idan akace da kai yaya imani da saukakkun litattafai yake?
السؤال
Tambaya: idan akace da kai yaya imani da saukakkun litattafai yake?
الجواب
Amsa: Sai ka ce: Shi ne ka ka sakankance kuma ka shaida cewa lallai Allah Madaukakin Sarki ya saukar da Litattafai ga Annabawansa da Manzanninsa Amincin Allah ya tabbata a garesu kuma ya fadi wasu daga cikinsu a littafinsa : Kamar Suhufu Ibrahim da Attaura ga Annabi Musa da Linjila ga Annabi Isa da Zabura ga Annabi Daud da kuma Alqurani ga Mafificin Annabawa Amincin Allah a gare su.
Kuma mafificinsu shi ne Al'qur'ani wanda shi ne zancen Allah kuma wanda yayi magana da shi a Hakika kuma Lafazinsa kuma Ma'anarsa daga Allah ta ke kuma ya jiyar da Jibirilu shi kuma ya Umarce shi da isar da sakonsa ga Annabinsa Muhammad Allah Madaukaki Sarki yace: "Ruhi Amintacce ya saukar da shi"(l'shura'a:198) kuma Allah "Mu ne Lallai muka sauka maka da Al'qurani Saukarwa:(Al'Insan:23( da kuma fadinsa: "to ka basu Mafaka har yaji zancen Allah" (Attaubah6)
kuma Allah ya kiyaye Alqur’ani daga gurbatawa ko kari ko ragi.Sannan an kawwameshi a takardu da kiraza har izuwa lokacin da Allah zai karbi rayukan muminai kafin a tashi alkiyama a karshen duniya, lokacine Allah zai dauke shi zuwa gareshi baa bin da zai saura nasa