Skip to content

Mace mai biƙi idan biƙinta ya fara a ranar shayarwe (takwas ga Zulhijja) kuma ta kammala rukunan hajji ban da ɗawafi da sa'ayi, saidai kuma ta lura kai-tsaye ta samu tsarki bayan kwana goma, shin za ta yi tsarki, ta yi wanka, ta yi rukunin da ya rage wanda shi ne ɗawafin hajji?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

س52: المرأة النّفساء إذا بدأ نفاسها يوم التروية، وأكملت أركان الحجّ عدا الطواف والسعي، إلا أنها لاحظت أنها طهرت مبدئيًّا بعد عشرة أيامٍ، فهل تتطهر، وتغتسل، وتؤدّي الرّكن الباقي الّذي هو طواف الحجّ؟

الجواب

AMSA TA 1:

Ba ya halatta a gareta, ta yi wanka ta yi ɗawafi har sai ta tabbatar da samun tsarki, abin da ake fahimta daga tambayar inda ta ce: (kai-tsaye / farko-farko) shi ne ba ta ga tsarki cikakke ba, ai kuwa lallai ne sai ta ga tsarki cikakke, duk lokacin da ta samu tsarki sai ta yi wanka, ta yi ɗawafi da sa'ayi.

Idan ta yi sa'ayi kafin ɗawafi, to, babu laifi, sabo da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - an tambaye shi a lokacin hajji game da wanda ya yi sa'ayi kafin ɗawafi, sai ya ce: "Babu laifi".

ﺟ52: لا يجوز لها أن تغتسل وتطوف حتى تتيقن الطّهر، والّذي يفهم من السّؤال حين قالت: (مبدئيًّا) أنها لم تر الطّهر كاملًا، فلابد أن ترى الطّهر كاملًا، فمتى طهرت اغتسلت، وأدت الطواف والسعي.

وإن سعت قبل الطواف فلا حرج؛ لأن النبي ﷺ سئل في الحجّ عمن سعى قبل أن يطوف، فقال:

«لَا حَرَجَ» [1].

[23] رواه أبو داود، كتاب المناسك، باب فيمن قدم شيئًا قبل شيء في حجه (2015).