Skip to content

Haƙiƙa na yi aikin hajji a bara, na yi dukkan ayyukan hajjin in ban da ɗawafin Ifada da ɗawafin bankwana, in da wani uzuri na shari'a ya hana ni yin su, sai na dawo gidana a Madina, da niyyar zan dawo a wata ranar; domin in yi ɗawafin Ifada da ɗawafin bankwana, sabo da rashin sanin al'amuran Addini irin nawa na dawo ina yin komai da wanda ba maniyyaci ba ya ke yi, na aikata duk abin da ya haramta a lokacin ihrami, sai na yi tambaya game da dawowata don yin ɗawafi, sai aka ce da ni: Ba zai yiwu ba in yi ɗawafi, na riga na ɓata komai, dole sai na sake -wato: Sai na sake wani aikin hajjin- a shekara mai zuwa, tare da yanka saniya ko taguwa, shin wannan ya inganta? shin akwai wata mafitar? mecece? shin da gaske aikin hajjina ya ɓaci? shin da gaske dole sai na sakeshi? ku sanar da ni abin da ya zama wajibi a kaina, allah Ya yi muku albarka.

السؤال

TAMBAYA TA 1:

س51: لقد قمت بأداء فريضة الحجّ العام الماضي، وأديت جميع شعائر الحجّ ما عدا طواف الإفاضة وطواف الوداع، حيث منعني منهما عذرٌ شرعيٌّ، فرجعت إلى بيتي في الـمدينة على أن أعود في يومٍ من الأيام؛ لأطوف طواف الإفاضة وطواف الوداع، وبجهلٍ منّي بأمور الدّين فقد تحللت من كلّ شيءٍ، وفعلت كل شيءٍ يحرم أثناء الإحرام، وسألت عن رجوعي لأطوف، فقيل لي: لا يصحّ لك أن تطوفي، فقد أفسدتّه، وعليك الإعادة -أي: إعادة الحجّ مرةً أخرى- في العام المقبل، مع ذبح بقرةٍ أو ناقةٍ، فهل هذا صحيحٌ؟ وهل هناك حلٌّ آخر؟ وما هو؟ وهل فسد حجّي؟ وهل عليّ إعادته؟ أفيدوني عمّا يجب فعله، بارك الله فيكم.

الجواب

AMSA TA 1:

Wannan shi ma yana daga cikin bala'in da ya ke faruwa sabo da bayar da fatawa ba tare da ilimi ba, to, yanzu kai a wannan yanayin ya wajaba a kanki sai kin koma Makka, ɗawafin ifada kawai za ki yi.

Amma shi ɗawafin bankwana ba ya wajaba a kanki matuƙar haila ki ke yi a lokacin fita daga Makka, sabo da mai haila ba ya zama lallai a kanta ta yi ɗawafin bankwana;

Saboda hadisin Abdullahi ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: "An umarci mutane da su sanya ɗawafi a ɗakin Allah shi ne abu na ƙarshe (Ɗawafin bankwana), sai dai an yi sauƙi ga mace mai haila".

A wata riwayar kuma ta Abu Dawud: [Ana buƙatar] ya kasance ƙarshen lamarin su da ɗakin Ka'aba (shine) ɗawafi.

Kuma sabo da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - lokacin da a ka ba shi labarin cewa nana Safiyya ta riga, ta yi ɗawafin Ifada cewa ya yi: "Kawai ta taho kenan",

Sai wannan ya nuna cewa ɗawafin bankwana yana faɗuwa daga kan mai haila.

Amma ɗawafin Ifada babu makawa sai kin yi shi, amma tunda kika kasance kin warwara daga komai a rashin sani, to, wannan ba zai cutar da ke ba, sabo da mara sanin da ya aikata wani abu daga cikin abubuwan da aka haramta na Ihrami babu komai a kansa;

Saboda faɗinSa - maɗaukakin sarki -: {Yã Ubangijinmu! Kada Ka kãmã mu, idan mun yi mantuwa, ko kuma mun yi kuskure}. (Al-Baƙara: 286).

Sai Allah Ya ce: "Haƙiƙa na yi".

Da faɗinSa: {Babu laifi a kanku game da abin da ku ka yi kuskuren sa, sai dai abin da zukatanku suka yi gangancin sa} [Al-ahzab:5],

Dukkanin abubuwan hanin da Allah Ya hanasu ga mai harama, to, idan ya yi su bisa jahilci ko mantuwa ko tilastawa, to, babu komai a kansa, sai dai a duk lokacin da uzurinsa ya kau, to, ya wajaba a kansa ya bar abin da ya shiga aikatawa.

ﺟ51: هذا أيضًا من البلاء الّذي يحصل من الفتوى بغير علمٍ، وأنت في هذه الحال يجب عليك أن ترجعي إلى مكة، وتطوفي طواف الإفاضة فقط.

أما طواف الوداع فليس عليك طواف وداعٍ ما دمت كنت حائضًا عند الخروج من مكة، وذلك لأن الحائض لا يلزمها طواف الوداع؛ لحديث ابن عباسٍ رضي الله عنهما:

«أُمِرَ النَّاسُ أَنْ يَكُونَ آخِرُ عَهْدِهِمْ بِالْبَيْتِ، إِلَّا أَنَّهُ خُفِّفَ عَنِ الْحَائِضِ» [1]،

وفي روايةٍ لأبي داود:

«أَنْ يَكُونَ آخِرُ عَهْدِهِمْ بِالْبَيْتِ الطَّوَافُ» [2].

ولأن النبي ﷺ لـمّا أخبر أنّ صفيّة طافت طواف الإفاضة قال:

«فَلْتَنْفِرْ إِذًا» [3]،

فدلّ هذا على أن طواف الوداع يسقط عن الحائض.

[19] أخرجه البخاري، كتاب الحج، باب طواف الوداع (1755)، ومسلم، كتاب الحج، باب وجوب طواف الوداع وسقوطه عن الحائض (380) (1328).

[20] أخرجه أبو داود، كتاب المناسك، باب الوداع (2002).

[21] أخرجه البخاري، كتاب الحيض، باب المرأة تحيض بعد الإفاضة (328)، ومسلم، كتاب الحج، الباب السابق (382) (1211).

أما طواف الإفاضة فلابد لك منه، ولـما كنت تحللت من كلّ شيءٍ جاهلةً فإن هذا لا يضرّك؛ لأن الجاهل الذي يفعل شيئًا من محظورات الإحرام لا شيء عليه؛ لقوله تعالى:

﴿...رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذۡنَآ إِن نَّسِينَآ أَوۡ أَخۡطَأۡنَاۚ...﴾

[البقرة:286]،

قال الله تعالى:

«قَدْ فَعَلْتُ» [4]،

وقوله:

﴿...وَلَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ جُنَاحٞ فِيمَآ أَخۡطَأۡتُم بِهِۦ وَلَٰكِن مَّا تَعَمَّدَتۡ قُلُوبُكُمۡۚ...﴾

[الأحزاب:5]،

فجميع الـمحظورات الّتي منعها الله تعالى على المحرم إذا فعلها جاهلًا أو ناسيًا أو مكرهًا فلا شيء عليه، لكن متى زال عذره وجب عليه أن يقلع عما تلبس به.

[22] أخرجه مسلم، كتاب الإيمان، باب بيان تجاوز الله تعالى عن حديث النفس (200) (126).