idan akace dakai: shin azabar kabari dani’imomin cikin sa sun tabbata a Kur’ani da Hadisi?
السؤال
Tambaya: idan akace dakai: shin azabar kabari dani’imomin cikin sa sun tabbata a Kur’ani da Hadisi?
الجواب
Amsa: sai kace: kwarai kuwa, domin Allah ya fadawa mutanen fir’auna cewa: wuta ce da aka bijiro dasu gareta da safe da yamma. Sannan a ranar Alkiyama (sai ace da mala’iku ku shigar da jama’ar fir’auna mafi tsananin azaba (Gafir 46) da fadinsa ‘da kaga lokacin da Mala’iku suke karbar rayukan kafirai, suna bugun fuskokin da bayansu, (sannan ace) ku dandani azabar kuna. (Anfal 5) da fadinsa: Allah zai tabbatar da muminai abisa tabbatacciyar Magana a rayuwar duniya da ta lahira ( Ibrahim 27) hakanan wani a dogon hadisi kudsi da Barra yazo cewa: wani mai kira zai yi kira daga aljanna, kuyi masa sutura daga aljannan, kuma ku bude masa kofa zuwa aljanna sai ya jiyo iskarta da kanshinta kuma a yalwata masa fadin kabarinsa iya ganinsa.Amma kafiri kuwa sai a dawo masa da ransa izuwa jikinsa, sannan mala’iku biyu su zo su zaunar da shi sai su ce masa wanene Ubangijinka sai yace wayyo! Ban sani ba. Sai su ce menene addininka sai wayyo! Wayyo! Ban sani ba. Sai su ce da shi: Ina labarin mutumin da aka aiko muku (da Annabta) sai yace wayyo! Wayyo! Bai sani ba, sai wani mai kira yayi kira daga sama yace: qarya yake ku yi masa shinfixa ta wuta, kuma ku saka masa tufafi na wuta, sannan ku buxe masa qofar wuta sai ya jiyo zafinta da iskarta, kuma kabarinsa ya yi masa qunci har sai gavovinsa sun sava da junansu. (A wata ruwayar ya qara cewa sai a haxa shi da (Mala’ika) da baya ji ba ya magana yana xauke da wani madoki na baqin qarfe wanda da za a bugi dutse da shi da sai ya zama garin qasa. Sai ya buge shi dukan da duk abin da yake gabas da yamma sai ya ji qararsa ban da mutum da aljan). Abu dawud ya ruwaito shi. Wannan dalili ne ya sa aka umarce mu da mu dinga neman tsari daga azabar qabari a kowacce sallah