Skip to content

Idan aka ce dakai yaya Imani da ranar lahira yake?

السؤال

Tambaya: Idan aka ce dakai yaya Imani da ranar lahira yake?

الجواب

Amsa: sai ka ce : shi ne a gaskata kuma a sakankance ba tare da kokwanto ba, da yin furuci da duk abin da Allah ya bayar da labarin zai faru bayan Mutuwa, tun daga Azaba ko ni’ima dake cikin kabari, da tashi daga kabari da taruwa don hisabi da hukunci har izuwa abubuwan da zasu faru a farfajiyar alkiyama na doguwar tsayuwa da kusantowar rana kwatankwacin mil daya kuma tafki da sikelin awo da raba takardun aiki da kafa sira a aman wutarJahannama da sauran abubuwan tashin hankali da zasu faru a wannan babbar Rana. Har da ‘yan Aljanna su shiga Aljanna ‘yan wuta si shiga wua kamar dai yadda yazo dalla dalla a kur’ani da hadizi. Hakanan a karkashin imani da ranar lahira akwai gasgata abinda ya tabbata na alamomin alkiyama kamar yawaitar fitina da kasha – kasha da girgizar kasa da kisfewar rana da zuwan Dujal da saukar Annabi Isa da fitowar Yajuju da Majuju da hudowar rana ta mafadarta sda makamantansu.

kuma dukkan wadan nan sun tabbata daga irin ingantattun Hadisai daga Manzon Allah tsira da aminci a gareshi ya bayar kuma aka rubutasu a manyan litattafan hadisi masu inganci.