Idan aka ce da kai yaya Imani da mala’iku yake?
السؤال
Tambaya: Idan aka ce da kai yaya Imani da mala’iku yake?
الجواب
Amsa: sai ka ce: shi ne gasgatawa da Amincewa da samuwarsu da siffofinsu da ikonsu da ayyukansu da abubuwan da ake umartarsu das u. da kuma cewa su halittu ne masu girma da daraja da Allah ya halicce su daga haske. Kamar yadda yake cewa: basa sabawa Allah abin day a sasu cesu, kuma suna aikata duk abin da aka umarcesu (Surah Taharim 6) kum suna da fikafikai biyu –biyu, uku-uku wasu hudu-hudu wasu fiye da haka. Kuma suna da yawan gaske kuma babu wanda yasan adadinsu sa Allah.Sannan ayi imani da cewa Allah ya dora musu wasu muhimman ayyuka. Akwai masu dauke da al’arshi akwai wadanda aka wakilta a mahaifar mace, da masu rubuta ayyukan talikai, da masu gadin bayin Allah, da masu tsaron Aljanna da masu tsaron wuta da wasunsu da kma. Wanda yafisu duka shine Jibril wanda yake kawo wahayi ga annabawa. Don haka sai muyi wani dasu a dunkule da kuma a rarabe, kamar yadda Allah ya sanar damu a cikin Alqur’ani, da kuma yadda yazoa sunnar annabinmu tsiran Allah da ainci a gareshi. Duk wanda yayi musun samuwar mala’iku to ya fadi wani abu daban da wanda Allah ya fada to ya zama kafiri don ya karyata abinda Allah da Manzon Alah suka fada