Skip to content

Tambaya . Idan aka tambaye ka shin muminai za su ga Allah ranar lahira?

السؤال

Tambaya . Idan aka tambaye ka shin muminai za su ga Allah ranar lahira?

الجواب

Amsa: Kace kwarai kuwa Zasu ga ga Ubangijinsu a Lahira kuma daga cikin Dalilan hakan fadinsa: "Wasu Fuskoki a wannan Rana suna cikin walwala suna Kallon Ubangijinsu" (Alkiyama:22-23)Lallai ku zaku ga Ubangijinku da kuma fadin Annabi : "Buhari da Muslim Suka rawaito shi, kuma Hadisai da yawa sun zo wadanda suke tabbatar da ganin Muminai ga Ubangijinsu kuma Sahabban Annabi duk sun hadu kan hakan da kuma wadanda suka biyo bayansu to duk wanda ya karyata da ganinsa to hakika ya karyata Allah da Manzonsa kuma ya sabawa Hanyar Muminai na Sahabai da wadanda suka zo bayansa, amma a Duniya ba zai yiwu a ganshi ba sabida fadin Annabi : "Lallai cewa ba zaku taba ganin Ubangijinku ba har sai kun Mutu" kuma Annabi Musa ya nemi hakan a Duniya kamar yadda ya zo a fadin Allah Madaukaki: "Kuma yayin da Musa ya zo don ganawa da mu kuma Ubangijinsa yayi Magana da shi ya ce Ubangiji ka nunana mun in ganka ya ce: ba zaka taba iya gani na ba" (Surat Al'a'araf: 143(