Ni ce zan je umara, sai na biyo ta miƙati alhalin ina haila, ban yi ihrami ba, na wanzu a garin Makka, sai sai da na samu tsarki, sai na yi harama daga Makka ɗin, shin hakan ya halatta? ko kuma me zan yi? menene ya ke wajaba a kaina?
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Ni ce zan je umara, sai na biyo ta miƙati alhalin ina haila, ban yi ihrami ba, na wanzu a garin Makka, sai sai da na samu tsarki, sai na yi harama daga Makka ɗin, shin hakan ya halatta? ko kuma me zan yi? menene ya ke wajaba a kaina?
س54: أنا ذاهبةٌ للعمرة، ومررت بالميقات وأنا حائضٌ، فلم أحرم، وبقيت في مكة حتّى طهرت، فأحرمت من مكة، فهل هذا جائزٌ؟ أو ماذا أفعل؟ وما يجب عليّ؟
الجواب
AMSA TA 1:
Wannan abin da ta yi bai halatta ba, matar da ta ke da niyyar umara, ba ya halatta a gareta ta ta ƙetare miƙati sai da ihrami ko da kuwa ta kasance mai haila ce, haka za ta yi harama tana hailar, kuma ihraminta ya ƙullu, ya inganta.
Dalili a bisa haka shi ne: Nana Asma'u 'yar Umais matar Abubakar - Allah Ya yarda da shi - ta haihu, alhalin Annabi ya sauka a Zulhulaifa, yana son zai yi hajjin bankwana, sai ta aiko (da tambaya) wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: yaya zan yi? sai ya ce: "Ki yi wanka, ki yi ƙunzugu da wani tufafi, sai ki ƙulla harama".
Jinin haila kamar jinin biƙi ne.
Sai mu ce da mace mai haila, idan ta zo wucewa ta miƙati, alhalin tana son yin umara ko hajji sai mu ce da ita: ki yi wanka, ki yi ƙunzugu da wani tufafi, sai ku ƙulla harama,
Ƙunzugu ma'anarsa ita ce: Ta ɗaura wani ƙyalle a farjinta, ta ƙulle shi, sannan ta yi harama, ko hajji ne, ko umara ne, saidai idan ta yi haramar kuma ta iso Makka, to, ba za ta je Ka'aba ba, ba za ta yi ɗawafi a cikinsa ba har sai ta samu tsarki,
Sabo da wannan ne Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce da Nana A'isha yayin da ta yi haila a tsakiyar umara, ya ce da ita: "Ki aikata abin da mahajjaci ya ke aikatawa, sai dai kada ki yi ɗawafi a Ka'aba" wannan riwaya ce ta Bukhari da Muslim,
A cikin "Sahihul Bukhari" Kuma, Nana A'isha ta ambaci cewa ya yin data samu tsarki, ta yi ɗawafi a Ka'aba, da safa da Marwa,
Wannan sai ya nuna cewa idan mace ta yi harama da hajji ko umara alhali tana haila, ko kuma hailar ta zo mata kafin ɗawafi, to, ba za ta yi ɗawafin ba, ba za ta yi sa'ayi ba har bayan ta yi tsarki ta yi wanka.
Amma da ta yi ɗawafin alhali tana da tsarki, bayan ta gama ɗawafin sai hailar ta zo mata, to, za ta ci gaba, ta yi sa'ayi ko da tana cikin hailar, ta ɗan datse gashin kanta, ta ƙarasa umararta, sabo da sa'ayi tsakanin safa da marwa, ba'a sharɗanta tsarki sabo da shi.
ﺟ54: هذا العمل ليس بجائزٍ، والمرأة الّتي تريد العمرة لا يجوز لها مجاوزة الميقات إلا بإحرامٍ حتى لو كانت حائضًا، فإنها تحرم وهي حائضٌ، وينعقد إحرامها، ويصحّ،
والدليل لذلك: أن أسماء بنت عميسٍ زوجة أبي بكرٍ رضي الله عنهما ولدت، والنبيّ ﷺ نازلٌ في ذي الحليفة، يريد حجة الوداع، فأرسلت إلى النبيّ ﷺ: كيف أصنع؟ قال:
«اغْتَسِلِي، وَاسْتَثْفِرِي بِثَوْبٍ، وَأَحْرِمِي» [1]،
ودم الحيض كدم النّفاس.
[24] تقدم تخريجه.
فنقول للمرأة الحائض إذا مرت بالميقات، وهي تريد العمرة أو الحج نقول لها: اغتسلي، واستثفري بثوبٍ، وأحرمي،
والاستثفار معناه: أنها تشدّ على فرجها خرقةً، وتربطها، ثم تحرم، سواء بالحجّ أو بالعمرة، ولكنها إذا أحرمت ووصلت إلى مكة لا تأتي إلى البيت، ولا تطوف به حتى تطهر، ولهذا قال النبيّ ﷺ لعائشة حين حاضت في أثناء العمرة، قال لها:
«افْعَلِي مَا يَفْعَلُ الْحَاجُّ، غَيْرَ أَلَّا تَطُوفِي فِي الْبَيْتِ حَتَّى تَطْهُرِي» [2]،
هذه رواية البخاريّ ومسلمٍ، وفي «صحيح البخاريّ» أيضًا،
«ذَكَرَتْ عَائِشَةُ أَنَّهَا لَمَّا طَهُرَتْ طَافَتْ بِالْبَيْتِ، وَبِالصَّفَا وَالْمَرْوَةِ» [3]،
فدل هذا على أن المرأة إذا أحرمت بالحجّ أو العمرة وهي حائضٌ، أو أتاها الحيض قبل الطواف، فإنها لا تطوف ولا تسعى حتى تطهر وتغتسل.
[26] البخاري، كتاب العمرة، باب عمرة التنعيم (1785).
[25] رواه البخاري، كتاب الحج، باب تقضي الحائض المناسك كلها إلا الطواف بالبيت (1650)، ومسلم، كتاب الحج، باب بيان وجوه الإحرام (120) (1211).
أما لو طافت وهي طاهرٌ، وبعد أن انتهت من الطواف جاءها الحيض، فإنها تستمرّ، وتسعى ولو كان عليها الحيض، وتقصّ من رأسها، وتنهي عمرتها؛ لأنّ السعي بين الصفا والمروة لا يشترط له الطهارة.