Skip to content

Wasu matan watan Ramadan na biyu yana shigo musu, alhali ba su azumci wasu kwanaki a Ramadan da ya gabata ba, menene wajibi a kansu?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Wasu matan watan Ramadan na biyu yana shigo musu, alhali ba su azumci wasu kwanaki a Ramadan da ya gabata ba, menene wajibi a kansu?

س20: بعض النّساء يدخل عليهن رمضان الثاني وهن لم يصمن أيامًا من رمضان السابق، فما الواجب عليهن؟

الجواب

AMSA TA 1:

Wajibi a kansu shi ne tuba zuwa ga Allah daga wannan aikin; sabo da ba ya halatta ga wanda akwai ramuwar Ramadan a kansa ya jinkirta shi zuwa Ramadan na biyu, ba tare wani da uzuri ba; sabo da faɗin Nana A'isha Allah - Ya yarda da ita -: Yakan kasance ana bi na azumin Ramadan, ba na samun ramawashi sai a Sha'aban.

Wannan yana nuna cewa ba ya halatta a jinkirta shi zuwa abinda ke bayan Ramadan na biyu, ya zama ya wajaba a kanta ta tuba zuwa ga Allah - mai girma da buwaya - daga abin da ta aikata, kuma ta rama kwanakin da ta bari, bayan Ramadan na biyun.

جـ20: الواجب عليهن: التوبة إلى الله من هذا العمل؛ لأنه لا يجوز لـمن عليه قضاء رمضان أن يؤخّره إلى رمضان الثاني بلا عذرٍ؛ لقول عائشة رضي الله عنها:

«كَانَ يَكُونُ عَلَيَّ الصَّوْمُ مِنْ رَمَضَانَ، فَمَا أَسْتَطِيعُ أَنْ أَقْضِيَهُ إِلَّا فِي شَعْبَانَ».

وهذا يدلّ على أنه لا يمكن تأخيره إلى ما بعد رمضان الثاني، فعليها أن تتوب إلى الله عز وجل مما صنعت، وأن تقضي الأيام التي تركتها بعد رمضان الثّاني.