Skip to content

Idan mace ta yi haila da ƙarfe ɗaya na rana misali, alhali kuma ita ba ta yi sallar Azahar ba, shin lallai ne sai ta rama wannan sallar bayan tsarki?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Idan mace ta yi haila da ƙarfe ɗaya na rana misali, alhali kuma ita ba ta yi sallar Azahar ba, shin lallai ne sai ta rama wannan sallar bayan tsarki?

س21: إذا حاضت المرأة الساعة الواحدة ظهرًا مثلًا، وهي لم تصلّ بعد صلاة الظّهر، فهل يلزمها قضاء تلك الصلاة بعد الطّهر؟

الجواب

AMSA TA 1:

A wannan akwai saɓani tsakanin malamai, a cikinsu akwai wanda ya ce: Ba ya zama lallai a kanta ta rama wannan sallar; saboda ba ta yi sakaci ba, kuma ba ta yi saɓo ba, domin ya halatta a gareta ta jinkirta sallar har zuwa ƙarshen lokacinta.

Daga cikinsu akwai wanda ya ce: Lallai ne ramuwa ta lazimceta, ai ramuwar wannan sallar; sabo da gamewar faɗinsa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:

"Wanda ya riski raka'a ɗaya daga cikin sallah, to, hakiƙa ya riski sallah".

Abin da ya fi mata mafita daga ruɗani shi ne, ta rama ta; sabo da sallah ce guda ɗaya, babu wahala a ramata".

ﺟ21: في هذا خلافٌ بين العلماء، فمنهم من قال: إنه لا يلزمها أن تقضي هذه الصلاة؛ لأنها لم تفرط، ولم تأثم؛ حيث إنه يجوز لها أن تؤخّر الصلاة إلى آخر وقتها.

ومنهم من قال: إنه يلزمها القضاء، أي: قضاء تلك الصلاة؛ لعموم قوله ﷺ:

«مَنْ أَدْرَكَ رَكْعَةً مِنَ الصَّلَاةِ فَقَدْ أَدْرَكَ الصَّلَاةَ» [1].

[5] تقدم تخريجه.

والاحتياط لها: أن تقضيها؛ لأنها صلاةٌ واحدةٌ، لا مشقة في قضائها.