GABATARWA Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga wanda aka aiko shi rahama ga talikai, da alayensa da sahabbansa da wanda ya yi koyi da sunnarsa, ya kuma nemi shiryuwa da shiriyarsa har zuwa ranar sakamako. Bayan haka: Wannan taƙaitaccen saƙo ne, wanda ya ƙunshi mafi muhimmancin abinda musulmi yake buƙata a cikin hukunce-hukuncen hadaya da layya da kuma yanka, mun tattara shi don masu ziyartar Harami biyu masu daraja maza da mata; domin su kasance cikin sani da fahimta game da al'amuran addininsu, muna roƙon Allah Mai karamci mai baiwa Ya anfanar da shi,…
Harshe: lang_ha
Shiryawa: Kwamitin Ilimi na Ƙungiyar hidimtawa Musulunci da yaruka daban daban.
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga wanda aka aiko shi rahama ga talikai, da alayensa da sahabbansa da wanda ya yi koyi da sunnarsa, ya kuma nemi shiryuwa da shiriyarsa har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:
Wannan taƙaitaccen saƙo ne, wanda ya ƙunshi mafi muhimmancin abinda musulmi yake buƙata a cikin hukunce-hukuncen hadaya da layya da kuma yanka, mun tattara shi don masu ziyartar Harami biyu masu daraja maza da mata; domin su kasance cikin sani da fahimta game da al'amuran addininsu, muna roƙon Allah Mai karamci mai baiwa Ya anfanar da shi, kuma Ya sanya shi mai kyau, kuma saboda Allah ne kaɗai, lallai Shi ne mafi alherin wanda ake roƙo, kuma Mafi karamcin wanda ake fata.Kwamitin Ilimi na Ƙungiyar hidimtawa Musulunci da yaruka daban daban.
HUKUNCE-HUKUNCEN HADAYA DA LAYYA
Hadaya: Duk abin da ake bayarwa ga Harami, kuma ake yankawa a cikinsa na dabbobin ni'ima da sauran su, an kira shi da haka; domin ana kai shi ga Allah ne - Maɗaukakin Sarki -.
Al'udhiyya da dammar alif da kasrinta: Abin da ake yankawa saboda Allah a ranar idi, da kuma ranakun Tashriƙ (yanyanan nama) don neman kusanci zuwa ga Allah.
Musulmai sun haɗu akan shar'antuwarsu.
Mafi alherin hadaya: Raƙuma, sannan shanu, idan an fitar da su cikakku; saboda tsadar farashi, kuma amfanar talakawa da yawan nama ne, sannan tumakai.
Ba ya isuwa sai ƙiba-ƙibar tunkiya, ita ce: Wacce ta cika wata shida, da mai fira daga wanda ba shi ba kamar raƙuma da shanu da akuyoyi. Mai fira daga raƙuma shine: Wanda ya cika shekara biyar, daga shanu kuma shine: Wanda ya cika shekara biyu, daga akuyoyi kuma shine: Wanda ya cika shekara ɗaya.
Kuma akuya tana isuwa a cikin hadaya ga mutum ɗaya, kuma a cikin layya tana isarwa mutum ɗaya da iyalan gidansa, kuma taguwa da saniya suna isuwa a cikin hadaya da layya ga mutum bakwai; saboda hadisin Jabir bin Abdullahi - Allah Ya yarda da su - ya ce:«Mun soke taguwa ɗaya ga mutum bakwai tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a shekarar Hudaybiyah, haka kuma saniya ɗaya ga mutum bakwai».Kuma a cikin wani lafazin:«Mun fita tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - muna niyyar Hajji, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umurce mu da muyi tarayya a raƙuma da shanu, kowanne bakwai daga cikinmu a cikin taguwa ɗaya».Kuma a cikin wani lafazin:«Munyi Hajji tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai muka soke raƙumi ɗaya ga mutum bakwai, da saniya ɗaya ga mutum bakwai» [1].[1] Muslim ne ya rawaito shi.
Da hadisin Abu Ayyuba al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - lokacin da aka tambaye shi: Yaya akeyin layya a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce:«Mutum ya kasance yana yin layya da akuya a madadinsa da kuma iyalan gidansa, sai su ci, su ciyar, har mutane suka fara yin alfahari da ita, sai ta zama kamar yadda kake gani»[2].[2] Tirmizi da Ibn Majah ne suka rawaito shi.
Akuya ta fi ɗaya bisa bakwai na taguwa da kuma saniya.
Ba mai isuwa a hadaya da layya sai kuɓutacce daga cuta da tawayar gaɓɓai da kuma rashin ƙiba; ba a yarda da dabba mai ido ɗaya bayyananne ba, ko makauniya, ko busasshiya, itace ramammiya wadda ba ta da ɓargo, ko gurguwa wadda ba ta iya tafiya tare da lafiyayya, ko nakasassa wadda ta rasa haƙoranta daga asali, ko tsohuwa wadda nononta ya bushe daga madara saboda tsufa. Haka kuma ba a yarda da mai cuta bayyananne ba; saboda hadisin Barra'u Ɗan Azib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya tsaya a cikinmu, ya ce:«Huɗu ba sa halatta a cikin dabbobin layya: Mai ido ɗaya wacce makantarta ta bayyana, da mara lafiya wacce rashin lafiyarta ya bayyana, da gurguwa wacce gurguncinta ya bayyana, da busasshiya wacce ba ta da ɓargo» [3].[3] Abu Dawud ya rawaito shi, da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah.
Imam Tirmizi - Allah ya yi masa rahama - ya ce:"Aiki ya tabbata akan wannan a wajen ma'abota ilimi" [4].[4] Tirmizi ne ya rawaito shi.
Lokacin yankan hadayar Tamattu'i da dabbobin layya yana farawa ne bayan sallar idi har zuwa ƙarshen kwanakin Tashriƙ a bisa ingantaccen ra'ayi.
Ana son ya ci daga cikin hadayarsa idan ya kasance hadayar Tamattu'i ko ƙirani ne, da kuma daga layyarsa, ya yi kyauta kuma ya yi sadaka a raba kashi uku; saboda faɗin Allah - Maɗaukakin Sarki -:(Sai ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da galabaitaccen matalauci)[Surah al-Hajj: 28].
Amma hadayar gyara, itace: Wacce aka yi saboda aikata wani abu da aka haramta daga cikin abubuwan da aka haramta yayin harama ko saboda barin wani wajibi; to ba ya cin komai daga gareta.
Wanda ya yi nufin yin layya; idan goma ga watan Zul-Hijjah ya shiga; to kada ya yanki wani abu daga gashinsa ko farcensa har zuwa lokacin yanka dabbar layya; saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:«Idan goma ta shigo (ga watan Zul-Hijja), kuma ɗayanku yana son yin layya; to kada ya yanki wani abu daga gashinsa ko farcensa, har sai ya yi layya» [5].[5] Muslim ne ya rawaito shi.
Idan ya aikata wani abu daga cikin wannan; to ya nemi gafarar Allah, kuma babu fidiya a kan sa.
Siffar yanka hadaya da layya da sauran abin da ake yanka kamar haka ne:
1- Ba wanda zai yanka sai musulmi mai mayyazewa mai hankali, ko mazuwa littafi, kuma mai yankan yana nufin yin yanka, kada ya yanka ga wanin Allah, ba ya ambaton sunan wanin Allah, yana ambaton sunan Allah a lokacin yanka ko sokewa, kuma ya yanka da abin yanka mai kaifi banda haƙori da farce, ya zubar da jini a gurin da ya dace, kuma dole ne mai yankan ya kasance yana da izini a shari'a wajen yankansa[6].[6] Ahkamul Udhiyya na mai yawan ilimi Muhammad bn Uthaymin, (shafi na 56 – 87).
2- Ya zaɓi dabbar layya, don haka ya yi kwaɗayi a kan dabbar layya cikakkiya; haƙiƙa:«Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi layya da raguna biyu masu farar fuska da baƙi-baƙi masu ƙaho, ya yanka su da hannunsa, ya ambaci sunan Allah, ya yi kabbara, kuma ya ɗora ƙafarsa akan fatun wuyayensu» [7].[7] Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
Ba'a son ya wasa wuƙa alhali dabba tana kallonsa; saboda abin da ya zo daga Ibn Umar - Allah ya yarda da su - ya ce:Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi umarni da a wasa wuƙaƙe, kuma a ɓoyesu daga (ganin) dabbobi, sai ya ce: «Idan ɗayanku zai yanka; to ya yi gaggawa» [9].[9] Ahmad da Ibn Majah ne suka rawaito shi.
4. Idan dabbar layya ta kasance daga cikin raƙuma ne; to ya soke shi a tsaye, hannunsa na hagu a ɗaure; saboda hadisin Abdullahi bin Umar - Allah Ya yarda da su -:"Cewa shi ya zowa wani mutumin da ya durƙusar da taguwarsa zai soketa, sai ya ce: Ka kashe ta a tsaye a ɗaure, shine sunnar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -" [10].[10] Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
5. Idan dabbar layya ta kasance ba daga cikin raƙuma ba ne; to ya yanka ta a kwance a gefen hagunta, kuma ya ɗora ƙafarsa akan fatar wuyanta; don ya samu tabbata daga gareta; saboda hadisin Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce:«Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya yi layya da raguna biyu, masu launin baƙi da fari, masu ƙahonni, ya yanka su da hannunsa, ya ambaci sunan Allah, ya yi kabbara, kuma ya ɗora ƙafarsa a kan fatar wuyansu» [11].[11] Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
An so yin kabbara: (Allahu Akbar) tare da ambaton Allah; saboda hadisin Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na halarci babbar sallah tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a filin sallah, lokacin da ya gama huɗubarsa sai ya sauko daga mimbarinsa, sai aka kawo rago, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yanka shi da hannunsa, kuma ya ce:«Da sunan Allah, Allah ne mafi girma, wannan daga gare ni ne da kuma wanda bai yi yanka ba daga al'ummata» [13].[13] Abu Dawud ne ya ruwaito shi, da Tirmizi, kuma Albani ya inganta shi.
7- Yanke maƙogwaro, da maɗaciya, maƙogwaro da majinata, da zubar da jini: Imam Ibn Baaz - Allah Yayi masa rahama - ya ce: (Lallai yankan shari'a na raƙuma da shanu da tumaki: yana da halaye uku:
Hali na farko: Mai yankan ya yanke: Maƙogwaro, da maɗaciya, da majinata, wannan shi ne mafi cikar yanka kuma mafi kyansa, idan an yanke waɗannan abubuwa huɗu; to yankan ya halatta a wurin dukkan malamai.
Hali na biyu: A yanke maƙogwaro da maɗaciya da ɗaya daga cikin majinata; wannan ya halatta kuma ingantacce ne mai daɗi, duk da bai kai na farko ba.
Hali na uku: A yanke maƙogwaro da maɗaciya kawai ba tare da majinata ba, wannan ma ingantacce ne, kuma wasu daga cikin malamai sun faɗi haka, hujjarsu ita ce faɗin Annabi - tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi -:«Duk abinda ya zubar da jini kuma aka ambaci sunan Allah a kansa to kuci shi, banda haƙori da farce» [14].Wannan shi ne abin zaɓi a wannan mas'alar [15].[14] Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.[15] Ka duba: Majmu'u fatawa Bin Baaz (26/18).
Allah ne abin roƙo Ya amfane mu da abin da muka sani, kuma Ya sanar da mu abin da zai amfane mu; lallai cewa Shi Mai yawan kyauta ne Mai karamci, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammad da iyalansa da aminci, aminci mai yawa.
TAƘAITACCEN BAYANI MAI AMFANI GA LADAN DA LIMAN DA MAI HUDUBA DA KUMA HUKUNCE HUKUNCEN MASALLACI
47 harsuna
TAƘAITACCEN BAYANI MAI AMFANI GA LADAN DA LIMAN DA MAI HUDUBA DA KUMA HUKUNCE HUKUNCEN MASALLACI
Littafin yana gabatar da cikakken bayani game da hukunce-hukuncen kiran sallah da ikama, da limancin sallah, da huɗubar Juma'a, da kuma ladubban masallaci; haka kuma yana tattauna ayyukan ladanai da limamai da masu huɗuba, yana kuma mai ƙarfafa muhimmancin koyon hukunce-hukuncen shari'a da suka shafi waɗannan ayyuka domin tabbatar da gudanar da su yadda ya kamata. Haka kuma ya ƙunshi nassoshin da aka ruwaito daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - tare da sharhinsu, don tabbatar da an yi aiki da su daidai.
Ko wanne abu yana nuni akan akwai mahalicci Wa ya halicci sammai da kasa da abinda ke tsakanin su na halittu masu girma wadanda ba’a iya gane yawansu? Wa ya kera wannan nagartaccan tsarin kayatacce a sama da kasa ? Wa ya halicci mutum ya kuma ba shi ji da gani da hankali? Ya sanya shi mai iko akan tsururutar ilimai da gane hakikanin abubuwa ? Yaya zaka fassara wannan kira gwananna dake na'urorin (gabban) jikinka da suke kuma a jukkunan kasantattu suna aiki? kuma wanene ya kage su? Ta yaya wannan kasantacce mai girma yake tsaruwa kuma yake tabbatuwa tare da ƙa’idojin sa, waɗanda suke kiyaye…