Skip to content

Shin ruwan da ya ke fita daga mace - fari ko rawaya - mai tsarki ne ko najasa? kuma shin yana wajaba a sake alwala sabo da shi, tare da sanin cewar yana zuba koda yaushe? kuma Menene hukunci idan ya kasance yana zuba a tsitstsinke, musamman cewa yawancin matan - musamman masu koyo - suna ɗaukar wannan danshi ne na ɗabi'a, alwala bata wajaba daga gare shi?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Shin ruwan da ya ke fita daga mace - fari ko rawaya - mai tsarki ne ko najasa? kuma shin yana wajaba a sake alwala sabo da shi, tare da sanin cewar yana zuba koda yaushe? kuma Menene hukunci idan ya kasance yana zuba a tsitstsinke, musamman cewa yawancin matan - musamman masu koyo - suna ɗaukar wannan danshi ne na ɗabi'a, alwala bata wajaba daga gare shi?

س35: هل السائل الّذي ينزل من المرأة -أبيض كان أم أصفر- طاهرٌ أو نجسٌ؟ وهل يجب فيه الوضوء، مع العلم بأنه ينزل مستمرًّا؟ وما الحكم إذا كان متقطّعًا، خاصةً أن غالب النّساء -لا سيما المتعلّمات- يعتبرن ذلك رطوبةً طبيعيةً، لا يلزم منه الوضوء؟

الجواب

AMSA TA 1:

Abin da ya ke bayyana a gareni, bayan bincike shi ne: Cewa ruwan da ya ke fita daga mace idan ya zamo ba daga mafitsara ba ne, kaɗai yana fita ne daga mahaifa, to, shi mai tsarki ne, sai dai yana warware alwala duk da ya kasance mai tsarki ne; sabo da ba a sharɗanta cewa abin da zai warware alwala sai ya zama najasa ba, ga rihi (hutu) nan da ta ke fita daga dubura, ba ta da wani jiki, amma duk da haka tana warware alwala.

A bisa wannan, idan ya fito wa mace, alhalin tana da alwala, to, ya warware alwalar, ya zama lallai a kanta ta sabuntata.

Idan kuma ya kasance mai zarcewa ne, to, shi ba ya warware alwala, sai dai za ta yi alwala sabo da sallah, idan lokacinta ya shiga, sai ta yi sallolin farilla da nafiloli a wannan lokacin, kuma ta yi karatun Al-ƙur'ani, ta aikata abin da ta so daga abin da aka halatta mata,

Kamar yadda malamai suka faɗi makamancin wannan ga mai yoyon fitsari, wannan shi ne hukuncin ruwan da ya ke fita a ɓangaren tsarki, shi ɗin mai tsarki ne, ta kuma ɓangaren warwarewar sa ga alwala, to, yana warwarewa, saidai idan ya kasance mai zarce mata ne, to, idan ya kasance mai zarcewane, to, ba ya warware alwala, saidai ya zama lallai a kan matar kada ta sake alwala don yin sallar sai bayan shigar lokaci, kuma ta yi kaffa-kaffa.

Amma in ya kasance mai tsitstsinke wane, kuma ya zama al'adarsa yana yankewa a lokutan sallah, to, za ta jinkirta sallar zuwa lokacin da ya ke yanke mata a cikinsa, matuƙar ba ta ji tsoron fitar lokacin ba, idan ta ji tsoron fitar lokaci sai ta sake alwala, ta nade - ta yi kaffa-kaffa - kuma ta yi sallah.

Babu bambanci tsakanin kaɗan da mai yawa; sabo da dukkaninsa ya fito ne ta kafar, sai ya zamo kaɗan ɗinsa da mai yawansa yana warwarewa, saɓanin wanda ya ke fita daga sauran jiki, kamar jini da hararwa, to, ba ya warware alwala, kaɗan ɗinsa ko mai yawansa.

Amma abin da wasu mata su ke ƙudir cewar baya warware alwala, to wannan ban san tushensa ba, sai dai wata magana ta Ibn Hazm - Allah Ya ji ƙansa - yana cewa: Haƙiƙa wannan baya warware alwala. Sai dai bai ambaci dalilin hakan ba, da yana da dalili na Al-ƙur'ani da Sunna ko maganar sahabbai; da ya zama hujja.

Ya zama lallai a kan mace, ta tsoraci Allah, ta yi kishin zama mai tsarki; haƙiƙa sallah ba ta karɓuwa ba tare da tsarki ba, ko da ta yi sallah sau ɗari, Kai, wasu malamai ma suna cewa: Haƙiƙa wanda ya ke sallah ba tare da tsarki ba ya kafurta; domin wannan, yana daga babin izglanci da ayoyin Allah - Maɗaukakin Sarki -.

ﺟ35: الظاهر لي بعد البحث: أن السائل الخارج من المرأة إذا كان لا يخرج من المثانة، وإنما يخرج من الرحم، أنّه طاهرٌ، ولكنه ينقض الوضوء وإن كان طاهرًا؛ لأنه لا يشترط للناقض للوضوء أن يكون نجسًا، فها هي الرّيح تخرج من الدّبر، وليس لها جرمٌ، ومع ذلك تنقض الوضوء.

وعلى هذا، إذا خرج من المرأة وهي على وضوءٍ فإنه ينقض الوضوء، وعليها تجديده.

فإن كان مستمرًّا فإنه لا ينقض الوضوء، ولكن تتوضأ للصلاة إذا دخل وقتها، وتصلّي في هذا الوقت الّذي تتوضأ فيه فروضًا ونوافل، وتقرأ القرآن، وتفعل ما شاءت ممّا يباح لها،

كما قال أهل العلم نحو هذا فيمن به سلس البول، هذا هو حكم السائل من جهة الطهارة، فهو طاهرٌ، ومن جهة نقضه للوضوء، فهو ناقضٌ للوضوء إلا أن يكون مستمرًّا عليها، فإن كان مستمرًّا فإنه لا ينقض الوضوء، لكن على المرأة ألا تتوضأ للصلاة إلا بعد دخول الوقت، وأن تتحفظ.

أما إن كان منقطعًا، وكان من عادته أن ينقطع في أوقات الصلاة، فإنها تؤخّر الصلاة إلى الوقت الّذي ينقطع فيه، ما لم تخش خروج الوقت، فإن خشيت خروج الوقت فإنها تتوضأ، وتتلجم -تتحفظ- وتصلّي.

ولا فرق بين القليل والكثير؛ لأنه كله خارجٌ من السبيل، فيكون ناقضًا قليله وكثيره، بخلاف الذي يخرج من بقية البدن كالدم والقيء، فإنه لا ينقض الوضوء، لا قليله ولا كثيره.

وأما اعتقاد بعض النّساء أنه لا ينقض الوضوء فهذا لا أعلم له أصلًا، إلا قولًا لابن حزمٍ رحمه الله، فإنه يقول: إن هذا لا ينقض الوضوء، ولكنه لم يذكر لهذا دليلًا، ولو كان له دليلٌ من الكتاب والسّنة أو أقوال الصحابة لكان حجةً.

وعلى المرأة أن تتقي الله، وتحرص على طهارتها؛ فإن الصلاة لا تقبل بغير طهارةٍ ولو صلت مئة مرةٍ، بل إن بعض العلماء يقول: إن الذي يصلّي بلا طهارةٍ يكفر؛ لأن هذا من باب الاستهزاء بآيات الله سبحانه وتعالى.