Mafi Yawan Bincike
Tace sakamako
Katuna 116
الموضوعات
التصنيف الشرعي
Amsa: sai ka ce: shi ne gasgatawa da Amincewa da samuwarsu da siffofinsu da ikonsu da ayyukansu da abubuwan da ake umartarsu das u. da kuma cewa su halittu ne masu girma da daraja da Allah ya halicce su daga haske. Kamar yadda yake cewa: basa sabawa Allah abin day a sasu cesu, kuma suna aikata duk abin da aka umarcesu (Surah Taharim 6) kum suna da fikafikai biyu –biyu, uku-uku wasu hudu-hudu wasu fiye da haka. Kuma suna da yawan gaske kuma babu wanda yasan adadinsu sa Allah.Sannan ayi imani da cewa Allah ya dora musu wasu muhimman ayyuka. Akwai masu dauke da al’arshi akwai wadanda aka wakilta a mahaifar mace, da masu rubuta ayyukan talikai, da masu gadin bayin Allah, da masu tsaron Aljanna da masu tsaron wuta da wasunsu da kma. Wanda yafisu duka shine Jibril wanda yake kawo wahayi ga annabawa. Don haka sai muyi wani dasu a dunkule da kuma a rarabe, kamar yadda Allah ya sanar damu a cikin Alqur’ani, da kuma yadda yazoa sunnar annabinmu tsiran Allah da ainci a gareshi. Duk wanda yayi musun samuwar mala’iku to ya fadi wani abu daban da wanda Allah ya fada to ya zama kafiri don ya karyata abinda Allah da Manzon Alah suka fada
Amsa: Sai ka ce: Shi ne ka ka sakankance kuma ka shaida cewa lallai Allah Madaukakin Sarki ya saukar da Litattafai ga Annabawansa da Manzanninsa Amincin Allah ya tabbata a garesu kuma ya fadi wasu daga cikinsu a littafinsa : Kamar Suhufu Ibrahim da Attaura ga Annabi Musa da Linjila ga Annabi Isa da Zabura ga Annabi Daud da kuma Alqurani ga Mafificin Annabawa Amincin Allah a gare su.
Kuma mafificinsu shi ne Al'qur'ani wanda shi ne zancen Allah kuma wanda yayi magana da shi a Hakika kuma Lafazinsa kuma Ma'anarsa daga Allah ta ke kuma ya jiyar da Jibirilu shi kuma ya Umarce shi da isar da sakonsa ga Annabinsa Muhammad Allah Madaukaki Sarki yace: "Ruhi Amintacce ya saukar da shi"(l'shura'a:198) kuma Allah "Mu ne Lallai muka sauka maka da Al'qurani Saukarwa:(Al'Insan:23( da kuma fadinsa: "to ka basu Mafaka har yaji zancen Allah" (Attaubah6)
kuma Allah ya kiyaye Alqur’ani daga gurbatawa ko kari ko ragi.Sannan an kawwameshi a takardu da kiraza har izuwa lokacin da Allah zai karbi rayukan muminai kafin a tashi alkiyama a karshen duniya, lokacine Allah zai dauke shi zuwa gareshi baa bin da zai saura nasa
Amsa: sai kace: zuciya ta yanke da kudirin cewa annabawa mutane ne zababbu a cikin yan Adam, Allah ne ya zabe su don su isar da sakon shari’ah ga bayinsa, da za su kirasu izuwa bautar Allah shi kadai ba shiraka. Da kuma fandarewa duk wata shirka da masu yenta. Kuma uta annabta zabi ne daga Allah, ba a samunta saoda kokari ko dagewa da bin Allah ko nagarta ko karfin basira. Allah yace: Allah ne yafi sanin a wurinda yake sanya manzaicinsa’ (Anam 124)
kuma farkon Annabawa shi ne Adam, farkon Manzo kuma shi ne Nuhu, cikamakinsu, kuma shine Muhammad dan Abdullahi bakuraishe – bahaushe, Allah ya yarda dasu baki dayansu. Duk wanda yayi inkarin wani annabi to ya zama kafiri, wanda kuwa yace shi annabi ne bayan Annabi Muhammad tsira da amincin Allah a gare shi to kafiri ne, mai karyata Allah a fadinsa: Muhammad bai zamo uba ga dayan mazajenku ba, sai dais hi manzon Allha ne kuma cikamakin annabawa. Kuma Manzon Allah yana cewa ‘babu wani Annabi bayana’
Amsa: sai ka ce : shi ne a gaskata kuma a sakankance ba tare da kokwanto ba, da yin furuci da duk abin da Allah ya bayar da labarin zai faru bayan Mutuwa, tun daga Azaba ko ni’ima dake cikin kabari, da tashi daga kabari da taruwa don hisabi da hukunci har izuwa abubuwan da zasu faru a farfajiyar alkiyama na doguwar tsayuwa da kusantowar rana kwatankwacin mil daya kuma tafki da sikelin awo da raba takardun aiki da kafa sira a aman wutarJahannama da sauran abubuwan tashin hankali da zasu faru a wannan babbar Rana. Har da ‘yan Aljanna su shiga Aljanna ‘yan wuta si shiga wua kamar dai yadda yazo dalla dalla a kur’ani da hadizi. Hakanan a karkashin imani da ranar lahira akwai gasgata abinda ya tabbata na alamomin alkiyama kamar yawaitar fitina da kasha – kasha da girgizar kasa da kisfewar rana da zuwan Dujal da saukar Annabi Isa da fitowar Yajuju da Majuju da hudowar rana ta mafadarta sda makamantansu.
kuma dukkan wadan nan sun tabbata daga irin ingantattun Hadisai daga Manzon Allah tsira da aminci a gareshi ya bayar kuma aka rubutasu a manyan litattafan hadisi masu inganci.
Amsa: sai kace: kwarai kuwa, domin Allah ya fadawa mutanen fir’auna cewa: wuta ce da aka bijiro dasu gareta da safe da yamma. Sannan a ranar Alkiyama (sai ace da mala’iku ku shigar da jama’ar fir’auna mafi tsananin azaba (Gafir 46) da fadinsa ‘da kaga lokacin da Mala’iku suke karbar rayukan kafirai, suna bugun fuskokin da bayansu, (sannan ace) ku dandani azabar kuna. (Anfal 5) da fadinsa: Allah zai tabbatar da muminai abisa tabbatacciyar Magana a rayuwar duniya da ta lahira ( Ibrahim 27) hakanan wani a dogon hadisi kudsi da Barra yazo cewa: wani mai kira zai yi kira daga aljanna, kuyi masa sutura daga aljannan, kuma ku bude masa kofa zuwa aljanna sai ya jiyo iskarta da kanshinta kuma a yalwata masa fadin kabarinsa iya ganinsa.Amma kafiri kuwa sai a dawo masa da ransa izuwa jikinsa, sannan mala’iku biyu su zo su zaunar da shi sai su ce masa wanene Ubangijinka sai yace wayyo! Ban sani ba. Sai su ce menene addininka sai wayyo! Wayyo! Ban sani ba. Sai su ce da shi: Ina labarin mutumin da aka aiko muku (da Annabta) sai yace wayyo! Wayyo! Bai sani ba, sai wani mai kira yayi kira daga sama yace: qarya yake ku yi masa shinfixa ta wuta, kuma ku saka masa tufafi na wuta, sannan ku buxe masa qofar wuta sai ya jiyo zafinta da iskarta, kuma kabarinsa ya yi masa qunci har sai gavovinsa sun sava da junansu. (A wata ruwayar ya qara cewa sai a haxa shi da (Mala’ika) da baya ji ba ya magana yana xauke da wani madoki na baqin qarfe wanda da za a bugi dutse da shi da sai ya zama garin qasa. Sai ya buge shi dukan da duk abin da yake gabas da yamma sai ya ji qararsa ban da mutum da aljan). Abu dawud ya ruwaito shi. Wannan dalili ne ya sa aka umarce mu da mu dinga neman tsari daga azabar qabari a kowacce sallah
Amsa: Kace kwarai kuwa Zasu ga ga Ubangijinsu a Lahira kuma daga cikin Dalilan hakan fadinsa: "Wasu Fuskoki a wannan Rana suna cikin walwala suna Kallon Ubangijinsu" (Alkiyama:22-23)Lallai ku zaku ga Ubangijinku da kuma fadin Annabi : "Buhari da Muslim Suka rawaito shi, kuma Hadisai da yawa sun zo wadanda suke tabbatar da ganin Muminai ga Ubangijinsu kuma Sahabban Annabi duk sun hadu kan hakan da kuma wadanda suka biyo bayansu to duk wanda ya karyata da ganinsa to hakika ya karyata Allah da Manzonsa kuma ya sabawa Hanyar Muminai na Sahabai da wadanda suka zo bayansa, amma a Duniya ba zai yiwu a ganshi ba sabida fadin Annabi : "Lallai cewa ba zaku taba ganin Ubangijinku ba har sai kun Mutu" kuma Annabi Musa ya nemi hakan a Duniya kamar yadda ya zo a fadin Allah Madaukaki: "Kuma yayin da Musa ya zo don ganawa da mu kuma Ubangijinsa yayi Magana da shi ya ce Ubangiji ka nunana mun in ganka ya ce: ba zaka taba iya gani na ba" (Surat Al'a'araf: 143(
Sai ka ce ta Hanyar tabbatarwa da cewa kowanne abu yana gudana ne akan Hukuncin Allah da qaddararsa, babu abin da zai faru sai da yardarm Allah, shi ya halicci duk ayyukan bayi masu kyau da marasa kyau. Kuma ya halicci bayi a bisa alheri da karvar gaskiya, kuma ya basu hankula da za su tantance abubuwa, ya basu ikon da za su yi zavi, ya bayyana musu gaskiya ya tsoratar da su daga bin vata, ya shiryar wanda ya so da falalarsa, ya avatar da wanda ya so da Adalcin sa, shi ne mai hikima, masani, mai jin qai, ba a tambayar dalilin da ya sa ya yi wani abu, amma su (Jama’a) ana tambayarsu.
Kuma ita Kaddara mataki hudu ce su ne Kamar haka:
Mataki na fakro shi ne imani da cewa sanin Allah ya kewaye dukkan komai, Allah ya san duk abin da ya faru da wanda yake faruwa, da ma yadda abin da bai faru ba, zai kasance
Mataki na biyu: Imani da cewa Allah ya rubuta komai da komai
Mataki na uku: Imani da cewa babu abin da zai faru sai da yardar Allah.
Mataki na Hudu: Imani da cewa Allah shi ya Halittawa komai jikkuna da Ayyuka da maganganu da motsi da rashin motsi da siffofi a duniyoyin da suke sama ko qasa, kuma dalilan duk waxannan suna da yawa a Alqur’ani da hadisai
Sai ka ce ba a faxa kai tsaye a ce Allah ne yake dora mutum akan aiki ko kuma a ce yana da zabi. Duk kkan wannan kuskure ne, bayanai daga Alqur’ani da hadisi sun tabbatar da cewa mutum yana da iko da ganin dama, kuma a haqiqa shi ne yake aikata ayyukana da kansa sai dai duk wannan bai fita daga sanin Allah da ikonsa ba, kuma fadin Allah da ya nuna haka shi ne duk wanda ya ga dama zai iya daidaituwa amman dai abin da kuka ga dama ba zai faru ba sai Allah Ubangijin talikai ya so (Surat Takwir 28 – 29). Da fadinsa: wanda ya so sai ya tuna shi, amma abu abin da za su tuna sai abin da Allah ya so, shi ne ma’abocin taqwa kuma ma’abocin gafara (Muddassir 55-56)
Amsa: Ka ce: Bai Inganta ba Imani ba tare da aiki ba aa dole ayi aiki domin aiki ginshiki ne na Imani kamar yadda furta shi wani bangare ne na Rukuninsa kuma wan nan shi ne abin da Malamai suka hadu akansa cewa imani Furuci ne da kuma aiki dalin haka kuma shi ne fadin Allah: "Kuma duk wanda yaje masa yana Mumini yayi Ayyukana gari to wadan nan suna da Darajoji Madaukaka(Taha:75) sai Allah yaShardma anta Imani da kuma Aiki baki daya don shiga Aljannah.
Sai ka ce: guda biyar ne shaidawa babu macancancin bauta sai Allah kuma Muhammad manzonsa ne, da tsayar da sallah da azumin watan ramadhan, da bayar da zakkah da hajjin xakin Allah mai a gare shi yace: ‘An gina musulnci a bisa aubuwan guda biyar: shaidawa babu abin bauta da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammadu manzonsa ne, da tsyar da sallah da bayar da zakka da hajji da azmin watan Ramadan (Bukhari da muslim).
Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: 'angina Musulunci kan abubuwa guda biyar:Sai ka ce: guda biyar ne shaidawa babu macancancin bauta sai Allah kuma Muhammad manzonsa ne, da tsayar da sallah da azumin watan ramadhan, da bayar da zakkah da hajjin xakin Allah mai a gare shi yace: ‘An gina musulnci a bisa aubuwan guda biyar: shaidawa babu abin bauta da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammadu manzonsa ne, da tsyar da sallah da bayar da zakka da hajji da azmin watan Ramadan (Bukhari da muslim)
Sai ka ce: Shaidawa babu abin bauta bisa cancanta sai Allah shi ne: babu abin bauta da gaksiya sai Allah kamar yadda Allah yace: “Tuna lokacin da Ibrahim yace da babansa da mutanensa, ni dai na yi hannun riga da abin da kuke bautawa. Sai dai wanda ya halicce ni (zan bautawa) don shi ne zai shiryar da ni. Kuma sai ya sanyata ta zama wata kalma ce da za ta wanzu a bayansa, ko me yi wuwa za su dawo. (Zukhruf 28) da kuma fadinsa. “Wannan kuwa saboda Allah shi ne gaksiya, abin da suke bautawa kuma shi ne qarya, sannan Allah shi ne madaukaki mai girma (Luqmana 29)
Ma’anar shaidawa cewa Muhammad manzon Allah ne shi ne mu sakankance, mu yi furuci cewa shi bawan Allah ne kuma manzonsa, sannan shi bawa ne ba a bauta masa shi Annabi ne ba a qaryata shi, ana yi masa biyayya ne cikin abin da yai umarni, ana gasgata shi cikin abin da ya bada labari, ana nisantar abin da yai hani ga barinsa kuma ya tsawatar, kuma ba a bautawa Allah sai da abin da ya shar’anta
Kuma haqqin manzon Allah akan al’ummarsa shi ne su mutuntashi, su girmama shi, sannan soyayya ita ce biyayya ta kai tsaye a kowanne lokaci gwagwadon iyawa. Allah maxakakin sarki ya ce: “ka ce (da su) in ai kun kasance kuna san Allah, to ku yi min biyayya, sai Allah ya so ku ya kuma gafarta muku zunubanku (Ali Imran 31).
Amsa: sai ka ce: Kalmar shahada ba kalma ba ce da za a faxa kawai ba tare da qudircewa ba, ture da dagewa wajen aiki da abin da ta qunsa da nisantar abin da ya sava mata. Har ma tana da wasu sharaxai guda bakwai da malamai suka fito da su daga cikin hujjojina shari’ah, sannan suka rubuta su tare da dalilansu daga qur’ani da hadisi; su ne.
1.sanin ma’anar abin da take korewa da wanda take tabbatarwa wato sanin cewa Allah shi kaxai ne babu abokin tarayya tare da shi, kuma shi ya cancanta a bauta masa da kuma abin da (Kalmar) take nunawa na koruwar duk wani abin bauta ba Allah ba tare da sanin abin da take hukuntawa da abubuwan da suke xanfare da ita da masu warwareta, da suke kore jahilci. Allah yace: “ka sani babu abin bauta a bisa cancanta sai Allah (Muhammad 19) da faxinsa “sai wanda suka shaida da gaskiya kuma suna sane (da abin da suka shaida) (zukhruf 86) kuma manzon Allah tisra da amincin Allah a gare shi yace “wanda ya mutu yana sane da cewa babu abin bauta sai Allah to zai shiga aljanna? (Muslim ne ya ruwaito shi.
2.Sakankancewa: shi ne qudircewa ta gaske wadda take kore kokwanto da kaikawo, wato tabbatacce a zuciya. Allah yana cewa “kaxai muminai su ne waxanda suka yi imani da Allah da manzonsa sannan a su yi kokwanto ba, kuma suka yi jihadi da dukiyoyinsu da rayukansu cikin tafarkin Allah. Waxannan sune masu gaskiya (Hujrat 25). Kuma manzon Allah yace: “Wanda yace na shaida cewa babu abin bauta da gaksiya sai Allah kuma ni manzon Allah ne, to babu wani bawa da zai gamu da Allah da su (waxannan kalmomin) kuma baya kokwanto face ya shiga aljannan. (Muslim ne ya ruwaito).
3.Tsarkake niyya da take kore shirka, a hanyar rairaye ibada da tsarkaketa daga dukkan xauxar shirka ko riya Allah mai girma yana cewa: “Ku ji da kyau! Tsarkakakken addini na Allah ne” (Zumar 3) da faxinsa “Kuma ba a umarce su ba sai don su bautawa Allah suna masu tsarkake zuciya gare shi da addini” kuma manzon Allah tsira da aminci a gare shi yace: “Mafi arzuta da cetona a cikin mutane ranar alqiyama shi ne wanda yace: “Babu abin bauta sai Allah yana mai tsarkake niyya a ziyarsa da ransa” (Bukahri ne ya ruwaito).
4.Soyayya ga wannan kalma da abin da take nufi, da farin ciki da hakan da qaunar a halitta da jivintar al’amuranshi da qin abin da yake warwareta, da barranta daga kafirai. Allah yace “daga cikin mutane akwai wanda yake riqon wasun Allah kishiyoyi, yana son su kamar yadda yake son Allah, amma waxanda suka yi imani sun fi son Allah. (Baqarah 165) manzon Allah tsira da amincin allah a gare shi yace “abu uku, duk wanda suka kasance tare da shi to ya sami xanxanon imani. Ya zama ya fi son Allah da manzonsa fiye da waninsu, kuma ya qaunaci mutum ya zama baya qaunarsa sai don Allah, sannan ya qyamaci cikin kafirci kamar yadda yake qyamar a jefa shi a wuta (Muslim ne ya rawaito shi)
5. (5). Gaskiya wadda ta ke kore qarya, tare da dacewar zuciya da gavovi da harshen da ya yi furuci da kalmar tauhidi, sai ya zama gavovi sun gasgata abin da zuciya ta faxa sai su dinga yin ayyuka na zahiri da na voye. Allah mai girma yace “lallai Allah zai bayyana waxanda suka yi gaskiya, kuma lallai zai bayyana wanxa suka yi qarya, (Ankabuta 3) Allah yana cewa “wanda ya zo da gaskiya kuma ya wanda ya gaskata da ita, to waxannan sune masu taqwa (zumar 33) kuma manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi yace “wanda ya mutu yana shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta, kuma Muhammad Manzon Allah ne, yana mai gasgatawa a zuciyarsa, to zai shiga aljanna. (Ahmad ne ya ruwaito).
- Jawuwa izuwa qasqantar da kai ga Allah, da xayanta shi da ibadada da zuwa da haqoqin ibada da suka shafi umarni da nisantar abubuwan hani cikin tsarkake niyya da kwaxayi da kyakkyawan fata da tsoron Allah mai girma, wanda yake cewa kuma ku kama zuwa ubangijinku kuma ku miqa wuya gare shi. (Zumar 54). Allah ya kuma cewa “duk wanda ya miqa kansa izuwa ga Allah, alhali yana mai kyautatawa to babu shakka yayi ruqo da igiya mai qwari. (Luqman 22)
7. Karva wanda yake kore juyarwa. Wato karvar kalma da zuciya da kuma duk abin da take nufi, amma kada ya qi karvarta daga wanda ya kira shi izuwa gareta, kawai saboda baya cikin mutanensa ko saboda girman kai. Allah mai girma yace “su sun kasance idan aka ce da su babu abin bauta bisa cantnata sai Allah sai su yi girman kai” (Saffat 35) mai yin wannan ba musulmi ba ne
Amsa: Sai kace: shi ne muhamamd xan Abdullahi xan Abdul muxxalib Xan hashim xan Abdu Manaf, wanda Allah ya zava daga quraishawa, su kuma sune zavavu a cikin zuriyar Annabi Isma’il Xan Ibrahim amincin Allah a garesu. Kuma Allah ya aiko shi ne, zuwa aljanu da mutane, ya saukar masa da littafi da hikima, ya sanya shi mafi alherin Annabawa kuma fiyayyensu aminci da tsiran Allah a gare su
Amsa: A. sai ka ce farkon abin da Allah ya fara wajabta wa shine imani da shi da kafircewa xagutu (duk abin da ya xauke hankali ga barin Allah) kamar yadda Allah mai girma ya ce “haqiqa mun aiko manzon ga kowacce al’umma (yana ce musu) ku bautawa Allah, ku nisanci xagutu daga cikinsu akwai waxanda Allah ya shiryar akwai kuma wanda vata ta tabbata a are shi. Ku yi tafiya a bayan qasa don ku ga yadda qarshen maqaryata ya zama (nahl 36). Xagutu shi ne abin da bawa zai qetare iyaka saboda shi ko bauta masa yake ko goyon baya, ko biyayya gare shi.
Amsa: Sai ka ce Allah ya bayyana wannan dalla-dalla, cewa ya halicci halitta, mutane da aljanu don su bauta masa shi kaxai ba tare da shirka ba, da yi masa biyayya ta hanyar kwatanta aikata abin a yai umarni da shi da gujewa abin da yai hani da shi. Allah ya ce “Ban halicci aljanu da mutane ba sai don su bauta min (Zariyat 56) Allah yace “Ku bautawa Allah kada ku yi shirka da his da komai. (Nisa’I 36).