Ina da uwa ta kai shekara sittin da biyar, ta kai shekara goma sha tara ba ta sake haihuwa ba, yanzu kuma tana fama da zubar jini, tsahon shekaru uku a haka, wannan wata rashin lafiya ce - wacce ta ke nuna - ta zo mata a wancan lokacin, duba da cewar za ta fuskanci azumi, wacce nasiha za ku yi mata? ire-irenta kuma yaya za su yi?
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Ina da uwa ta kai shekara sittin da biyar, ta kai shekara goma sha tara ba ta sake haihuwa ba, yanzu kuma tana fama da zubar jini, tsahon shekaru uku a haka, wannan wata rashin lafiya ce - wacce ta ke nuna - ta zo mata a wancan lokacin, duba da cewar za ta fuskanci azumi, wacce nasiha za ku yi mata? ire-irenta kuma yaya za su yi?
س33: لي والدةٌ تبلغ من العمر خمسةً وستّين عامًا، ولها مدة تسع عشرة سنةً وهي لم تأت بأطفالٍ، والآن معها نزيف دمٍ، لها مدة ثلاث سنواتٍ، وهو مرضٌ -يبدو- أتاها في تلكم الفترة، ولأنها ستستقبل الصّيام، فكيف تنصحونها؟ وكيف يتصرف مثلها؟
الجواب
AMSA TA 1:
Irin wannan matar da zubar jini ya sameta hukuncinta: Ta bar sallah da azumi tsawon lokacin al'adarta ta baya, wacce kafin wannan abin da ya sameta (take a akanta) idan ya kasance a al'adarta haila tana zuwar mata a farkon wata tsawon kwanuka shida misali, to, za ta zauna daga farkon kowane wata tsawon kwana shida ba za ta yi sallah ba, ba za ta yi azumi ba, idan ta ƙare sai ta yi wanka ta yi sallah ta yi azumi.
Yadda wannan da ire-irenta za su yi sallah shi ne: Za ta wanke farjinta cikakkiyar wankewa, sai ta tare shi, sai ta yi alwala, za ta yi haka ne bayan shigar lokacin sallar farilla, haka nan za ta yi idan tana so za ta yi nafila a lokatan da ba na farillai ba.
A wannan yanayin - sabo da kuma kar ta sha wahala - ya halatta ta haɗe sallar Azahar tare da La'asar, da sallar Magariba tare da Isha'i; don ya zama aiki ɗaya za ta yi ga salloli biyu: Sallar Azahar, da La'asar.
Wani guda ɗayan kuma sabo da salloli guda biyu: Sallar Magariba, da Isha'i. da kuma guda ɗaya sabo da sallar Asuba, maimakon ta yi haka sau biyar, za ta yi ne sau uku.
Zan sake maimaitawa a karo na biyu: Idan ta tashi yin tsarki za ta wanke farjinta, ta kuma toshe shi da tsumma, ko makamancinsa don abinda zai futo ya sauƙaƙa, sannan ta yi alwala, ta yi sallar Azahar huɗu, La'asar huɗu, Magariba uku, Isha'i huɗu, Asuba biyu, ai: ba za ta yi ƙasaru ba, kamar yadda wasu gama-gari su ke zato,
Sai dai ya halatta ta haɗe tsakanin salloli biyu Azahar da La'asar, da kuma tsakanin sallar Magariba da Isha'i, Azahar da La'asar ko dai jinkirtawa ko kuma gaggautowa, haka nan Magariba tare da Isha'i ko dai gaggaotowa ko jinkirtawa, idan tana son ta yi nafila da wannan alwalar, to, babu laifi a kanta.
ﺟ33: مثل هذه المرأة التي أصابها نزيف الدم حكمها: أن تترك الصلاة والصوم مدة عادتها السابقة قبل هذا الحدث الذي أصابها، فإذا كان من عادتها أن الحيض يأتيها من أول كلّ شهرٍ لمدة ستة أيامٍ مثلًا، فإنها تجلس من أول كلّ شهرٍ مدة ستة أيامٍ لا تصلّي ولا تصوم، فإذا انقضت اغتسلت وصلت وصامت.
وكيفية الصلاة لهذه وأمثالها: أنّها تغسل فرجها غسلًا تامًّا، وتعصبه، وتتوضأ، وتفعل ذلك بعد دخول وقت صلاة الفريضة، وكذلك تفعله إذا أرادت أن تتنفل في غير أوقات فرائض.
وفي هذه الحال -ومن أجل المشقة عليها- يجوز لها أن تجمع صلاة الظّهر مع العصر، وصلاة المغرب مع العشاء؛ حتى يكون عملها هذا واحدًا للصلاتين: صلاة الظّهر، والعصر.
وواحدًا للصلاتين: صلاة المغرب، والعشاء، وواحدًا لصلاة الفجر، بدلًا من أن تعمل ذلك خمس مراتٍ تعمله ثلاث مراتٍ.
وأعيده مرةً ثانيةً، فأقول: عندما تريد الطهارة تغسل فرجها، وتعصبه بخرقةٍ أو شبهها حتى يخف الخارج، ثم تتوضأ، وتصلّي الظّهر أربعًا، والعصر أربعًا، والمغرب ثلاثًا، والعشاء أربعًا، والفجر ركعتين، أي: أنها لا تقصر، كما يتوهمه بعض العامة،
ولكن يجوز لها أن تجمع بين صلاتي الظّهر والعصر، وبين صلاتي المغرب والعشاء، الظّهر مع العصر إمّا تأخيرًا أو تقديمًا، وكذلك المغرب مع العشاء إما تقديمًا أو تأخيرًا، وإذا أرادت أن تتنفل بهذا الوضوء فلا حرج عليها.