Idan aka ce dakai menene shidawa babu abin bauta da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammadu manzonsa ne?
السؤال
Tambaya: Idan aka ce dakai menene shidawa babu abin bauta da cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammadu manzonsa ne?
الجواب
Sai ka ce: Shaidawa babu abin bauta bisa cancanta sai Allah shi ne: babu abin bauta da gaksiya sai Allah kamar yadda Allah yace: “Tuna lokacin da Ibrahim yace da babansa da mutanensa, ni dai na yi hannun riga da abin da kuke bautawa. Sai dai wanda ya halicce ni (zan bautawa) don shi ne zai shiryar da ni. Kuma sai ya sanyata ta zama wata kalma ce da za ta wanzu a bayansa, ko me yi wuwa za su dawo. (Zukhruf 28) da kuma fadinsa. “Wannan kuwa saboda Allah shi ne gaksiya, abin da suke bautawa kuma shi ne qarya, sannan Allah shi ne madaukaki mai girma (Luqmana 29)
Ma’anar shaidawa cewa Muhammad manzon Allah ne shi ne mu sakankance, mu yi furuci cewa shi bawan Allah ne kuma manzonsa, sannan shi bawa ne ba a bauta masa shi Annabi ne ba a qaryata shi, ana yi masa biyayya ne cikin abin da yai umarni, ana gasgata shi cikin abin da ya bada labari, ana nisantar abin da yai hani ga barinsa kuma ya tsawatar, kuma ba a bautawa Allah sai da abin da ya shar’anta
Kuma haqqin manzon Allah akan al’ummarsa shi ne su mutuntashi, su girmama shi, sannan soyayya ita ce biyayya ta kai tsaye a kowanne lokaci gwagwadon iyawa. Allah maxakakin sarki ya ce: “ka ce (da su) in ai kun kasance kuna san Allah, to ku yi min biyayya, sai Allah ya so ku ya kuma gafarta muku zunubanku (Ali Imran 31).