Hakiƙa na taso daga 'Yanbu'u sabo da yin umara ni da iyalaina, amma lokacin isowata Jidda sai matata ta wayi gari tana haila, sai dai na kammala umarar ni kaɗai ba tare da matata ba, menene hukunci game da matata?
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Hakiƙa na taso daga 'Yanbu'u sabo da yin umara ni da iyalaina, amma lokacin isowata Jidda sai matata ta wayi gari tana haila, sai dai na kammala umarar ni kaɗai ba tare da matata ba, menene hukunci game da matata?
س55: لقد قدمت من ينبع للعمرة أنا وأهلي، ولكن حين وصولي إلى جدة أصبحت زوجتي حائضًا، ولكنّي أكملت العمرة بمفردي دون زوجتي، فما الحكم بالنّسبة لزوجتي؟
الجواب
AMSA TA 1:
Hukunci game da matarka shi ne: Ta zauna har sai ta yi tsarki, sannan ta rama umararta;
Sabo da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da Nana Safiyya - Allah Ya yarda da ita - tayi haila sai ya ce: "Shin tsaremu ta ke son yi?" sai su ka ce: ai ta yi (ɗawafin) Ifada, sai ya ce: "Ashe sai ta taho kawai".
Faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "Shin tasremu za ta yi?" dalili ne a kan cewa mace za ta yi zamanta ne -idan ta yi haila kafin ɗawafin Ifada- har sai ta samu tsarki, sannan ta yi ɗawafi.
Haka nan ɗawafin umara kamar ɗawafin Ifada ne; sabo da shi rukuni ne a cikin umara, idan mai aikin umara ta yi haila kafin ɗawafi sai ta jira har sai ta yi tsarki, sannan ta yi ɗawafi.
ﺟ55: الحكم بالنّسبة لزوجتك: أن تبقى حتى تطهر، ثم تقضي عمرتها؛ لأن النبي ﷺ لـما حاضت صفية رضي الله عنها قال:
«أَحَابِسَتُنَا هِيَ؟» قَالُوا: إِنَّهَا قَدْ أَفَاضَتْ. قَالَ: «فَلْتَنْفِرْ إِذًا» [1]،
فقوله ﷺ: «أحابستنا هي؟» دليلٌ على أنه يجب على المرأة أن تبقى -إذا حاضت قبل طواف الإفاضة- حتى تطهر، ثمّ تطوف.
[27] تقدم تخريجه.
وكذلك طواف العمرة مثل طواف الإفاضة؛ لأنه ركنٌ من العمرة، فإذا حاضت المعتمرة قبل الطواف انتظرت حتى تطهر، ثم تطوف.