Mafi Yawan Bincike
الغاية من الحياة
Manufa daga rayuwa* (Samuwar Mahalicci) Mutum yana tambayar kansa a cikin tafiyar tunaninsa game da asalin halittu da wanda ya ƙirƙiro su: Wa ya halicci sammai da ƙasa da abinda ke cikinsu na halittu? Ta yaya wannan kasantaccen mai girma yake tsaruwa kuma yake tabbatuwa tare da ƙa’idojin sa waɗanda suke kiyaye shi kiyayewa ta ƙwarewa tsawon shuɗewar waɗannan shekarun? Shin wannan kasantacce (halittu) shi ne ya halicci kansa? Ko ya zo ne ba daga wurin kowa ba? Ko kuma an same shi ne kawai kwatsam?
These files are generated automatically from the book's text; their layout may differ from the printed edition.
Manufa daga rayuwa*
(Samuwar Mahalicci)
Mutum yana tambayar kansa a cikin tafiyar tunaninsa game da asalin halittu da wanda ya ƙirƙiro su:
Wa ya halicci sammai da ƙasa da abinda ke cikinsu na halittu?
Ta yaya wannan kasantaccen mai girma yake tsaruwa kuma yake tabbatuwa tare da ƙa’idojin sa waɗanda suke kiyaye shi kiyayewa ta ƙwarewa tsawon shuɗewar waɗannan shekarun?
Shin wannan kasantacce (halittu) shi ne ya halicci kansa? Ko ya zo ne ba daga wurin kowa ba? Ko kuma an same shi ne kawai kwatsam?
Wa ya halicce ka, yakai mutum?
Idan ka duba jikin ka a ƙarƙashin na'urar bincike, za ka ga duniya mai cike da daidaici da al'ajabi, domin kowacce tantanin halitta a jikinka tana ɗauke da bayanan gado da lambobin su masu rikitarwa. Shin ka taɓa tambayar kanka wa ya rubuta waɗannan lambobin? Kuma wa ya sanya su a wurin da ya dace?
Kowanne gini mai tsawo, da kowanne gida mai sauƙi, yana ba da labarin wanda ya ƙera shi; shin zai yi wu a ce wannan duniyar mai faɗi da kyawunta da daidaicinta da tsarinta na cikakkun bayanai ta samu ne ba tare da wani mai ƙera ba?!
Ya kai mutum, kamar yadda hankalinka ba zai yarda a ce maka: Ai wannan wayar mai kaifin basira mai kyau ta bayyana kwatsam ba tare da mai tsara ta ko mai ƙera ta ba, ko kuma wata haɗaɗɗiyar hanyar sadarwa ta na'urori mai rikitarwa tana aiki da jituwa da daidaici ba tare da mai tsara ko mai kula ba, haka nan hankalin da ya dace ba zai yarda a ce masa: Ai wannan kaunun mai girma da duk abin da ke cikin ta na tsari da ƙayatarwa da dokoki masu kyau da tsari mai kyau ta samu ne ba tare da Mahalicci ba?!
Aya ta Alƙur'ani ta zo a bayyane don fuskantar da hankali zuwa ga zurfin tunani a kan wannan muhimmiyar tambayar. Allah Mahalicci - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya na cewa:
Don haka, ayar tana gabatar mana da yiwuwar hali uku a hankalce:
1. Shin zai yi wu wannan kaunun ta samu daga babu? Wannan ba zai yi wu ba; domin babu ba ya samar da komai.
2. Shin zai yi wu ta halicci kanta? Wannan ma ba zai yi wu ba; domin abu ba ya halittar kansa.
3. Sai dai yiwuwar da take da ma'ana, ita ce cewa wannan kaunun tana da Mahalicci Mai girma Mai iko.
Duk wani sashi na wannan kaunun, daga ƙwayar zarra mafi ƙanƙanta zuwa taron taurari mafi girma, yana nuna girman Mahaliccinsa; ba zai yi wu a hankalalce a ce wannan tsari mai kyau ya samo asali daga hargitsi ba. Hankali yana kore cewa wannan kaunun ta samo asali ne daga babu, ko kuma wannan tsari mai ban mamaki mai rikitarwa ya kasance sakamakon kwatsam marar hangen nesa!
(SIFFOFIN MAHALICCI)
Kamar yadda hankali mai kyau da halitta ta asali suke jagorantar mutum zuwa ga imani da samuwar mahaliccin kaunu, su ma suna tunkuɗa mu zuwa ga lura akan siffofin wannan mahalicci da haƙƙinSa a kanmu.
Haƙiƙa lura a cikin siffofin wannan Mahalicci yana buɗe mana ƙofofi na fahimta mai zurfi akan wajibcin siffantuwarSa da cikakken cika da tsarkakarSa daga dukkan wata tawaya.
wannan yana nufin cewa Mahalicci yana da dukkan siffofin kyau da girma, Shi - tsarki ya tabbatar maSa - mai iko a kan kowanne abu ne, masani ne a kan kowanne abu, mai hikima a cikin duk abin da Ya halitta Ya kuma ƙaddara. Kuma wannan cika ba kawai yiwuwa ba ce amma wajibi ne na hankali, domin duk wata tawaya a cikin siffofinSa zata haifar da ɓaci a cikin halitta da gudanarwa, wannan kuwa yana koruwa tare da abin da muke gani na kyautatuwa a cikin kaunu.
Kamar yadda tsarkakewa daga tawaya ke nuni da cewa Mahalicci Mawadaci ne daga halittunSa, ba Ya buƙatuwa zuwa ga wani, bari dai dukkaninsu mabukatane gare Shi a samuiwarsu da wanzuwarsu. Kuma Shi - tsarki ya tabbatar maSa - tsarkakakke ne daga barin abokin tarayya da ɗa, domin su alamomi ne na tawaya da gajiyawa, kuma Allah - tsarki ya tabbar masSa - Ya tsarkaka daga waɗannan gaba ɗaya.
Idan muka yi la’akari zuwa ga kaunu da lura da nazari, zai kai mu ga yaƙini cewa wanda ya samar da kaunu da wannan ƙayatarwar ba zai yi wu ba sai ya kasance Mahalicci cikakke cikin ZatinSa da SiffofinSa da AyyukanSa, tsarkakakke daga kowanne aibi ko naƙasa, Shi kaɗai Ya cancanci bauta da miƙa wuya.
Tabbatar da siffofin kamala ga Ubangiji tsarki ya tabbata a gare shi, yana nuni da kaɗaitakarSa da cewa Shi ne kaɗai mai cikakkiyar kamala daga dukkanin waninSa, domin cikakkiyar kamala ba ta dacewa sai da abu ɗaya, don haka ya wajaba ya kasance Shi kaɗai ne Ya cancanci a bauta maSa ba tare da waninSa ba.
Allah - tsarki ya tabbatar maSa - ba kawai Mahaliccin wannan kaunun bane! Bari dai, Shi ne Mamallaki mai tasarrufi a cikinta, wanda a hannunSa lamurran kowanne abu yake, wanda yake juya lamurranta da hikimarSa; babu wani abu da zai faru a cikin wannan kaunun sai da izininSa da nufinSa. Shi ne Mai yawan azirtawa wanda Ya ɗauki nauyin arzikin bayinSa, Ya samar musu da abinda suke buƙata daga sabubban rayuwa da wanzuwa.
To idan Allah ne Mahalicci mai girma wanda Ya ke da siffofin kamala da girma kuma Shi ne Ya samar da mu kuma Ya samar da kaunu daga babu, kuma Shi ne mamallakin duk abin da ke cikin ta, kuma Shi ne mai azurtarmu da kuma kewaye mu da rahamarSa, kuma Shi ne mai tsarawa da tasarrufin kowane abu; Shin bai wajaba a garemu ba mu gode maSa mu kuma nemi yadda zamu sami yardarSa da kuma yadda zamu cika haƙƙin da ya wajaba a kanmu kuma mu yi aiki don cimma manufar da Ya halicce mu saboda ita?!
(MANUFAR HALITTA)
Shin zai yi wu a hankalce Allah ya halicce mu sannan bai bayyana mana menene Yake so daga garemu ba?
Me yasa muke a nan? Mece ce manufa da burin samuwarmu a rayuwa?
Me zai faru da mu bayan mutuwa?
Ka yi tunani tare da ni idan wani mutum ya gina wani katafaren gida mai tsada, ya kuma cika shi da sabbin kayan fasaha, har ya gama gina shi, sai ya yi gaggawar rushe shi gaba ɗaya. Shin za mu iya kiran wannan mutum da mai hikima? Ashe ba bayyananne ba ne cewa irin wannan hali wasa ne wanda bai dace da mai hankali ba?
Idan wannan aiki bai karɓu ba a haƙƙin mutum, to yaya za mu yi tunanin cewa Allah mai hikima masani, Ya halicci wannan kaunun mai kyau da kyautatawa, sannan Ya rusa shi ba tare da wata manufa ko hikima ba?!
Allah Ya halicci mutane don wata babbar hikima, ita ce bautarSa Shi kaɗai ba tare da abokin tarayya ba, kuma Ya halicce su don Ya jarraba su a cikin wannan duniya, kuma Ya sanya masu lokaci da za a tashe su a ranar Alƙiyama don a yi masu hisabi akan ayyukansu; wanda ya yi imani da Allah kuma ya amsa kiranSa yana da ni'imar Aljanna yana mai dawwama a cikinta, wanda kuma ya juya baya ga gaskiya yana daga cikin mutanen wuta.
(Haƙƙin Allah a bisa mutane su bauta maSa kada kuma su yi shirkar wani abu da Shi.)
Lalle ibada ba ta kasancewa sai ga wanda ya cancance ta, kuma daga cikin manyan abubuwan da ke tabbatar da cancantar ibada shi ne abin bauta ya kasance Mahalicci mai shiryarwa mai azurtawa wanda yake da siffofin cika.
Amma waninSa, daga cikin halittu masu rauni marasa iko da ba su mallaki wani amfani ko cutarwa ga kansu ba, ba ya halatta a juyar musu wani abu daga cikin ibada. Lalle bauta wa waɗannan gumaka da halittu masu rauni yana nufin karkacewa daga daɓi'ar da ta dace wadda ta tabbatar da wajibcin bautawa Allah Shi kaɗai, Mahaliccin kaunu - tsarki ya tabbatar maSa -.
To ibada haƙƙi ce wajibi a kanmu domin ita ce manufar samuwarmu, kuma ita ce shaida ta godiyarmu da amincewarmu da rububiyar Allah da uluhiyarsa. Duk wanda ya kau da kai daga bautar Allah ko ya yi shirka da wani tare da Shi, to lalle ya zalunci kansa kuma ya kauce daga hanyar gaskiya wacce Allah Ya so wa bayinSa, kuma zai sami sakamakon aikinsa a lahira.
Ka yi tunanin wani ya ba ka miliyan ɗaya, yaya za ka yi masa godiya? Babu shakka za ka gode masa kuma ka yaba masa da godiya. Yanzu, idan wani ya ce maka zai ba ka miliyan biyu don ka ba shi idonka, za ka yarda? Tabbas, mai hankali ba zai yarda da hakan ba!
Ka yi tunani cewa Allah Maɗaukaki ne wanda Ya halicce ka, kuma Ya girmama ka da ji da gani, kuma Ya kewaye ka da ni'imomi da ba za a iya ƙirgawa ba. Shi ne wanda ke gudanarda jini a cikin jijiyoyinka, kuma Yana azurtar da kai da ruwa da iska, kuma a kowanne a lokaci kana buƙatarSa. Da ba don rahamarSa da kulawarSa ba, da ka halaka kuma ƙarfinka ya ɓace. Lalle ne Shi Maɗaukaki Ya ɗauki nauyin azurtar da kai tun kana cikin mahaifar babarka, ba ka da iko da komai.
Shin, wannan Mahalicci Mai girma bai cancanci ka nemi yardarSa ba?! Shin bai cancanci ka gode maSa akan ni'imominSa ba, ka kuma yi imani da Manzannin da Ya aiko su don su shiryar da kai zuwa ga hanyar gaskiya da farin ciki?!
Shin, wannan Mahalicci Mai girma bai cancanci ka bauta maSa ba kamar yadda Yake so, ba kamar yadda kake so ba?! Ka yi tunani idan kana son ka ba mahaifiyarka kyauta, shin za ka zaɓi abin da zai gamsar da son ranka, ko za ka yi ƙoƙari wajen sanin abin da take so don ka faranta mata rai da abin da ya dace da ita? Haka nan bautar Allah Maɗaukaki, bai kamata ta kasance bisa ga son ranmu ko al'adunmu na gado ba, sai dai kamar yadda Ya so, kuma bisa ga yadda Ya umarce mu.
Ita ibada ba kawai al'adu ko daɓi'u ba ce, amma bayani ne na miƙa wuya gaba ɗaya da ƙauna ta gaskiya ga mahalicci, da amincewa cewa wanda Ya halicce mu kuma Ya yi mana ni'imomi Shi ne mafi cancanta mu bauta maSa Shi kaɗai ba tare da abokin tarayya ba a kan tsarin da Yake yarda da shi. Shin za mu bauta wa Allah kamar yadda muke so, alhali kuwa Shi ne masani mai hikima wanda Ya san abin da ya dace da mu kuma Yake yarda da shi?
Tabbas ibada ta gaskiya tana fitowa daga fahimtar mu ga girman Allah da jin falalarSa da rahamarSa. Kuma duk lokacin da muka kusanci aiwatar da umarninSa, muka tsarkake a cikin biyayya gare Shi kamar yadda Ya so, sai kusancinmu da Shi ya ƙaru, da kuma yarda da mu ta ƙaru. Shin, wannan al’amari mai tsarki bai cancanci mu tsarkake shi tsantsa ba, nesa da son zuciyarmu da al'adunmu?
{Lalle ne, addini a wurin, Allah Shi ne Musulunci}
Saboda haka Allah Ya aiko da yawa cikin Annabawa da Manzanni don su sanar da mu game da manufar kasancewarmu a duniya da kuma manufar rayuwa, kuma dukkan Manzanni saƙon su guda ne wato saƙon Musulunci, amma akwai waɗanda suka jirkita suka canza abin da manzannin da suka gabata suka zo da shi. Sai Allah Ya aiko da cikamakin Manzanni (Annabi) Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) Ya saukar masa da saƙo na ƙarshe ga bil'adama wato Alƙur'ani mai girma. Akwai hujjoji masu yawa na hankali da na kimiyya da ke tabbatar da cewa Alƙur'ani maganar Allah ne, kuma shi ne littafi guda ɗaya da ba a taɓa jirkita shi da canza shi ba, kuma Allah Ya sanar da mu a cikin Alƙur'ani cewa ba zai karɓi daga wani mutum ba sai addinin Musulunci, kuma dukkan Manzanni saƙonsu guda ne wato kira zuwa ga Tauhidi na mahalicci da bautarSa Shi kaɗai ba tare da shirka ba.
Abinda ya bambanta Musulunci da sauran addinai shi ne, Musulmai su ne kaɗai masu iya gabatar da dalilai na hankali da tabbaci na kimyya, ta hanyar dogaro da madogara na ilimi masu tabbas, don tabbatar da cewa Alƙur'ani mai girma da ke hannunsu a yau shi ne zancen Allah Mahalicci - tsarki ya tabbatar maSa -, tsararre daga kowanne canji da jirkita.
Alƙur'ani mai girma shi ne littafin da Allah ya saukar ga Annabinsa Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - kuma ya ƙalubalanci bil'adama tun fiye da shekaru dubu da ɗari huɗu da suka gabata akan su zo da kwatankwacinsa, ko da sura ɗaya makamanciyarsa, sai suka kasa hakan, kuma har yanzu wannan ƙalubalen yana nan ba tare da wani ya iya kawo wani abu da ya yi daidai da shi a cikin Balaga, bayani, mu'ujiza, da shari'a ba, kuma Allah Ya faɗa a cikin Alƙur'ani Yana ƙalubalantar dukkan halittu:
Amma duk da haka, babu wanda ya iya kawo wani abu da ya yi kama da shi ko ma kusa da shi a tsawon zamani.
Kuma mu’ujiza a cikin Alƙur'ani ba kawai a cikin harshensa wanda ya kai ƙololuwa a fasaha da bayani ba, a’a ya haɗa da dalilai na hankali da kuma na kimiyya waɗanda suke ƙarfafar da cewa shi zancen Allah ne:
Saboda Alƙur'ani ya yi magana akan gaskiyar ilimin kimiyya waɗanda ba a gano su ba sai bayan ɗaruruwan shekaru da saukar sa, kamar matakan rayuwar jariri a cikin mahaifiyarsa, inda Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Ya ce game da halittar mutum:
{Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya.Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma..."
Wane ne ya faɗa wa Manzo Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da wannan gaskiyar alhali a zamaninsu babu na'urorin bincike na likitanci da za su bayyana irin waɗannan al'amurra?! Kuma wannan misali ne guda ɗaya daga cikin misalai da dama waɗanda ke bayyana ga duk mai adalci cewa asalin wannan Alƙur'ani na Ubangiji ne kuma cewa littafi ne na sama da aka saukar daga Mahaliccin kaunu, - tsarki ya tabbata a gare Shi -.
Alƙur'ani shi ne littafi guda ɗaya da Allah Ya lamunce kiyaye shi, sai Ya ce:
Tsawon shekaru masu yawa, Alƙur'ani ya kasance yadda yake, an kiyaye shi a cikin zukatan miliyoyin (mutane), kuma an rubuta shi daidai a cikin masahifai, ba tare da ƙari ko ragi ba, saɓanin sauran littattafai da suka fuskanci jirkitawa da canji.
Alƙur'ani ya zo da tsare-tsare masu cike da kamala waɗanda ke tsara rayuwar mutum da al'umma, kuma suna daidaita tsakanin ruhi da jiki, wanda falsafancin ɗan Adam ba su iya cimmawa ba. Dokokin Alƙur'ani suna magana da hankali kuma suna dacewa da ɗabi'a.
To Alƙur'ani ba littafin ɗan Adam bane, a'a saƙon Allah ne ga bil'adama, cike da manya-manyan dalilai na hankali da na kimiyya, kuma an kiyaye shi daga jirkita, domin ya kasance dalili mai dawwama a kan gaskiyar saƙon Musulunci da mu'ujizarsa.
Idan Alƙur'ani mai girma yana ƙunshe da hujjoji bayyanannu waɗanda suke tabbatar da cewa shi zancen Allah ne, to abin da ya dace da hankali da kuma tunani mai kyau shi ne imani da shi da kuma bin abinda ya zo da shi, maimakon dogaro da wasu littattafai da suka sami tasiri da cushe na mutane a cikin rubutasu.
Hankali lafiyayye yana jagorantar mu zuwa ga cewa zancan Mahalicci, wanda Ya halicci kaunu kuma Ya kyautata tsarin ta, shi ne mafi gaskiyar tushe don sanin gaskiya. Kuma idan muka samu wannan mu'ujiza a harshe a cikin Alƙur'ani, da tabbaci na kimiyya, da cikakkun dokoki, tare da kariyarsa daga jirkita tsawon zamani, babu makawa mu yarda cewa zancan Allah ne.
Saboda haka, imani da abinda ya zo a cikin Alƙur'ani ba zaɓi na imani kawai ba ne, a'a hukunci ne na hankali da ya yi daidai da azancin neman gaskiya. Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
{"Lalle ne wannan Alƙur'ãni yanã shiryarwa ga (hãlayen) waɗanda suke mafi daidaita".}
Shi ne wanda Yake shiryar da mutum zuwa hanya madaidaiciya, Yake amsa tambayoyinsa manya a wannan duniya, Yake nuna masa manufar rayuwarsa.
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya bayyana a cikin Alƙur'ani mai girma cewa Bai halicce mu don wasa ba, sai dai Ya halicce mu don bautarSa Shi kaɗai, sai - Maɗaukakin Sarki - Ya ce:
Allah Ya bamu labari a cikin Alƙur'ani cewa wannan rayuwar duniya da muke rayuwa ita kawai wani mataki ne na ɗan lokaci da za ta ƙare nan ba da jimawa ba, amma tabbatacciyar rayuwa madawwamiya za ta kasance a lahira lokacin da muminai za su shiga Aljanna kuma kafirai su shiga wuta. Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce:
{Kuma wannan rãyuwa ta dũniya ba ta zamo ba, fãce abar shagala da wãsã kuma lalle Lãhira tabbas, ita ce rãyuwa, dã sun kasance sunã sani.}
To Mahaliccin da Ya halicce mu daga babu, tabbas Mai ĩkon yi ne a kan dawo da mu zuwa rayuwa bayan mutuwa. Kuma a cikin abin da ke kewaye da mu daga cikin ayoyin Allah a kaunu, muna shaida hujja bayyananniya akan ikon Allah wanda ba shi da iyaka wajen rãyar da abin da ya mutu. Kamar yadda Allah ke fitar da wuta daga bishiya koriya, kuma Ya ke fitar da amfanin gona da 'ya'yan itãce daga ƙasa mai bushewa kuma Ya halicci jariri a cikin mahaifiyarsa daga ɗigon ruwa, lalle Shi, - Mai tsarki -, Mai ĩko ne a kan rãyar da matattu kuma Ya tashe su daga kaburburansu don sakamako a ranar Alƙiyama, lalle ne Allah Mai ĩkon yi ne a kan kõme.
Allah - Maɗaukakin Sarki - a cikin Al-ƙur'ani mai girma Ya ce:
Shin, kuma Wanda Ya halitta sammai da ƙasã bai zama Mai ĩkon yi ba ga Ya halitta kwatankwacinsu? Na'am, zai iya! Kuma Shĩ Mai yawan halittãwa ne, Mai ilmi."
UmurninSa idan Yã yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, "Ka kasance," sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi).
Sabõda haka, tsarki yã tabbata ga Wanda mallakar kõwane abu take ga HannãyenSa, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.}
Daga cikin zalunci da rashin adalci shi ne rayuwar azzalumi da wanda aka zalunta ta ƙare ba tare da hisabi ko sakamako ba. Ta yaya zai yi wu a ce mai laifi ya tsira daga uƙubarsa, yayin da wanda aka zalunta ya rasa haƙƙinsa? Lallai Allah - Maɗaukakin Sarki - Ya sanya ranar Alƙiyama a matsayin lokacin adalci, domin Ya sakawa kowanne mutum da abinda ya gabatar, Ya kuma sakawa dukkanin mai kyautatawa bisa ayyukansa na alheri, kuma Ya yi wa dukkanin mai laifi da azzalumi uƙubar abinda ya aikata na sharri da zalunci.
(ME YA SA MUSULUNCI)
---
Mutum yana tambaya, me ya sa Musulunci ba wani addini ba?!
Haƙiƙa Allah Ya aiko manzanni, kuma Ya saukar da littattafai domin mu san waye Allah, kuma mu san yadda za mu bauta maSa. Allah Ya bayyana mana cewa wannan rayuwar jarrabawa ce, kuma wanda ya bauta wa Allah kuma ya aikata ayyuka na gari zai sami sakamako da aljanna, amma wanda ya juya baya ga Allah kuma ya ƙi bauta maSa ko ya bauta wa waninSa, to Allah zai Yi masa hisabi kan ƙin gaskiya ranar alƙiyama.
Addinin da dukkanin manzanni suka zo da shi shi ne Musulunci, yana nufin miƙa wuya da sallamawa ga nufin Mahalicci da bauta wa Allah Shi kadai ba tare da shirka ba, da imani da dukkanin manzanni.
Haƙiƙa babban abin da ya bambanta mutum daga sauran halittu shi ne hankali, aikinsa tunani da bincike kan gaskiya.
Tabbas, Musulunci addini ne mai dacewa da hankali mai kyau da ɗabi'a madaidaiciya, yana bayar da amsoshi masu ma'ana ga manyan tambayoyin samuwa: me yasa muke nan? Mece ce manufar rayuwarmu? Kuma mece ce makoma bayan mutuwa?
Addinin Musulunci yana wajabta imani da dukkan manzanni, don haka musulmai suna imani kamar yadda Allah Ya bayyana a cikin Alƙur'ani cewa (Annabi) Isa bawan Allah ne kuma manzonSa ne, kuma shi ba ɗan Allah ba ne; domin cewa Allah Mai girma ne kuma ba zai yiwu Ya zama Yana da mata ko da ba, domin Shi Ya wadatu daga gare su da kuma komai. Allah Ya bamu labari a cikin Alƙur'ani cewa (Annabi) Isa ya kasance Annabi ne da Allah Ya ba shi mu'ujizoji masu yawa, kuma Allah Ya aiko shi dOn kiran mutanensa zuwa ga bautar Allah Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya, kuma Ya bamu labari cewa (Annabi) Isa bai nemi mutane su bauta masa ba, a'a ya kasance shi da kansa yana bautawa mahaliccinsa. Idan kana son ka kasance mai imani da (Annabi) Isa bisa gaskiyar da Allah ke so, to ya zama wajibi ka shiga cikin addinin Musulunci ka yi imani da abin da Allah Ya ambata a cikin Alƙur'ani, domin shi ne littafin da aka kiyaye wanda ya zo don sabunta saƙon Tauhidi da Allah Ya aiko da shi ga dukkan Annabawa da manzanni na baya.
Kuma Allah ya ba mu labari a cikin Alƙur'ani cewa Annabi Isa ya umarci mutanensa da su bautawa Allah shi kaɗai kuma ya gargaɗe su kan shirka, Allah Ya ce a cikin Alƙur'ani mai girma:
{Lalle ne haƙĩƙa waɗanda suka ce: "Lalle ne Allah, shĩne Masĩhu, ɗan Maryama," sun kãfirta. Alhãli kuwa Masĩhu yã ce: "Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku bauta wa Allah Ubangijina, kuma Ubangijinku." Lalle ne shĩ, wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne, Allah Yã haramta masa Aljanna. Kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai.
Lalle ne, haƙĩƙa, waɗanda suka ce: "Allah na ukun uku ne," sun kãfirta, kuma babu wani abin bautãwa fãce Ubangiji Guda. Kuma idan ba su hanu daga abin da suke faɗa ba, haƙĩƙa, wata azãba mai raɗaɗi tãnã shãfar waɗanda suka kãfirta daga gare su.
(KA TAMBAYI KANKA YA KAI MUTUM)
Ya kai mutum, ta yaya hankalinka zai yarda cewa gunki wanda ka ƙera da hannunka shi ne Allah wanda kake masa sujada kuma kake neman taimako daga gare shi?! Ta yaya zaka yarda ka bautawa saniya wadda ake yankata kuma ake ci?! Shin yana daga cikin hankali mai hankali ya bautawa abin halitta irinsa, wanda yake jin yunwa da ƙishirwa kuma bai iya kare kansa daga mutuwa ko cuta ba?! Kuma ta yaya za a bautawa Isa ɗan Maryam, alhali kuwa shi mutum ne wanda yake buƙatar abinci da abin sha, kuma yana mai da kansa ga Mahaliccinsa da sallah?! Shin zai yi wu ga hankali ya yi tunanin cewa Allah Yana Yi wa kanSa sallah ?!
Shin Allah ba Shi ne mai siffantuwa da girma, wanda Ya ke da cika ta kai tsaye, wanda Ya ke tsarkakakke daga kamanceceniya da misali, kuma duk abinda ke cikin sararin samaniya yana ƙarƙashin ikonSa da mulkinSa? Ta yaya za a yi tunanin cewa Mahaliccin sammai da ƙasa zai sauko ya zama jariri, sannan ya miƙa kansa ga halittarsa don su gicciye shi? Lallai waɗanda ake gicciyewa da kashewa su ne 'yan adam masu ƙarewa, amma Mahalicci shi ne mai rai wanda ba Ya mutuwa, mai tsayuwa wanda gyangyaɗi ko bacci basa ɗaukarSa. Shin ba daga cikakken girmanSa da ɗaukakarSa ba ne Ya kasance tsarkakakke daga irin wannan?
Haƙiƙa Allah Ya sanar da mu a cikin Alƙur'ani mai girma cewa dukkanin manzanni sun zo da saƙo guda ɗaya wanda yake taƙaituwa a kan kiran mutanensu zuwa ga bautar Allah Shi kaɗai ba Shi da abokin tarayya. Amma a tsawon zamani, wasu sun karkatar da wannan saƙo madawwami, suka ɓoye hasken Tauhidi da Annabawa suka zo da shi, sai Allah Ya aiko da manzo na ƙarshe Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), Ya saukar masa da Alƙur'ani mai girma don ya sabunta saƙon Tauhidi da dukkanin manzanni suka zo da shi a baya.
Ya kai mutum, haƙiƙa gaskiyar da dukkanin manzanni suka zo da ita, ita ce cewa Allah Shi kaɗai ne Ya cancanci bauta, ba gumaka ba, ba kuma bishiyoyi da dabbobi ba, ba Almasihu Isa (tsira ya tabbata a gare shi) ba, ba kuma yanayi ba, ba kuma rana ba, ba kuma wata ba.
Mutum ana haifarsa ne akan ɗabi'ar Musulunci mai tsarki, wadda ke shiryar da shi zuwa ga Ubangijinsa ta hanyar ɗabi'a da hankali, amma yanayin dake kewaye da shi, na iyali ko al'umma, na iya sauya wannan ɗabi'ar kuma ya tura shi zuwa wata hanya.
Ka kwatanta tsakanin addinin da yake umartar ka da bautawa Mahalicci guda cikakke, da kuma addinin da yake siffanta Allah da gazawa da rauni, to wanne ne daga cikinsu ya dace da hankali da ɗabi'a?
kuma a ƙarshe muna cewa gare ka, ya kai ɗan Adam:
Tabbas, Musulunci addini ne na hankali da ɗabi'a, kuma shi ne addini guda ɗaya da Mahalicci Mai girma Ya shar’anta ga ɗan Adam, shi ne addinin alheri da tsira ga mutane baki ɗaya, ba ya banbance wani asali akan wani asali, ko launi akan wani launin, mutane a cikinsa madaidaita ne, wani ba ya banbanta a musulunci akan waninsa sai da gwargwadan aikinsa na gari. Kuma shi ne addini guda ɗaya da yake gaskata dukkan Annabawa kuma yana sanya kusancin bawa ga Mahaliccinsa kai tsaye ba tare da buƙatar wani tsani ba, kuma shi ne addinin da yake umarni da tunani da nazari kuma yana ƙarfafa yin amfani da hankali da tunani mai ma'ana.
Yana wajaba akan kowanne mutum mai hankali ya yi gaggawar shiga Musulunci, ta hanyar yin imani da Allah Ubangiji, da Musulunci (a matsayin) addini, da (Annabi) Muhammad (a matsayin) manzo, wannan wani al'amari ne babu wani zaɓi ga mutum a cikinsa, domin Allah Zai tambaye shi ranar Alƙiyama a kan abin da ya amsawa manzanni da shi; idan ya kasance mumini ne to rabo da tsira mai girma sun tabbata gare shi, idan kuma ya kasance kafiri ne, to taɓewa mabayyaniya ta tabbata gare shi.
Idan kana son farin ciki a duniya da lahira, kuma kana son yanke mafi girman shawara a rayuwarka, to ya wajaba ka shiga Musulunci ta hanyar faɗin waɗannan kalmomi kana mai imani da su daga zuciyarka:
(Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaida cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne), da wannan zaka zamo musulmi.
Allah - Maɗaukakin Sarki - a ckin AlKur'ani mai girma Ya ce:
{Kuma wanda ya nẽmi wanin Musulunci ya zama addini, to, bã zã a karɓa daga gare shi ba. Kuma shi a Lãhira yana daga cikin mãsu hasãra.}
(Sannan ka fara koyon shari'o'in Musulunci sannu a hankali; don ka aikata abin da Allah Ya wajabta a kanka)
Za a iya sanin Musulunci ta ziyartar wannan shafin:
Related books
All books
HANYOYI MASU AMFANI DON SAMUN RAYUWA MAI DAƊI85 harsunaHANYOYI MASU AMFANI DON SAMUN RAYUWA MAI DAƊI
Littafin Hanyoyi masu amfani don samun rayuwa mai daɗi na Shaikh Abdurrahman bn Nasir al-Sa’di - Allah Ya yi masa rahama - yana magance sabubban tabbataccen jin daɗi na haƙiƙa daga mahangar imani mai zurfi, yana shiryar da mai karatu zuwa nutsuwar zuciya ta hanyar imani da aiki na gari, da zikirin Allah, da gamsuwa da abin da Allah Ya bayar, da tafakkuri a kan ni’imomi, da kyautatawa, da dogaro ga Allah, da haƙuri, da kyakkyawan ƙimanta al’amura, da salo mai kyau. Yana sanya taswira ga rayuwa mai natsuwa a gabanka, madaidaiciya, kuma mai daɗi duk da juyin-juya-halin rayuwa.
TAƘAITACCEN BAYANI A KAN AƘIDAR MUSULUNCI75 harsunaTAƘAITACCEN BAYANI A KAN AƘIDAR MUSULUNCI
Littafin yana bayyana tushen imani waɗanda suka haɗa da imani da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da ManzanninSa, da ranar lahira, da ƙaddara; kuma yana gabatar da ƙa'idojin asali waɗanda wajibi ne a kan musulmi ya yi imani da su kuma ya yi aiki da abin da suka wajabta, yana mai ƙarfafa muhimmancin dangantaka da Allah ta hanyar zurfafa fahimtar aƙidar Musulunci.
WANENE YA HALICCE NI? KUMA SABODA ME?75 harsunaWANENE YA HALICCE NI? KUMA SABODA ME?
Ko wanne abu yana nuni akan akwai mahalicci Wa ya halicci sammai da kasa da abinda ke tsakanin su na halittu masu girma wadanda ba’a iya gane yawansu? Wa ya kera wannan nagartaccan tsarin kayatacce a sama da kasa ? Wa ya halicci mutum ya kuma ba shi ji da gani da hankali? Ya sanya shi mai iko akan tsururutar ilimai da gane hakikanin abubuwa ? Yaya zaka fassara wannan kira gwananna dake na'urorin (gabban) jikinka da suke kuma a jukkunan kasantattu suna aiki? kuma wanene ya kage su? Ta yaya wannan kasantacce mai girma yake tsaruwa kuma yake tabbatuwa tare da ƙa’idojin sa, waɗanda suke kiyaye…
MUSULUNCI89 harsunaMUSULUNCI
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin ƙai. Shin ka tambayi kanka: Wa ya halicci sammai da ƙasa da abinda yake cikinsu, na halittu masu girma? Wa ya ƙera wannan ƙwararran tsari nagartacce a cikin su?