Ta yaya mai haila za ta sallaci raka'o'i biyu na ihrami? Shin ya halatta ga mace mai haila maimaita ayoyin Al-ƙur'ani Mai hikima a ɓoye, ko a'a?
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Ta yaya mai haila za ta sallaci raka'o'i biyu na ihrami? Shin ya halatta ga mace mai haila maimaita ayoyin Al-ƙur'ani Mai hikima a ɓoye, ko a'a?
س47: كيف تصلّي الحائض ركعتي الإحرام؟ وهل يجوز للمرأة الحائض ترديد آي الذّكر الحكيم في سرّها، أو لا؟
الجواب
AMSA TA 1:
Na farko: Ya kamata mu sani cewa Ihrami ba sallah a gareshi; haƙiƙa ba wani abu da ya zo daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa Ya shar'anta wa al'umar sa wata sallah ta Ihrami, ko ta maganar sa, ko aikin sa, ko iƙirarin sa.
Na biyu: Haƙiƙa wannan mace mai haila wacce ta yi haila kafin ta yi harama, zai iya yiwuwa ta yi harama alhali tana haila;
Sabo da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarci Asma'u bint Umais matar Abubakar Allah - Ya yarda da su - yayin da ta haihu a Zulhulaifah, sai ya umarce ta da ta yi wanka, ta yi ƙunzugu da tufafi, ta yi harama, haka nan ma mai haila, kuma za ta wanzu cikin Ihraminta, har sai ta samu tsarki, sannan ta yi ɗawafi a Ka'aba, ta yi Sa'ayi.
Amma abin da ya faɗa a tambayar: Shin za ta karanta Al-ƙur'ani? to, Eh, mai haila tana da haƙƙi ta karanta al-ƙur'ani a lokacin buƙata ko maslaha, amma idan ba wata buƙata ko maslaha, kawai tana son karantawa ne don ibada, da neman kusanci zuwa ga Allah, to, abin da ya fi shi ne ka da ta karanta.
ﺟ47: أولًا: ينبغي أن نعلم أن الإحرام ليس له صلاةٌ؛ فإنه لم يرد عن النبيّ ﷺ أنه شرع لأمته صلاةً للإحرام لا بقوله، ولا بفعله، ولا بإقراره.
ثانيًا: إن هذه المرأة الحائض الّتي حاضت قبل أن تحرم يمكنها أن تحرم وهي حائضٌ؛ لأن النبي ﷺ أمر أسماء بنت عميسٍ امرأة أبي بكرٍ رضي الله عنهما حين نفست في ذي الحليفة، أمرها أن تغتسل وتستثفر بثوبٍ، وتحرم [1]، وهكذا الحائض أيضًا، وتبقى على إحرامها حتى تطهر، ثمّ تطوف بالبيت، وتسعى.
[18] رواه مسلم، كتاب الحج، باب حج النبي ﷺ (2137).
وأما قوله في السّؤال: هل لها أن تقرأ القرآن؟ فنعم، الحائض لها الحقّ أن تقرأ القرآن عند الحاجة أو المصلحة، أمّا بدون حاجةٍ ولا مصلحةٍ، إنما تريد أن تقرأه تعبّدًا وتقرّبًا إلى الله، فالأحسن ألا تقرأه.