lalle ba ya halatta su yi musun abin da ya tabbata na daga al'amuran gaibu da ba su riske shi ba.
*
IMANI DA ƘADDARA
Ƙaddara (da yi wa Dal fataha, a ce: ƘADAR): Ƙaddarawar Allah - Maɗaukakin sarki - ga kasantattu, gwargwadan abin da saninSa ya gabata da shi, kuma hikimarSa ta hukuntar da shi.
Imani da ƙaddara yana ƙunsar al'amura huɗu:
Na ɗaya: Imani da cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Masani ne da dukkan komai, a dunƙule da rarrabe, tun fil'azal kuma har abada, daidai ne hakan ya kasance daga abin da ya ke da alaƙa da ayyukansa, ko da aikin bayinSa.
Na biyu: Imani da cewa haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya rubuta haka a Allo abin kiyayewa, (Allon ƙudura), a cikin waɗannan al'amura biyun Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa: {Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yanã sanin abin da yake a cikin sama da ƙasa? Lalle ne wancan yanã cikin Littafi lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne 70} [al-Hajj: 70].
Da hadisin Abdullahi ɗan Amr ɗan Ās na cikin Sahih Muslim - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: «Allah Ya rubuta ƙaddarorin halittu kafin Ya halicci sammai da ƙasa da shekaru dubu hamsin» [20]. [20] Muslim ne ya fitar da shi: Littafin Ƙaddara, babin muhawarar (Annabi) Adamu da (Annabi) Musa - amincin Allah ya tabbata a gare su -, lamba ta (2653).
Na uku: Imani da cewa dukkan kasantattu ba sa kasancewa sai da son Allah - Maɗaukakin sarki -, daidai ne shin sun kasance daga abin da yake da alaƙa da ayyukansa, ko abin da yake da alaƙa da ababen halitta. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce cikin abin da yake da alaƙa da aikinSa: {Kuma Ubangijinka Yanã halitta abin da Yake so kuma Yake zãɓi...} [al-Ƙasas: 68]. Kuma Ya ce: {...Allah Yanã aikata abin da Yake so} [Ibrahim: 27]. Kuma Ya ce: {Shi ne wanda Yake suranta ku a cikin mahaifu yadda Yake so...} [al-Imraan: 6]. Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce a cikin abin da yake da alaƙa da aikin ababen halitta: {...Kuma dã Allah Yã so lalle ne, dã Yã bã su ĩko a kanku, sa'an nan, haƙĩka, su yãke ku...} [al-Nisa': 90]. Kuma Ya ce: {...Kuma dã Ubangijinka Yã so, dã ba su aikatã shi ba, don haka ka bar su da abin da, suke ƙirƙirãwa} [al-An'am: 112].
Na huɗu: Imani da cewa dukkanin kasantattu ababen halittar Allah - Maɗaukakin sarki ne -, da zatinsu, da siffofinsu, da motsinsu. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Allah ne Mai halitta dukan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme 62} [az-Zumar: 62]. Kuma - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce: {...Ya halitta dukan kowane abu, sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarãwa} [al-Furƙan: 2]. Kuma Ya ce dangane da AnnabinSa Ibrahim - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa shi ya cewa mutanensa: {Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa? 99} [as-Sāffāt: 96].
Imani da ƙaddara - a bisa abin da muka siffanta - ba ya kore cewa bawa ya kasance yana da abin da yake so a ayyukansa na zaɓi, da kuma iko a kansu; domin shari'a da abin da yake faruwa, masu nuni ne a bisa tabbatar da haka a gare shi.
Amma shari'a: Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Yace a kan Mashi'a (abin so): {...to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa} [an-Naba': 39]. Kuma Ya ce: {...ku je wa gõnakinku yadda kuka so...} [al-Baƙara: 223]. Ya ce a kan Iko: {Sai ku bi Allah da taƙawa gwargwadon abin da kuka sãmi ĩko. Kuma ku saurãra kuma ku yi ɗã'ã...} [At-Tagabun: 16]. Kuma Ya ce: {Allah ba Ya kallafa wa rai fãce ikon yinsa, yana da lãdar abin da ya tsirfanta, kuma a kansa akwai zunubin abin da ya yi ta aikatãwa...} [al-Baƙara: 286].
Amma abin da yake faruwa: Haƙiƙa kowanne mutum yana sanin cewa yana da abin da yake so da kuma iko, da sune yake aiki, da sune kuma yake bari, yake kuma rarrabewa tsakanin abin da yake faruwa da nufinsa, kamar tafiya, da abin da yake faruwa ba tare da nufinsa ba, kamar makyarkyata. Sai dai nufin bawa da ikonsa suna faruwa ne da abin da Allah - Maɗaukakin sarki - Ya so da kuma ikonSa, saboda faɗar Allah - Maɗaukakin sarki -: {Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu. 28 Kuma ba za ku so ba, sai Allah, Ubangijin talikai, Ya so 29} [at-Takweer: 28-29]. Domin cewa wannan kasantacce dukkaninsa mallaki ne na Allah - Maɗaukakin sarki -, babu wani abu da zai kasance a cikin mulkinSa, ba tare da saninSa da ganin damarSa ba.
Imani da ƙaddara- a bisa abin da muka siffanta- ba ya baiwa bawa wata hujja a bisa barin (wani abu) daga wajibai, ko aikata (wani abu) daga saɓo. A kan wannan ne, kafa hujja da shi ɓatacce ne, ta wasu fuskoki:
Na Farko: FaɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Waɗanda suka yi shirki zã su ce: "Dã Allah Yã so dã ba mu yi shirki ba, kuma dã ubanninmu ba su yi ba, kuma dã ba mu haramta wani abu ba." Kamar wannan ne mutãnen da suke a gabãninsu suka ƙaryata, har suka ɗanɗani azãbarMu. Ka ce: "Shin, kunã da wani ilmi a wurinku dõmin ku fito mana da shi? Bã ku bin kõme fãce zato kuma ba ku zama ba fãce ƙiri-faɗi kawai kuke yi 148} [al-An'am: 148]. Da ace wata hujja ta kasance a gare su da ƙaddara to da Allah bai ɗanɗana musu azabarSa ba.
Na biyu: FaɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -: {Manzanni mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kan Allah bãyan Manzannin. Kuma Allah yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima 165} [an-Nisa': 165]. Da a ce ƙaddara ta kasance wata hujja ce ga masu saɓawa, da ba a koreta da aiko manzanni ba, domin saɓawa bayan aiko su mai afkuwa ce, da ƙudirar Allah - Maɗaukakin sarki -.
Na uku: Abin da Bukhari da Muslim suka ruwaito shi - lafazin na Bukhari ne - daga Aliyu ɗan Abu Ɗalib- Allah Ya yarda da shi- cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Babu wani daga cikinku face an rubuta masa mazauninsa a wuta ko a Aljanna». Sai wani mutum daga cikin jama’a ya ce: Ya Manzon Allah shin ba za mu dogara ba? Sai ya ce: «A’a, ku aikata, domin kowa an sauƙaƙa masa». Sannan ya karanta: {To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa 5} [al-Lail: 5]. A cikin wani lafazin na Muslim: «Kowanne (ɗaya) abin yassarewa ne ga abin da aka halicce shi don shi» [21]. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi umarni da aiki, kuma ya yi hani daga dogara ga ƙaddara. [21] Bukhari ne ya fitar da shi a cikin littafin ƙaddara, babin umurnin Allah ƙaddara ce maƙaddariya, lamba ta (6605), da Muslim a cikin littafin ƙaddara, babin yadda ake halittar ɗan Adam a cikin mahaifiyarsa da rubuta arziƙinsa da ajalinsa da aikinsa da rashinsa sa'a da sa'arsa, lamba ta (2647).
Na huɗu: Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya umarci bawa kuma Ya hane shi, kuma bai ɗora masa nauyin (wani abu ba) sai abin da yake da iko. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Sai ku bi Allah da taƙawa gwargwadon abin da kuka sãmi ĩko. Kuma ku saurãra kuma ku yi ɗã'ã...} [at-Tagabun: 16]. Kuma Ya ce: {Allah ba Ya kallafa wa rai fãce ikon yinsa...} [al-Baƙara: 286]. Da a ce bawa ya kasance abin tilastawa a bisa aiki, da ya zamo abin ɗorawa abin da ba shi da ikon kuɓuta daga gare shi, wannan kuwa ɓatacce ne; saboda haka idan ya aikata saɓo da rashin sani, ko mantuwa, ko tilastawa, babu laifi a kansa; domin cewa shi abin yi wa uzuri ne.
Na biyar: Cewa ƙaddarar Allah - Maɗaukakin sarki - sirri ne ɓoyayye, ba a sanin shi sai bayan faruwar abin ƙaddarawar, kuma nufin bawa ga abin da yake aikatawa, mai rigaya ne a bisa aikinsa. Saboda haka sai nufinsa aiki ya kasance bai ginu ba a bisa wani sani daga gare shi da ƙaddarar Allah, a wannan lokaci ne hujjarsa da ƙaddara take koruwa, domin babu wata hujja ga mutum cikin abin da ba shi da saninsa.
Na shida: Haƙiƙa cewa mu muna ganin mutum, yana kwaɗayi a bisa abin da yake dacewa da shi na daga al'amuran duniyarsa, har sai ya riske shi, ba ya bauɗewa ga barinsa zuwa abin da ba ya dacewa da shi, sannan ya kafa hujja a bauɗewarsa da ƙaddara. To, idan hakane, don me yake bauɗewa daga abin da zai amfane shi a al'amuran Addininsa, zuwa abin da zai cutar da shi, sannan ya kafa hujja da ƙaddara? Shin sha’anin al'amuran biyu bai zama ɗaya ba?!
Ga wani misali nan a gare ka da zai bayyanar da hakan:
Da hanyoyi biyu zasu kasance a gaban mutum: Ɗaya daga cikinsu za ta tiƙe da shi zuwa wani gari dukanninsa hayaniya ce da rashin tsari; kisa, da wawaso, da keta mutunci, da tsoro, da yunwa. Ta biyu: Zai tiƙe da shi zuwa wani gari dukkaninsa tsari ne, da aminci tabbatacce, da rayuwa mai yalwa, da girmamawa ga rayuka da mutunci da dukiyoyi, to a hanyoyi biyunnan wacce zai bi?
Haƙiƙa shi zai bi hanya ta biyu ne, wacce zata kai shi zuwa gari mai tsari da aminci, ba zai yi wu ba ga dukkan wani mai hankali har abada ya bi hanyar garin hayaniya da rashin tsari, da tsoro, ya kuma kafa hujja da ƙaddara. To, me ya sa yake bin hanyar wuta a al'amarin Lahira, ba hanyar aljanna ba, kuma ya kafa hujja da ƙaddara?
Wani misalin kuma: Zaka ga mara lafiya, ana umartarsa da magani, sai ya sha shi, alhalin ransa ba ya sha'awarsa, kuma a hana shi (cin) abinci wanda zai cutar da shi, sai ya bar shi, alhalin ransa yana sha'awarsa, dukkanin haka, don neman waraka da aminci, Ba zai yi wu ba ya hanu daga shan magani, ko ya ci abin ci wanda zai cutar da shi, kuma ya kafa hujja da ƙaddara. To, saboda me mutum yake barin abin da Allah da ManzonSa suka umarce shi da shi, ko ya aikata abin da Allah da ManzonSa suka hana shi, sannan kuma ya kafa hujja da ƙaddara?
Na bakwai: Cewa mai kafa hujja da ƙaddara a bisa abin da ya bar shi na daga wajibabbu, ko ya aikata shi na daga saɓo, da wani zai yi shisshigi a gare shi ya ɗauki dukiyarsa, ko ya keta alfarmarsa, sannan ya kafa hujja da ƙaddara, ya ce: Kada ka zarge ni haƙiƙa shisshigina ya kasance ne da ƙaddarar Allah- ba zai karɓi hujjarsa ba. To ta yaya ba zai karɓi kafa hujja da ƙaddara a shisshigin wani a kansa ba, kuma ya kafa hujja da ita ga kansa a shisshiginsa ga haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki -?!
Ana ambaton cewa sarkin muminai Umar ɗan Khaɗɗab an kawo wani ɓarawo zuwa gare shi, da ya cancanci yanke (hannu), sai ya yi umarni da a yanke hannunsa, sai ya ce: Ka saurara ya sarkin muminai, kaɗai na yi sata ne da ƙaddarawar Allah, sai Umar ya ce: Muma kuma kaɗai zamu yanke (hannunka) da ƙaddarawar Allah.
Imani da ƙaddara yana da fa'idoji masu girma, daga cikin su:
Ta farko: Dogaro ga Allah - Maɗaukakin sarki - yayin aikata sabubba, ta yadda ba zai dogara a kan shi kansa sababin ba, domin kowanne abu (yana kasancewa) da ƙudirar Allah - Maɗaukakin sarki -.
Ta biyu: Domin kada mutum ya yi jiji da kansa, lokacin da ya sami abin da yake so; domin saminsa wata ni'ima daga Allah - Maɗaukakin sarki - ne, da abin da Allah Ya ƙaddara shi daga sababin alkhairi da nasara, jiji da kansa kuwa zai mantar da shi godewa wannan ni'imar.
Ta uku: Nutsuwa, da hutun rai da abin da yake gudana a gare shi, daga ƙaddarorin Allah - Maɗaukakin sarki -. Ba zai damu ba da rasa wani abin so, ko faruwar wani abin ƙi, domin hakan da ƙaddarawar Allah ne, wanda mulkin sammai da ƙasa ya tabbata a gare Shi, shi kasantacce ne babu makawa, kuma a cikin hakan Allah - Maɗaukakin sarki - ya ce: {Wata masifa bã zã ta auku ba a cikin ƙasã kõ a cikin rayukanku fãce tanã a cikin littãfi a gabãnin Mu halitta ta. Lalle wannan, ga Allah, mai sauƙi ne. 22 Domin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kubce muku, kuma kada ku yi farin ciki da abin da Ya ba ku. Kuma Allah bã Ya son duk mai yawan alfahari, mai yawan girman kai 23} [al-Hadid: 22-23]. Kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: «Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amurransa alheri ne, sai dai hakan baya kasancewa ga kowa sai ga mumini, idan abin farin ciki ne ya same shi sai ya godewa Allah sai ya zamar masa alheri, idan kuma na sharri ne ya same shi sai ya yi haƙuri, shi ma sai ya zamar masa alheri» [22]. [22] Muslim ne ya fitar da shi: a cikin Kitabu z-Zuhd war ra-ƙa'iƙ, Babin: Muminin duk al'amuransa alheri ne, lamba ta (2999).
Haƙiƙa jama'a biyu sun ɓata (a sha'anin) ƙaddara:
Na farkonsu: Jabariyya waɗanda suka ce: Haƙiƙa bawa abin tilastawa ne a kan akinsa, ba shi da nufi ko iko.
Ta biyu: Alƙadariyya waɗanda suka ce: Haƙiƙa bawa mai cin gashin kansa ne da aikinsa, a nufi, da ƙudira (iko), babu wani gurbi ga abin da Allah - Maɗaukakin sarki - Yake so da kuma ikonSa a cikinsa (aikinsa).
Maida martani ga Jama'a ta farko (Aljabariyya) a shari'a da abin da ke faruwa:
Amma a shari'ah: Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya tarbattarwa bawa nufi da ganin dama, Ya kuma raɓa aiki zuwa gare shi. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {...Daga cikinku akwai wanda yake nufin duniya kuma daga cikinku akwai wanda ke nufin Lãhĩra...} [āli- Imran: 152]. Kuma Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma ka ce: 'Gaskiya daga Ubangijinku take.' Sabõda haka wanda ya so, to, ya yi ĩmãni, kuma wanda ya so, to, ya kãfirta. Lalle ne Mũ, Mun yi tattali dõmin azzãlumai wata wuta wadda shãmakunta, sun ƙẽwaye da su...} Karanta har zuwa ƙarshen ayar. [al-Kahf: 29]. Kuma (Allah) - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Wanda ya aikata aiki na ƙwarai to sabõda kansa ne, kuma wanda ya mũnanã, to, yanã a kansa. Kuma Ubangiwinka, bã Mai zãlunci ga bãyin Sa ne ba 46} [Fussilat: 46].
Amma abin da ke faruwa: Haƙiƙa kowanne mutum ya san bambanci tsakanin ayyukansa na zaɓi waɗanda yake aikatasu da nufinsa: Kamar ci da sha, da siyarwa da siye, da kuma tsakanin abin da ke faruwa a gare shi, ba tare da nufinsa ba: kamar makyarkyata sanadiyyar zazzaɓi, da faɗowa daga rufi. Shi a na farko mai aikatawa ne mai zaɓi da nufinsa, ba tare da tilasci ba, a na biyu kuma ba mai zaɓi ba ne, ko nufi ba, ga abin da ya afku a gare shi.
Maida martani a kan Jama'a ta biyu (Alƙadariyya) a shari'a da hankali:
Amma a shari'a: Haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Shi ne Mahaliccin komai, kowane abu mai kasancewa ne da abin da Yake so, kuma haƙiƙa Allah - Maɗaukakin sarki - Ya bayyana a littafinSa cewa: Ayyukan bayi suna faruwa ne da ganin damarSa, sai Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {...Kuma dã Allah Yã so dã waɗanda suke daga bãyansu, bã zã su yi yãƙi ba, daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu. Kuma amma sun sãɓa wa jũna, sabõda haka daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni, kuma daga cikin su akwai wanda ya kãfirta. Kuma dã Allah Yã so dã bã zã su yãƙi jũna ba, kuma amma Allah Yana aikata abin da Yake nufi} [al-Baƙara: 253]. Kuma (Allah) - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma dã Mun so dã Mun bai wa kõwane rai shiriyarsa to, amma magana ta tabbata daga gare Ni! Lalle ne Inã cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya 13} [as-Sajda: 13].
Amma a hankali: Haƙiƙa wannan kasantacce dukkaninsa mallakar Allah - Maɗaukakin sarki - ne, mutum kuma yana daga wannan kasantacce; shi mallakar Allah - Maɗaukakin sarki - ne, ba zai yi wu ba ga wanda aka mallaka ya yi tasarrafi a mulkin mamallaki, sai da izininSa da sonSa.
*
MANUFOFIN AƘIDAR MUSULINCI
Alhadaf (a harshen larabci) ana faɗinsa da ma'anoni masu yawa, daga cikin su akwai: (karan bara da ake kafawa don koyon jifa zuwa gare shi, da kuma dukkan wani abu da ake son cimmasa).
Manufofin aƙidar Musulunci: Abubuwan nufinta da tuƙewar fa'idojinsu kyawawa, ababen tabbatarwa a bisa riƙo da su, su kuma masu yawa ne nau'i nau'i, daga cikin su akwai:
Na farko: Tsarkake niya da ibada ga Allah - Maɗaukakin sarki - Shi kaɗai; domin cewa Shi ne Mahalicci, ba Shi da abokin tarayya, sai ya wajaba cewa niyyar ibada ta kasance a gare Shi, Shi kaɗai.
Na biyu: Tace hankali da tunani daga ruɗani mai faruwa daga wofantar zuciya daga wannan aƙidar; domin duk wanda zuciyar sa ta wofanta daga gare ta (aƙida) to, ko dai (ya zamo) zuciyar sa babu wata aƙida (ingantacciya) a cikinta, kuma mai bautar ra’ayi na zahiri ne kawai, ko kuma mai faɗawa ne a cikin nau’ukan ɓata na aƙidu, da tatsuniyoyi.
Na uku: Hutu na rai, da na tunani, babu wata damuwa a rai, ba raurawa a tunani, domin wannan aƙidar tana sadar da mumini ga Ubangijinsa. Sai ya yarda da shi a matsayin Ubangiji Mai tsarawa, Mai hukunci Mai shar'antawa, sai zuciyarsa ta nutsu da ƙaddararsa, kuma ƙirjinsa ya yalwatu ga Musulunci, ba ya neman wani abin da ba shi ba.
Na huɗu: Kuɓuttar nufi (niyya) da aiki daga bauɗewa a bautar Allah - Maɗaukakin sarki -, ko ma'amalantar ababen halitta; domin yana daga ginshiƙanta, imani da Manzanni, wanda ya ƙunshi bin hanyarsu ma'abociyar tsira a niyya da kuma aiki.
Na biyar: Yankewa da ƙoƙari a cikin al'amura, ta yadda ba zai bar wata dama ba ta aiki nagari ba face sai ya yi amfani da ita a cikinsa, don ƙaunar lada, kuma ba zai ga gurin saɓo ba, fa ce sai ya nisance shi, don tsoron uƙuba, domin yana daga ginshiƙanta, imani da ta shi, da sakamako a kan ayyuka.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Kuma ga kõwanne, akwai darajõji daga abin da suka aikata. Kuma Ubangijinka bai zama mai shagala ba daga abin da suke aikatãwa 132} [al-An'am: 132]. Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi kira zuwa ga wannan manufa a cikin faɗinsa: «Mumini ƙaƙƙarfa ya fi alkairi da soyuwa a wajen Allah sama da mumini rarrauna, akwai alkairi a kowanne, ka yi kwaɗayin yin abin da zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah, kada ka gaza. Idan wani abu ya same ka kada ka ce: Da na aikata kaza da kaza, da kaza da kaza ya kasance, sai dai ka ce : Ƙaddarar Allah, abin da Ya so zai aikata, domin cewa (da a ce) tana buɗe aikin Shaiɗan». Muslim ne ya rawaito shi [23]. [23] Muslim ne ya fitar da shi: Littafin Ƙaddara, babi a cikin umurni da ƙarfi, da barin kasawa, da neman taimako daga Allah, da miƙa al’amuran ƙaddara ga Allah, lamba ta (2664).
Na shida: Samar da al'umma mai ƙarfi, da take bada dukkanin (abu) mai tsada da mai sauƙi, a wajen tabbatar da Addininta, da kafa ginshiƙansa, ba tare da la'akari da abin da zai same ta ba, a kan tafarkin hakan. A kan wannan ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa: {Mũminan gaskiya kawai, sũ ne waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzonSa, sa'an nan ba su yi shakka ba, kuma suka yi jihãdi da dũkiyarsu da kuma rãyukansu, cikin tafarkin Allah. Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya 15} [al-Hujurat: 15].
Na bakwai: Saduwa zuwa arzƙin duniya da lahira, da gyara ɗaidaiku da jama'a, da samun lada da abubuwan girma. A kan wannan ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yake cewa: {Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa 97} [an-Nahl: 97].
Waɗannan sune sashin manufofin aƙidar Musulunci. Muna ƙauna daga Allah - Maɗaukakin sarki - Ya tabbatar mana da su, da dukkanin musulmai, haƙiƙa Shi Mai yawan kyauta ne kuma Mai karamci ne. Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai.
Allah Ya yi tsira da aminci ga Annabinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa baki ɗaya.
Ta cika da alƙalamin mawallafinta.
Muhammad bin Salih al-Usaimeen