Skip to content

Ni mace ce cikina ya zube a wata na uku shekara guda kenan, ban yi sallah ba har sai da na yi tsarki, kuma [yanzu] an ce da ni: Ya wajaba a kanki ki yi sallar, to, yaya zan yi, ga shi ni ban san takamaimai adadin kwanakin ba?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Ni mace ce cikina ya zube a wata na uku shekara guda kenan, ban yi sallah ba har sai da na yi tsarki, kuma [yanzu] an ce da ni: Ya wajaba a kanki ki yi sallar, to, yaya zan yi, ga shi ni ban san takamaimai adadin kwanakin ba?

س29: أنا امرأةٌ أسقطت في الشهر الثالث منذ عامٍ، ولم أصلّ حتى طهرت، وقد قيل لي: كان عليك أن تصلّي. فماذا أفعل، وأنا لا أعرف عدد الأيام بالتحديد؟

الجواب

AMSA TA 1:

Sanannen abune a wajen malamai shi ne: Cewa mace idan ta yi ɓari na [cikin] wata uku, to, ba za ta yi sallah ba, sabo da idan mace ta yi ɓarin ɗan tayin da halittar sa ta mutum ta bayyana, to, jinin da zai fito mata ya zama jinin biƙi, ba za ta yi sallah a cikinsa ba.

Malamai sun ce: Zai yiwu halittar ɗan tayi ta bayyana, idan ya cika kwana tamanin da ɗaya, wannan kuwa ƙasa da wata uku kenan, idan ta tabbatar cewar ɗan tayin ya zube ne a wata uku, to, abin da ya sameta jinin cuta ne, ba za ta bar sallah ba sabo da shi.

Wannan mai tambayar lallai ne ta tuno a ranta, idan ɗan tayin ya zube ne kafin kwana tamanin, to, za ta rama sallah, idan kuma ta kasance ba ta san kwana nawa ta ɓari ba?

To, za ta ƙaddara, ta yi kirdado, sai ta rama abin da ya fi rinjaye a zatonta cewa ba ta sallace shi ba.

ﺟ29: المعروف عند أهل العلم: أن المرأة إذا أسقطت لثلاثة أشهرٍ فإنها لا تصلّي؛ لأن المرأة إذا أسقطت جنينًا قد تبين فيه خلق إنسانٍ فإن الدم الّذي يخرج منها يكون دم نفاسٍ لا تصلّي فيه.

قال العلماء: ويمكن أن يتبين خلق الجنين إذا تم له واحدٌ وثمانون يومًا، وهذه أقلّ من ثلاثة أشهرٍ، فإذا تيقنت أنه سقط الجنين لثلاثة أشهرٍ فإن الذي أصابها يكون دم فسادٍ، لا تترك الصلاة من أجله.

وهذه السائلة عليها أن تتذكر في نفسها، فإذا كان الجنين سقط قبل الثمانين يومًا فإنها تقضي الصلاة، وإذا كانت لا تدري كم تركت؟

فإنها تقدّر، وتتحرى، وتقضي على ما يغلب عليه ظنّها أنها لم تصلّه.