Hailata ta wata-wata ta zo min, ina cikin sallah, me zan yi? Shin zan rama sallar dangane da lokacin hailar?
السؤال
TAMBAYA TA 1:
Hailata ta wata-wata ta zo min, ina cikin sallah, me zan yi? Shin zan rama sallar dangane da lokacin hailar?
س32: دخلت عليّ العادة الشهرية أثناء الصلاة، ماذا أفعل؟ وهل أقضي الصلاة عن مدة الحيض؟
الجواب
AMSA TA 1:
Idan haila ta faru, bayan shigar lokacin sallah - kamar ta yi haila bayan zawali (karkatar rana daga tsakiyar sama) da rabin awa misali - to, bayan ta yi tsarkin hailar za ta rama wannan sallar da lokacinta ya shiga alhali tana da tsarki;
Sabo da fadinSa - maɗaukakin sarki -: {Lallai Sallah ta kasance farilla ce mai lokaci a kan muminai} [Al-Nisa'i: 103].
Ba za ta rama sallah game da lokacin hailar ba; sabo da faɗinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin hadisin nan mai tsawo:
"Shin idan tana haila ba ta yin sallah da azumi ba?",
Malamai sun yi Ijma'i a kan cewa ba za ta rama sallar da ta tsere mata ba a lokacin haila.
Amma idan ta sami tsarki, kuma ya kasance abin da ya yi saura na lokaci gwargwadon raka'a ɗaya ne, ko fiye da haka, to, haƙiƙa za ta yi sallar wannan lokacin da ta sami tsarki a cikinsa; sabo da fadinsa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -:
"Wanda ya riski raka'a kafin rana ta faɗi, to, haƙiƙa ya riski la'asar",
Idan ta samu tsarki a lokacin La'asar, ko kafin ɓullowar rana, kuma ya kasance abin da ya rage a faɗuwar rana ko hudowarta gwargwadon raka'a ɗaya ne, to, za ta yi sallar La'asar a mas'ala ta farko, [za ta yi] Asuba a mas'ala ta biyu.
ﺟ32: إذا حدث الحيض بعد دخول وقت الصلاة -كأن حاضت بعد الزوال بنصف ساعةٍ مثلًا- فإنها بعد أن تطهر من الحيض تقضي هذه الصلاة التي دخل وقتها وهي طاهرٌ؛ لقوله تعالى:
﴿...إِنَّ ٱلصَّلَوٰةَ كَانَتۡ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ كِتَٰبٗا مَّوۡقُوتٗا﴾
[النساء:103].
ولا تقضي الصلاة عن وقت الحيض؛ لقوله ﷺ في الحديث الطويل:
«أَلَيْسَتْ إِذَا حَاضَتْ لَمْ تُصَلِّ، وَلَمْ تَصُمْ؟» [1]،
وأجمع أهل العلم أنها لا تقضي الصلاة التي فاتتها أثناء مدة الحيض.
[12] تقدم تخريجه.
أما إذا طهرت، وكان باقيًا من الوقت مقدار ركعةٍ فأكثر، فإنها تصلّي ذلك الوقت الذي طهرت فيه؛ لقوله ﷺ:
«مَنْ أَدْرَكَ رَكْعَةً مِنَ الْعَصْرِ قَبْلَ أَنْ تَغْرُبَ الشَّمْسُ، فَقَدْ أَدْرَكَ الْعَصْرَ» [2]،
فإذا طهرت وقت العصر، أو قبل طلوع الشمس، وكان باقيًا على غروب الشمس أو طلوعها مقدار ركعةٍ، فإنها تصلّي العصر في المسألة الأولى، والفجر في المسألة الثانية.
[13] تقدم تخريجه.