Menene hukuncin mace ta zauna a masallaci mai alfarma [Ka'aba ko Masallacin Annabi] alhali tana haila; sabo da ta saurari hadisai da huɗubobi?
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Menene hukuncin mace ta zauna a masallaci mai alfarma [Ka'aba ko Masallacin Annabi] alhali tana haila; sabo da ta saurari hadisai da huɗubobi?
س34: ما حكم وجود المرأة في المسجد الحرام وهي حائضٌ؛ لاستماع الأحاديث والخطب؟
الجواب
AMSA TA 1:
Ba ya halatta ga mace mai haila ta zauna a masallaci mai alfarma ko waninsa daga cikin masallatai, sai dai ya halatta gareta ta wuce ta masallacin, ta ɗauki buƙatarta a ciki da abin da ya yi kama da hakan;
Kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce da Nana A'isha, yayin da ya umarceta, ta zo masa da ɗan abin ɗora fuska a sujjada, sai ta ce, ina cikin masallaci kuma haila na ke yi. sai ya ce: "Ai hailar taki ba a hannunki ta ke ba",
Idan mai haila za ta wuce ta masallaci, alhali tana da amincin wani abu na jini ba zai ɗiga a masallaci ba, to, babu laifi a kanta.
[1] Al-khumrah: Ita ce abin da mai sallah ya ke sujjada a kai, an kira shi da khumrah ne; sabo da yana rufe fuska, ai yana lulluɓe shi.
Amma idan tana son ta shiga ta zauna ne, to, wannan ba ya halatta.
Dalili a bisa haka shi ne: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarci mata a sallar idi cewa su fita zuwa filin sallar idi ('yan mata, da waɗanda ake tsarewa a gidaje, da masu haila) sai dai ya umarci masu haila da su ware daga filin sallar idin,
Sai wannan ya yi nuni a kan cewa ba ya halatta mai haila ta zauna a masallaci don sauraron huɗuba, ko sauraron darasi da hadisai.
ﺟ34: لا يجوز للمرأة الحائض أن تمكث في المسجد الحرام ولا غيره من المساجد، ولكن يجوز لها أن تمر بالمسجد، وتأخذ الحاجة منه وما أشبه ذلك؛ كما قال النبيّ ﷺ لعائشة حين أمرها أن تأتي بالخمرة[1]، فقالت: إنها في الـمسجد، وإنّي حائضٌ، فقال:
«إِنَّ حَيْضَتَكِ لَيْسَتْ فِي يَدِكِ» [2]،
فإذا مرت الحائض في المسجد، وهي آمنةٌ من أن ينزل دمٌ على المسجد، فلا حرج عليها.
[14] الخمرة: هي السجادة يسجد عليها المصلي، وسميت خمرة؛ لأنها تخمر الوجه، أي: تغطيه.
[15] مسلم، كتاب الحيض، باب جواز غسل الحائض رأس زوجها وترجيله (11) (298).
أما إن كانت تريد أن تدخل وتجلس فهذا لا يجوز.
والدليل على ذلك: أن النبي ﷺ أمر النّساء في صلاة العيد أن يخرجن إلى مصلى العيد -العواتق، وذوات الخدور، والحيض- إلا أنه أمر أن يعتزل الحيض المصلى [3]،
فدل ذلك على أنّ الحائض لا يجوز لها أن تمكث في المسجد لاستماع الخطبة، أو استماع الدرس والأحاديث.
[16] البخاري، كتاب العيدين، باب خروج النساء والحيض (974)، ومسلم، كتاب العيدين، باب ذكر إباحة خروج النساء في العيدين إلى المصلى (10) (890).
من أحكام الطهارة في الصلاة