Skip to content

Idan aka ce da kai wane abu ne farkon abin da Allah ya wajabta akan bayinsa?

السؤال

Tambaya: Idan aka ce da kai wane abu ne farkon abin da Allah ya wajabta akan bayinsa?

الجواب

Amsa: A. sai ka ce farkon abin da Allah ya fara wajabta wa shine imani da shi da kafircewa xagutu (duk abin da ya xauke hankali ga barin Allah) kamar yadda Allah mai girma ya ce “haqiqa mun aiko manzon ga kowacce al’umma (yana ce musu) ku bautawa Allah, ku nisanci xagutu daga cikinsu akwai waxanda Allah ya shiryar akwai kuma wanda vata ta tabbata a are shi. Ku yi tafiya a bayan qasa don ku ga yadda qarshen maqaryata ya zama (nahl 36). Xagutu shi ne abin da bawa zai qetare iyaka saboda shi ko bauta masa yake ko goyon baya, ko biyayya gare shi.