Idan aka ce da kai waxannan sharuxan Kalmar shahada.
السؤال
Tambaya: Idan aka ce da kai waxannan sharuxan Kalmar shahada.
الجواب
Amsa: sai ka ce: Kalmar shahada ba kalma ba ce da za a faxa kawai ba tare da qudircewa ba, ture da dagewa wajen aiki da abin da ta qunsa da nisantar abin da ya sava mata. Har ma tana da wasu sharaxai guda bakwai da malamai suka fito da su daga cikin hujjojina shari’ah, sannan suka rubuta su tare da dalilansu daga qur’ani da hadisi; su ne.
1.sanin ma’anar abin da take korewa da wanda take tabbatarwa wato sanin cewa Allah shi kaxai ne babu abokin tarayya tare da shi, kuma shi ya cancanta a bauta masa da kuma abin da (Kalmar) take nunawa na koruwar duk wani abin bauta ba Allah ba tare da sanin abin da take hukuntawa da abubuwan da suke xanfare da ita da masu warwareta, da suke kore jahilci. Allah yace: “ka sani babu abin bauta a bisa cancanta sai Allah (Muhammad 19) da faxinsa “sai wanda suka shaida da gaskiya kuma suna sane (da abin da suka shaida) (zukhruf 86) kuma manzon Allah tisra da amincin Allah a gare shi yace “wanda ya mutu yana sane da cewa babu abin bauta sai Allah to zai shiga aljanna? (Muslim ne ya ruwaito shi.
2.Sakankancewa: shi ne qudircewa ta gaske wadda take kore kokwanto da kaikawo, wato tabbatacce a zuciya. Allah yana cewa “kaxai muminai su ne waxanda suka yi imani da Allah da manzonsa sannan a su yi kokwanto ba, kuma suka yi jihadi da dukiyoyinsu da rayukansu cikin tafarkin Allah. Waxannan sune masu gaskiya (Hujrat 25). Kuma manzon Allah yace: “Wanda yace na shaida cewa babu abin bauta da gaksiya sai Allah kuma ni manzon Allah ne, to babu wani bawa da zai gamu da Allah da su (waxannan kalmomin) kuma baya kokwanto face ya shiga aljannan. (Muslim ne ya ruwaito).
3.Tsarkake niyya da take kore shirka, a hanyar rairaye ibada da tsarkaketa daga dukkan xauxar shirka ko riya Allah mai girma yana cewa: “Ku ji da kyau! Tsarkakakken addini na Allah ne” (Zumar 3) da faxinsa “Kuma ba a umarce su ba sai don su bautawa Allah suna masu tsarkake zuciya gare shi da addini” kuma manzon Allah tsira da aminci a gare shi yace: “Mafi arzuta da cetona a cikin mutane ranar alqiyama shi ne wanda yace: “Babu abin bauta sai Allah yana mai tsarkake niyya a ziyarsa da ransa” (Bukahri ne ya ruwaito).
4.Soyayya ga wannan kalma da abin da take nufi, da farin ciki da hakan da qaunar a halitta da jivintar al’amuranshi da qin abin da yake warwareta, da barranta daga kafirai. Allah yace “daga cikin mutane akwai wanda yake riqon wasun Allah kishiyoyi, yana son su kamar yadda yake son Allah, amma waxanda suka yi imani sun fi son Allah. (Baqarah 165) manzon Allah tsira da amincin allah a gare shi yace “abu uku, duk wanda suka kasance tare da shi to ya sami xanxanon imani. Ya zama ya fi son Allah da manzonsa fiye da waninsu, kuma ya qaunaci mutum ya zama baya qaunarsa sai don Allah, sannan ya qyamaci cikin kafirci kamar yadda yake qyamar a jefa shi a wuta (Muslim ne ya rawaito shi)
5. (5). Gaskiya wadda ta ke kore qarya, tare da dacewar zuciya da gavovi da harshen da ya yi furuci da kalmar tauhidi, sai ya zama gavovi sun gasgata abin da zuciya ta faxa sai su dinga yin ayyuka na zahiri da na voye. Allah mai girma yace “lallai Allah zai bayyana waxanda suka yi gaskiya, kuma lallai zai bayyana wanxa suka yi qarya, (Ankabuta 3) Allah yana cewa “wanda ya zo da gaskiya kuma ya wanda ya gaskata da ita, to waxannan sune masu taqwa (zumar 33) kuma manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi yace “wanda ya mutu yana shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta, kuma Muhammad Manzon Allah ne, yana mai gasgatawa a zuciyarsa, to zai shiga aljanna. (Ahmad ne ya ruwaito).
- Jawuwa izuwa qasqantar da kai ga Allah, da xayanta shi da ibadada da zuwa da haqoqin ibada da suka shafi umarni da nisantar abubuwan hani cikin tsarkake niyya da kwaxayi da kyakkyawan fata da tsoron Allah mai girma, wanda yake cewa kuma ku kama zuwa ubangijinku kuma ku miqa wuya gare shi. (Zumar 54). Allah ya kuma cewa “duk wanda ya miqa kansa izuwa ga Allah, alhali yana mai kyautatawa to babu shakka yayi ruqo da igiya mai qwari. (Luqman 22)
7. Karva wanda yake kore juyarwa. Wato karvar kalma da zuciya da kuma duk abin da take nufi, amma kada ya qi karvarta daga wanda ya kira shi izuwa gareta, kawai saboda baya cikin mutanensa ko saboda girman kai. Allah mai girma yace “su sun kasance idan aka ce da su babu abin bauta bisa cantnata sai Allah sai su yi girman kai” (Saffat 35) mai yin wannan ba musulmi ba ne