Skip to content

Shin ya inganta wannan matar ta yi sallar walaha da alwalar Asuba?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Shin ya inganta wannan matar ta yi sallar walaha da alwalar Asuba?

س37: هل يصحّ أن تصلّي تلك المرأة صلاة الضّحى بوضوء الفجر؟

الجواب

AMSA TA 1:

Hakan ba ya inganta; sabo da sallar walaha tana da lokaci, ba makawa sai ta yi mata alwala, bayan shigar lokacinta; sabo da wannan kamar mai istihala ce, haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarci mai istihala da ta sake alwala a lokacin kowace sallah.

Lokacin Azahar: Shi ne, daga zawalin rana zuwa lokacin La'asar.

Lokacin La'asar kuma: Daga fitar lokacin Azahar zuwa fatsi-fatsin rana, na larura kuma zuwa faɗuwar rana.

Lokacin Magariba: Daga faduwar rana zuwa ɓuyan jan shafaƙi.

Lokacin Isha'i: Daga ɓuyan jan shafaƙi zuwa tsakiyar dare.

ﺟ37: لا يصح ذلك؛ لأن صلاة الضّحى مؤقتةٌ، فلابد من الوضوء لها بعد دخول وقتها؛ لأن هذه كالمستحاضة، وقد أمر النبيّ ﷺ المستحاضة أن تتوضأ لكلّ صلاةٍ.

ووقت الظّهر: من زوال الشمس إلى وقت العصر.

ووقت العصر: من خروج وقت الظّهر إلى اصفرار الشمس، والضرورة إلى غروب الشمس.

ووقت المغرب: من غروب الشمس إلى مغيب الشفق الأحمر.

ووقت العشاء: من مغيب الشفق الأحمر إلى نصف الليل.