Skip to content

Mace ce hatsari ya rutsa da ita, kuma ta kasance a farko farkon cikinta, sai ɗan tayin ya ɓare sakamakon zubar jini mai tsanani, shin ya halatta ta sha, ko kuma za ta ci gaba da azumin? shin idan ta sha akwai zunubi a kanta?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Mace ce hatsari ya rutsa da ita, kuma ta kasance a farko farkon cikinta, sai ɗan tayin ya ɓare sakamakon zubar jini mai tsanani, shin ya halatta ta sha, ko kuma za ta ci gaba da azumin? shin idan ta sha akwai zunubi a kanta?

س28: امرأةٌ أصيبت في حادثةٍ، وكانت في بداية الحمل، فأسقطت الجنين إثر نزيفٍ حادٍّ، فهل يجوز لها أن تفطر، أو تواصل الصّيام؟ وإذا أفطرت فهل عليها إثمٌ؟

الجواب

AMSA TA 1:

Za mu ce ne: Haƙiƙa mai ciki ba ta yin haila, kamar yadda Imam Ahmad ya ce: Mata suna gane samun ciki ne ta hanyar ɗaukewar haila. Haila - kamar yadda malamai suka ce - Allah - maɗaukakin sarki - Ya halicceta ne sabo da hikimar abinci ga ɗan tayi a cikin mahaifiyar sa, idan ciki ya samu sai haila ta ɗauke.

Saidai wasu matan hailar ta kan zarce da su a bisa al'adarta kamar yadda ya ke kafin cikin, to, irin wannan za ayi mata hukuncin cewa hailarta haila ce ingantacciya; sabo da hailar ta ci mata gaba, kuma hailar bata tasirantu da cikin ba, sai wannan hailar ta zamo, ta hana dukkan abin da hailar mara ciki ta ke hanawa, kuma ta wajabta abin da ta ke wajabtawa, kuma ta sarayar da abin da take sarayarwa.

A ɗunkule dai: Jinin da ya ke fitowa daga mai ciki nau'i biyu ne:

  • Nau'in da za'a yi masa hukuncin haila, shi ne wanda ya zarce mata kamar yadda ya kasance kafin samun ciki, ma'anar haka shi ne: Cikin bai yi wani tasiri agareshi ba, sai ya zamo haila ne.

Nau'i na biyu: Shi ne jinin da ya bijirowa mai ciki iya bijirowa, ko dai sabo da wani hatsari, ko ɗaukar wani abu, ko faɗowa daga wani abu, da makamancin sa to, ita wannan jininta ba na haila ba ne, kaɗai jinin wata jijiya ne.

A bisa haka ba zai hanata sallah ba, ko azumi, kai, ita tana cikin hukuncin masu tsarki.

Amma idan hatsarin ya jawo ɗanta ya sauko, ko kuma cikin da ta ke ɗauke da shi, to, ita a nan kamar yadda malamai su ka ce: In ya fito alhalin halittar mutum ta bayyana a tare da shi, to, jininta bayan fitowar tasa, za a lissafa shi amatsayi biƙi, za ta bar sallah da azumi, kuma mijinta zai nisanceta har sai ta yi tsarki.

Idan ɗan tayin ya fito, alhalin ba a cika halittarsa ba, to, ba za'a yi izina da shi a matsayin jinin biƙi ba, ya zama jinin cuta, ba zai hanata sallah ba, ko azumi, ko waninsu.

Malamai sun ce: Mafi ƙarancin lokacin da tsarin halittar ya ke bayyana: Shi ne kwana tamanin da ɗaya; sabo da ɗan tayin yana cikin mahaifiyar sa.

Kamar yadda Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya zantar da mu, shi mai gaskiya ne abin gasgatawa, ya ce: "Haƙiƙa ɗayanku ana tara halittar sa a cikin mahaifiyar sa kwana arba'in, sannan ya kasance gudan jini misalin haka, sannan ya kasance gudan tsoka misalin haka, sannan ya aiko masa Mala'ika, zai umarce shi da kalmomi huɗu, sai ya rubuta arziƙin sa, da ajalin sa, da aikin sa, kuma matsiyaci ne, ko mai arziƙi".

Ba zai yiwu ba a halicce shi kafin haka, a mafi yawanci cikar halittar ba ta bayyana kafin kwana casa'in, kamar yadda wasu malamai suka ce.

ﺟ28: نقول: إن الحامل لا تحيض، كما قال الإمام أحمد:

"إنما تعرف النّساء الحمل بانقطاع الحيض".

والحيض -كما قال أهل العلم- خلقه الله تبارك وتعالى لحكمة غذاء الجنين في بطن أمّه، فإذا نشأ الحمل انقطع الحيض.

لكن بعض النّساء قد يستمرّ بها الحيض على عادته كما كان قبل الحمل، فهذه يحكم بأن حيضها حيضٌ صحيحٌ؛ لأنه استمر بها الحيض، ولم يتأثر بالحمل، فيكون هذا الحيض مانعًا لكلّ ما يمنعه حيض غير الحامل، وموجبًا لـما يوجبه، ومسقطًا لـما يسقطه.

والحاصل: أن الدم الّذي يخرج من الحامل على نوعين:

نوعٌ يحكم بأنه حيضٌ، وهو الّذي استمر بها كما كان قبل الحمل، فمعنى ذلك: أن الحمل لم يؤثّر عليه، فيكون حيضًا.

والنوع الثاني: دمٌ طرأ على الحمل طروءًا، إما بسببٍ حادثٍ، أو حمل شيءٍ، أو سقوطٍ من شيءٍ ونحوه، فهذه دمها ليس بحيضٍ، وإنما هو دم عرقٍ،

وعلى هذا فلا يمنعها من الصلاة، ولا من الصوم، بل هي في حكم الطاهرات.

ولكن إذا لزم من الحادث أن ينزل الولد أو الحمل الذي في بطنها فإنها على ما قال أهل العلم: إن خرج وقد تبين فيه خلق إنسانٍ فإن دمها بعد خروجه يعدّ نفاسًا، تترك فيه الصلاة والصوم، ويتجنبها زوجها حتى تطهر.

وإن خرج الجنين وهو غير مخلّقٍ فإنه لا يعتبر دم نفاسٍ، بل هو دم فسادٍ، لا يمنعها من الصلاة، ولا من الصّيام، ولا من غيرهما.

قال أهل العلم: وأقلّ زمنٍ يتبين فيه التخليق: واحدٌ وثمانون يومًا؛ لأن الجنين في بطن أمّه، كما قال عبد الله بن مسعودٍ رضي الله عنه: حدثنا رسول الله ﷺ وهو الصادق المصدوق، فقال:

«إِنَّ أَحَدَكُمْ يُجْمَعُ فِي بَطْنِ أُمِّهِ أَرْبَعِينَ يَوْمًا، ثُمَّ يَكُونُ عَلَقَةً مِثْلَ ذَلِكَ، ثُمَّ يَكُونُ مُضْغَةً مِثْلَ ذَلِكَ، ثُمَّ يُبْعَثُ إِلَيْهِ الْمَلَكُ، وَيُؤْمَرُ بِأَرْبَعِ كَلِمَاتٍ، فَيُكْتَبُ رِزْقُهُ، وَأَجَلُهُ، وَعَمَلُهُ، وَشَقِيٌّ أَوْ سَعِيدٌ» [1]،

ولا يمكن أن يخلق قبل ذلك، والغالب أن التخليق لا يتبين قبل تسعين يومًا، كما قال بعض أهل العلم.

[10] رواه البخاري، كتاب أحاديث الأنبياء، باب خلق آدم وذريته (3333)، ومسلم، كتاب القدر، باب كيفية خلق الآدمي في بطن أمه (1) (2643).