Mafi Yawan Bincike
Tace sakamako
Katuna 116
الموضوعات
التصنيف الشرعي
Amsa: Sai ka ce: Addu’a tana daga cikin manyana ibadu, kamar yadda Allah yace: “kuma ubangijinku yace: ku roqe ni zan amsa muku, lallai waxanda suke girman kai da barin bauta ta, to za su shiga jahannama sun a qasqantattu (Gafir 60) a cikin hadisi manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi yace addu’a itace ibada (tirmidhi ne ya ruwaitoshi. Kuma saboda muhimmancinta da girmanta a addini akwai ayoyi fiye da xari uku da suka zo a alqur’ani akanta. Ita addu’a nau’I biyu ce: addu’a ta ibada da addu’a ta roqo, kuma kowacce daga ciki tana Damfare da ‘yar uwarta
Addu’ar Ibada itace: bin Hanya izuwa ga Allah mai girma don neman afkuwar wani abin da ake nema ko ije wani abin baqin ciki ko yaye cuta ta hanyar tsarkake ibada gare shi, shi kaxai. Allah mai girma yace: da kuma zun nun lokaci da ya tafi yana mai fushi, har ya yi zaton ba za mu yi ikon mu akansa ba, sai ya yi kira a cikin duffai ya ce babu abin bauta sai kai, tsarki ya tabbata a gareka, lallai ni ina cikin azzalumai, sai muka amsa masa, muka tserar da shi daga baqin ciki, kuma kamar haka muke tseratar da muminai. (Anbiya 87 -88)
Addu’ar roqo: ita ce roqon abin da zai amfani mai roqon na daga jawo wani amfani ko yaye wata cuta. Allah mai girma yace: ya ubangijinmu lallai mu mun yi imani, ka gafarta mana zunubanmu kuma ka kiyaye mu Azabar wuta (Ali Imran 16).
Addu’a da kowanne irin nau’I aka yi ta, ita ce tsantsar ibada, kuma tafi kowacce ibada ibada sauqin yi, da kuma girma matsayi ta amfani, ita ce hanya mafi qarfi wajen tare abin qi da samun abin nema da yardarm Allah.
Amsa: Sai ka ce Allah ba ya karvar aiki har sai ya cika sharaxai biyu, na farko aikin ya zama don Allah a ka yi shi, don Allah yace ba a umarce su ba sai don su bautawa Allah suna masu tsarkake niyya da addini a gare shi, kuma masu tsarkake niyya da addini a gare shi, kuma masu karkacewa vata. (Bayyinah 5) da faxina Maxaukakain Sarki “Duk wanda yake fatan ya gamu da Allah (lafiya) to sai ya aikata aiki mai kyau kuma kada ya haxa kowa da Allah a ibada (Kahfi 110).
Sharadi na biyu shi ne lallai aikin ya dace da shari’ar da manzon Allah tsira da amincin Allah ya zo da ita. Kuma dalilin haka shine faixn Allah mai girma ka ce (musu) idan dai kuna son Allah to ki yi biyayya a gare ni, sai Allah ya so ku. (Ali Imran 31).Da kuma faxin manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi “duk wanda ya aikata aikin da babu umarnin mu a cikinsa to za a juyar masa da shi” (Muslim ne ya rawaito shi) don haka idan aiki ai dace da shiryarwar manzon Allah tsira da amincin a gare shi ba to ba za a karva ba ko da kuwa mai yinsa ya tsarkake niyyarsa.
Amsa: Sai ka ce a’a, dole ne kyawun niyya wato ikhlasi da aiki su dace da shari’ar manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi, hujjar haka itace faxin Allah “Duk wanda yake fatan ya gamu da Allah (lafiya) to sai ya aikata aiki mai kyau kuma kada ya haxa kowa da Allah a ibada (Kahfi 110) Allah ya sharxanta a cikin wannan ayar cewa ba za a karvi aiki a sai da kyakykyawar niyya, da kuma dacewarsa da shari’ar manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi
Amsa: sai ka ce: nau’I uku ne: 1). Tauhidin rububiyya: shi ne qudurcewa da gakse cewa Allah ne mai halitta mai arzutawa mai jujjuya al’amuran talikai baki xaya babu abokin tarayya a tare da shi, ba shi da mataimaki. Wato wannan shi ne kaxaita Allah a cikin ayyukansa. Allah Madaukakin Sarki, yace: “Shin akwai wani mai halitta da ba Allah ba wanda yake arzutaku daga sama da qasa babu abin bauta sai shi, to ta yaya ake juyar da ku” (fadir 3). Kuma Allah ya ce Allah shi ne mai Arzutawa, mai ikon yi mai matabbacin qarfi (Zariyat 58) kuma Allah ya ce yana juya ikon yi al’amari daga sama zuwa qasa (Sajadah 5) haka nan Allah ya ce: “Ku ji da kyau, da halitta da umarni duk na Allah ne, albarkatun Allah ubangijin talikai sun halitta’ (a’araf 54)
Na biyu: Tauhidin sunaye da siffofi shine qudurce wa cewa Allah yana da sunaye maus tsarki da siffofi cikakku tabbatattu a Alqur’ani da hadisi ba tare da kwatantawa ko misaltawa ko canjawa ko kyalewa ba kuma babu waqni au kamar shi.allah malukakin sarki yana cewababu wani kamar allah kuma shi mai jine mai mai ganine(shura’11)kuma alllah mai girma yace allah yan suna ye masu kyau ko roke shi dasu,
Na Uku: tauhidin kuluhiyy’shine dayanta Allah da ibada shi kadai da shi da abokai tarayya a wanin shi ne dayanta Allah ta hanyar ayyukan bayi na bauta allah mai suna masu tsar kake niyya a addini kuma masu karka cewa varna (bayyinah 5)kuma Allah y ace bamu aiko wani annabi baya gabaninka face muna yin wahayi gareshi cewa babu abinda bauta sai ni (don haka)ku bauta min (Anbiya 25)
Amsa: to kace wannan shi ne Shirka Allah Madaukakin Sarki ya ce: " "Tabbas wadanda suka ce Allah shi Almasihu Dan Maryam kuma Almasihu ya ce da su:ya ku Bani Isra'i'la ku bautawa Allah Ubangijina kuma Ubangijinku kuma cewa Lallai duk wanda yayi Masa Shirka to hakika Allah ya haramta masa shiga Aljanna kuma Makomarsa Wuta kuma Azzalumai basu da Mataimaka"(Ma'ida72) da kuma Fadinsa: "Lallai Allah baya gafartawa idan akai masa Shirka kuma yana gafarta abinda yake koma bayanta ga wanda ya so" (Alnisaa"48) to kasancewarsa Madaukakin Sarki baya gafarta shi to wannan Dalili nena girman Zunubin, kuma hakan yana bayyane cikin fadinsa tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi yayin da aka tambaye shi wane zunubi ne yafi girma sai ya ce: "Kasanya kishiya ga Allah alhalin shi ya halicce ka" Buhari da Muslim suka rawaito shi
Shirka ita ce a sanya wani yazama dai dai da Allah ko Malaika ne ko Manzo ko waliyi ko makamantansu. Ta yadda mutum zai qudurce wani abu na siffofin Ubangiji ko wani abin da Allah qevan ce shi da shi kamar halitta ko mulki ko sarrafa ko kuma ya dinga neman kusanta izuwa gareshi (abin taraya) sai ya dinga kiransa (da neman buqata) ko qaunar wani abu awajensa ko tsoronsa ko dogaro da shi ya dinga kwaxayi awajansa banda allah ko a wajensa da wajen Allah. sai ya sarrafar da wani ibada zuwa gareshi ko da dukiya ko da jiki a fili ko a Boye
Amsa: Kace kashi biyu ce:
1.Shirka babba: Ita ce juyar da wani nau’I na ibada zuwa ga wanin Allah, kamar dogaro ga wanin Allah, ko neman taimako daga matattu, ko yin yanka don wanin Allah, ko bakance ga wanin Allah, ko sujjada da neman agaji daga wanin Allah a abin da babu mami iya yinsa sai Allah, kamar neman agaji daga wanda ba ya nan ko matacce babu wanda zai yi wannan jahilcin sai wanda ya qudurce cewa za su iya amsa masa addu’arsa, kuma za su iya aikata abin da babu wanda zai iya sai Allah. To wannan ya xorawa abin halitta siffofin ubangiji, don haka sai ya qasqantar da kai gare shi,kuma ya wulaqanta gare shi irin wulaqantar bauta, ya zama yana dogaro akansa, yana neman agajinsa da kiransa yana roqonsa abin da wani halitta da zai iya yinsa. Wannan ya isa abin mamamki a ce wai a nemi agaji da gajiyayye, wanda ba zai iya cutar da kansa ko ya amfanar da shi da komai ba, bai mallaki mutuwa ko rayuwa ko tashi ba, wanda ba zai iya hana cuta ta same shi ba yaya zai iya hana tag a waninsa, misalin wannan shi ne kamar wanda ruwa ya ciwo ne ya dinga neman taimako daga wanda shima ruwan ya ciwo shi, Allah sarki! Amma ta yaya basirar wasu take shafewa, hankulansu su tafi, har su dinga aikata irin wannan shirka da ta savawa sharia, ta savawa hankali ta ci karo da abin da shi ne haqiqa.
2 Shirka qarama: itace kamar ‘yar qaramar riya. Manzon Allah tsira da amincin Allah a gare shi yace mafi girman abin da nake jiye muku tsoronsa shine qaramar shirka. Da aka tambaye shi sai yace ita ce riya (Muslim ne ya ruwaito shi). Hakanan kamar rantsuwa da wanin Allah. Kamar yadda Manzon Allah tara da amincin Allah yace duk wanda ya rantse a wanin Allah to ya kafirta ko yayi shirka Tirmizi ne ya rawaito).
Amsa: Kace kashi biyu ne>
1.Karamin kafirci: shi ne wanda dalilai na shari`ah suka ambace shi da suna kafirci, amma ba babban ba, kuma ana kiran sa da kafircewa ni`ima ko kuma karamin kafirci kamar yakar musulmi, da korewa kai nasaba, da kukan mutuwa, da kwatankwacin haka daga dabi`u na jahiliyya. Manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: (zagin musulmi fasikanci ne yakar sa kuma kafirci ne) Bukhari ne ya rawaito. Kuma manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: ( mutm biyu cikin mutane akwai kafirci tare da su: masu suka cikin nasaba, da masu koke-koken mutuwa). Muslim ne ya rawaito. Wadannan ayyuka basa fitar da mutum daga addini saidai su suna cikin manyan kaba`irai, muna neman tsari daga Allah. i
2.Karamin kafirci: shi ne wanda dalilai na shari`ah suka ambace shi da suna kafirci, amma ba babban ba, kuma ana kiran sa da kafircewa ni`ima ko kuma karamin kafirci kamar yakar musulmi, da korewa kai nasaba, da kukan mutuwa, da kwatankwacin haka daga dabi`u na jahiliyya. Manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: (zagin musulmi fasikanci ne yakar sa kuma kafirci ne) Bukhari ne ya rawaito. Kuma manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: ( mutm biyu cikin mutane akwai kafirci tare da su: masu suka cikin nasaba, da masu koke-koken mutuwa). Muslim ne ya rawaito. Wadannan ayyuka basa fitar da mutum daga addini saidai su suna cikin manyan kaba`irai, muna neman tsari daga Allah. i
Amsa : to ka ce : kala biyu ne: Babban munafurci, da karamin munafurci.
Amma shi babban munafirci : shi ne bayyanar da imani da kuma boye kafirci , wannan shi ne mafi girman alamomin sa yin gaba da addinin musulunci da nuna kiyayya ga cin nasarar sa da gaba da ahalin sa musulmai, da kuma tashi tsaye don yakar su da bata musu addinin su
Shi kuma karamin Munafirci : Shi ne yin kamanceceniya da ayyukan munafikai ba tare da boye kafirci a cikin zuciyar sa ba , kamar wanda idan zai yi Magana zai yi karya, idan kuma ya yi alkawari sai ya saba, idan kuma aka amince da shi sai ya yi ha`inci ; Manzon Allah mai tsira da aminci ya ce : (Alamar munafiki guda uku ce : Idan zai yi Magana sai ya yi karaya , kuma idan aka amince masa sai ya yi ha`inci , idan kuma yayi alkawari sai ya saba ). Bukhari ne ya rawaito shi.
Sai ka ce : Mai warwarewa shi ne mai lalatawa kuma mai batawa , duk lokacin da ya hau kan wani abu zai lalata shi kuma zai bata shi , kamar abubuwan da suke warware alwala wadanda daga aikata su alwalar sa ta lalace, kuma dole ne ya sake maimaita ta , kwatankwacin su ne irin abubuwan da suke warware musulunci wadanda idan bawa ya aikata su to musuluncin sa ya baci ya lalace, mai aikata su kuma ya fice daga kwaryar musulunci zuwa kafirci , kuma hakika malamai sun ambaci nau`ika da yawa a cikin babuka na ridda da hukuncin mai yin ridda daga abubuwan da za su iya fitar da musulmi daga addinin sa kuma jinin sa da dukiyar sa su halasta, kuma mafi hadarin su mafi girmansu da mafi yawan wanda suka fi faruwa, da wanda malamai suka hadu akan su; su ne masu warwarewa guda goma : Na farkon su : Yin shirka a cikin bautawa Allah madaukaki, Allah madaukaki ya ce: Lallai ne Allah baya gafarta ayi shirka da shi, kuma yana gafarta abinda ya ke bayan wannan, (an-nisa`I : 116). Kuma Allah madaukakin sarki ya ce: Lallai ne shi wanda ya yi shirka da Allah to tabbas Allah ya haramta masa aljanna, kuma makomar sa wutam kuma babu wasu mataimaka ga azzalumai. (al-ma`ida: 72.). yana daga abinda ke warware musulunci shi ne kiran wanin Allah, da neman agaji da kuma neman tsarin su, da yin bakance da yin yanka a garesu kamar wanda zai yiwa aljani yanka ko ga wani kabari, ko ga wani waliyyi rayayye ne ko matacce domin neman janyo wani alheri ko tunkude wata cutuwa kamar yanda jahilai wadanda aka yaudare su da karyace-karyace da shubuhohin shaidanu batattu suke aikatawa.
Na biyu : Wanda ya sanya wani tsani tsakanin sa da tsakanin Allah yana rokar su, yana kuma rokon su ceto, yana kuma dogaro da su cikin neman biyan bukatun sa da abubuwan da yake so na duniya da lahira, to hakika ya kafirta da ijima`in malamai. Allah madaukaki ya ce: Kuma ka ce: kadai ni ina kiran ubangiji na kuma ba na hada shi da kowa a bauta. ( Al-jinn: 20)
Na uku : Duk wanda bai kafurtar da mushirikai ba , ko ya yi kokwanto a cikin kafircin su, ko yake ganin ingancin hanyar da suke tafiya akanta, to ya kafurta, Allah madauakaki ya ce: Kuma yahudawa suka ce: Uzairu dan Allah ne, kuma nasaara suka ce masihu dan Allah ne, wancan zancen su ne da bakunan su, suna kama da maganar wadanda suka kafirta gabanin su, Allah ya la`ance su , ta yaya aka karkatar da su. (Suat Attauba: 30). Saboda yadda da kafirci shima kafirci ne, kuma addini baya ingantuwa sai da kafircewa dagutu ta hanyar kudurce bacin duk addinin da ba na musulunci ba da yin gaba da shi, da kaurace masa da kuma kauracewa ahalinsa, da yakar su gwargwadon iko.
Na hudu : Duk wanda ya kudurce cewa wanin shiryarwar annabi mai tsira da aminci ta fi shiryarwar sa cikar kamala, ko kuma cewar Hukumcin wanin sa ya fi nasa hukumcin kyautatuwa, kamar wanda ya ke fifita hukumcin dagutai da kuma tsarin dokokin da mutane suka kirkiroma kansu da hukumce-hukumcen su akan hukumcin Allah da manzon sa, Allah madaukaki ya ce: To a`aha ! Ina ratsuwa da ubangijin ka, ba za su yi imani ba sai sun yadda da hukuncin ka cikin abin da ya saba a tsakanin su, sa`annan kuma basu sami wanu kunci a cikin zukatan su ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama cikakkiyar sallamawa. (an-nisa`i : 65). Kuma duk wanda ya gabatar da darikun shehunnan bata da abubuwan da suka kago da bidi`o`insu akan ingantacciyar sunna alhali yana sane cewa ita sunnar annabi ce, duk wanda ya aikata wannan to shi kafiri ne da Haduwar malamai
Na biyar : Wanda duk ya fusata da wani abu daga cikin abinda manzon Allah mai tsira da aminci ya zo da shi ko da ya yi aiki da shi to hakika ya kafurta, Allah madaukaki ya ce : Wannan saboda cewa lallai su, sun ki abin da Allah ya saukar, domin haka ya bata ayyukan su. ( Suarat Muhammad: 9
Na shida : wanda duk ya yi Izgili da wani abu na daga addinin manzon Allah mai tsira da aminci- kamar wanda yake yin izgilanci da sashin Hukunce-hukuncen sa da shari`o`in sa da sunnonin sa ko abinda ya bada labarin su, ko kuma ya rika izgilanci da abin da Allah ya tanadar da shi na daga lada ga masu yi masa da`a, ko kuma ukubar da ya tanadar ga masu sabo daga abinda Allah da manzon sa mai tsira da Aminci suka bada labari gameda shi to hakika ya kafirta, dalili kuwa shi ne fadin Allah madaukaki : ka ce shin da Allah da ayoyin sa da manzon sa kuka kasance kuna yiwa izgilanci? Kada ku kawo wani uzuri hakika kun kafirta a bayan imanin ku. (Suat Tauba: 65-66.)
Na bakwai : Sihiri, kuma baya kasancewa sai ta hanyar amfani da aljanu da shaidanu da kuma yin tarayya da su da aikata ayyukan kafirci domin neman yaddar su , daga ciki akwai jujjuyawa da tausasawa mai tasiri a cikin jikkunan mutane, da kuma cikin hankulan su, duk wanda ya aikata shi ko ya yadda da shi to hakika ya kafirta, dalilin haka shi ne fadin Allah madaukaki : kuma basu sanar da kowa har sai sun ce : mu fitina ce kawai, saboda haka kada ka kafirta. (Suat Al-bakara:102).
Na takwas : Taimakawa mushirikai da kuma yin taimakekeniya da su, da taimakon su wajen cin Nasara akan Musulmai, dalili kuwa shi ne fadin sa Allah madaukaki : Kuma wanda ya jibince su daga gare ku, to lallai ne shi yana daga gare su, lallai Allah baya shiriyar da mutane azzalumai. (Suat Al-ma`ida : 51).
Na tara : Wanda duk ya kudurci cewa wasu sashin mutane zasu iya fita daga karkashin shari`ar annabi Muhammad mai tsira da aminci- kamar yadda ya yalwaci khidr ficewa daga shari`ar annabi musa amincin Allah ya tabbata a gareshi to shi kafiri ne saboda fadar Allah madaukaki : Duk wanda ya nemi wani addinin da ba na musulunci ba to baza a karba daga gareshi ba kuma shi a lahira yana daga cikin asararru . (Suat Alil-imrana: 85)
Na goma: Bijirewa daga Addinin Allah (musulunci), baya koyar sa kuma baya aiki da shi, dalili kan haka fadin sa Allah madaukaki: Kuma wanene yafi zalunci bisa ga wanda aka tunantar da ayoyin ubangijin sa, sa`annan ya bijire daga barin su, lallai mu masu daukar fansa ne daga masu laifi. (As-sajdah : 22) . Abin nufi da bijirewa daga addinin Allah shi ne : Rashin koyon abin da ya zamar masa dole na daga abinda Addinin sa baya ingantuwa sai da sanin shi daga ginshikan Addininsa
Bayan ambaton wadannan abubuwan masu warware musulunci; ya kyautu a garemu da mu yi tambihi guda biyu masu muhimmanci su ne :
- Cewa Amabaton wadan nan abubuwa masu warware musulunci domin a tsorata daga garesu, kuma a tsoratar da mutane da su guje su, domin shedanu da mataimakan su masu gurbatar hankali masu batarwa suna zaman dako wajen hana musulmi bin hanya mai kyau, sai su ribaci sakacin wasu daga cikin su kuma su ribaci jahilcin su domin su fitar da su daga cikin kwaryar gaskiya zuwa batacciyar hanya, kuma domin su juyar da su ga barin hanyar aljanna zuwa wuta
- Cewa saukar da wadan nan abubba masu warware Addini bisa hakikanin yadda suke yana daga aikin manyan malamai masu zurfi cikin ilimi, sune wadanda suke sanin dalilai da hukunce-hukunce da kiyayewa ga saukakken hukunce-hukuncen da ke kan mutane, ba kowa ne yin hakan yake halasta a gareshi ba
Amsa / Sai a ce : Ba`a yiwa wani Hukunci da wuta ko aljanna sai wanda nassoshi suka zo cikin yimusu hukunci, saidai ana fatan samun lada ga mai kyautata aiki kuma ana jin tsoron ukuba ga mai munana aiki, kuma muna cewa duk wanda ya mutu akan imani to makomarsa zuwa aljanna ce, kuma duk wanda ya mutu akan shirka da kafirci to shi dan wuta ne kuma tur da makoma.
Amsa/ Sai a ce: ba`a yiwa Musulmi Hukunci da kafirci saboda aikata zunubai da sabo ko da kuwa manya ne, matukar dai basu daga cikin lafuka masu kafirtarwa wadanda nassoshin shari`a na cikin kur`ani da sunna suka yi nuni a kansu kuma Sahabbai da manyan malamai suka fadesu , zai zamo akan imanin sa kuma ya kasance daga masu sabo na ahalin tauhidi matukar bai afka cikin babban kafirci ko babbar shirka ko kuma babban Munafurci ba
Amsa: Lamarin Harshe yana da girma domin da kalma ce mutum yake shiga musulunci kuma yana iya fita daga cikin sa da furta kalma, muna neman tsarin Allah Tuntuben harshe da zamiyar sa mataki-mataki ne, daga cikin su akwai Kalmar kafirci wadda ta ke bata imani kuma ta ke rusa ayyuka, kamar zagin Allah, ko zagin manzon sa mai tsira da aminci, ko wadansu kalmomi da zai siffanta wasu masu girma da waliyyai da siffofin rububiyya, da neman agajin su da kuma jingina duk wani alheri da abinda zai faru ga mutum zuwa garesu daga cikin su akwai lafazan da ake yabon su wanda ake wuce gona da iri a cikin sa, tare da sanya su sama da matsayin su na `yan adantaka, da kuma yin rantsuwa da su, ko kuma yin izgilanci da shari`a da batanci ga hukunce-hukuncen ta, daga cikin su akwai kalmomi na yin fushi da hukunce-hukuncen Allah da ya shar`anta, ko kuma yin fushi tare da bijirewa bisa abin da kaddara ta hukuntar masu radadi na daga abubuwan ki masu faruwa anan duniya daga masifun da suke samun jikin dan adan da dukiya da `ya`ya, da wasun su
Yana daga cikin manyan kaba`iran da suke cutar da imani kuma suke tauye shi: Giba da annamimanci , lallai mu kiyayi kanmu matukar kiyayewa kuma mu tsare harsunan mu ga barin duk wani lafazi da ya sabawa shari`ar Allah da sunnar annabin sa mai tsira da aminci , Manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: ( Lallai wallahi bawa yana furta Kalmar da zata janyo masa yaddar Allah wadda baya bata kulawa amma sai Allah ya daga shi da ita (Kalmar) zuwa wasu darajoji , kuma lallai cewa bawa wallahi zai yi Magana da Kalmar da zata janyo masa fushin Allah wadda baya damuwa da ita amma zai fada cikin wutar Jahanna saboda ita) . Bukhari ne ya rawaito
Sai ka ce : Aikin Mumini baya yankewa sai da Mutuwa , dalilin haka shi ne fadin Allah madaukaki : Kuma ka bautawa ubangijin ka har mutuwa ta zo maka . (al-hijr : 99) . abin da ake nufi da yakini anan shi ne mutuwa, saboda dalilin fadin manzon Allah mai tsira da aminci daga usman dan maz`un yayin da ya rasu : (amma shi usman wallahi hakika mutuwa ta zo masa). Bukhari ne ya fitar da shi. kuma saboda annabi mai tsira da aminci bai rabu da yin aiki cikin tsawon rayuwar sa ba , anan ba ana nufi da ma`anar yakini wata daraja daga imani da mumini zai kai daga kan ta ya tsaya da yin aiki ba ko kuma ace an dauke masa yin aiki ba, kamar yanda wasu karkatattu su ke riya shi
Amsa/ sai ka ce: wanda ke jijjuya al-amarin sammai da kasa da wadanda ke cikin su da abinda ke tsakanin su shi ne Allah shi kadai ne ba shi da abokin tarayya, babu wani mamallakin da ba shi ba, kuma ba shi da abokin tarayya babu mai taimakon sa kuma babu mataimaki a gareshi, tsarki da godiya sun tabbata a gareshi, Allah madaukakin sarki ya ce: Ka ce: ku kirayi wadanda kuka riya (cewa abubuwan bautawa ne) ba Allah ba, ba sa mallakar kwatankwacin kwayar zarra a cikin sammai kuma basa mallakarsa a cikin kasa, kuma basu da wani rabon tarayya a cikin su (sammai da kasa) kuma ba shi da wani mataimaki daga garesu. (saba`a: 22)