Skip to content

Mai tambaya tana cewa: Ita tunda azumi ya wajaba a kanta tana yin azumin Ramadan, amma ita ba ta rama kwanakin da ta sha su a sakamakon haila ba, sabo da rashin sanin adadin kwanakin da ta sha, yanzu tana neman a shiryar da ita izuwa abin da ya wajaba a kanta ta aikata?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Mai tambaya tana cewa: Ita tunda azumi ya wajaba a kanta tana yin azumin Ramadan, amma ita ba ta rama kwanakin da ta sha su a sakamakon haila ba, sabo da rashin sanin adadin kwanakin da ta sha, yanzu tana neman a shiryar da ita izuwa abin da ya wajaba a kanta ta aikata?

س30: سائلةٌ تقول: إنها منذ وجب عليها الصّيام وهي تصوم رمضان، ولكنها لا تقضي صيام الأيام التي تفطرها بسبب الدورة الشهرية، ولجهلها بعدد الأيام التي أفطرتها، فهي تطلب إرشادها إلى ما يجب عليها فعله الآن.

الجواب

AMSA TA 1:

Yana baƙanta mana ace irin wannan yana faruwa a tsakanin matan musulmi, domin haƙiƙa wannan barin -ina nufin: barin abin da ya ke wajaba a kanta na azumi- ko dai ya kasance sabo da jahilci, ko ya kasance saboda sakaci, duk kansu biyun masifa ne; sabo da jahilci maganinsa ilimi da tambaya,

Amma shi sakaci maganinsa shi ne tsoran Allah - mai girma da ɗaukaka, da halartoShi, da tsoron uƙubarSa, da yin gaggawa zuwa abin da zai jawo yardarSa.

Ya zama lallai a kan wannan matar ta tuba zuwa ga Allah daga abin da ta aikata kuma, ta yi istigfari, ta yi kirdadon ranekun da ta bar su gwargwadon ikonta sai ta rama su, da wannan ne za ta kuɓutar da kanta, muna fatan Allah Ya karɓi tubanta.

ﺟ30: يؤسفنا أن يقع مثل هذا بين نساء المؤمنين، فإن هذا الترك -أعني: ترك قضاء ما يجب عليها من الصّيام- إما أن يكون جهلًا، وإما أن يكون تهاونًا، وكلاهما مصيبةٌ؛ لأن الجهل دواؤه العلم والسّؤال،

وأما التهاون فإن دواءه تقوى الله عز وجل، ومراقبته، والخوف من عقابه، والمبادرة إلى ما فيه رضاه.

فعلى هذه المرأة أن تتوب إلى الله مما صنعت، وأن تستغفر، وأن تتحرى الأيام التي تركتها بقدر استطاعتها فتقضيها، وبهذا تبرأ ذمتها، ونرجو أن يقبل الله توبتها.