Skip to content

Idan aka ce da kai yaya Imani da Hukuncin Allah da kuma qaddara yake?

السؤال

Idan aka ce da kai yaya Imani da Hukuncin Allah da kuma qaddara yake?

الجواب

Sai ka ce ta Hanyar tabbatarwa da cewa kowanne abu yana gudana ne akan Hukuncin Allah da qaddararsa, babu abin da zai faru sai da yardarm Allah, shi ya halicci duk ayyukan bayi masu kyau da marasa kyau. Kuma ya halicci bayi a bisa alheri da karvar gaskiya, kuma ya basu hankula da za su tantance abubuwa, ya basu ikon da za su yi zavi, ya bayyana musu gaskiya ya tsoratar da su daga bin vata, ya shiryar wanda ya so da falalarsa, ya avatar da wanda ya so da Adalcin sa, shi ne mai hikima, masani, mai jin qai, ba a tambayar dalilin da ya sa ya yi wani abu, amma su (Jama’a) ana tambayarsu.

Kuma ita Kaddara mataki hudu ce su ne Kamar haka:

Mataki na fakro shi ne imani da cewa sanin Allah ya kewaye dukkan komai, Allah ya san duk abin da ya faru da wanda yake faruwa, da ma yadda abin da bai faru ba, zai kasance

Mataki na biyu: Imani da cewa Allah ya rubuta komai da komai

Mataki na uku: Imani da cewa babu abin da zai faru sai da yardar Allah.

Mataki na Hudu: Imani da cewa Allah shi ya Halittawa komai jikkuna da Ayyuka da maganganu da motsi da rashin motsi da siffofi a duniyoyin da suke sama ko qasa, kuma dalilan duk waxannan suna da yawa a Alqur’ani da hadisai