Shin filin sa'ayi yana daga cikin Harami? shin mai haila za ta iya kusantar sa? shin yana wajaba a kan wanda ya shiga Harami ta filin sa'ayi ya yi sallar gaisuwar masallaci?
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Shin filin sa'ayi yana daga cikin Harami? shin mai haila za ta iya kusantar sa? shin yana wajaba a kan wanda ya shiga Harami ta filin sa'ayi ya yi sallar gaisuwar masallaci?
س56: هل المسعى من الحرم؟ وهل تقربه الحائض؟ وهل يجب على من دخل الحرم من المسعى أن يصلّي تحية المسجد؟
الجواب
AMSA TA 1:
Abin da ya ke bayyane shi ne cewa filin sa'ayi ba ya daga cikin masallacin, shi ya sanya ma suka samar da katanga da ta raba tsakanin su, sai dai katanga ce gajera, babu kokwanto a kan cewa hakan alherine ga mutane; domin da an shigar da shi cikin masallaci ya zama ɓangare a cikinsa, da sai ya zama idan mace ta yi haila tsakanin ɗawafi da sa'ayi, to, da an hana ta yin sa'ayi.
Fatawar da zan bayar ita ce: Idan ta yi haila bayan ɗawafi kafin sa'ayi, to, za ta yi sa'ayin; sabo da filin sa'ayin ba'a ɗaukar sa a matsayin masallacin.
Amma game da (sallar) gaisuwar masallaci, sai a ce: Idan mutum ya yi sa'ayi bayan ɗawafi, sannan ya dawo masallaci, to, zai sallaceta, da zai bar yin (sallar) gaisuwar masallaci, to, babu komai a kan sa,
Abin da ya fi shi ne ya yi amfani da damar, ya yi sallah raka'a biyu; sabo da falalar sallah a wannan wajen.
ﺟ56: الّذي يظهر أن المسعى ليس من المسجد، ولذلك جعلوا جدارًا فاصلًا بينهما، لكنه جدارٌ قصيرٌ، ولا شك أن هذا خيرٌ للناس؛ لأنه لو أدخل في المسجد وجعل منه، لكانت المرأة إذا حاضت بين الطواف والسعي امتنع عليها أن تسعى.
والّذي أفتي به: أنها إذا حاضت بعد الطواف وقبل السعي فإنها تسعى؛ لأن المسعى لا يعتبر من المسجد.
وأما تحية المسجد فقد يقال: إن الإنسان إذا سعى بعد الطواف، ثم عاد إلى المسجد، فإنه يصلّيها، ولو ترك تحية المسجد فلا شيء عليه،
والأفضل أن ينتهز الفرصة، ويصلّي ركعتين؛ لـما في الصلاة في هذا المكان من الفضل.