Skip to content

Wata mata ce ta yi tafiya zuwa aikin Hajji, sai hailarta ta wata ta zo mata tun kwana biyar da tafiyar ta ta, bayan ta iso Miƙati sai ta yi wanka ta ƙulla Ihrami, alhali ba ta tsarkaka daga hailar ba, yayin da ta iso Makka abar girmamawa sai ta zauna a wajen harami, ba ta yi komai ba daga ayyukan Hajji ko Umara ba, sai ta zauna kwana biyu a Mina, sannan ta samu tsarki, ta yi wanka, ta idar da dukkan ayyukan Umara alhalin tana cikin tsarki, sai kuma jinin ya dawo mata alhalin tana ɗawafin Ifada na Hajji, saidai cewa ita taji kunya, ta cika ayyukan Hajjin, ba ta gaya wa waliyyinta ba sai bayan sun dawo garinsu, to, menene hukuncin hakan?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

س48: سافرت امرأةٌ إلى الحجّ، وجاءتها العادة الشهريّة منذ خمسة أيامٍ من تاريخ سفرها، وبعد وصولها إلى الميقات اغتسلت وعقدت الإحرام، وهي لم تطهر من العادة، وحين وصولها إلى مكة المكرمة ظلت خارج الحرم، ولم تفعل شيئًا من شعائر الحجّ أو العمرة، ومكثت يومين في منًى، ثم طهرت، واغتسلت، وأدت جميع مناسك العمرة وهي طاهرٌ، ثمّ عاد الدم إليها وهي في طواف الإفاضة للحجّ، إلا أنها استحت، وأكملت مناسك الحجّ، ولم تخبر وليها إلا بعد وصولها إلى بلدها، فما حكم ذلك؟

الجواب

AMSA TA 1:

Hukunci game da wannan shi ne: Jinin da ya same ta a ɗawafin Ifada in ya kasance jinin haila ne wanda ta san shi da ɗabi'ar sa, da ciwon sa, to, ɗawafin Ifadar bai inganta ba, ya zama lallai ta dawo Makka; don ta yi ɗawafin Ifada, sai ta yi haramar Umara da ɗawafi da Sa'ayi, ta ɗan rage gashinta, sannan ta yi ɗawafin Ifada.

Amma idan wannan jinin ya kasance ba na haila ba ne, jini ne na ɗabi'a sananne, kawai dai ya samu ne sabo da tsananin cinkoso, ko razani ko abin da ya yi kama da haka, to, ɗawafinta ya inganta a wajen waɗanta ba sa sharɗanta tsarki domin yin ɗawafi.

Idan ba ta samu damar dawowa ba a mas'ala ta farko, ta yadda ta kasance a gari mai nisa, Hajjinta ingantacce ne; sabo da ba za ta iya yin sama da abin da ta aikata ba.

ﺟ48: الحكم في هذا: أنّ الدم الّذي أصابها في طواف الإفاضة إذا كان هو دم الحيض الّذي تعرفه بطبيعته وأوجاعه فإن طواف الإفاضة لم يصح، ويلزمها أن تعود إلى مكة؛ لتطوف طواف الإفاضة، فتحرم بعمرةٍ من الميقات، وتؤدّي العمرة بطوافٍ وسعيٍ، وتقصّر، ثم تطوف طواف الإفاضة.

أما إذا كان هذا الدم ليس دم الحيض، الدم الطبيعيّ المعروف، وإنما نشأ من شدّة الزّحام أو الروعة أو ما شابه ذلك، فإن طوافها يصحّ عند من لا يشترط الطهارة للطواف.

فإن لم يمكنها الرّجوع في المسألة الأولى، بحيث تكون في بلادٍ بعيدةٍ، فحجّها صحيحٌ؛ لأنها لا تستطيع أكثر ممّا صنعت.