Skip to content

Duk wanda ya sauka wani masauki, sai ya ce: Ina neman tsarin kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, to, babu abin da zai cutar da shi har ya bar wannan masaukin

Daga Khaulah ’Yar Hakim Al-Sulamiyyah, ta ce: Na ji Ma’aikin Allh tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:

Duk wanda ya sauka wani masauki, sai ya ce: Ina neman tsarin kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, to, babu abin da zai cutar da shi har ya bar wannan masaukin.

«مَنْ نَزَلَ مَنْزِلًا ثُمَّ قَالَ: أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ، لَمْ يَضُرَّهُ شَيْءٌ حَتَّى يَرْتَحِلَ مِنْ مَنْزِلِهِ ذَلِكَ».

Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana nunawa al’ummarsa mafaka da matsera masu amfani, waɗanda za su kawar masa da duk abin da mutum yake tsoro, a lokacin da yake a wani wuri a nan doran ƙasa, shin yana halin tafiya ne ko shaƙatawa, ko wanin haka: sai ya nemi tsari da mafaka da kalmomin Allah cikakku a falalarsu da albarkarsu da amfaninsu, wanda ba su da kowane aibi da tawaya, daga sharrin duk abin halitta, to, sai ya amintu a inda ya sauka, muddin yana nan babu abin da zai cutar da shi.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Neman tsari ibada ne, kuma shi ne abin da ya kasance daga Allah maɗaukaki ko sunayanSa ko kuma siffofinSa.

Halaccin neman tsarin Allah da zancenSa, domin sifa ce daga cikin siffofinSa mai tsarki, saɓanin neman tsari daga wani abin halitta wannan shirka ne.

Falalar wannan Addu’ar da kuma albarkarta.

Neman mafaka da zikiri dalili ne na tsare bawa daga sharri.

Lalata neman tsari da wanin Allah kamar aljan da matsafa da shedanu da sauransu.

Shar’antuwar wannan Addu’ar ga duk wanda ya sauka wani wuri a halin zaman gida ko tafiya.

Manazarta

Sahih Muslim (4/ 2080) (2708).

Kari (9)

مجموع الفتاوى (6/ 230).

القول المفيد على كتاب التوحيد.

لابن عثيمين (1/ 253).

الملخص في شرح كتاب التوحيد.

لصالح الفوزان (ص111).

الجديد في شرح كتاب التوحيد.

لمحمد القرعاوي (ص122).

معجم اللغة العربية المعاصرة.

لأحمد مختار (2/ 869).