Skip to content

Shin lallai ne ga mai haila sai ta sauya tufafinta, bayan tsarkinta, tare da sanin cewa, ba wani jini ko najasa da ya same su?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Shin lallai ne ga mai haila sai ta sauya tufafinta, bayan tsarkinta, tare da sanin cewa, ba wani jini ko najasa da ya same su?

س18: هل يلزم الحائض تغيير ملابسها بعد طهرها، مع العلم أنه لم يصبها دمٌ ولا نجاسةٌ؟

الجواب

AMSA TA 1:

Hakan ba lallai ne a kanta ba; sabo da haila ba ta najasta jiki, kaɗai dai jinin haila, yana najasta abin da ya haɗu da shi, kawai, shi ya sa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gre shi - ya umarnci mata, idan jinin haila ya taɓa tufafin su, sai su wanke shi, su yi sallah a cikin tufafin su.

ﺟ18: لا يلزمها ذلك؛ لأن الحيض لا ينجّس البدن، وإنما دم الحيض ينجّس ما لاقاه فقط، ولهذا أمر النبي ﷺ النّساء إذا أصاب ثيابهن دم حيضٍ أن يغسلنه، ويصلّين في ثيابهن.