Mace ce ta sha azumin kwana bakwai a Ramadan, alhalin tana cikin biƙi, kuma ba ta rama ba har Ramadan na biyu ya sameta, kuma ya zago mata a Ramadan na biyu kwana bakwai alhalin tana shayarwa, ba ta rama ba; da hujjar tana da wata rashin lafiya, menene ya wajaba a kanta ga shi kuma Ramadan na uku ya kusa shigowa? Ku fa'idantar da mu, Allah Ya saka muku da alheri.
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Mace ce ta sha azumin kwana bakwai a Ramadan, alhalin tana cikin biƙi, kuma ba ta rama ba har Ramadan na biyu ya sameta, kuma ya zago mata a Ramadan na biyu kwana bakwai alhalin tana shayarwa, ba ta rama ba; da hujjar tana da wata rashin lafiya, menene ya wajaba a kanta ga shi kuma Ramadan na uku ya kusa shigowa? Ku fa'idantar da mu, Allah Ya saka muku da alheri.
س19: امرأةٌ أفطرت في رمضان سبعة أيامٍ وهي نفساء، ولم تقض حتى أتاها رمضان الثاني، وطافها من رمضان الثاني سبعة أيامٍ وهي مرضعٌ، ولم تقض؛ بحجّة مرضٍ عندها، فماذا عليها وقد أوشك دخول رمضان الثالث؟ أفيدونا أثابكم الله.
الجواب
AMSA TA 1:
Idan wannan matar ta kasance kamar yadda ta ambata game da kanta -cewa tana cikin rashin lafiya, kuma ba ta da ikon ramawa- to, duk lokacin da ta samu iko, sai ta azumce shi; sabo da tana da uzuri, ko da Ramadan na biyu ya zo.
Amma idan ya kasance, ba ta da uzuri, kawai dai tana langaɓewa ne kawai, tana sakaci, to, haƙiƙa ba ya halatta a gareta ta jinkirta ramuwar Ramadan zuwa wani Ramadan na biyu.
Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Yakan kasance ana bi na azumi, ba na samun ikon rama shi sai a Sha'aban.
A bisa wannan, ya wajaba a kan matar ta yi nazari a kanta, idan ya zamo ba ta da uzuri, to, ta saɓawa Allah, Lallai ta tuba zuwa ga Allah, kuma ta gaggauta ramuwar abin da ya ke kanta, na azumin, idan kuma tana da uzuri, to babu laifi a kanta, ko da ta jinkirta tsawon shekara ɗaya ko biyu.
ﺟ19: إذا كانت هذه المرأة كما ذكرت عن نفسها -أنها في مرضٍ، ولا تستطيع القضاء- فإنها متى استطاعت صامته؛ لأنها معذورةٌ، حتى ولو جاء رمضان الثاني.
أما إذا كان لا عذر لها، وإنما تتعلل وتتهاون، فإنه لا يجوز لها أن تؤخّر قضاء رمضان إلى رمضان الثاني، قالت عائشة رضي الله عنها:
«كَانَ يَكُونُ عَلَيَّ الصَّوْمُ، فَمَا أَسْتَطِيعُ أَنْ أَقْضِيَهُ إِلَّا فِي شَعْبَانَ» [1].
[4] البخاري، كتاب الصوم، باب متى يقضي قضاء رمضان (1950)، ومسلم، كتاب الصيام، باب في جواز تأخير قضاء رمضان (151) (1147).
وعلى هذا، فعلى هذه المرأة أن تنظر في نفسها، إذا كان لا عذر لها فهي آثمةٌ، وعليها أن تتوب إلى الله، وأن تبادر بقضاء ما في ذمتها من الصّيام، وإن كانت معذورةً فلا حرج عليها، ولو تأخرت سنةً أو سنتين.