Skip to content

Idan aka ce da kai shin mutum xora shi ake yi akan ayyukansa ko yana da zabi?

السؤال

Idan aka ce da kai shin mutum xora shi ake yi akan ayyukansa ko yana da zabi?

الجواب

Sai ka ce ba a faxa kai tsaye a ce Allah ne yake dora mutum akan aiki ko kuma a ce yana da zabi. Duk kkan wannan kuskure ne, bayanai daga Alqur’ani da hadisi sun tabbatar da cewa mutum yana da iko da ganin dama, kuma a haqiqa shi ne yake aikata ayyukana da kansa sai dai duk wannan bai fita daga sanin Allah da ikonsa ba, kuma fadin Allah da ya nuna haka shi ne duk wanda ya ga dama zai iya daidaituwa amman dai abin da kuka ga dama ba zai faru ba sai Allah Ubangijin talikai ya so (Surat Takwir 28 – 29). Da fadinsa: wanda ya so sai ya tuna shi, amma abu abin da za su tuna sai abin da Allah ya so, shi ne ma’abocin taqwa kuma ma’abocin gafara (Muddassir 55-56)