Skip to content

idan aka ce da kai: yaya imani da Annabawa da Manzannin yake?

السؤال

Tambaya: idan aka ce da kai: yaya imani da Annabawa da Manzannin yake?

الجواب

Amsa: sai kace: zuciya ta yanke da kudirin cewa annabawa mutane ne zababbu a cikin yan Adam, Allah ne ya zabe su don su isar da sakon shari’ah ga bayinsa, da za su kirasu izuwa bautar Allah shi kadai ba shiraka. Da kuma fandarewa duk wata shirka da masu yenta. Kuma uta annabta zabi ne daga Allah, ba a samunta saoda kokari ko dagewa da bin Allah ko nagarta ko karfin basira. Allah yace: Allah ne yafi sanin a wurinda yake sanya manzaicinsa’ (Anam 124)

kuma farkon Annabawa shi ne Adam, farkon Manzo kuma shi ne Nuhu, cikamakinsu, kuma shine Muhammad dan Abdullahi bakuraishe – bahaushe, Allah ya yarda dasu baki dayansu. Duk wanda yayi inkarin wani annabi to ya zama kafiri, wanda kuwa yace shi annabi ne bayan Annabi Muhammad tsira da amincin Allah a gare shi to kafiri ne, mai karyata Allah a fadinsa: Muhammad bai zamo uba ga dayan mazajenku ba, sai dais hi manzon Allha ne kuma cikamakin annabawa. Kuma Manzon Allah yana cewa ‘babu wani Annabi bayana’